Chapter 4
by @zahrabmrs02
Page 4 💬⌨️
Sannu a hankali komai ya fara.
Ni da Jafar ba da gaggawa muka saba ba. Da farko waya ce, sai messages. Simple conversations—how was your day?, are you okay?—amma suna zuwa da wani irin dadi da ban saba ji ba.
A hankali... a hankali...
Sai na fara lura da wani abu mai ban tsoro
Ina dariya idan ina magana da shi.
Ina jin nutsuwa.
Ina jin kaina.
Ban yi niyyar hakan ba. Ban shirya ba. Amma Jafar ya shiga rayuwata ba tare da na lura ba. Ya kasance mai sauraro, kuma bai taba sa ni jin kamar nauyi ba.
Ya ce min idan semester ya ƙare, Insha Allah, zai zo ya gan ni. Wannan kalma "Insha Allah" ta taba zuciyata fiye da yadda zan iya bayyanawa
A bangaren roommates dina , rayuwa tana tafiya kamar kullum. Ni da nusaiba muna yawan zama tare, muna kashe lokaci da hirarraki marasa nauyi—dramas, dariya, da korafe-korafe na rayuwa. Ita ce wadda ke ganin canjin da ke faruwa a kaina, ko da ban faɗa ba.
Precious ma tana nan—mai faɗin gaskiya kai tsaye, ko da zata yi zafi. Ta kan ce:
"Kiyi a hankali. Kada ki manta me kika zo yi
sai Fateeha —mai shiru, ba ta shiga maganar kowa. mutane suna yawan magana a kanta saboda shiru da natsuwarta. Wasu suna cewa raini ne, wasu kuma ba su fahimce ta ba. Nusaiba dai tace min depression ta shiga Sabida ita kadai ke makaranta a Nigeria kaf gidansu .Wanda har yanzu ba Wanda ya San dalilin hakan
Nusaiba maganarta bata ɓoye komai. Duk abin da ta ji, sai ta faɗa.
Zainab adetayo coursemate dina ita kadai ce qawata a kaf department dinmu cos ni ban cika son tarkacen qawaye ba hasalima bani da qawa sai Addata
Lokaci exams ne, hankalina ya cunkushe. A wannan lokacin ne Jafar ya kira ni ya ce min ya shigo Nigeria. Zuciyata ta buga da ƙarfi. Ban san dalilin farin cikin da na ji ba—amma na san ya wuce normal.
Yace zai zo mu gaisa .
Me zai faru ranar da zan gan shi, na ji tsoro da farin ciki a lokaci guda. What if bai zama yadda nake tunani ba? What if na yi expecting da yawa? Wat if ban masa ba ?although yana da pics dina sama da Kala 20 Wanda fateeha ta mun da latest iPhone 6s dinta kuma ba karya nayi kyau dai dai misali
Yadda fateeha taga na rude Akan zuwan jafar sai da ta tanka,farhana take it easy baa wa soyayyah haka calm down kar ki Bari ya gane Kina masa irin wanan son."
Farhana you're just in 100vl first semester har kin fara samari cewar precious.allow her breath mana yan secondary ma soyyyah suke Ballanta ita cewar Nusaiba tana juya ido .Kallo precious ta mun mai Cike da
maanoni be careful farhana (kiyi hankali )tayi ficewarta .gskia farhana ki Dena Bari precious na juya ki ,Kawai dan tasan Hamman ki ,ji yadda take baki warning Kamar wata uwar ki Shegiya bakin ciki tace bata da saurayi ,bance komai ba haka ma fateeha muka bar nusaiba na maganganun ta
Washegari yayan nusaiba yazo wani assignment Zaria, idan ya biyo dubata babes kuzo muje ku gaisa da yaya Aminu ,hijab na zumbula har qasa yayinda fateeha tasa abaya
Mun same su a bakin hostel a jikin wata ash Corolla muka gaisa cikin mutunchi da girmawa ,sai a lokacin na Lura da wani a cikin motar ya juya baya kofa a bude farooq Ka juyo ku gaisa mana inji yaya Aminu
A tare muka gaishe shi ya amsa da nitsuwa ba haniya ba Izza,ya cigaba da abinda yake a waya ,nusaiba sai busybody (iyayi)ake wa Wanda aka kira da farooq ,mukayi sallama zamu koma ciki inda farooq ya tsayar damu ya bamu 5k each gashi ku qara pocket money. mu ka amsa da godiya
Bayan tafiyar su ,nusaiba ta fara bamu labarin farooq , yaya farooq kenan sarkin kyauta shi ko ba yawa sai ya bayar ,yana birge ni matsalar bashi da cash (kudi).
Ba irin samarin da suke da hayaniya bane shi mutum ne mai natsuwa—ba ya son surutu, ba ya son shiga rigimar mutane. Amma duk da haka, yana da ƙwazo sosai.
Faruk student ne kaduna state university , yana final year dinsa. Asalinsa dan taraba state ne Duk da karatu, bai zauna jiran kowa ya dauke nauyin sa ba . Yana aiki a cafén yaya Aminu (yayan nusaiba ), wani computer café da ke cikin kasu —wurin da ake buga documents, online registrations, da duk wani computer-related work.
Nan yake zuwa a Dik lokacin da bashi da lecturers
Computer guru ne sosai. Yana iya aiki da sauri, cikin tsari, ba da kura-kuran da yawa ba. Duk wanda ya je café ɗin, sai ya yaba masa da yadda yake kula da mutane.
Duk da yana aiki inda kura ke tashi, hayaniya da cunkoso—Faruk bai saba da rayuwar banza ba. Tarbiyyarsa ta fito karara. Yana girmama mutane, yana girmama kansa, kuma baya raina kowa.
Ba mai sanya kaya na alfarma ba ne. Ba ya yin showing. Amma aiki? Aiki baya wasa da shi.
Yana zaune tare da mahaifiyar sa garin kaduna ,ta Shara sosai a harkar business da real esate .Bayan rabuwarsu da mahaifin farooq ta dawo Kaduna da zama.Mahaifinsa old money ne yayi kudi dan har ambassador na kasa kasa yayi yanzu yayi retire yana taraba .
Abun haushi yaki sakin jiki yaci arzikin iyayensa a cewar sa Shima zai nema nashi Kamar yadda Suma suka nema ,ya kan ce wa yaya Aminu rufun asiri ne kawai dakuma Katon gida amma baba Tinda yayi retire rayuwar ba Kamar ta da bace ,bazan zauna mu cinye dan abinda ya rage masa ba .kuma kudin mamma bazasu tsole masa ido ya kasa neman nasa ba .
Wai duk ina kika San labarin farooq haka nusaiba?fateeha ta katse ta .
Yaya Aminu ne ke bamu labari ,ta qara da cewa naji kunyar 5k din ya bamu wallahi .
To ina lefin 5k din da ya bamu Kefa kika ce student ne yayi kokari ma .Nima na tofa
Aa farhana bana son harkar raini 5k din me,ni kunya naji ma ya da bamu .
ay Gara shi ya bamu 5k each ,shi yayan naki mai cafe ay be bamu ko sisi ba . fateeha tace tana kokarin hawa bunk dinta
kala nusaiba bata ce ba .
Daga nan aka bar maganar farooq
Washegari
Yau ne mukayi zamu hadu da jafar ,inda nayi suggesting mu hadu a eatery kar Hammana yazo wucewa ya ganmu .ki ara abayar fateeha Kisa gskia, baki da wani Kayan kirki farhana cewar nusaiba ,Yauwa Kisa pink din nan zata miki kyau. na shirya tsaf cikin pink abayar fateeha da black hill and black bag ,fateeha tace to sai kin dawo farhana call me when the needs arise
Na shiga eatery inda na tarar da few faces ,Chan na hango sa a empty sit ,na qarasa cike da nitsuwa da fargaba
Salam ina yini Mine, na fada tare da jan kujera kaina a sunkuye
my farhana dago ki kalle ni mana,kiyi order abinda kike so sai muyi hira Ruwa ma ya isa still ban bari munyi eye contact ba.,no haba my farhana order something jafar ya qara insisting .na bar maka zabi Mine
Tin shigowata sai yanzu na daga kai kalle shi ,ya rabb camera bata kyautawa jafar ba ,skin dinsa Kamar mai skin care very glowy he's black amma baki mai kyau masha Allah kyaunsa daidai misali ,munyi hira ya qara jadada min yadda yake sona.inda yace zai je abuja wajan abbi ya gabbatar da Kansa Kafin ya Koma Cyprus .
Baa nan gizo ke sakar ba,jafar ya rike min hannu ,na kalle shi cike da mamaki……..
Bayan murmushi
XahraB(Mrs)
ZAHRA B MRS