ƘWAI BIYU

Chapter Eleven

by @thehealerspen654

Misalin karfe takwas na safe, Radiya ta gama shiryawa tsaf zata tafi asibiti. Saboda yau morning ne da ita. 


Sai dai babbar matsalar itace: bata da isasshen kudin mota. Kasancewar wata yayi nisa.Kuma kuɗin da suke wajenta ba zasu kai ta, su dawo da ita ba.


A sanyaye ta juya ta kalli Uncle Sani da yake kwance yana bacci kasancewar ana hutun makaranta bai fita ba. Har zata tashe shi, ko zai kai ta, amma sai ta fasa, saboda tun ranar da suka samu matsala dashi, har yanzu bata kula shi, shima baya kula ta. 


Ta zaɓi ta rabu dashi ne, saboda bata son ta sakar masa fuska ya kawo mata wasu dalilai da zai saka ta aikata abinda bai dace ba. Saboda tasan halinsa da iya tsara zance, sannan da kafiya da naci akan abinda ya saka a gaba, musamman akan abinda ya shafi kudi.


Hakan ya saka ta miƙe ta ɗauki jakarta ta fice ta nufi asibitin, zuciyarta cike da tararradin yadda za'a yi ta samu kuɗin motar komawa gida. 


Musamman da ita bata iya roƙon kuɗi a wajen wani ba, ko da rance. Hakan ya saka wunin ranar tayi shi ne, ran ta babu daɗi.


Bayan ta gama aikinta ta fara shirin tafiya gida. Can wata dabara ta faɗo mata. Kasancewar asibitin da take aiki a unguwar Gadon Ƙaya yake, kuma Dr. Saleema a unguwar Sabon Titn Mandawari gidanta yake.


Sai ta yanke shawarar, zata bi ta, ta rage mata hanya saboda ita tana da mota. Saboda Sabon Titi yafi mata kusa da gidansu,  akan Ɗorayi. Kuma tana tabbacin cewar, idan taje gida Abbas  zai bata kuɗin mota.


Hakan kuwa akayi, tabi Dr. Saleema suka tafi. Tayi sa'a kuwa ta kawo ta har junction ɗin Mandawari, daga nan ta sauka da niyyar zata hau wani ya ƙarasa da ita agadasawa. 


Ai kuwa Dr. Saleema tana yin U-turn, Radiya ta miƙe ƙafarta, tai ta tuƙin tsaye, har ta isa gida.


Tana isa ta iske an gama abinci, nan fa ta ware cikinta taci ta ƙoshi suka sha hira da Umma da Anty Ummie. Sannan daga bisani tabi Abbas kasuwa, suka keɓe sukayi hirar zumunci.


Sai dai yanayin da taga Abbas ya birkitata sosai, saboda wata rama da taga yayi abun ya bata tsoro. Da ta tambaye shi, sai yace mata lafiyarsa ƙalau, babu abinda yake damunsa.


Bayan sun kammala hirarsu, ya ɗauko naira dubu biyar ya bata. Ta saka hannu ta karɓa tana murna, sannan daga bisani suka yi sallama dashi ta taho gida ta dauki jakarta, sannan ta nufi gidanta.


Haka Radiya take rayuwarta a sannu a hankali. Sam bata son matsala, bata son damuwa, bata son abinda zai ɗaga mata hankali. Shiyasa take zaune lafiya. 


Amma kuma, ƙaddarar da Ubangiji yake shirya mata a ɓoye, tana ƙoƙarin ta sauya rayuwarta...na har abada.


Misalin karfe biyu na dare. Sauban yana zaune akan sallayarsa, yana roƙon Ubangiji maɗaukakin Sarki da ya kawo masa mafita akan wannan alkawarin da ya daukarwa dan uwansa. Saboda shi kansa ya sani ba mai yiwuwa bane, amma tun da ya saka Ubangiji a farko, ya sani zai warware masa komai.


Yau tsawon wata guda kenan babu wata alama da zata nuna akwai nasara. Sannan gashi Sultan ya titsiye shi, akan ya ɗaukar masa alkawarin cewar: ba zai taɓa yin wani yunƙuri akan lalata auren Radiya ba, domin cikar burinsu.


Haka dole ya haƙura da ƙudirin da yake cikin zuciyarsa, ya rungumi addu'a akan Ubangiji ya sauya musu da mafi alkhairi. Sannan ya bawa ɗan uwansa wadda tafi Radiya, wadda zata share masa hawaye.


A ɓangaren Sultan kuma, yana daurewa ne kawai, amma damuwar sa tafi gaban mai tunani. A kullum addu'a yake yi akan Allah ya cire masa Radiya a cikin zuciyarsa. Amma kullum son ta, da ƙaunar ta ƙara ƙaruwa suke yi.


Duk da ya bijerewa duk wasu abubuwa da zasu iya tuna masa da ita, duk wani file da ya danganci case ɗinta ya saka an goge shi, komai ya tafi kamar ba'a taɓa halittarta ba. Amma sai dai, ya kasa goge ta acikin zuciyarsa.


Lokacin da ya fahimci cewar: a kullum addu'a yake yi, amma abun ƙara yawa yake yi, sai tunaninsa ya sauya, ya fara hasashen ko wannan addu'ar da yake yi ba akan daidai yake yin ta ba?


Saboda kullum al'amarin nasa sake ta'azzara yake yi. Sai ya sauya akalar addu'ar tasa zuwa: Ubangiji ya zaɓa masa mafi alkhairi...game da Radiya.


             •••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••


BAYAN WATA UKU


Tsawon wannan lokacin da zuwan Radiya Abuja, al'amura sun sauya mata matuka, saboda babu isasshiyar jituwa tsakanin ta da mijinta Uncle Sani. 


Duk da ta sakko sosai tana ƙoƙarin yi masa magana, saboda ta gaji da zaman doya da manjar da suke yi. Amma shi a ɓangarensa, sam babu daɗi, saboda ta manta rabon da mu'amalar aure ta haɗa su.


Duk yadda zatayi don ganin ta kyautata masa amma yaƙi sauraron ta. Domin a faɗar sa, ta ƙare masa zagi da cin mutuncin da idan wani ne yayi masa...har abada ba zai taɓa mantawa dashi ba, ballantana matarsa ta sunnah.


Hakan yayi matuƙar jefa ta cikin damuwa. Shi kuma haka yake so, yana sane yake wahalar da ita. Bai fito ya nuna mata matsalarsa akan aikin da taƙi amincewa bane ƙarara.


Saboda ya san halin ta da da wayo da taurin kai. Ya fake da fushin ƙarya domin ya gana mata azaba a fakaice saboda yasan tana matuƙar son sa.


To babban abinda yafi damunta a yanzu shine: albashinta sam baya isar ta, gashi Uncle Sani ya matse hannunsa, ya daina kai ta wajen aiki, sam baya bi ta kanta. Hakan ya saka gabaɗaya albashin ta a kuɗin mota yake tafiya.


Wannan ya saka yawan zuwan ta gida ya ƙaru, har ta kai Abbas ya fara tuhumar ta akan ko akwai wata matsalar?


Amma sai ta fake da cewar: shi take zuwa ta gani saboda ta lura kwana biyu jikinsa ya motsa yana yawan yin rashin lafiya.


Tana cikin wannan yanayin watarana ta dawo daga wajen aiki, sai ta biya ta gidan su. Tana shiga ta iske an dawo da Abbas daga kasuwa,  jikinsa ya tashi yana kwance a tsakar gida, sai gumi yake yi da wani matsanancin haki. 


Da sauri ta ƙarasa in da yake, yana ganin ta ya riƙo hannunta yana so yayi mata magana...amma hakin da yake yi ya hana shi. 


Wani matsanancin kuka ne ya kufce mata. Haka suka taru gabaɗayansu suna kuka,  sannan daga bisani Sadiq ya samo abun hawa aka dangana dashi zuwa asibiti.


Asibitin Malam Aminu Kano suka nufa dashi kai tsaye. Suna isa ta yiwa Dr. Nazir waya. Bayan ya ƙaraso yayi iya bakin ƙoƙarinsa aka bawa Abbas gado, sannan daga bisani aka fara kula dashi.


Sai da aka gudanar da gwaje-gwaje, waɗanda da suka kai tsawon kwana uku, sannan daga bisani aka tabbatar da ainahin abinda yake damun Abbas.


A ranar wata Laraba bayan tattara takardun gwaje-gwajen likitan da yake bakin aiki ya kira Radiya, saboda Dr. Nazir ne ya haɗa su, abokin aikin sa ne. Hakan ya saka a ƴan kwanakin nan suka ɗan saba da Radiya.


Jikinta a sanyaye ta nufi office ɗin likitan tare da yin sallama. Bayan ya amsa yayi mata umarnin da ta zauna a ɗaya daga cikin kujerun da suke office ɗin. A sanyaye ta zauna tare da zuba masa ido. 


Saboda ta lura da yadda ya rufe file ɗin jikinsa a sanyaye. A matsayinta na ma'aikaciyar jinya, ta sani dole akwai matsala babba.


A sanyaye ya ɗago ya kalle ta. Ya lura da yadda yanayinta ya sauya, jikinta yayi sanyi, amma dole ya daure ya kalle ta ya fara magana:


"Na sani ke ma nurse ce, kin san duk wasu abubuwan da suka danganci lafiya. To bana buƙatar nayi miki nuƙu-nuƙu ko na ɓoye miki gaskiya."


Jinjina kanta tayi. Jikinta ya fara tsuma, tana jiran taji meye asalin abinda yake damun yayanta Abbas.


"Wasu daga cikin jijiyoyin zuciyar yayanki Abbas sun toshe. A duk lokacin da zuciyarsa ta buga, maimakon jinin yayi gaba don bawa sabo hanyar fita...to sai ya koma baya, wanda a likitance ake kiran wannan larurar da Severe Nitral Valve Regurgitation.


Wannan komawar da jinin yake yi baya, yana tilastawa zuciyarsa yin aiki fiye da kima, wanda hakan zai jawo ta fara kumbura, ko girmanta ya ƙaru, sannan daga ƙarshe tayi rauni."


Sunkuyar da kanta tayi ƙasa, saboda tsananin bugun da ƙirjinta yake yi, ga wasu hawaye da suka fara taruwa a idonta. Sannan a sanyaye ta ɗago tace masa:


"To yanzu meye mafita?" 


Doguwar ajiyar zuciya yayi, sannan ya sake kallon ta cike da tausayawa yace:


Dogon numfashi yaja. Sannan yace:


"Babbar matsalar itace: ciwon ya daɗe yana cin jikinsa a hankali, ko da an bashi magunguna a yanzu ba zasu warkar dashi ba, zasu rage masa raɗaɗi ne na ƴan lokuta. 


Saboda haka babban abinda yafi da cewa dashi shine  ayi masa buɗaɗɗiyar tiyata. Itama kuma sai anyi cikin gaggawa, matuƙar ana so ya rayu."


A hankali ta share hawayen da yake fuskarta, sannan ta kalle shi ta ce:


"Daga nan zuwa yaushe yakamata ayi masa aikin?"


Jinjina kansa yayi. Sannan ya sake kallonta yace:


"Radiya gaskiya bazan ɓoye miki ba, duk yadda za'a yi kar a wuce wata uku daga yanzu ba'a yi masa wannan aikin ba. Don a hakan ma idan ya kai wata biyu a haka, to komai zai iya faruwa. 


Sannan ina baku shawarar idan da hali ku fita dashi ƙasar waje kawai, kamar India ko Egypt, abun zai fi zuwa da sauri. Saboda anan Nigeria za'a iya jan lokaci sosai. 


Can kuma za'a yi cikin sauri, kuma kusan kuɗi daya ne da nan. Don ina jin a India baya wuce dollar dubu takwas zuwa dollar dubu goma."


Sake jinjina kanta tayi, sannan tayi masa godiya ta fice daga office ɗin.


Maimakon ta koma wajen da su Umma suke a zaune, sai ta ɗauki hanya ta tafi can wani waje, in da babu kowa ta zauna ta kifa kanta ta fara gurzar kuka mai tsuma zuciya.


Hankalinta bai daɗa tashi ba, sai da ta duba adadin kuɗin aikin a naira. Banda kuɗin visa da sauran abubuwan da za'a kashe, a ƙalla zasu tanadi naira-million-goma-sha-biyar.


Sai sannan wautar da tayi ta faɗo mata. Da ta biyewa Uncle Sani ya cuceta, ya raba ta da komai nata, sai gidan da suke ciki kawai, sai kuma zoben gold ɗin da yake hannunta, wanda kimarsa kwata-kwata bata kai naira-million-ɗaya-ba.


Ta tabbata da kadarorinta suna nan, gida ɗaya zata iya sakawa a kasuwa ta siyar ta nemawa yayanta magani. Amma sai dai kash! dana sani ƙeya ce, a baya take.


Tana cikin wannan yanayin kamar daga sama taji an dafa ta. Tana ɗagowa suka yi ido huɗu da Sadiq. Waje ya nema ya zauna kusa da ita, ya zuba mata ido cike da damuwa.


Saboda shima kansa jikinsa ya bashi akwai babbar matsalar da take damun Abbas. Ballantana kuma yadda yaga duk dauriyar Radiya ta keɓe kanta ita kaɗai tana kuka.


Ganinsa ya saka ta sake fashewa da kuka. Sannan ta kalle shi tace:


"Zamu rasa yaya...ciwon zuciya mai tsanani ya kama shi...bana jin zai haura wata uku..."


Shima kukan ne ya kufce masa. Sai da suka yi mai isarsu, sannan tayi zumbur ta miƙe tsaye, shima ya miƙe yana kallonta. Sannan ta kalle shi tace:


"Bazan iya zuba ido ina gani Yaya ya mutu ba...yaya Sadiq bazan iya ba...zanyi iya yi na...amma don Allah karka faɗa musu ainahin abinda yake damunsa  kaji."


Jinjina kansa yayi, sannan ya kalle ta yace:


"Nawa ne kuɗin aikin?"


"A ƙalla mu tanadi naira-million-goma-sha-biyar." Ta faɗa tana jinjina yawan kudin.


Cikin sauri ya kalle ta yace:


"Radiya zan siyar da gidana da nake ginawa, kema ki siyar da wani abun, sai mu haɗa mu biya masa kawai."


Jinjina kan ta tayi alamar gamsuwa duk da har cikin zuciyar ta ta sani ba ta da wani abu a yanzu da zata daga ta siyar in dai ba gidan da suke ciki ba. Kuma tabbatar babu wanda yasan da hakan.


To idan ta ɗaga gidan da suke ciki ta siyar....wanne bayanin zata yiwa ƴan uwanta idan sun fahimta?


Da wannan zullumin ta nufi gida ba tare da ta biya in da su Umma suke ba. A sanyaye ta shiga ɗaki ta kifa kanta da gwiwa ta buɗe sabon shafin kuka.


Bayan Uncle Sani ya dawo ya tarar da ita a wannan halin ya tausaya mata a zahiri, musamman da ta bashi labarin komai. 


Amma a can ƙasan zuciyarsa, sai ya tsinci kansa da wani farin ciki, saboda yana tunanin Allah ya kawo wata damar da zata saka Radiya tayi abinda yake jira.


Bayan ta idar da sallar isha'i ta juyo ta kalle shi tace:


"Ina takardun gidan nan?"


Cikin sauri ya kalle ta yace:


"Me zakiyi dasu?"


Ɗago kanta tayi. Fuskar ta a ɗaure babu alamar wasa tace:


"Ina bukatarsu ne. Idan kuma shima gidan ka siyar sai naji."


Da sauri ya miƙe ya nufi cikin wani akwatinsa da yake ajiye mahimman takardu, ya fara ƙoƙarin ɗakko takardun. 


Saboda tun da yaji ta fara wannan zancen, to dab take da fara yi masa tone-tone, shi kuma duk duniya abinda ya tsana yaji kenan.


Bayan ya lalubo su ya miƙo mata. Ta karɓa ta saka a jakarta ta zuwa aiki. Sannan ta cigaba da zama akan daddumar tana lazimi. Babu yadda baiyi da ita ba akan taci abinci taƙi,  haka ta kwana da yunwa.


Washegari da sassafe ta fara shirin tafiya asibiti wajen Abbas. Bayan ta tashi Uncle Sani ta sanar masa da ya samo dillalai da zasu taya wannan gidan saboda siyar dashi zatayi.


Cikin razani Uncle Sani ya kalle ta. Zaiyi magana ta katse shi da cewar:


"Baka buƙatar na sanar da kai matsayin yaya a rayuwata, kasan komai. Saboda haka ko zamu kwana a kwararo sai in da ƙarfina ya ƙare akan samar masa lafiya."


Sannan ta miƙe ta dauki jakarta ta nufi asibitin.


Tana isa ta iske jikin nasa da sauƙi, don ya farka. Ganin hakan ya saka tace da Sadiq yaje gida ya huta zata zauna ta kula dashi.


Haka kuwa akayi, bayan Sadiq ya fita ta ƙare masa kallo. Taga duk ya galabaita, ta ƙarasa kusa dashi ta gaishe shi ya amsa mata sama-sama, sannan ta fara kici/kicin dama masa custard domin ya sha.


Bayan ta kammala damawa ta ƙarasa in da yake ta fara ƙoƙarin bashi a baki, amma ya kawar da kansa gefe.


Cikin sanyayyiyar murya tace:


"Yaya kayi haƙuri ka daure ka sha, zaka ji ƙarfi a jikinka."


Sake ɗaure fuskarsa yayi, yaƙi juyo da kansa, alamar baya son haɗa ido da ita. Ganin hakan ya saka zuciyarta ta fara rawa, take hawaye suka fara zirya a fuskar ta. Cikin muryar kuka ta ci gaba da roƙonsa.


"Jin ya…