Bayan Murmushi

Chapter 6

by @zahrabmrs02

page 6💬⌨️


Bayan na fito daga motar Jafar, zuciyata tana cike da tashin hankali. Na ji kamar dole ne in samu wanda zan faÉ—a wa abin da ke raina, wanda zai saurare ni ba tare da yanke hukunci ba.

Sai na nufi hostel ɗin Zainab Adetayo, ƙawata. Ita ce mutum ɗaya da na san zan iya shiga wajenta a kowane hali. Da na shiga harabar hostel ɗin, zuciyata ta ɗan sauka kaɗan, amma har yanzu tunanina na can.

Na same ta a É—aki. Ita kadai a dakin ,Da ta gan ni, ta gane akwai matsala tun kafin na buÉ—e baki. Fuskar ta nuna damuwa.

“Farhana, me ya faru?” ta tambaya.

Na zauna a gefen gadon, na ɗauki lokaci kafin na fara magana. Daga ƙarshe na faɗa mata komai — kissing ɗin da Jafar ya yi, yadda abin ya same ni cikin firgici da tashin hankali, yadda zuciyata ta rikice .

Zainab ta saurare ni ba tare da katse ni ba. Bayan na gama, ta ja numfashi sannan ta ce:

“Farhana, ki yi haƙuri. Amma gaskiya, irin wannan life style ɗin nasu ne.”

Na É—aga kai na kalle ta, ban gane ba.

Ta ci gaba da cewa, “Jafar fa ɗan masu kuɗi ne. Sun saba da rayuwa irin haka — hulɗa, sassauci, abubuwan da ba kowa ke ɗauka da muhimmanci ba. A wurinsu, ba komai ba ne.”

Kalmominta sun shiga raina da nauyi. A gare ta, kamar tana ƙoƙarin kwantar min da hankali. Amma a gare ni, kalmomin suna ƙara mini ruɗani. Abin da ya faru ba ƙarami ba ne a zuciyata, ko da yake a wurin wasu zai iya zama abu na yau da kullum.

Na yi shiru, ina tunani. Na fara tambayar kaina ko matsalar tana wurina ne, ko kuwa akwai bambanci mai girma tsakanin ni da duniyar da Jafar ya fito.

Ki gwada kiran sa mu gani ta fada tare da miko min wayata ,yaki dauka na fada a sanyaye ,qara masa kira daya mu gani,yayi rejecting na fada ina fashe wa da kuka ,rungume ni tayi tana dan bubbuga bayana a hankali cikin shigar rarrashi ,sai da ta tabbatar na dan sami nitsuwa ta rakoni har bakin hostel dinmu

Na bar hostel É—in su Zainab da zuciya mai cike da tunani. Abin da ta faÉ—a ya daÉ—e yana juyawa a raina, amma ban samu kwanciyar hankali ba..

Da na shiga, na tarar da Precious tana ta safa da marwa. Daga kallonta ka san tana cikin damuwa. Ta na zagaye É—akin kamar mai neman abu mai muhimmanci.

“Me ke faruwa?” na tambaye ta.

Ta juya da sauri, ta ce, ke nake nema tin dazu daga fita biki dawo ba ,na Kira wayar ki baki dauka ba 

Sorry wayar na silence  nace tare da kokarin cire hijab dina ,daga hostel dinsu zainab nake naje muyi sallama 

A dai-dai lokacin ne, Nusaiba tace Wai precious me yasa kike nuna Kamar kin fimu son farhana ne ?mantawa kike addinmu daya ?. Haba sai kace wata uwarta Kin bi duk kin takura mata 

Precious ta kalle ta kai tsaye, ba tare da ɓata lokaci ba ta ce:

“Nusaiba, ki yi hankali. Ki daina min rashin kunya. Ba duk abin da kike yi ake ɗauka da wasa ba.” Kuma kar ki qara mun gorin addini ki fita a idona ta fada a zafafe,da kyar muka sassanta su nida fateeha dan precious Yau ranta ya baci fiye da kima ,duk bakin nusaiba Yau shiru tayi

Shiru ya ratsa É—akin.

Kowa da tunaninsa.

Kowa da abin da ke cin ransa.

Yau haka zanyi bacci ba tare da Jin muyar jafar dina ba sai hawaye zirrr…

Washegari da safe, na tashi da shiri. Na yi sallama da roommates dina, su sai zuwa yamma zasu tafi . na tsaya a babban titi, ina jiran Nepap. Sai ga Jafar ya bayyana a gaban idanuna. Abin ya bani mamaki sosai, domin jiya kwana nayi ina ƙoƙarin kiran sa, amma ya ƙi amsawa ,shigo muje na kaiki abuja ban son Musu kuma ,

Ba tare da bata lokaci ba, ya taimaka min da kaya a booth, ya buɗe min ƙofar gaba kamar yana ganin cewa ni mace ce da ya kamata a kula da ita. Wannan abu ya bani wani irin ɗumi a zuciya.

Mun fara tafiya tare, kuma sai ya ce, â€śZan bi ki Abuja, zan kama hotel har zuwa jibi. Daga nan zamu je na gaisa da abbi asannan zan wuce Yola.”ya qara da cewa so nake Kafin ki gama next semester na turo gidanku ,ni yanzu na gama karatu na a Cyprus project kawai Zan koma nayi ,ina dawowa kuma Kinga Zan fara aiki a Kamfanin daddy,nace to mine Allah kaimu lafiya ,bai tayar da maganar jiya ba ,Nima ban tayar ba 

Bayan tafiyarmu na ɗan lokaci, mun tsaya a wani eatery Jafar ya mana take away. Daga nan sai muka ci gaba da tafiya zuwa Abuja. Ba mu yi hira sosai ba a hanya; kawai yana amsa wayoyi jifa-jifa yayin da yake tuƙa mota.

Mun iso Abuja cikin lokaci kaÉ—an, sakamakon gudu da Jafar yake yi a hanya,Ina muka nufa ya fada tare da juyowa yana Kallona 

Nayi shiru na É—an lokaci, ka sauke ni kawai. Zan karasa da kaina  Abbi zaiyi fada Idan ya ganmu tare

Jafar ya yi shiru, yana kallona daga gefe, amma bai ce komai ba. Na ji ƙarfin zuciyata da ɗan tsoro

Jafar ya miko mini bundle É—in 1k Guda biyu  Sai kamshi suke, yana É—an murmushi yace, â€śGashi kiba auta sameena.” Na rike bundlen da hannu, na yi masa godiya Na yi niyyar cewa ya bar shi Sabida diddi na san zata iya yin fada amma a lokacin na tsare zuciyata, ina Ć™oĆ™arin kaucewa rikici.

Bayan mun gama sallama , ya fita ya nemo drop din   taxi din da zai kai ni har gida. Ina zaune cikin mota ya bude min kofa  yace muje ga taxi din an samu, Bayan na shiga ya leko cikin window farhana ,nace Naam ,ina sonki ,tare da mun Kallo mai cike da soyayyah . Kafin na bashi amsa ya juya da Sauri ,Muna tafe ina murmushi tare da tunanin rabin Raina jafar 

Na isa gida, zuciyata cike da  Farin cikin ganin  yan gidan mu fuskokinsu cike da farin ciki da murna abbi na fara hugging ,nayi missing Dinka abbi na fada ina matse kwallah Nima nayi missing dinki mamana ,pilot din abbi ya fada yana murmushi,diddi na same ku lfy ?alhamduillah farhana ya  hanya ?Adda Sabrina tace, na dafa miki abincin da kika fi  so ,take na rungume ta ,Tnks a lot favorite sis ,Wai ina sameena ?na tambaya ina dube dube ,Tana school Kin San yanzu ta shiga SS class  sai 4 take dawowa suna lesson cewar diddi

Na zauna a dan karamin dining tebar dinmu, abincin na fara chi . Na san a wannan gida, duk da damuwar da ke cikin zuciyata, akwai wuri da zai kula da ni, da zai sa ni jin daÉ—i.

Sai na lura da Abbi yana kallona da É—an kulawa da tsantsar É—abi’a, kamar yana Ć™oĆ™arin fahimtar duk abin da ke damuna, amma ba ya matsawa. Wannan ya sa na ji wani É—an nutsuwa, da duk wani abu da ya faru da Jafar dakuma dawowar mu abuja tare 


XahraB(Mrs)