Chapter 9
by @zahrabmrs02
Page 9 💬⌨️
Bude ido nayi a hankali,hannuna na kalla makale da qarin ruwa
a hospital nake take komai ya fara dawo mun daki daki ,ko dai wasa suke ?Allah yasa mafarki nake ?
Hamma na furta na hankali sai a lokacin ya Lura na tashi
“Farhana, lafiya? Ya jikin ?me ke damunki ya jero min tambayoyi a jere .ina ganin stress yayi min yawa nace cike da kasala ,Allah qara lfy Zan je nayi laasar Akwai abinda kk so na taho miki dashi ne ?Aa Nagode Hamma .
Yana fita Precious da Nusaiba. Har suna rige rigen matsowa kusa dani,Sannu farhana Allah kara miki lafiya suka fada a tare ,nusaiba na kalla cikin hawaye ,da gaske ne abinda kika fada min dazu ?jafar dina zaiyi aure ,kuma ba ni zai aura ba?kiyi hakuri farhana ta fada kanta a kasa Ku bani wayata na Kira shi maybe auren dole zaa masa jafar bazai mun haka na fada ina kokarin tashi ,saurin kwantar dani precious tayi jikin ki ba Karfi dan Allah ki kwanta kar ki fadi,ku bani wayata nace ina kokarin qara mikewa ,WhatsApp na shiga it’s 2015 already an fara WhatsApp call Tin march ,luckily yana online ,hello jafar da gaske ne aure zaka yi na fada ba tare da sallama ko amsa maganar sa ba ,oh wow waya fada miki ?anyways da gaske ne ,amma dai auren dole zaa maka ko?na fada a raunane ,ji nayi kusan mutum hudu Sun kwashe da dariya a daya background dinsa .a speaker yasani kenan ?kin taba gani anyi wa namiji auren dole ?mun dade da Yasmin .kuma tun haduwa ta dake da ina tare da ita.dayake a hands free nasa shi ,me yasa ?me na maka ?kana nufin all this while ba sona kake ba?gskia ba zance bana sonki ba amma bani da niyar auren ki cos da ita na fara haduwa yace cikin ko in kula ,menene matsayin zuwan Ka Wajan abbi na fada hawaye na qara zubo min ,just for fun yace tare da kashe wayar ,wani kukan na qara fashewa dashi ,ya dinga mun yawo da hankali yana taba jikina yadda yaso da niyyar aure ,Allah na gode maka da Baka bani ikon bashi kaina ba,Allah ka yafe mun .
An sallameni nace Wajan zee zani na kwana bana son ganin fateeha suka rako ni hostel dinsu zee tare da alkawarin kawo mun kayana Kala 3 Kafin na dawo hostel,kwana nayi ina kuka zee na rarrashina ,sai tsine ma jafar take Nidai ba bakin magana ko class bana zuwa .farhana Yau Muna da test ki daure muje ki yi test din nan ,ki kyale ni ko naje ba komai Zan iya rubutawa ba.kwace wayata zee tayi cikin mamaki tace Wai har yanzu biki Dena bin jafar ba ?wani irin rashin zuciya ne haka farhana ? ta fada a zafafe ,na kasa zainab zuciyata zafi ,kirjina ciwo jafar nake so ki taimaka min sai kuma ta dawo rarrashina kiyi hakuri ki kaiwa Allah kukan kiyi kokari ki cire shi a rai ,ga farooq nan Kinki ki saurare shi ,at least zai dan debe miki kewa bawan Allah duk ya susuce ,kinki cin abinci ,ji yadda kk rame dan Allah.ajiyar zuciya na sauke tare da cewa na gode zee Allah barmu tare ,su uku ne dakin su lucky rommies dinta ba mazauna bane ,sai suyi sati basa nan Sun tafi yawo duniya , shysa zama da ita ya mun dadi ,zee ruwan wanka har Bandaki take kai mun .
Allah ya Hana Ka Farin ciki jafar ,kace kuka na nishadi yake saka ko ?to na Barka da Allah na rubuta tare da blocking dinsa
Bakuwar number naga an Kira ni da ita assalamu alaikum nace Bayan na amsa wayar aka amsa daga daya bangaren sunana hajiya maimuna daga kaduna ina magana da farhana ne ?eh nice ina yini hajiya lfy Alhamduillah ya school ?lfy lou. biki gane ni ba ko?nice maman lamido ,lamido kuma gskia ban gane shi ba,Afwan farooq ne dayake lamido muke kiran sa a gida ,take naji kunya ta Kama ni, Dama na Kira ne naji me auta yayi aka Dena daukan wayarsa duk yabi ya dame ni ,ko cafe din nasu ya Dena lekawa ,ciki da inda inda nace kiyi hakuri mamma Nima na dan yi rashin lafiya ne kwana biyu shysa Subhnallahi ,to Allah ya baki lafiya kuma ayi hakuri dan Allah a dauki wayar lamido ta fada tana dariya nogodr mamma Allah ya qara girma .
Zee tace kiga dai yadda farooq ke sonki farhana ,wancan shegen be taba hadaki da yan gidansu ba ko a waya dayake mayaudari ne.
Na tattara na Koma hostel dinmu inda su precious sai rawar jiki suke suna cewa sunyi missing dina ,fateeha na gefe a rakube ,na zama very silent yar hirar da muke Dik da Dena .tsaki nusaiba taja…fateeha ji yadda munafincin ki ya maida farhana duk ta canza yar hirar ma ta Dena.
Ke kar ki kuskura ki zage ni wacce akayi abun ma bata dauka da zafi sai ke yar Neman masifa fateeha ta fada a zafafe suka fara cacar baki,girls it’s okay wallahi kuka cigaba Wajan zainab Zan koma gaba daya da zama na rantse .
Nagaji da Habaicin nusaiba dole Yau sai kun zauna na fada muku komai cewar fateeha ,farhana kiyi hakuri wallahi ban gane jafar Yasmin zata aura ba cos ba wata shakuwa ce tskaninmu ba
anyi creating group din biki ,a ranar da muka dawo school Naga pre wedding kasa bacci nayi ranar.Sabida mamaki da tsoro na rasa yadda zanyi na fada miki,duba da irin son danaga Kina masa ,wallahi ban so kika sani ta wannan hanyar ba ki yafe mun ,ba yaudarar ki nayi ba ,mukayi shiru Kafin na numfasa ba komai fateeha komai ya wuce Allah ya hakan shine mafi alkairi na gareni
Bayan murmushi