Page-61
*FASAHA WRITER'S ASSOCIATION*
(*F.W.A)*©✍️
⭐⭐⭐
Ƙungiya masu aiki cikin salon hikima da fasaha gurin juya tunanin al-umma, kaifin alƙalumansu ya zarta takobi ©✍
___________________________________________________
بسم الله الرحمن الرحيم.
اللهم صلي وسلم على نبينا محمد.
❁ 𝐒𝐀𝐍𝐀𝐃𝐈𝐍 Ƙ𝐀𝐃𝐃𝐀𝐑𝐀𝐓𝐀 ❁
Free book📓
By: _*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_
Page6️⃣1️⃣
_wata ranar Lahadi, ranar da ba zan taɓa mantawa da shi ba, ranar da wani babban al'amari ya faru, abun da ko kaɗan bai taɓa gushewa daga cikin raina ba, abun da ya ke sani jin tsanar kaina a duk lokacin da na tuna shi. Na dawo daga gurin aiki a matuƙar gajiye, ga ɓacin rai da ya yi min yawa sakamakon rasa wani babban haɗaka da na yi a company. Ina zaune na ɗaura hannu a saman kaina, yayin da na ke furzar da isaka mai zafi daga bakina, a wannan lokacin Khairat ta iso gabana bayan ta yi sallama, sannan ta zauna a gefena. Da ƙyar na iya amsa mata sallamar domin ko maganar ba na buƙatar yi yanzu. "Imm... dama ina son yin wata magana da kai" ta faɗi tana sunkuyar da kanta, ba tare da na juyo inda ta ke ba na buɗi baki na ce, "ba yanzu ba!" Ba ta ji daɗin yadda na amsa mata ba, hakan yasa ta yi shiru kamar tana jiran na ɗan lafa kafin ta sake magana, "ba wani abu ba ne dama, wani gefen igiyar wutar ɗakina ya tsinke, shine na ke son ka duba..." ban san lokacin da na juyo ina kallonta cikin ɓacin rai ba na furta, "ba ki ji me na ce ba ne! Me yasa ba ki da tunani?! Na ce ba yanzu ba ba na son magana, amma kin takura min, kin san asarar da na yi a wannan ranar kuwa, za ki yi min wani maganar igiyar wuta? Ko dole sai an gyara yau idan ba haka ba zai ja miki matsala!?" Hawaye ya tarun mata a idonta, wanda ɓacin ran da na ke ciki ya hanani ganinsa, haɗiye ƙwallahn ta yi cikin sanyin murya ta ce, "ka yi haƙuri, ban yi tsammanin haka zai ɓata maka rai ba ne, kawai dai hankalina ya gaza kwanciya akansa ne, shine na ce zan faɗa..." zumbur na miƙe ina kallonta, ɓacin ran da ban samu damar saukewa à wurin aiki ba na fara ƙoƙarin sauke mata, kalamanta ba masu zafi ba ne, amma yanayin da na ke ciki yasa ni jin zafinsu. Wani irin tsawa na daka mata sai da yasa ta razana, ta ɗago tana kallona da mamaki haɗi da fargaba na fara cewa, "Khairat! Ke ba kya gane abun da ake cewa ne?! To ba zan gyara igiyar ba, in kinso ki canza ɗakin kwana ba suna nan da yawa ba? Haba don Allah! Ki daina takura min da yawa mana, ki fita a rayuwata!" Ina yin maganar na nufi ɗakina ina huci, ban san kalmar da na furta ita ce za ta jawo min jarrabawa mafi girma ba. Hawayen da ke cike a idonta ta matse, wasu su ka biyo baya, haƙiƙa kalamaina sun karyar mata da zuciya sosai, a ko da yaushe burinta ta faranta min ko da ba zan yi zamar mata da miji da ita ba, sai dai sam ban yi tunanin wannan ba. Bayan na shiga ɗaki akan gado na zube ina sauke numfashi, ban san ya akayi fushin nan ya fito a gareni ba, ni ban san me ya ke damuna ba ma, domin abun da na yi mata kuma ya tsaya min a rai, "me na yi haka ne? Ya kamata na yi mata haka?" Na tambayi kaina. Ita kuwa Khairat cikin matsanancin damuwa da sanyin jiki ta koma ɗakinta, a kan gadonta ta kwanta tana sauke numfashi, sai kuma kuka ya kufce mata, magan-ganuna su ka shiga yi mata yawo a ƙwaƙwalwa, musamman kalmar 'ki daina takura min mana, ki fice a rayuwata!' Shine babban abun da ya fi tokare mata rai. Ta ji a ranta cewa mafarkin da ta ke da shi akan wata rana zan so ta ƙarya ce, tana ganin Haidar baya sonta kuma ba zai taɓa sonta ba, hasalima tsanarta shine a cikin ransa. Tunani sun yi mata yawa a cikin kanta har ta kasa jin wani ƙara da ya fara tashi kamar tartsatsin wuta. Ba komai ba ne wannan ƙarar kuwa sai wannan igiyar wutar da ta sanar da ni, ƙarfen jikin igiyoyin biyu sun haɗu da juna, ko jiya sai da ta ji ƙararsa kaɗan wanda ya razanata. Abu ya yi ta cigaba Khairat tana cikin ɗaki tunani ya cinyeta. Igiya ya fara fitar da wuta daga baya ya soma kama labule, hayaƙi tun yana fita a hankali har ya fara ƙarfi, guri kam ya gama turnuƙewa da hayaƙi yayin da wuta ke cigaba da mamaye gurare. Sai a sannan hankalin Khairat ya dawo jikinta sakamakon warin hayaƙi da ya tsananta. Hankalinta ya yi matuƙar tashi, ta sauka daga kan gado tana tari idanuwanta sun kasa gane mata komai, ta yi ƙoƙarin ƙwallara ihu amma maƙogoronta ya maƙale. Haka ta fara firfitar da ido tana ta tari, ɗaki kuwa bai sarara ba yana ɗorawa da aikinsa. A wannan lokacin ina cikin ɗaki har na fara barci, amma kwatsam na tashi saboda wani irin bugu da zuciyata ya ke ta faman yi, wanda ban san me dalilin ba. Abubuwan da ya faru su ka dawar min rashin jin daɗi ya ƙaru. "Me yasa zan yi mata kausasan kalamai bayan ba ta da masaniya akan matsalata?" Na aikawa kaina tambayar sai kuma na sauke numfashi haɗi da miƙewa, "ya kamata na je na ba ta haƙuri". A hankali na baro sashina ina nufan na ta, abun mamaki na ga gurin kamar ya ɗan yi duhu, ba duhu na haske ba sai dai wani abu mai kamar hayaƙi da na gani a wurin. Ina cigaba da tafiya sai na fara jin wasu saututtuka ƙanana suna tashi wanda ban gama gane na mené ba. Tun kafin na ƙarasa ɗakin na shiga cikin taashin hankali da fargaba zuciyata ya cigaba da bugawa, saboda hayaƙi da ya yiwa gurin yawa sosai. Da gudu na ƙarasa ɗakin ina zare ido saboda ganin da na yi wani gefen ɗakin Khairat ne ya kama da wuta. Kafin wannan ranar ban taɓa shiga wani tashin hankalin da ya kai sa ba, ta ke jikina ya hau kyarma na fara kiran sunanta, amma shiru ban ji amonta ba ko kaɗan. Cikin rikicewa tsantsa na ke afkawa saƙo-saƙo ina kiran sunanta yayin da hayaƙi da kuma zafin wuta ke ratsa jikina da idanuwa, na rufe baki na da hannu ɗaya ina bincikawa hawayen tashin hankali na tsiyaya sosai a cikin idona. Ban haƙura ba na cigaba da dubata duk da ba gani sosai na ke yi ba, sannan kuma ni kaina zan iya samun illah a cikinsa. Wutar ya yi yawa har yana son mamaye ɗakin gaba ɗaya, har na sadaukar ba zan ganta ba, a karo na farko a rayuwata, ina jin tsoron zan rasa wani ɓangarena, na galabaita da yawa numfashi na sarƙe min, wani ƙarfen tsayar da jaku-kuna ya girgiza ya kusa faɗowa kaina, na yi saurin yin gefe na faɗi kusa da ita. Bugawar zuciyata ya haura tsammani, kiran sunanta na ke yi sosai amma Khairat ba ta motsi. Nan na fara tunanin yadda zan yi cikin rikicewa. Na ɗaga ido ina kallon yadda ɗakin ya mamaye muma kanmu yana gaf da lamushemu, zanin gadon da ke kusa na samu damar ɗauka na lulluɓe Khairat da shi, cikin ikon Allah na fito na sauke Khairat a falo ina jijjigata da ambatan sunanta, amma shiru ba amsa_
Dakatawa Haidar ya yi don hawayen da ya ci ƙarfinsa, yayin da ni kuma kukan na ke yi haiƙan har cikin zuciyata, ji na ke kamar à gabana na ke ganin abubuwan da ya ke ce min. Ya ɗago ya kalleni tare da sake wani murmushin ƙarfin hali yana miƙo min hanki-cif don na goge fiskata. Bayan na amsa na goge shima ya goge na sa nan ya sauke numfashi ya ciga da cewa.
_kuskure ɗaya ya jawo min wannan babban al'amarin, da sauri na fice da ita daga cikin falon zuwa waje don kaita asibiti, sai a sannan na sanarwa masu gadi da su yi maza su san abun yi don kashe gobarar, ni kuma na yi asibiti da ita kamar hankalina baya jikina, don ban iya tuƙi ba sai driver na sa ya tuƙamu. Ko da mu ka isa asibiti aka karɓeta da gaggawa aka shiga da ita emergency. Bayan tsawon lokacin da na ɗauka sai ga likita mai kirki ya iso gareni, a lokacin ƙirjina ya tsananta bugu kamar zai faso waje, ba komai ba ne kuma sai tsoron amsar da ka iya fitowa daga furucinsa, domin idan har wani abu ya sami Khairat ba zan yafewa kaina ba, ni ne SANADIN jefata cikin Wannan halin. Sai da likita ya sauke numfashi sannan ya sanar da ni cewa ta tsira daga hatsari cikin ikon Allah, har ya ƙara min da faɗin in godewa ubangijina domin kuwa shine ya nuna mu'ujizansa akan Khairat, saboda ba zai ɓoye min ba hayaƙi ya taru a cikinta sosai, amma yanzu alhamdulillah. Ban san lokacin da na zube ƙasa ba na ɗaga hannu ina yiwa ubangijina kirari akan ni'imar da ya yi mini ina hawaye. Washe gari bayan ta farka, na isa kusa da ita jajayen idanuna akanta, damuwa ya mamaye min zuciya. Kallona ta ke yi itama ta saki murmushin da yasa na ji komaina ya tsaya, zuciyata ta yi wani irin sanyin da ban saba ji ba, ban taɓa tsayawa na kalli fiska matata da kyau ba kamar ranar, wani yanayin da ya daɗe yana fitowa kaɗan a raina ranar ya fito sosai. Amma bayan duk wannan, abun da na ji ya fito daga bakinta ya razani irin wanda ban taɓa ji ba, cikin sanyin muryarta da ya ƙara lafewa saboda jinya ta ce, "me yasa ka damu à kaina Haidar? Ba kana son in fita à cikin rayuwarka ba? Me yasa ka ceceni?" Sai a lokacin na kuma tunawa da furucin da na yi mata bayan, 'ko dole sai an gyara yau idan ba haka ba zai ja miki matsala!?' Rintse idona na yi bayan kalaman sun faɗa min cikin ƙirji, "na san ba ka taɓa sona ba, na zame maka takura ne kawai a cikin rayuwarka, na gode da ka taimaki numfashina, ina ganin lokaci ya iso da za ka rabu da duk wata matsalarka" cewar Khairat, da sauri na buɗe idanuwana da su ka kuma rinewa ina kallonta, bakina na kyarma na ce, "me ki ke nufi Khairat?" Ta ce, "ka sake ni! Shine abun da zai zame maka salama da natsuwa" na ji kalmar kamar wanda ake shirin feɗewa, da muryar inda-inda na ce, "ssss... saboda me zan sakeki Khairat? Do you know what you're saying?!" Gefe ta yi da kanta a hankali ta ce, "me yasa za ka yi mamakin abun da na ce bayan farin ciki yakamata ka yi? Idan don su Ummee ne ba ka son sakina kada ka damu zan san yadda zan yi na fahimtar da su", faɗin Khairat, kafin na fita à cikin halin da zuciyata ya ke shiga saboda tsabar rawa na kuma jefa mata tambayar, "Khairat ko ba kya sona ne?" "Me amfanin hakan zai min bayan ba ka sona a cikin zuciyarka Haidar?" "Waya ce miki ba na sonki? Wallahi ina sonki kuma ba zan iya rabuwa da ke ba!" Maganar ya fito a bakina ba tare da na shirya masa ba. Da sauri ta juyo da dubanta gareni tana giɗa kai alamar rashin yarda, "wannan abun da ya faru bai kamata ya canza maka tunaninka ba, ni na san ba ka sona"..... Khairat ta ƙi yarda da cewa ina sonta da gaske, tafi ɗauka saboda abun da ya faru ne kawai na ke nuna mata hakan. Bayan an sallemeta nan gida mu ka dawo da ita kafin a gyara wancan gidan duk da cikin sa'a ɗaki ɗaya ne kawai ya samu problem. Amma Ummee ta ce a kawota gida don ta kula da ita har jikin ya warware, har izuwa lokacin dama babu wanda ya san irin zaman da na yi da Khairat à baya. Duk yadda zan yi don in fahimtar da Khairat ina matuƙar sonta na yi, amma ta ƙi yarda, duk da cewa ita tana so na, amma ta kasa gasgata ƙaunata akanta. Na shiga damuwa, takaici da tsanar kaina, me yasa na ƙi ba ta kulawa? Me yasa na ƙi sauraronta? Me yasa na kasa gane darajarta à tare da ni tun baya? A duk lokacin da na tuna da wahalar da ta sha sanadin sakacina, ina matuƙar jin haushi..... Tabbas na jima da fara sonta, amma ban gane ba sai bayan wannan abun ya faru. Na sha zarya, na sha magiya da roƙo amma Khairat ce min ta ke yi kawai in rabu da ita shine mafi alkhairi a zamanmu_
Haidar ya yi shiru yana yin dariya mara sauti, ni dai kallonsa kawai na ke yi ina jinjina irin abun da ya faru da shi. Ganin ya jingina har da lumshe ido ya sani saurin cewa, "yaya Haidar ina fa jinka, ba ka ƙarasa bani labarin ba" ido ɗaya ya buɗe yana murmushi ya ce, "wai barci na ke son na yi sai na ƙarisa.
Giɗa kai na yi na miƙe ina faɗin, "à ah wallahi sai na ƙarasa min so na ke na ji yadda soyayya ya ƙarasa yin walagigi da yaya Haidar" shiru bai amsa min ba ya yi shiru kamar ya yi barcin, ganin bai da niyyar tashi ƙarasa min labarin kamar ma barcin wai ya yi. Kawai na fara girgiza kujerar da ya ke kai ina kiran sunansa, da sauri ya miƙe tsaye ya dunƙule hannuwansa biyu kamar mai shirin dambe yana juyawa bayansa ya ce, "wa ya ke girgiza min duniyar mafarkina ya ke son tada ni haka? Kun san ƙarfin da na ke da shi kuwa?"
Ya kai ƙarshe yana juyowa inda na ke yana kuma juya hannun kaman wani ɗan yoga. Ban san lokacin da dariya ya kufce min ba, yinsa na ke abuna sosai har da kama ciki na koma na zauna akan kujera, shima dariyar ya ke ya zauna kusa da ni muna ta darawa.
Shi ya fara shiru idonsa akaina yana kallon yadda na ke nishaɗi, bai san me yasa ba, amma akwai wani abu na musamman da ya ke ji game da ni. Samu na yi na sarara ina kallonsa na ce, "yaya Haidar ka sani dariyar da ban shirya masa ba wallahi" "hakan na ke so ya kasance a kan fiskarki ako da yaushe" ya faɗi yana murmushi nima na maida masa martani sannan na ce a cigaba da labarin to".
_na shiga cikin ƘADDARAR soyayyar da ko à mafarki ban tsammaci hakan ba, bayan Khairat ta ji sauƙi mu ka koma gidanmu, duk da ce min ta ke yi ba za mu daɗe ba. Na sha wahala gurin fahimtar da Khairat, sai daga baya ta amince ta yarda da cewa ina sonta, "Khairat ki yafe min duk abun da na yi miki don Allah, na yi kuskure a baya, na aikata miki abubuwa da dama, a matsayinki na matata kin kasa samun kulawata, ba na tsayawa na ji damuwarki ko wani matsalarki, don Allah ki yafe min, insha Allah na yi miki alƙawarin baki kulawa da soyayya wanda ba ki samu ba abaya", kalaman da na sanar da ita bayan ta amince da ni. Ta yi farin ciki sannan ta ce, "babu buƙatar ka nemi yafiya a gareni, domin kai mutumin kirki ne, na riga da na daɗe da yafe maka komai, nima ka yafe min azabtar da kai da na yi" tun daga nan mu ka kasance ma'aurata na haƙiƙa, masu son juna da kulawa abun sha'awa ga kowa, har izuwa lokacin da Allah ya nufa Khairat ta samu ciki, komai namu ya kasance daidai, muna ganin zamu samu ɗa mu gina zuri'armu cikin farin ciki, ashe dai akwai abun da ƘADDARA ta zaɓa mu bu sani ba. Na kaita asibiti bayan naƙuda ya kamata, cikin ikon rabbi ta haifi yarinya mace kyakykyawa, ita da jaririyar duk suna lafiya, mun yi farin ciki mara misaltuwa sosai a wannan lokacin, kwatsam daga baya kuma yanayinta ya sauya, jini ya ɓalle mata, abun ya ba mu mamaki, ko lokacin da ta ke ɗauke da ciki bai ba ta wahala ba kwata-kwata, domin ko wuyar laulayi ba ta sha ba, amma sai ga shi yanzu kuma wani sabon tashin hankali ya afku, kamar da wasa abu kam ya zama gaske, wannan ɓallewar jinin shine silar rasuwarta_
Wasu zafafan hawaye su ka sauko à idon Haidar wanda ya yi daidai da saukar nawa nima. Ya juyo ya kalleni cikin rauni sosai ya ce, "à ranar Juma'ar nan na rasa masoyiyata Khairat, na rasa duk wani farin cikina" ya faɗi wanda hakan yasa ni ƙasa da kai na fashe da kuka, na tausaya masa matuƙa.
Hanki-cif ɗin na ɗago ina share masa hawaye, tare da rarrashinsa don na san abun da ya ke buƙata yanzu kenan. Bayan zuciyarsa ta ɗan yi sanyi ya ce, "bayan rasuwarta na sanyawa 'yar da ta haifa sunanta. Na daɗe ina jinyar wannan matsalar kafin daga baya ya zame min tarihi, duk da ba duk ba don ba zai taɓa goguwa a tare da ni ba, sai dai Nuriyyah, wani lokaci muna barin damuwarmu ne ba wai don mun manta ba, no, sai dai don mu amince cewa hakan yana daga cikin ƘADDARARMU ne, kuma ya riga da ya faru ba za mu iya sauyawa ba, amma kar mu cire farin ciki mu ɗaura baƙin ciki a rayuwarmu don wani abu ya samemu".
Murmushi na yi masa tabbas kalamansa daidai ne, "yaya Haidar ina son ganin hoton Khairat" ciro wayarsa ya yi yana zaƙulo min hoton, sannan ya miƙo min. Ina amsan wayar na zare ido sosai saboda tozalin da idona ya yi kan hoton, da sauri na ɗago ido ina kallonsa cike da mamaki na ce, "wa... wannan ita che Khairat din?!" Da mamaki ya giɗa min kai alamar eh. Zuciyata na harbawa na maida kaina kan hoton tare da miƙewa a hankali na kai hannuna akai"......
Last page
___________________________________________________
Ya labarin Haidar da Khairat ya sauka a zuciyarku? Shin Nuriyyah ta san Khairat ɗin ne? A ina ta santa?
_*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_