RIYANN

Chapter 10

by @pinkyjay

RIYANN 🌷 
Free page 

PAGE---14---15🦋



Raihan ne ya yi gyaran murya kana ya ce "Naufal akwai maganar da nikeso muyi." "To ina jinki." Bai da mu ba yadda ya amsa mai, ya ce "Da ma munjima ni da Zainab muna soyayya, to gaskiya ne aurenta nikeson yi saboda Daddy ya matsa min na fitar da mata, ko ya haɗa ni da wannan sha-shar mai zubin fulawa." 


"Wacece me zubin fulawa.?" Naufal ya tambaye shi, "Umaima nike nufi da ta fita yanzu." "Wai da ma ba ƙanwarka bace!.?" "Sosai ko ɗiyar ƙanen Daddy ce da ke ƙauye ya ɗauko ya na riƙo har ya sa makaranta." "Ikon Allah shi ya sa na ga baku kama da juna sosai, kafi kama da Ya Haydar." 

"Ni ba wannan ba yanzu ya zanyi inaso kayi min iso wurin Daddy." Shiru Naufal ya yi ya na tunani gaskiya Raihan ya na halin kirki sam ba halinsu ɗaya tun su na yara be taɓa jin Raihan ya ce ga wacce ya ke so ba, hasali ma mata basu gabansa, ta re suka je London karatu, amma be sauya halinsa ba,


tabbas ƙanwarsa ta samu miji na gari, kallon Raihan ya yi kana ya ce "Shikenan gobe kazo da safe kafin ta fita." Cikin farin ciki ya rungume Naufal, ya na godiya, jin jina kai ya yi tabbas ba ƙaramin so ya ke ma Zainab ba, sun jima su na fira kafin ya koma gida,


sai tunanin Umaima ya ke gaskiya ta na da dirin macen da ya ke son aure, ko da ya isa gida, bai tarar da kowa Atika mai aiki ta tambaya ina su Ummie suka je nan ta ke faɗa mai Daddy ya je GRA ne ya duba an kammala aikin gidansa to shine su Ummie da sauran ma'aikata suka je gyaran gidan, 


motarsa ya koma ya nufe GRA wani makeken get ya danna hon get Man ya zo ya buɗe mai, Wow ma sha wajen gidan ya haɗu sosai an ƙawata shi fitilo da fulawoyi masu kyau , ga wurin ajiye motoci, sai ƙofar shiga parlon gidan guda biyu ce saboda gidan ɓangare biyu ne cikins ya shiga


 har masu aiki sun kammala gyara part ɗin har kayansa an kwashe, ciki ya shiga babban parlou ya ji manyan kujeru na alfarma maroon color da labulayen farare da ratsin maroon ciki sai ƙaton Tv da sauran kayan mo re rauwa, sai ka hau saman bene nan ɗakunan bacci suke


3bedroom ne ko wane ya na ɗauke da parlo da kitchen sai wurin cin abinci, ya sha gyara sosai amma ɗakin Riyann ya fi na Naufal haɗuwa kayan parlonta da bedroom duk Pink color ne fari, sosai ɗakin ya yi kyau sai Naufal na shi blue da fari, ɗayan ɗakin kuma kayan ciki brown color ne da fari, nan ya sa me su Ummie saboda Daddy ya fita, 


gaida Ummie ya yi kana Zainab da Riyann suka gai da shi can ciki ya amsa, kana ya ce "Ummie ina Daddy ya tafi.?" "Nima bansaniba amma ya ce min mu haɗu gida kawai yanzu da ankawo kayan kitchen ɗin Riyann zamu wuce gida." "Okey ni zan fita." "Adawo lafiya."
Ya fita sai ga motar Company da Daddy ya siya ma Riyann kayan ɗaki sun kawo kayan kitchen, 


get Man ya taimaka musu suka jira komai yadda ya kamata, kayan da Daddy ya yi ma Riyann sai ma sha Allah kamar ɗayar shugaban ƙasa, sai ƙarfe takwas na dare suka koma gida, sai nan da sati biyu Riyann zata ta re, washegari da safe bayan kammala cin abinci, 

Naufal ke faɗa ma Daddy yadda sukayi da Raihan sosai ya ji daɗi ya san Raihan sosai yaron kirki, ƙarfe goma ya zo gidan ya samu tarba mai kyau, nan Daddy ya ce zai kira Mahaifinsa, suyi magana a tsaida rana saboda Ingila zai wuce da matarsa, can ya samu aiki,


bayan ya fito wurin Daddy ɗakin Naufal ya shiga suka ɗan taɓa hira kafin Naufal ya ce "Raihan number sisterka zaka bani." "Me zakayi da ita Naufal.?" "Babu ruwanka idan zaka bani ka bani." "To bazan bayar ba." Nan suka rinƙa rikici Naufal da zuciya ya fita ya bar Raihan nan, 

shima fita ya yi nan ya haɗu da su Zainab zasu fita, Riyann ce ta "Ina kwana?" "Lafiya lau Amarya ya gida." Ya tambaye ta cikin kulawa, "Alhmdllah." Kawai ta ce ta yi gaba abinta ta basu wuri kallon Zainab ya yi kana ya ce "Amaryar jibi antashi lafiya na ga yau bazan samu gaisuwa ba." 


____Dariya ta yi kana ta ce "Sorry barka da safiya." "Barka." "Kaga Riyann ko itace na tura ma hoton ta jiya." "Eh na gane ta ba laifi yarinyar na da hankali da natsowa, gaskiya Naufal ya yi dacen mata." "Haka ne kam Allah ya sa Ya Naufal ya so ta ya riƙeta tsakani da Allah wallahi tausayinta nikeji sosai, ba Uwa ba Uba, bata da kowa sai mu, kasan halin Ya Naufal indai baya Sonta ya na iya cutar da ita." Ta ƙarashe maganar kamar zata yi kuka,

jin jina kai ya yi tabbas maganarta abin duwaba ce amma ta yu ya sauya hali, "In Sha Allah babu abinda zai faru sai alkhairi." "Allah ya sa." Ya ce "Amin." Kana ya suka wace ya shiga motarsa itakuma suka shiga tasu direba ya ja su zuwa kasuwa,


______Naufal na fita BUK ya nufa wurin Suraj amma bai gansa ba ya kira wayarsa wata mace ta ɗauka, takaici ne ya cika sa ya fito zai shiga motarsa sai ga Umaima ta ce "Ya Naufal barka ." Juyowa ya yi ganin wacce ya ke muradi a zuciyarsa, "Yauwa barka." "Wa kake nima ne.?"


____"Wani Abokina amma baya nan." "Okey to." "Ina za ki je." Gida zan koma na gama abinda zanyi." "Okey muje na sauke ki." "Na gode amma da kabarshi Direba zaizo ɗaukata." Ɓata fuska ya yi kana ya ce "To shikenan tun da siyar dake zanyi." Ya shige mota, zai ta da, "Sorry zan shiga." Buɗe ma ta gaban motar ya yi ta shiga,


____ kana ya ja suka fita duk abinda ya faru akan idanun Meerat , wani murmushin mugunta ta sa ki kana ta soma magana ita ka ɗai "Wallahi Umaima sai ke raina kanki tun da ki ka yi min haka, saikeyi nadama akan abinda ki ka aikata min, sai na sa ke koma ke da banza duk ɗaya sai na rabaki da wannan guy ɗin." 

Rashida ce ta dafa Meerat, ta ce "Ai dama ke ki ka yi sake wallahi karki daga ma ta ko ta akaifar susa, ai wannan cin amanar ta yi yawa wallahi." Kallon Rashida ta yi kana ta ce "Ai bazan bi ta kanta ba yanzu sai anyi auren lokacina zai fara."

Naufal kowa wani babban shago ya je ya yi ma ta siyayya sosai kana ya sauketa gida ya karɓe number ta, Raihan na zaune harabar gidan ya na aiki da laptop ɗinsa, mamaki ne ya cika shi amma sai ya sha re kamar bai gansu ba, shima Naufal haka, ya ja motarsa ya fita,


_____wasa-wasa Soyayya mai ƙarfi ta shiga tsakanin Umaima da Naufal, har su na zancen aure yau ta kama saura sati ɗaya Riyann ta ta re, gashi Zainab na koya ma ta karatun boko ta na ganewa sosai saboda ta yi piramare a ƙauyensu, Daddy na zaune wurin hutawarsa, Naufal ya zo ya gaida sa kana ya sauke kansa ƙasa,

ya na son yin magana amma ya kasa Addu'a ne ya ce" Son kamar da magana a bakinka.?" "Eh Daddy da ma tun kafin in tafi London karatu na samu wacce nike so mu na soyayya, bayan nadawo ne mukaje wurin su Baffa, shine ka ɗaura min aure da Riyann." 

"To yanzu me ka keso ayi.?" "Am Em Daddy aurenta nike son yi Daddy ka taimaka min kabari na aure zaɓina." "Yanzu Naufal miye illar Mamana da ko tarewa batayi ba za ka ɓollo da zancen aure, zan duba maganar bazan tauye ma hakkinka ba amma kasani wallahi! Wallahi Muhammad ka kuskura ka cutar da Mamana kai da matarka sai na yi ma abinda ko kare ba'ayi ma ba."


Cikin farin ciki ya ce "Na amince Daddy zan kiyaye." "Da ya fi ma kana ka ba Ummienku miliyan goma zata haɗa ma Mamana kayan lefe." "To Daddy." Kana ya fita Daddy ya kira Ummie ya sanar da ita komai, har ga ranta bata ji daɗin zancen auren ba amma bata nuna ma Daddy sai cewa ta yi Allah ya sanya alkhairi,

cikin satin Daddy da wasu abokansa suka nema ma Naufal auren Umaima, ankai kuɗin aure da sa rana sati biyu masu zuwa, za'ayi bikin ne da na Zainab, saboda ranar Litinin za'a kawo lefe, Ummie kuma ta yi Dubai ta haɗu ma Riyann lefe na gani na faɗa, saiti biyu ta yi mata na akwati, Daddy Kuma ya yi mata saiti ɗaya, Naufal kuwa Daddy ya ce mai Ummie bazata je ko ina ba ya je ya haɗa lefen da kansa saboda cikin Ummie ya shiga watan haihuwa,