Chapter 9
by @pinkyjay
Bismillahi Rahamanin Raheem 💫
🌷 RIYANN 🌷
Free page
PAGE 12---13🦋
_______Zainba ta zuba musu abinci tuwun shinkafa da miyar taushe ta ji naman kai da tantakwashi, da zoɓo kaɗan Riyann ta ce abincin saboda mugun kallon da Naufal ke yi ma ta duk sai ta ji ta takura, Ummie ce ta kula da haka, amma batace komai, saboda Daddy ya kirata ya sanar da ita komai,
_____________________da ma ta san dole hakan sai ta faru ko fiye da haka wayar Naufal ce ta yi ringing ya na duba ya ga sunan abokinsa Suraj É—agawa ya yi "Hi friend how far.?" "Fine ya akayi ne.?" Naufal ya faÉ—a saboda ya san Suraj bazai kirasa abanza ba, "Raihan ne ya ce min kana gari shine na ce bara na kira ka na ji zaka shigo ne.?"
"Eh zan shigo kana ina ne.?" "Ina school ne." "Okey sai na shigo." Ya datse kiran, kana ya ta shi ya nufe Bedroom ɗin sa Daddy ne ya dakatar da shi ya na cewa"Naufal zo nan ai ban gama magana da kai ba." Saukowa ya yi da ga saman bene da fara hawa, ya dawo ya zauna, gyran murya Daddy ya yi kana ya ce "Da ga yau kabar ɓangaren nan wancen ɓangare zaka koma da nayi saboda Yayana ya dawo ya zauna,
amma ya ƙi saboda yanzu kai zaka koma can kai da matarka kafin a kammala aikin gidanka." "To Daddy." Kawai ya ce kana ya wuce bedroom ɗinsa, ya yi wanka ya shirya cikin ƙananan kaya, blue ɗin wando fa farar riga mai layin blue da ga sama, sosai kalar ta ƙara fito kyan sa, taje sumar kansa ya yi da tasha mayukan gyara,
takalma ya saka sawu ciki kana ya É—auki key É—in motarsa dirowa ya janyo ya É—auki kuÉ—i ya saka aljihu kana ya fito, bai samu kowa ba a parlon duk sun haura sama, saboda haka ya fita abinsa sai BUK harabar makarantar ya tsaya kana ya kira Suraj, sai ga shi "Aboki gani ba ai na ga shigowarka."
"Okey." Kawai ya ce kana suka shiga ciki Umaima, ce da Meerat zaune gefe su na duba wani abu a waya kamar ance ma Meerat É—ago idanunta ya sauka kan Naufal, baki da hanci ta saki ta na kallonsa,
Umaima ce ta kai duban ta ga Meerat ganin hankalinta baya jikinta ne ya sa ta zungure ta, ta dawo natsuwarta "Meerat wai me ki ke kallo haka da ya ja hankalinki.?"
Da hannu kawai ta nuna na ma Umaima Naufal, samun zaune ta yi saboda har waje Abbanta ya na fita da su amma bata taɓa ganin hamsond guy irin Naufal ba,
Meerat ganin Umaima ta fita shiga ruÉ—ani ya sa ta ce "Besty wannan nau ne saboda haka karki sama ranki samunsa." Kallon Meerat ta yi rin ba ki da hankali kafin ta mai da kanta ga wayarta da ke ringin,
É—aukar kiran ta yi ta re da shi ta ta kama hanyar barin wurin, bayan ta gama amsa wayar ne ta dawo ta kalli Meerat ta ce "Ni zan tafi gida sai mun haÉ—u gobe bye."
"To Bestyna bye." Saboda ba ƙaramin daɗi ta ji ba da tafiyar Umaima, saboda tasan indai ta na wurin tabbas ko da ta samu kan Naufal da ya ga Umaima, babu abinda zaiyi da ita,
saboda ta san tafi ta komai ga kyau uwa uba kuma Babanta mai kuɗi ne ita kuma ba ƴar kowa bace, amma ta na da farin jinin samari da wannan ƙarfin gauwa ta kama hanyar,
kafteriya da ta ga su Naufal sun shiga, ta na shiga ta hango su zauna su na hira sai murmushi Naufal ke sa ki wanda ya ƙara ma kyakkyawar fice ɗin sa kyau,
ɗan nesa da su ta zauna ta sa a'kawo ma ta lemo, yadda ta yi maganar cikin wata murya, ya sa Naufal da Suraj ɗagowa su na kallonta, cikin gilas ɗin da ya saka ma face ɗin sa ya ƙare ma ta kallo,
fara ce dogowa kyakkyawa amma ba sosai ba ta na da manyan idanu masu jan hankalin Namiji sai ta na da cikar gashin gira, da cikar ƙirji ma sha Allah, kamar su yi magana,
mai da kallonsa ya yi ga Suraj ya na sun ƙarin bayani akanta saboda ya ga abinda ya fi ƙauna ajikin mace Naufal na son mace mai cikar ƙirji,
"Aboki wacce ita.?" "Sunanta Meerat Aliyu Rimi, ya akayi ne.?" "Ba komai ka samo min Number ta." "Okay an gama." Kana suka ta shi suka fita, saboda gidansu Raihan ya ke son zuwa,
Umaima kuwa ta na fita ta samu gefin hanya ta yi fakin kana ta buÉ—e mota ta fita ta na jiran fitowar Naufal ta ce ya sauke ta gida motarta ta lalace,
ta jima wurin kusan mintuna talatin, kana ta hango fitowarsa, nan da nan ta mai da fice É—in ta kalar tausayi kamar ta yi kuka, haka Nuafal ya wuce ta da gudu saboda ba ya tuki a hankali,
har ya yi nisa ya dawo da baya saboda hango number motar Raihan, ga kuma mace tsaye a wurin, wata ajiyar zuciya ta saki kana ta ƙara fata fuska, ahankali ya sauke gilashin motar,
ya na dubin ta inda zai ga Raihan amma bai gansa ba, kana cikin muryarsa mai daÉ—i ya ce "Hi." Ahankali ta É—ago kanta ta ce "Assalamu alaikum."
Murmushi ne ya suɓuce mai kana ya ce "Wa'alaku salam Please ina mai motar nan.?" Ɗan fari ta yi da idanu alamar bata gane ba, kana ya ce "Raihan nike magana akai."
Rausayar da kai ta yi kana ta ce "Ayya wai Ya Raihan ka ke ne ma.?" "Yes." "Sorry ya na gida na fito da motarsa ne saboda tawa ta É—an samu matsala."
"Okay me kikeyi anan.?" "Am am mai ne ya ƙara narasa yadda zan yi." "Okay muje na sauke ki." "Thanks." Bai koma kallonta ba, kana ta zagayo ta zauna gaban motar ya ja suka nufe unguwar Sharaɗa,
mamaki ne ya cika ta ganin sun iso bakin get ɗin gidansu, sai danna hon ya ke, Baba mai gadi ne ya leƙo ganin Naufal ne da sauri ya buɗe get ya shigo ya akayi ya san gidansu,
fakin ya yi kana ya fito ya nufi hanyar shiga cikin babban parloun gidan ita dai ta bayansa, kana ya murɗa ƙofar ya shiga da sallama, Mommyn Raihan ce a parloun, ta kallon Arewa24 ,
jin murayar wanda ya yi sallamar ne ya sa ta É—ago cikin sakin fuska ta amsa sallamar ta na faÉ—in "Lale marhaban Naufal ne agidan namu saukar yaushe.?"
So sa kai ya yi kana ya ce " Mommy an wuni lafiya ya gida.?" "Lafiya lau ya su Hajiya Ummie.?" "Alhmdllah." " Ma sha Allah." Dai-dai nan Umaima ta shigo ta "wash Allah Mommy na gaji." ta faÉ—a jikinta, ture ta Mommy ta kana ta ce ,
"Umaima ba ki Abokin Yayanki ba ko gaisuwa babu.?" Kallonsa ta yi kana ta ce "An wuni lafiya.?" Bai kula ta ba sai ce ma Mommy ya yi Raihan na ciki ta ce mai Eh ya nufe É—akin,
ita kuma ta raka shi da idanu, kwance ya tarar da Raihan, ya naÉ—a mai duka ga baya, ya zubara, ya na ya neman kai ma Naufal duka, su na dariya, "Naufal ai nazata Amarya ba zata bari ka fito ba."
"To fa wace amarya kuma.?" saboda sam ya manta da Riyann, dariya Raihan ya yi kana ya ce "Riyann nike nufi." "Kai wane munafuki ya faÉ—a ma wannan magana.?"
"Ba wani munafuki sai gaskiya, Naufal angon Riyann mai lokaci." Ya ƙarshe maganar ya na dariya saboda ya ƙular da Naufal sosai, kuma bazai faɗa mai inda ya ji zancen ba,
"Ka ga Malam ka isheni wallahi zan yi tafiyata, munafurcin banza kawai." Ya miƙe zai bar wurin Raihan ya riƙo sa "Haba My friend me ya yi zafi.?" "Ka ga ka faɗa min wane munafuki ya faɗa ma wannan zance.?"
"To gida naje neman ka,Daddy ya ce min ga matarka, ɗiyar Baffa Abdullahi, da ya rasu, wallahi friend zaka mo re mata gaskiya yarinyar ta haɗu ba ƙarya, ban taɓa tunanin za'a samu mace mai kyau irinta a Nigeria ma sha......"Ka ga Malam ka rufe min bakinka."
Naufal ya faÉ—a cikin fushi "kwantar da murayar Raihan ya yi ya na lallashin abokinsa, kana suka shiga hira sosai, Umaima ce ta shigo É—akin da sallama,
ta je musu tiren da tashigo da shi, kana ta ce "Ya Raihan ga key ɗin motar ka." Karɓa ya yi kana ya ce "Allah ya sa ba ki ɗaukar min zugar ƙawayenki a mota ba.?"
"No Ya Raihan ban ɗauka ba yanzu ma na saka Sambo direba ya ɗauko ta saboda tsayawa ta yi a hanya." "Wallahi Umaima ba ki jin magana ya akayi motar ta tsaya, idan ba ɓarna ki ka yi min ba mota ko sati batayi ba."
Cikin shagwaɓa ta ce"Am mai ne ya ƙare fa, wannan abokin naka ma ya taho da ni gida." Ta na yarfe hannu kamar wacce za'a daka, kallon Naufal ya yi don ya tabbatar ya san halin Umaima da ƙarya wani lokaci,
ganin bai yi magana ba ya sa Umaima da da kafaÉ—arsa ta ce "Ya Naufal ba ta re Mika so ba.?" ÆŠaga kai ya yi alamar Eh, kana Raihan ya ce,
"To naji Allah ya soki wace ba mutane wuri." Murguɗa mai baki ta yi kana ta ce "Ai ba wurin ka nazo ba Yayana na kawo ma abin taɓawa."
Buɗe filat ɗin ta yi dan bun naman kaza ne da zoɓo, kana ta ce "Yaya Naufal gashi aci lafiya, karka samma Ya Raihan." Ta fita da guda saboda tasan dukanta zaiyi idan ya sauko kan gadon, da idanu Naufal ya raka ta saboda yadda ta ke shagwaɓar ba ƙaramin burgesa ta yi, ga shi ko ina na jikinta rawa ya ke,
To fa ko dai Naufal ya kamu ne to ya zaiyi da Riyann? Muje zuwa dai don jin yadda zata kasance