BLOOD CROWN (THE HEIRS APPARENT)
PAGE _______ 60 & 61
by @swrites22
Ɗauke kai Sahnish yayi yana hana raunin zuciyar sa bayyana saboda maganganun Hushaima. Suna tafiya da Constable zai maidata cell ta ce , "Akwai kuɗi a jaka ta ka ja qanin nawa gefe ka bashi su duka kace ya baka wani abu a ciki".......... Take constable ya sake fuska harda faɗin, "Ba matsala in da akwai abinda kike buqata ma ki faɗa sai a kawo".......... Bata ce dashi komai ba ta yi shigewar ta. Komawa yayi wurin su tare da kiran Sahnish ɗin wani office, binsa yayi suka shiga ya ɗauko jakar tare da sa hannu ya ɗauko kuɗaɗen kusan dubu dari uku ya bashi tare da ɗan makullin sannan ya ce, "Tace ka bani wani abu a ciki"......... Ba musu Sahnish ya zaro dubu talatin ya bashi, hararar Sahnish ɗin yayi kafin ya ce, "To jeka dama shi ne abinda tace a baka ai"........ Saka kuɗin Sahnish yayi a aljihu sannan ya juya ya fita wurin su baba ilerika tare da faɗin suzo su tafi. Sai da suka fito ya ce, "Baba mun gode sosai da kulawar ka ALLAH ya saka da alheri".
"Bakomai Sahnish yanzu ina zaka ne?"......... Faɗar Baba ilerika a daidai lokacin da suka fito daga station ɗin, tirjewa Shazeen tayi tare da fasa kuka tana nuna ƙofar station ɗin da hannunta. Sahnish da shi ma yake jin kamar ya fashe da kukan ya daure ya ce, "Shazeen yanzu zamu dawo mu tafi da ita ai, ki daina kukan kizo mu tafi "........."Ni yaya ka barni anan wurin aunty Hushaima kaje ka dawo"........."Ah ah Shazeen nan wajen akwai karnuka masu cizo, kizo dai muje mu dawo"......... Sai dai Firr Shazeen taki tafiya a lalle sai dai a barta a wurin Hushaima ko kuma a fito da ita su tafi.
"Kaga Sahnish kana ƙara ɓata lokaci kuma kaga dare yayi kar ka rasa abinda zaka siyawa Hushaima ɗin, azo kuma ta kwana bataci komai ba ka ɗauki yarinyar nan mu wuce kawai"........ Shawarar baba ilerika Sahnish ya ɗauka ya sunkuya ya ɗauki Shazeen tana tirjewa tana ihu suka wuce. "Baba a ina kake tunanin zamu samu abinda za'a siyawa Hushaiman ".
"Ai Sahnish inaga yanzu saidai ka siya mata abun kanti kawai dan whl yanzu baza ka samu kowa ba sha biyu fa saura".........."To me za'a siya mata a kantin?".
"Ka siya mata ko kifin gwangwani da biredi ma "..........." To". Sahnish yace sannan suka cigaba da tafiya har suka samu wani kanti suka siya mata harda ruwa da maganin sauro sannan suka koma suka bawa Constable Junaid ya kai mata.
Abun hawa Baba ilerika ya tsaida musu sannan ya ce, "Sahnish kana da yar dubu uku haka ?".......... Saida ya shiga tuk tuk ɗin ɗauke da Shazeen da ta sha kuka ta gaji harta fara bacci baiwar ALLAH. Ya ce, "Ba gida zaka bane Baba?".
"Ah ah dama Kai na tsarewa abun hawan saboda ga yarinya a hannun ka karka wahala".......... Hannu Sahnish ya saka a aljihu ya zaro dubu biyar ya bashi, karɓa yayi tare da faɗin, "Ah tou madallah godia nake Sahnish, in kun ƙarasa zan kiraka naji kunje lpy".
"To". Sahnish yace sannan ya bawa me tuktuk ɗin umarnin tafiya.
Ko da suka ƙarasa gida ɗakin Hushaima ya buɗe suka shiga ya kwantar da Shazeen sannan ya zauna gefenta dan shi kam kwata kwata ba ma ya jin baccin, tashin hankali yayiwa zuciyar sa qawanya tunani kawai yake yadda za'ayi ya fito da Hushaima, wanna wace irin baqar Rana ce? ko da wasa bai taba zaton akwai ranar da Hushaima zatayi kwanan cell ba, yana cikin wannan yanayi kiran Baba ilerika ya shigo Wayarsa kamar yadda ya faɗa kira yayi yaji sun isa gida lpy sannan ya kashe.
Shi dai Sahnish yadda yaga dare haka yaga rana da safe ya tashi Shazeen ta yi shirin makaranta ya samo mata abinda zata karya dan shi bayajin akwai abinda zai iya sawa cikin sa bayan Hushaima na can kulle bataci komai ba. Yana miqa Shazeen makaranta ya wuce police station ɗin duk da sunce sai 10am DPO zai shigo hakan bai hanashi zuwa da wuri ba, tsayawa yayi ya saya musu kunu da ƙosai sannan ya wuce ciki, samu yayi su Constable na shirin shifting wasu zasu shigo, nan ya sanar da Constable Junaid yana son yaga Hushaima Sannan ya bata abun kari, ba musu Constable ya buqaci ya ɗanɗana duk abinda ya kawo kamar yadda doka ta tanada sannan ya shiga ya kirawo masa ita.
Fitowa tayi idanunta sun ɗan tasa ga alamun rashin bacci a tattare da ita, kwana ɗaya duk tayi wata firi firi da ita kamar kazar mayu Amma Kuma kallo ɗaya zaka mata kasan bata karaya ba Kuma babu nadama ko dana sani a zuciyarta sai ma wutar ɗaukan fansa dake sake ruruwa, cikin ƙoƙarin ɓoye damuwa ta ce, "Sahnish Kun kwana lpy?".
"Hmmm da sauki dai, dan ni dai kasa rintsawa nayi kawai tunani na a wani hali kike a wanna wurin".
"Karka damu Sahnish Kai dai kawai kayi min ƙoƙari na samu fita daga nan ɗin saboda a fahimta ta yarinyar iyayen ta nada ƙarfi Kuma kasan yanayin ƙasar Nifaz a gurbace take da cin hanci dole zamu fuskanci barazana. Ina Shazeen ta tafi makaranta ko?".
"Ta tafi, ga wanna Abun karyawa ne na taho Miki dashi "........ Kallon sa tayi da faɗin, " kai ma ai baka karya ba"....... ɗan shafa Kai yayi kafin ya ce, " Na karya mana".
Karɓa tayi tana faɗin, "Haba Sahnish na sanka fa dan haka Ka samu wani abu kaci kafin DPO ɗin ya shigo, kaga ba dama bare na zauna anan muci wanna tare".
"Shikenan zan fita in samu wani Abun Amma ba zanyi nisa ba Ina nan ɗin har yazo, ALLAH yasa Abubuwan suzo da sauqi"......... Da haka suka rabu Constable ya maidata cell shi Kuma ya fita Neman abinda zaici.
Ƙarfe goma dai dai DPO ya shigo kamar yadda suka faɗa, yayinda goman tayiwa Baba ilerika a ƙofar police station ɗin. Bayan Sahnish ya gaishe da DPO ɗin ya tashi da niyyar binsa, wani Sargeant ya dakatar dashi da faɗin ya tsaya tukunna sai DPO ya shiga office ya zauna, komawa yayi ya zauna a daidai lokacin kuma baba ilerika ya shigo. Bayan sun gaisa da Yan sandan ya ce, "Sahnish ashe Kai kana nan ma tun ɗazu nake gwada wayar ka bata shiga ai".
"Ba caji ne baba, Ina kwana ".........." Lpy kalau, to ya ake ciki ya shigo ne?"..........Ya ƙarashe Yana zama kan benci gefen Sahnish ɗin. Kafin Sahnish ya bashi amsa Sargeant ɗin nan ya fito tare da fadin suna iya shiga wurin DPOn. Tashi sukayi suka bi bayan sa har office na DPO, gaishe shi suka yi ya nuna musu wurin zama sannan ya bawa Sargeant umarnin tafiya.
"Ranka ya daɗe mune yan uwan Hushaima"........ Baba ilerika ya faɗa. "Okayy kunji abinda ya faru ko?" .
"Munji Ranka ya daɗe Amma muna neman alfarmar a bamu bailing ta yaso duk abinda za'ayi ma sai ayi daga baya"........... Baba ilerika ya sake amsa masa. Girgiza Kai DPO yayi da faɗin, "Baza mu iya baku bailing ta ba a halin yanzu domin batun fa da ake yanzu yarinyar da abinda ya haɗosu tana ICU ne ba'a sa halin da take ciki ba. Kuma ma kamar yadda kuka ji mahaifan wanna yarinya sun buqaci a turaku kotu domin a bi musu hakkin ƴar su".
"Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, Ranka ya daɗe baza mu iya ganin ka ba a sasanta".
"Baba wanna ba batu bane na sasantawa mu aiki muke don Kare hakkin Al'umma, ƴarka me laifi ce domin attempting kisan Kai tayi".
"Ranka ya daɗe whl tsautsayi ne Hushaima ko Dabba baza ta iya kashewa ba bare mutum"......... Faɗin Sahnish cikin matsanan cin tashin hankali.
"Yaro wanna ba magana ta bace ni dama abinda yasa na neme ku saboda mu faɗa muku ne ku shirya in da hali ku ɗauka mata lawyer "........... "Yanzu baza a iyayin komai akai ba kenan ranka ya daɗe?".
"Baafa za a iyayin komai ba na gaya ma, in Kun gama Kuna iya tafiya"......... Dpo ya faɗa Yana buɗe wasu file file dake gaban sa alamun ya gama magana.
Duk yadda Sahnish da Baba ilerika suke tunanin Abun ya wuce nan sunyi iya bakin ƙoƙarin su Amma DPO ya ma ƙi sauraren su wanna Abun ba ƙaramin ɗagawa Sahnish hankali yayi ba. Yana cikin tunanin mafita a ƙofar police station ɗin Amla ta faɗo masa a rai aron wayar baba ilerika ya ƙarɓa ya saka number Amlan dan ya haddace ta tun da daɗewa. Saida ya mata missed call biyu sannan ta ɗaga Amma batayi magana ba, " Hello Amla".
"Sahnish!". Ta faɗa dan ta gane muryar sa. "Naam Amla Ina kwana?"......... "Mun tashi lpy Sahnish? Ya Shazeen da Besty?"......... Wani zazzafan numfashi ya furzar sannan ya ce, "Akan bestyn taki ne ma dalilin Kiran, jiya Hushaima a cell ta kwana sun samu dan matsala da wata yarinya a inda take aiki harta fasa mata Kai da kwalba to har yanzu yarinyar bata farfaɗo ba gashi ance iyayen ta sun buqaci a turasu kotu, amma kuma an hanamu bailing ta duk iya ƙoƙarin da zanyi nayi amma ba wani alamun nasara saisa na nemeki".
"Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, haba Sahnish ya ma za'ayi ka barta ta kwana a cell Dan girman ALLAH, meysa baka Kira ni ba tun a Daren"........ Faɗa sosai Amla take kafin daga ƙarshe ta ce, "yanzu a wani police station ɗin kuke"........."Ta nan wurin Alolo barrack".
"Shikenan gani Nan zuwa"........ Ta faɗa tare da kashe wayar.
Bari mu ɗanji alaqar dake tsakanin Hushaima da Amla. Hushaima da Amla sun yi kusan shekaru biyu da sanin juna ta sanadiyyar faɗa da Hushaima ta shigarwa Amla a wani restaurant lokacin ita Hushaiman tana aiki a wurin matsayin waitress, tazo kawowa Amla abinda tayi order ne ta tarar suna faɗa da wata yarinya in da ta fuskanci ita yarinyar ce tayiwa Amla rashin kunya ai kuwa taci uban yarinyar ta lakada mata shegen duka, sosai Amla taji daɗin hakan har take maidawa Hushaiman abinda ya faru a ƙarshe ma ta karɓi number ta, dan Hushaima akwai shiga rai in taso, akayi Sa'a kuma itama Amlan tana da son jama'a ba kuma ta da ƙyamar talaka.
Bata San komai game da Hushaima ba bayan ƙannen ta biyu sai ko zaman kansu da suke, ko da ta tambayeta game da iyayen su sai taga Hushaiman ta canza mata fuska wanna ya sanya bata Ƙara bi takan maganar ba dan ma karsu samu matsala kamar yadda itama Hushaima ɗin bata taɓa tambayar ta wani abu da ya shafi rayuwar ta ba saidai in ita ta faɗa mata. Wani abu gami da Hushaima yadda bata so a tambayeta wani abu dangane da rayuwar ta haka baza ta tambayi wani ba saidai in ganin damansa ya faɗa da kansa, bata son sanin sirrin kowa in dai ita zata riqe nata.
A bangaren mahaifiyar Amla kuwa lokacin data san da alaqar ƴarta dasu Hushaima ba ɓata lokaci tayi mata iyaka da su, Dan ita Macace da bata san talaka Kuma bata da mutunci ko daidai da kwayar zarra bare da taji labari su Hushaiman zaman kansu suke kuma talakawa ne, saidai duk da haka ita Amla bata fasa muamala da su Hushaiman a ɓoye ba domin tana jin su kamar yan uwanta na jini ko dan ta taso ita kaɗai ce a wurin mahaifan ne.
Amla ya' ɗaya ce tilo ga Alhaji zawaad Wanda duk wani buri nasu sun tattara sun ɗaura kan ta, sai dai ita tun tasowar ta bata da wani buri da ya wuce ta zama runaway model kuma ALLAH ya cika mata burinta dan yanzu ba qasar da bata zuwa fashion modeling, mahaifanta kuwa sun mara mata baya 100 percent dan duk abinda take so duk muninsa to su ma suna so. WANNAN KENAN.
-----------------------√
AURELLON SULTANATE 💎
Ko da ummu ta koma ɗaki tasan baza ta samu me Martaba a yanzu ba dan haka ta Kira wazirin fada yana ɗagawa ya fara mata kirari, bata ce komai ba har ya gama sannan ta ce, " Wazir meke faruwa a fada?".
"ALLAH ya Kara Miki lpy, Sheikh yassar ne ya yanke jiki ya faɗi, yanzu haka an tafi dashi asibiti".
"Me ya sameshi toh?"..........."Haka kawai Ranki ya daɗe, dan lpy lau ya shigo daga yankin sa na west yazo kawowa Sultan gaisuwa, an ma daɗe zaune ana hira dashi kawai akaga ya bingira, kusan zan iya cewa irin abinda ya faru dasu marigaya Sheikh Sameer"......... A cikin zuciyarta ta shiga maimaita kalmar innalillahi wa Inna ilaihir raju'un kafin tayi ƙarfin halin faɗin, "Shikenan Wazir Nagode".
"Hutawar ki lpy Giwar Sultan".......... Ajje wayar tayi kawai tare da dafe kanta tunanin ta yafi karkata kan Anya kuwa Reeslan baisan wani abu ba ko Kuma dasa hannun sa, saurin kauda wanna tunanin tayi kafin ta ɗauki waya ta Kira Imam Maher . "Assalamu alaikum sheikha"
.......... "Wa alaikum Salam warahamatullah Imam".
"Mun wuni lpy sheikha, ya jikin Maleekh ?"..........." Alhamdulillah imam, da ALLAH ina son ganin ka anjima in Kun tashi daga fada".
"To sheikha in yanzu ma kikace sai na Taho ai".
"Sai anjiman dai"........... Ta faɗa tare da ajje wayar a gefen ta. Jakadiya ce tayi sallama sannan ta shigo dan duk cikin khadimai ba Wanda ke shigowa har uwar ɗakan Ummu Kai tsaye sai jakadiya saboda yadda ummu ta yarda da ita ta Kuma maida ita abokiyar shawarar ta saboda gaskiya da riqon amanar jakadiyan. A ƙasa jakadiya ta zauna tare da faɗin, "ALLAH taimaki sheikha, ALLAH ya Ƙara lpy da girma ya Kare mana ke".
"Jakadiya ya ake ciki, kin bashi ruwan addu'ar?".......... Shuru jakadiya tayi tare da sunkuyar da kanta ƙasa kwata kwata bata so ta ce da Ummu ga abinda Reeslan ɗin yayi saboda karta haɗashi da mahaifiyar sa Amma Kuma to me zatace mata dan baza ta iya yiwa ummu ƙarya ba, Dan haka ta katse shurun da faɗin, "Reeslan Maleekh ya buqaci a barshi ya huta sai anjima a bashi, a takaice dai bai sha ba yanzun".
Girgiza Kai ummu tayi da faɗin, "Kai Kai Kai lamarin Reeslan sai ALLAH, ina ruwan shan ruwan addu'a da hutu, tukunna ma shi zai sha ko Rouslan, kaiiii allahumma ka shirya min yaron nan"........ ta ƙarashe Maganar cikin tsantsar damuwa.
"Sheikha ko akwai wata matsala ne?"........ Ajiyar zuciya ummu ta sauke tare da faɗin, "Jakadiya wata musiba ke shirin tunkaro mu wadda nake ga idan nayi shuru Abun zai cigaba da faɗaɗa ne har yayi girman da baza mu iya tarewa ba".
"Subahanallahi ranki ya daɗe wani Abun ne ya faru?".
"Reeslan ne .........." Nan ummu ta kwashe abinda ke faruwa ta faɗa mata, cikin jimami da kuma damuwa jakadiya ta ce, "Ranki ya daɗe bana son ki sa damuwar abun nan a zuciyar ki, inason ki tuna Maleekh fa likita ne Kuma duk mutanan nan da suke faɗuwa a gabansa ne, kinga kuwa zai iya gane wani abu game dasu, misali ko sun samu bugun zuciya na farar ɗaya wanda zai yi wuya ace sun tashi kinga kuwa hakan ba zai zama laifi ba".
Girgiza Kai ummu tayi da faɗin, "Jakadiya ba likitan da ya isa yace wannan mutumin mutuwa zaiyi bazai tashi ba sannan kuma ya mutu, ni na fara zargin ko dai Reeslan na da kambun baka ne bamu taɓa sani ba".
"To Kuma Ranki ya daɗe ke fa yanzu kikace ba Wanda ya isa yace mutum zai mutu kuma ya mutu, haka ma in kanbum bakan ne ai ba'a iya haka zai tsaya ba, ranki ya daɗe Karki manta fa a hannu na su Maleekh suka tashi idan har da suna da irin wannan Matsalar ni zan fara sani. Kawai abinda nakeso ki kwantar da hankalin ki, ki cire duk wani zargi a ranki mu bar hakan a matsayin lokacin su ne yayi kawai".
"Toh Jakadiya ba'a qin ta mutum, Amma nayi waya da imam anjima zaizo inason mu tattauna kan wanna batun".
"Ranki ya daɗe tattauna wannan batu da Imam kamar fitar da zancen nan ne, kuma kinsan kina da magauta zagaye dake hakan zai kawo tsirko da tsegumi, kuma ALLAH ya taimake ki nasan ko Sultan zaiso wannan maganar ta kasance sirri, saboda Tsakanin Reeslan Maleekh da Rouslan Maleekh dole a cikin su ne ɗaya zai gaji kujerar nan idan Maganar nan ta fita hakan zai zama barazana ne a garesu"........... Shuru Ummu tayi tana nazarin maganganun Jakadiya wanda suke kan hanyar gaskiya, lalle shawara tana da daɗi, kallon jakadiya tayi da faɗin, "Nagode da shawara jakadiya, kina iya tafiya".
Tashi jakadiya tayi da faɗin, "ki huta lpy Sheikha"........... Da Kai kawai ta amsa mata ita Kuma ta juya ta fita.
____________kai Sahel me haka nake gani?".......... Wata dattijuwar mata da zata Kai shekaru 57 ta faɗa cikin firgici da tashin hankali, tana sanye da kayan da kallo ɗaya zaka mata ka tabbatar da dukiya da mulki sunbi jininta, kyakyawar gaske ce saidai ita ba fara bace tarr ɗin nan, sheikha Balqis kenan mata ta biyu wurin Mai martaba.
Cikin yanayin maye ya ce, "Um... ummie me ya shi sh shigo dake Nan ne wai, k...ke ke bakya zama wuri ɗaya..aa"..........Ya ƙarashe Yana warfa hannu alamun meysa, baiyi aune ba yaji saukar mari. "Ni zaka tonawa asiri Sahel, duk faɗi tashin da nake a kanka ka rantse sai ka bani kunya ko? Tukunna a gidan uwar wa ka kwaso wannan kayan shaye shayen? Sahel Ni zaka sa a bala'i Sahel?"....... kuka ta fashe dashi saboda takaici da kuma baqin ciki, ita kaɗai ta san ya takeji a zuciyarta. Sosai ta tsaya a kan Sahel don son ya fito a nutsatstse kuma kamili saboda ganin ya'yan Ummu sun ɗauko hanyar da ba zai yiwu a basu mulki ba kasancewar shi Rouslan kullum cikin laulayi yake, shi kuma Reeslan kamar a fiffisge yake ba cikakkiyar nutsuwa a tare dashi wani sa'in, hakan yasa ta dage ganin ita nata ya fito a kamili mai hankali da nutsuwa tunda su uku ne maza in har yan biyun Ummu basu samu ba to shi za'a bawa amma gashi duka ɗaya yana neman watsa mata ƙasa a ido. Dadin dadawa kayan shaye shayen da ta gani a tattare dashi wanda hakan ba ƙaramin laifi bane a Masarautar tasu dan sam ba'a shigo da wani abu da ya danganci maye, duk kuma wanda aka samu da wannan laifin hukuncin shekaru ashirin ne a prison tare da horo me tsanani wannan yasa hankalin ta Daɗa tashi.
"Ki... K.. kiyi hakuri to za za a gyara ".......... Girgiza kanta tayi hawaye na cigaba da sauka akan fuskarta, a zuciye ta shiga bincika ɗakin saidai abinda ta gani ya sa a tsorace ta ja baya tare da dafe bango saboda wata Hajijiya data ɗibeta, ƙwayoyin maye ne da Syrup harda cocaine ta tarar a cikin kayansa, ba inda baya rawa a jikinta shi kuwa inaa tuni ma ya tafi bacci, yadda zuciyarta ke bugawa yasa ta rasa addu'ar da zata karanta, sai da tayi kusan minti biyu kafin ta samu bakin karanto Allahumma ajirni fi musibati. Kusan minti uku ta ƙara kafin tayi ƙarfin halin zuwa tasa Hannu ta fara kwashe kwayoyin ta nufi toilet ta zuba tayi flushing, Syrups ɗin ma ta juye ta bisu da ruwa, kwalaben ne dai ta rasa ya zatayi dasu sai ta zubasu a dustbin ta sanya hannu ta ciro ledar ta ƙulle ta Ajje su bayan ƙofar toilet ɗin. Zufar dake goshinta ta share sannan ta ƙarasa gaban washing basin ta wanke fuskarta da hannuwanta ta fito, alkyabbarta ta ɗauka ta sanya sannan ta fita tare da kulle ɗakin ta waje ta sashin ta, tana fitowa khadiman da suke mata rakiya suka rufa mata baya har suka dawo ainahin bangaren nata. "Ki turomin khadima Shafeeqa"......... ta faɗa kamar ba ita ba saboda tayi ƙoƙarin ganin damuwarta bata bayyana ba.
Tana shiga ɗakinta ta cire alkyabbarta ta ta nemi wuri kan sofa ɗin dake ciki ta zauna tana sauke numfashi, ba'a fi minti biyu ba khadima Shafeeqa tayi sallama ta shigo tare da zubewa a gabanta ta shiga jero mata kirari, ita kuwa bata ma san tanayi ba tayi zurfi a tunanin da take, sai can ta farga, juyowa tayi ta kalle ta sai kuma ta ɗauke kai tare da faɗin, "Dr Ashir zaki kiramin yanzu, don banajin daɗi ina buqatar yazo ya gwada BP na".........."Subahanallah, an gama ranki ya daɗe yanzu za'a kira shi , ALLAH ya ƙara lpy ALLAH ya ƙara miki nisan kwana"......... ɗaga mata kai kawai take harta gama ta tashi zata fita sai kuma ta ce, "Dawo Shafeeqa".......... cikin hanzari ta dawo ta zauna. "Menene a bakin ki?".........Ɗan susa kai khadima Shafeeqa ta fara kafin ta ce, "Ranki ya daɗe dama... Dama mun samu labari ne cewa an Kai Sheikh yassar Asibiti ranga ranga ba yadda yake, ban sani ba ko kin samu labari".......... Dukda Halin da take ciki sai da ta saki wani shu'umin murmushi kafin ta ce , "kina iya tafiya".
"Hutawarki lpy gimbiyar Aurellon"........ ta faɗa tare da juyawa ta fice.
Wayarta ta ɗauka bayan fitar khadimarta ta tare da dannawa wata number Kira ana ɗagawa ta ce, "Abubuwa na tafiya yadda ake so kenan?"........ Daga ɗaya bangaren akace, kwarai Me gadon zinari domin Shi ma ana zaune aka ga ya ɓingira.
Murmushi Marar sauti tayi sannan ta ce, "in Sha ALLAH Sahel shi ne zai mulki aurellon sai dai fa wani hanzari ba gudu ba".......... Shuru tayi yayinda na cikin wayar ya ce, "ALLAH yasa ba wata matsalar bace Sheikha"......... Sai da ta nisa kafin ta ce, "Ba abinda nake ɓoye ma, Sahel yana son sanyani a tashin hankali bansan ta ya ya samu........." Duk abinda ya faru da abubuwan data gani a ɗakin Sahel ɗin ta kwashe ta faɗa masa sannan ta ɗora da faɗin, "Yanzu bansan yadda za'ayi a fita da kwalaben nan ba. Abun da yafi ɗaure min Kai shi ne a ina ya samu irin wa'annan kayan bayan irin tsaron dake Aurellon tun daga kan jami'an mu zuwa na'urorin su ? Abun yayi matuqar ɗaure min Kai tare da ban tsoro fa".......... Cikin son ya kwantar mata da hankali ya ce, "Zanyi wannan binciken ta ƙarƙashin ƙasa, sannan kuma batun kwalabe karki damu nasan yadda za'ayi zan aiko da amintattun yara na akwai yadda za'ayi su fita dasu ba tare da an sani ba".
"Nagode Kwarai da gaske, saidai wani hanzari ba gudu ba, ina tsoro abinda zai biyo baya tunda Sahel ya fara da haka".......... "Karki damu Sheikha ba abinda zai gagara zan je wurin malamin nan a bashi sunan Sahel ɗin ya masa aikin da za a mantar dashi duk wani abun shaye shaye"........ Cikin farin cikin Sheikha Balqis ta ce, "kai amma Nagode kwarai da gaske, in kai min haka ka gama mun komai in sha ALLAH muna gama waya zaka ga saqo"..........."Ai ni ne da Godia Sheikha, burin mu kawai Sahel ya hau kujerar Aurellon "........ Cikin jin daɗi ta ce, "in sha ALLAH. Sai na jika"......... Ta katse maganar saboda Knocking da ake yi, bada izinin shigowa tayi inda khadima Shafeeqa ta shigo tare da sanar da ita Dr ya ƙaraso yana falo.
____________A wannan lokacin yan Aiken Queen Hirut suka ƙarasowa, Arrow and bow ɗaya daga cikinsu ta saita tare da harbawa daidai saitin wata Bell, wadda ta kaɗa sau uku ƙaran ta ya gauraye kusan rabin Aurellon, ita wannan Bell ɗin ita ke sanar da isowar su, takanas saboda su aka maqala ta, saboda ada idan suka zo saidai suyi ta musu ruwan Arrow a cikin masarautar har sai an gani an shaida isowarsu wanda hakan ke cutar da wasu da dama dan wani lokacin ya kan samu wasu mutanan, wasu su raunata wasu su mutu.
Wazir ya ce, "ALLAH ya taimaki Sultan kamar fa wa'ancan mutanan ne suka kawo saqo"......... Girgiza Kai Sultan yayi alamar yaji, juyawa wazir yayi wurin jagoran masu aike da Kuma karɓa ya ce, "Mutallab a aika maza a ƙarɓo saqon yanzu".
"Annnnn gama wazirin aurellon"........Ya faɗa Yana tashi sannan ya risina alamar girmamawa ga Sultan kana ya juya ya fita domin isar da saqo zuwa ga mutanan nasa cewa aje a ƙarɓo.
*TO MY PPLE YANZU FA WASAN YA FARA, YANZU NE AINAHIN BLOOD CROWN ZAI ƊAU SAITI, SAI DAI KUMA STEP 1 YAZO GANGARA, DUK KUMA ABINDA ZAKU GANI A YANZU SHIMFIƊA NE KAWAI, AINAHIN GUNDARIN LABARIN YANA STEP 2. STEP 1 NE KAWAI FREE STEP 2 ZUWA ƘARSHE PAID NE AKAN #500 KACAL, KU HANZARTA KUYI PAYMENT KAR A BARKU A BAYA, DAN BAMA A FARA KOMAI BA ABINDA KE CIKIN STEP 1 BAIFI KA SANYA COKALI A KOGI DOMIN ƊAIBO RUWA BA. KU DAGA JIN SUNAN KUNSAN AKWAI RIKITA RIKITA, HARGITSI, TASHIN TASHINA, SARQAQIYA DA KUMA ZAZZAFAR ƘURA. KU HANZARTA KUYI PAYMENT, 2356673754, RUKAYYA AHMAD MUHAMMA UBA BANK . SAI KI TUROMIN EVIDENCE TA WANNAN NUMBER ***.*