Her wish
by @realsmasher
💠💠💠💠💠
©®AS-2023.
*Bᴀsᴇᴅ ᴏɴ ᴀ ᴛʀᴜᴇ sᴛᴏʀʏ*
*♡WAZEER¸.•💥*
(A Tᴡɪsᴛ Oғ Fᴀᴛᴇ)
Bʏ.
*HAWWA__B__KUMO.*
(Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*
*AREWABOOKS:REALSMASHER.*
*TIKTOK:ASLISMASHER.*
https://www.arewabooks.com/u/realsmasher
••••••••••
*It's all about:#Love one another,#Twist,#Betrayal,#Friends,#Fate,#Romance,#Hated & #Lost..*
'''Alhamdulillah alaa kulli halin! Hope you guys had a great sallah vibes.. Allah ya karɓi ibadunmu yasa muna cikin bayin da aka ƴanta,ameen..'''
28
#Her wish!
Buɗe ido sosai Muniba tayi fuskarta na cika da murmushi tace "don Allah fa?" Baniynah tace "wallahi Allah kuwa da gaske,yanzun nan saukowata Umma ta kira Mami ta faɗa mata,su Abba ne ma suka amshi kuɗin" Muniba na zaunawa gefen Mami saman kujera tace "Maa sha Allah.. Gaskiya i'm happy for Safwa,Allah ya tabbatar da alkhairinsa.. In sha Allah za muje muyi mata Allah ya sanya alkhairi" Baniynah tace "in sha Allah.. But ko dai za muje yanzu ne tunda babu abunda muke yi?" Mami dai murmushi take kafin tace "na ji daɗin yanda Hjy Murja ta sanar min maganar nan,dama ina cewa saura Safwa in sha Allah.. Ashe al'amarin Allah yana kusa² bamu sani ba" Muniba da duk murna ya cikata tace "alhamdulillahil-lazii bini'imatihi tatimussalihaat!" Baniynah tace "Sweetheart za muje ɗin yanzun?" Mami tace "idan za kuje ku shirya kafin maghreeb yayi muku,and make sure kun dawo da wuri" Muniba na kallon Baniynah tace "to ai ni fita zan yi fa" marairaicewa Baniynah tayi kamar me shirin roƙo tace "ina za ki? Please ki bari na ɗauko veil ɗina mu tafi don Allah,in ya wuce yau bamu san yaushe kuma za muje ba,sai dai ko mu kirata a waya,ni kuma abunda ba na so kenan gara muje har gida.. Kuma ai Mami ma ta bamu permission" Muniba ta kalleta ta kalli Mami kafin tace komai Mami tace "just go and pick up kuje,ai nima ina sane na barku kuje yanzun" a hankali Muniba ta gyaɗa kai tace "ok!" Tana tashi tsaye take cewa "Mami na je waje.. Darling ki same ni a balcony,i will wait u there" Mami tace "a'ahhh! Kin je waje as in? Ki jira ta sauko ku wuce mana" Muniba ta gyaɗa kai tace "toh!" Gudu² Baniynah ta wuce sama ta ɗauko veil da plat shoe,ko tsaiwa ta gyara fuska bata yi ba ta sauko da gudu kamar wanda aka biyo,Mami ta ɗaga kai ta bita da kallon mamaki,tace "duk fitar ne yasa kike guje² Baby? Ki dunga bi a hankali please,slightly kika faɗi zai iya zama wani abu,u have to be careful ban son ko ƙwarzanewa ku samu har na kaiku gidajenku" dariya Baniynah tayi tace "Mami mun tafi" Mami tace "kin ɗauko muku key ɗin ne??" Baniynah tace "ehh!" Mami tace "alright! Sai kun dawo,Allah ya tsare ya dawo min da ku lafiya,kwa ce ina gaida Hjy Murja da Mamanku kafin na samu na shiga yi mata Allah ya sanya alkhairi" suka amsa suna ficewa. A balcony Baniynah ta ƙarasa yafa veil ɗinta,tana shirin yin magana Muniba tace "In-law ɗinki ne fa ya zo" Baniynah ta waigo da sauri ta kalleta tace "amma me yasa baki faɗa min ba tun muna ciki?" Muniba tace "toh ai na ga kin matsu ki fita yawo ne,it seems like ƙafarki na scratching" Baniynah ta fara dariya tace "wallahi na gaji da zaman ne,so nake na fita Mami kuma ta hana mu,yau kawai ina gani ta bamu dama sai na tsaya wasa?" Muniba tayi murmushi tace "to sai kin dawo ni yanzu bazan iya zuwa ba,idan ya tafi zan zo ko muyi waya" Baniynah tayi shiru a hankali kuma sai tace "Mmmm! Think mu haƙura da zuwan" Muniba tace "saboda me za'a haƙura? Ai idan kin je kamar na je ne" Baniynah tace "um'um! Gaskiya bazan iya zuwa ni kaɗai ba,ma yi mata waya kawai,idan mun samu chance kuma sai muje ɗin" ɗan jim Muniba tayi tana kallonta,a hankali kamar me tunani tace "Mmmm! Kin san me za'ayi?" Baniynah tace "um'um!" Muniba tace "kawai mu tafi can ɗin sai na sanar masa dama fita za muyi,na san bazai ce wani abu ba,ko yace zai dawo anjima" Baniynah tayi murmushi tace "babu matsala?" Muniba tayi mata murmushi also tace "Mmmm" Baniynah tace "ok! Muje.." Tun kafin su iso Lieut Abuu Turab ke kallon Muniba,he don't want any further explanation,yanayin fuskarta duk da ta shafa powder ya tabbatar masa ta yi kuka,a hankali ya kwantar da kansa jikin seat yana kallonta har suka iso tare da yi musu sallama,amsawa yayi idanunsa akanta ya kasa daina kallonta,Baniynah ta buɗe ido tana kallonsa,sai kuma ta kalli Muniba da ta sauke kanta ƙasa,murmushi tayi tace "awwnnn! Yayana good evening" ɗan lumshe idanunsa yayi tare da sauke ajiyar zuciya ya juya kansa yana kallon Baniynah yace "evening dear how are u? Ya Maminmu?" Baniynah tace "i'm good.. Mami tana nan lafiya lau alhamdulillah.." Muniba da bata ɗago kanta ba tace "ina yini?" Hankalinsa duka a kanta ya amsa,kafin fuskarsa a ɗan sake sanin idan yayi magana da ita ba lallai ta amsa masa ba,ya kalli Baniynah yace "it seems like za ku je wani waje,right?" Baniynah ta gyaɗa masa kai tana kallon Muniba dake fidgeting fingers ɗinta,a hankali ya ɗan shafi fuskarsa yace "ok! Get in please,ina za muje?" Baniynah tace "za muje gida ne" yace "arghm! Babu matsala za mu iya tafiya muyi accompanying ɗinku?" Baniynah ta girgiza kai tace "yes! There's not" yace "ok! Thanks" da kansa ya sauko motar ya buɗe musu back seat,tsaiwa Muniba tayi ta ƙi shiga,ya tsaya kawai yana kallonta kafin ya buɗe baki yace "get in please,we will talk a can,ok? Don't let Hammad ya san something is happening tsakaninmu.. Please!!" Kamar baza ta ce komai ba sai kuma dai ta gyaɗa masa kai ta taho a hankali,yana sauke wani nauyayyar ajiyar zuciya yace "thanks" sanda ta shiga motar ya rufe kafin ya wuce ya shiga front,Hammad da tun zuwansu yake waya yana ajiye wayar hannunsa yace "Aunty'nmu barka da wannan lokaci" Muniba ta ɗago kanta kaɗan tana murmusawa tace "Yaa Hammad barka dai,ya Mom,sisters da aiki?" Yace "lafiyarsu lau alhmdllh" suka gaisa da Baniynah,kafin ya kalli Lieut Abuu Turab yace "where are we heading to?" Lieut yace "gidan Uncle" Hammad yace "alright!" Daga haka ya tada motar suka fice gidan.
*WAZEER*
Zaune yake office da wayarsa a hannunsa,kiran Safwa yake son yi tunda ya kunna wayar,sai ya ɗauka sai kuma ya tsaya yayi shiru yana tunanin me zai ce mata? Ya san bai kyauta ba,bai kirata ya sanar mata abunda ya faru ba,at least ya ci ya kira ya rarrasheta da kalaman da za su sanyaya mata rai,amma duk bai yi haka ba,ko even yaje ma duk ya kasa saboda fargabar abunda zai faru,tunanin abubuwa da yawa yake da suka cunkushe masa ƙwaƙwalwa,yana wannan yanayin ƙarar faɗowar text yasa shi dawowa hayyacinsa,kallon wayar da dama take hannunsa yayi,sunan Safwa da ya gani sanda yasa gabansa wani irin mummunar faɗuwa,a hankali ya danne ya buɗe ya shiga bin content ɗin da idanunsa da suke cikin eye glasses ɗinsa,ba kaɗan ba kalaman da yaci karo da su suka taɓa shi,suka girgiza ji da ganinsa,cikin wani irin yanayin tashin hankali ya miƙe tare da ɗaukan car keys ɗinsa ya fita,bai damu da yanayinsa ko shigar dake jikinsa ba ya fito office da wani irin sauri,yanzu kam yana jin ya samu dalilin da zai kaishi gidansu,munanan sunaye gami da kalaman da ta aiko masa sosai suka tada masa hankali,bare akai ga batun zagin da tayi masa wanda a tunaninsa ko da wani cikin iyayenta ya kashe a gaban idanunta,ya yi muni bare haka bai faru ba,to me yayi zafi? Wani zuciyar yace "kana da laifi Wazeer.. Me yasa baka kira ko kaje ka mata bayani ba? Maybe da ta fahimceka ta maka uzuri ai" tafiya yake yana alla² ya kai inda yake muradi,yana isowa carline ya buɗe motarsa ya shiga ya tada ya bar Company,kai tsaye daga industrial estate GRA ɗin su Safwa ya nufa,bai yi tunanin komai ba,bai kuma tuna kowa ba,even kansa bai tsaya dubawa ba yayi parking,yana zaune cikin motar ya ɗauki wayarsa ya shiga kiran line Safwa,sai dai ga mamakinsa har wayar ya katse ba'a ɗauka ba,ya sake kira no response,at least ya kirata ya kai 5 times,abunda bai taɓa yi ba a dukkanin tsayin rayuwarsa ya kira waya sama da sau 1,kira na ƙarshe yana kusa da yankewa Safwa ta amsa cikin gadara tace "mayaudari,macuci,kuma azzalumi me kake kirana kayi min?" Cikin wani calm murya da kalamanta suka ƙona yace "come out and throw it out,i think za ki fi iya faɗan whatever kike so when ga ni ga ki,i'm outside and waiting,just come out right now" yana faɗan haka ya katse wayar tare da lumshe idanunsa yana sauke numfashi da calming kansa.
*SAFWA*
In not less than 3 minutes Safwa ta fito gida cikin ɓacin rai,motar data gani tsaye ƙofar gidansu yasa ta ɗan yi jim,then kuma ta fito tana ɗan kalle²n inda za ta hangoshi,don ta san bai da arzikin hawa irin wannan tsadadden motar da ko su da suka fishi rufin asiri babu irinsa a gidansu,dai² lokacin kuma motar su Muniba ya shigo line,kallon motar Safwa ta dunga yi though bata san me ita ba ko su waye a ciki,tana tsaye gurin har motar yayi parking Muniba ta fara buɗewa ta sauko daga ciki fuskarta a sake da murmushi ta taho tana cewa "amarya da kanta a waje kuma? What are u doing here? Kada ƙurar gari ya ɓata mana ke fa,kin san yanzu kin shigo season na ɓoye kai.. Ko kuma dai kina neman wani ne?" Waro idanunta Safwa tayi sai kuma ta taho tana faɗin "amarya ko kuma amare? Cewa za kiyi ƙamshinku naji tun daga nesa shi yasa na kasa zama sai da na fito taranku" Muniba tayi dariya,Baniynah data sauko mota tace "ko kuma mu muka kasa zama ba daga jin labarin muka taso muzo Allah ya sanya alkhairi" Safwa tayi dariya tana rungume Muniba tace "awwnnn! I'm sorry Babes,kun samu labari kafin na kira na sanar muku" Muniba tace "kai haba babu komai wallahi" lokaci ɗaya Safwa ta manta da wani kiran da Aley yayi mata,ganinsu yasa kawai ta sake ta manta damuwarta da rashin mutuncin da tayi masa tanadi,Muniba na tsaye gaban Safwa fuskarta da murmushi akai kamar kowane lokaci tace "so how are u doing? Ya su Umma?" Safwa tace "mu shiga mana Umma suna nan lafiya" Muniba tace "alright! But tare muke da surukinki kuma" Safwa tayi ƴar dariya,abunda bai taɓa faruwa ba tun saninta da Lieut,tana kama hannun Muniba tace "ok! Muje idan mun gaisa da su sai mu shiga ciki" Muniba ta gyaɗa mata kai tace "ok!" Suna isowa gurin motar Lieut da ya sauke ƙafarsa ɗaya waje yana waya ya kalli Muniba,irin kallon nan na kana son yin magana akan abu amma kuma baka san me maganar naka zai zama ba,Muniba ta ɗan kalleshi suka haɗa ido,a hankali ta sakar masa murmushin da ya narkasa a gurin,sai dai bata ce komai ba ta jira ya gama maganar da yake,da sauri yace "ok! Hold on.. I will call you right back.." Yana faɗan haka ya katse kiran,fuskarsa sake duk da ba dariya yake ba,Safwa dake murmushin kissa tana kallonsa don a yanzu gani take ta fi ƙarfin tsaiwa tana feeling wani abu akan wani,tunda ta samu Hamood Waziri kawai troop ɗinta ya gama kama kurciya,cike da iyayi tace "barka da zuwa officer" ba shi ko Hammad ba hatta Baniynah sai da suka kalleta,kamar dai irin baƙon nan da bata sani ba,ko irin ƙananan constabulary ɗinnan sababbin shiga aikin force masu son yin suna da son a san aikin da suke,da yake shi ya fahimci inda ta nufa kawai ya gyaɗa mata kai yace "how are u doing Miss?" Safwa na dariyar rainin wayo tace "i'm good.. Ya aiki da ƙawata? Hope ana kula mana da ita yanda ya dace?" Yayi murmushi idanunsa har lokacin akan Muniba yace "alhmdllh.. Aikinta ya zama wajibi,u know sarauniyar mata dole sai da kulawa,da ace ina da dama even flies bazan bari su sauka jikin veil ɗinta ba saboda za su iya zuba mata wani ciwo,so amma tunda mun kama hanyar zama abu guda,i will take a good care of her,kin san na fi sonta da kaina" Safwa da kalamansa suka ƙona saboda ta san magana ya mayar mata tana ɗan fuskewa ta saki murmushin yaƙe tace "yeah! I can see.. Allah ya ƙara muku son juna" Lieut yayi wani tsadadden murmushi har dimples ɗinsa suna bayyana yace "ameen yaa hayyu yaa ƙayyum.. Ur du'a means everything to me,na gode sosai Miss" Safwa tace "ahhh! Ai ƙawata ta wuce komai a gurina" ya ɗan gyaɗa kansa yace "yeah! I can see" gaisawa Safwa sukai da Hammad,kafin a hankali Muniba dake gefen Lieut tace "Baby! Ka yima ƙawata Allah ya sanya alkhairi,yau an kawo gaisuwarta.." Lieut ya ɗan gyaɗa kai yana murmusawa yace "maa sha Allah,Allah ya sanya alkhairi ƙawarmu,rabbi yasa gidan zama ne" Safwa tace "ameen².. Thank u" Hammad ma yayi mata Allah ya sanya alkhairi kafin Lieut dake ta kallon Muniba yana mata magana da ido yace "so when are u coming out idan kun shiga ciki? Ko mu tafi sai mu dawo mu mayar da ku gida?" Girgiza kai tayi a ɗan shagwaɓe ta kumbura masa baki ta ƙi cewa komai,Lieut da yaga me tayi ya ɗan buɗe ido sosai yace "ok²! Ba sai kin min rigima ba,i will wait ok!?" Ta gyaɗa masa kai a hankali,Baniynah dake kallon dramarsu ta rufe baki tana dariya tace "Yayana ka ƙyaleta kawai,tana samun hira mantawa za tayi kana jiranta fa" Muniba ta watsa mata uwar harara tace "ai dake an faɗa miki kowa ma irinki ne me kafirin surutu" Baniynah tace "a'a kawai dai na ga ke ɗin musulmin surutu gareki,idan kin shiga kika sami hira baza ki manta ana jiranki ba,kuma tsakaninki da Allah ba gaskiya ma na faɗa ba? Muna shiga kika samu hira za ki tuna ne?" Safwa dake dariya tace "guy's wait.. Na san in ban zama midfielder ba baza kuyi shiru ba,yanzu muje dai ku gaisa da Umma sai ta dawo,ok?" Muniba ta harari Baniynah ita kuma tayi mata tongue out,shagwaɓe fuska tayi kamar za tayi kuka ta kalli Lieut tace "ka ganta ko?" Da sauri Lieut dake murmushin dramar su ya kalli Baniynah yana ɗan ɗaure fuskarsa yace "ƙanwata kina so mu samu matsala dake?" Da sauri Baniynah tace "haba Yayana ta ina zan so haka ta faru? Ai sai maƙiya su yi mana dariya" yace "ok! To ki bi min mata a hankali,kin san ba na son abunda zaisa ta ɓata rai ko yasa ta kuka,damuwa bai dace da kyakkyawar fuskarta ba" Baniynah tana masa salute cike da barkwanci tace "an gama Yayana,haka ba zai kuma faruwa ba" yace "thank u.." Yana kallon Muniba yayi ƙasa² da murya yana kwantar da kansa yace "she's sorry.. Baza ta sake ba daga yau,ok?" A hankali ta gyaɗa masa kai,yace "how many minutes za ki ɗauka idan kin shiga ciki kafin ki fito?" Tace "muna gaisawa da Umma" yace "ok! A fito lafiya,a gaida Umma ayi mata Allah ya sanya alkhairi" tace "zan sanar mata in sha Allah" hannun Muniba Safwa ta riƙo tace "shall we dearest?" Muniba ta gyaɗa mata kai tace "Mmmm!" Tana kallon Lieut kamar yanda yake yi ko gajiya babu tace "i'm coming Bee" a hankali ya lumshe mata idanu alamun babu komai,Safwa tayi musu sallama shi da Hammd da hankalinsa ke kan waya then suka wuce. A parlour sanda suka shigo suka tarar da Umma zaune tana hutawa,bata wani jima sosai da shigowa gidan ba ta ɗan shiga gidajen maƙota da suke mutunci sosai ta sanar musu kuɗin auren Safwa da aka kawo,Umma na amsa sallamar da suka yi tace "a'ahh! Muniba ku ne tafe da yammar nan?" Muniba dake tsugunawa jikin kujera kusa da Umma tace "wallahi kuwa Umma.. Ina yini?" Umma ta amsa "lafiya lau.. Ya gida da shirye²? Ya Dr?" Muniba tace "lafiya lau alhmdllh,ta ce a gaisheku,tana miki addu'ah da Allah ya sanya alkhairi kafin ta zo" Umma tace "Allah sarki! Ina amsawa,na gode ƙwarai,ai nima ina cewa zan je har gidan na sanar mata ko zuwa gobe" Muniba na ɗan murmusawa tace "Allah sarki.. Sai kuma muka ji abun alkhairi Umma?" Umma tace "wallahi fa,lokaci ya yi" Muniba tace "Allah ya sanya alkhairi ya tabbatar" Umma na ƴar dariya tace "ai ku za'a yiwa murna,mu ƴan tayi ne.. Allah dai ya baku sa'a ya zaunar da ku a gidajenku lafiya" Muniba tayi murmushi kawai ta kasa amsawa,wayarta da ya ɗan yi beeping ta kalla kafin ta tashi tana cewa "Babe! Bari na leƙa na dawo na bar mutane a waje suna jirana" Umma dake kallonta tana murmushi tace "ko dai tare da surukin nawa kuke ne?" Muniba tayi ɗan murmushi cikin ƴar kunyar data kamata tace "na fita Umma" Umma tace "toh shi kenan a gaisheshi,tunda bazai shigo mu gaisa ba" Muniba tayi waje da sauri cike da kunya. Hira Baniynah sukaita yi da Safwa,hakan kuma baisa Safwa ta tuna kiran da Aley yayi mata ba,har sai da Muniba ta shigo bayan Lieut sun tafi,wanda suka yi akan za su dawo ɗaukansu,zuwan dama bai shirya masa ba,dole ce tasa ya taso a lokacin,tana shigowa ta zauna suka ci gaba da hira da dariya har akai kiran maghreeb sukai sallah kafin tace ma Baniynah "Darling! Ki tashi muje mu gaida Mama kafin su dawo ɗaukanmu" Umma dake jinsu wani lokaci har tasa baki cikin hirar nasu tace "laaaaa! Dama baku je can gidan bane?" Safwa tace "zuwansu kenan muka haɗu a waje,ku tashi muje gidan na gaida Mama nima dai yau,na kwana biyu ban shiga ba,na san dai Mama will say Safwa dama kina nan? Wato saboda su Muniba basa nan shi yasa bazan ganki kin shigo min mu gaisa ba sai kinji sun zo ko?" Dariya dukansu suka yi har Umma dake cewa "ehh lallai kam ai ko nice Hjy Batoolu haka zan ce sai da kika gansu za ki shigo min? In ta kama ma ni nace ki fice min a gida ban nemeki ba" Safwa tace "wallahi dai ban kyauta ba nima na sani" Umma tace "to ku gaida gida Muniba,mun gode Allah ya bar zumunci" suka amsa Baniynah na cewa "laaa! Umma ina surukina yake kuwa?" Umma na dariya tace "suna islamiyya basu taso ba,kin san tunda akai masa prefect can suke sallar maghreeba sannan su dawo" Baniynah tace "Allah sarki! Ai Bilal akwai himma,Allah ya taya shi riƙo.. Idan ya shigo kice masa mun zo kuma zan dawo" Umma tace "to shi kenan zan faɗa masa" sukai mata sallama suka fita. A ƙofar gida sanda za su wuce suna magana Safwa ta kalli motar dake parke har lokacin a gurin,cikin tarin takaicin yadda aka ajiye motar daf² tace "wai motar waye wannan yazo ya ajiye shi a nan? Sai Baba ya dawo ya tarar da shi ne? To ta ina zai bi ya wuce da na shi motar?" Muniba suka kalli motar,Baniynah na cewa "ai kin san mutanenmu da neman rigima,ka san ba ƙofar gidanka bane sai kazo kawai kayi blocking hanya kayi tafiyarka ka hana masu gida sukuni" Muniba dai bata ce komai ba bayan "Allah ya kyauta" suka ce "ameen.."
*WAZEER*
Tunda yazo yake cikin mota zaune yana dakon fitowarta,kasancewar glasses ɗin motarsa was tinted yasa ba lallai kayi tsammanin da mutum a ciki ba,yana kallo ta tsaya dube²n ta inda yake,sai dai tuna cewar bai zo mata a siffar data bayyana shi ba wani bane ko ɗan wane,yasa shi sauke ajiyar zuciya,a hankali jikinsa cike da kasala ya kai hannu zai buɗe motar,sai dai bai kai ga saukowa ba yaga ta wuce ta nufi gurin motar da ya shigo line,yana kallo ta wuce gurin ƙawayenta da suka zo,tsaiwarsu a gurin da hirar da suka yi,har zuwa wucewarsu cikin gida duk akan idanunsa komai ya faru amma bai iya ya katsesu ba,wannan dalilin yasa ita ko su Muniba babu wanda ta kula da mutum a cikin motar,ko even Safwa tayi tunanin shi ne ko tuna ya kirata duk Allah bai sa ta yi ba. Yana zaune ya yi shiru yana tunanin lokacin da za su sake fitowa,sai dai shiru har akai kiran maghreeb ya fito yayi alwala ya shiga masallaci,sanda aka idar da sallah ya fito ya sake komawa cikin motarsa ya zauna,tsadadden wayarsa dake ajiye gefe ya kalla kafin yasa hannu ya ɗauka,yana ƙoƙarin kiranta ya sanar mata yana waje tun ɗazu yana jiranta aka buɗe gidan,su 3 ne dai yanzuma kamar yanda suka wuceshi ɗazu. Jikinsa a mugun mace ya buɗe motar a hankali ya sauko tare da rufewa,ƙaran buɗewa da rufe motar yasa Safwa juyawa saboda bata yi tsammanin da mutum a ciki ba,hoping and praying that bai ji maganar da sukai ba,sai dai me? Tana kallon fuskarsa ta waro idanunta waje,da mamaki a idanunta ta shiga jifansa da wani kallo mai cike da shock tace "Aley!" Sai kuma ta kalli motar da take ganinsa tsaye jikinta da irin kayan da yake sanye da su,kusan za ka iya ganin mamaki ƙarara shimfiɗe a fuskarta,Muniba da Baniynah da har sun ɗan yi gaba,jin Safwa ta ambaci sunan wanda basu san waye ba yasa su tsayawa tare da juyowa. Kallo ɗaya ya yiwa Muniba ya ɗauke idanunsa akanta,tun ɗazu da ya gansu ya ganeta,a hankali yana lumshe idanunsa ya furta "assalamu alaikum warahmatullah wabarkatuh!" Muniba da Baniynah suka haɗa baki gurin amsa masa "wa'alaikumus salaam warahmatullah wabarkatuh.." Ɗan gyara fuskarsa yayi zuwa yanayin kamewa da ɓoye damuwar da yake ciki,suka gaisa da su a mutunce kafin ya kalli Safwa data kafeshi da kallo tana cika yace "don Allah idan babu damuwa zan ga friend ɗinku na wasu minutes.." Baniynah tace "ohh! Babu damuwa,Babe sai kin shigo bari mu je" ba don Safwa na so ba ta gyaɗa musu kai tace "ok!" Baniynah sukai masa sallama shi kuma yayi musu godiya suka wuce suka barsu a gurin. Wani irin irritating kallo Safwa ke masa tana sauke numfashi kamar me tattaro dukkanin ɓacin ranta,damuwarta da fushin da take da shi,idanunsa a kanta zuciyarsa na bugawa da tambayarsa "me za kace Wazeer? Taya za ka iya kare kanka?" Tambayar da Safwa ta aiko masa ya katse masa hanzari "me ya kawoka kofar gidanmu?" Cikin ɗan ruɗewa ya furta "arghm! Safwa i am so sorry.." Ɗaga masa hannu tayi cikin sauri,da kausasasshen murya tace "what!? I should be sorry? Bayan ka yaudareni sannan ka kashe wayarka,yanzu kazo gidanmu ka rasa me za kace min sai in yi haƙuri? Da haƙurin ya mutu sadakar nawa ka bayar Aliyu? Ok! Fine,na ji in yi haƙuri what next?" Lumshe idanunsa yayi yana girgiza mata kai yace "i don't have intention of decieving u,ko in ɓata miki lokaci alhalin na san ba aurenki zan yi ba" a fusace tace "ka ga Malam don Allah idan iya wannan maganar ne ya kawoka na ji kuma na gode,amma ka sani baka cuceni ba wallahi,idanma ka yi min haka ne don ka wulaƙanta ni,ni a yanzu na fi ƙarfin ajinka,don Allah ya min gam da katar na samu miji,and ba da wani jimawa ba,in the next few couple of weeks zan yi aure,saboda haka idan ka tafi kada kayi tunanin dawowa rayuwata coz Allah ya musanya min da wanda ya fika komai a duniya da ɗiya mace za ta buƙata,he's not a dull kamar kai,babban mutum ne,and a wealthy irin dai wanda kowace ɗiya mace za tayi mafarkin samu.. So best of luck Aley,na gode sosai da Allah yasa na buɗe idanuna tun da wuri na saurari maganar mahiafiyata,da na dage akan sai kai,da yanzu ina nan ina cizon yatsa,koma na faɗa ramin da ba lallai na iya fitowa ba sai dai talauci da fatara su rufe min idanu.." Tana faɗan haka taja siririn tsaki tai gaba without ta tsaya ta saurari single word da zai fito bakinsa. Wani irin mamakinta ne ya gama kashe masa jiki da jiyoyi,maganganunta sosai suka sa harshensa yin nauyi ya rasa abun faɗa,yana kallo ta shige ta barshi tsaye a nan,abu ɗaya zuwa biyu da yake tunani a can ƙasan ransa kuma yake tambayar kansa shi ne,da gaske Safwa aure za tayi ko kuma ta faɗa masa haka ne saboda tana fushi da shi? Me ya faru da ita lokaci ɗaya yaga ta sauya? Shin ina soyayyarsa da yake gani a tare da ita? Al'amarin ya mugun ɗaure masa kai ya bashi matuƙar mamaki da tsoro,dama haka tana iya faruwa ka juyawa abunda kake so baya cikin ɗan ƙanƙanin lokaci? Ya jima a tsaye a nan yana saƙawa da warwara akan al'amarin,sanda aka fara kiran sallar ishaa kafin ya sauke nauyayyar ajiyar zuciya ya wuce tare da buɗe motarsa ya shiga yaja ya bar GRA ɗin.
*MUNIBA*
Ko da Safwa ta shigo ta samesu suna hira babu damuwar komai a fuskarta ta zauna suka gaisa da Mama,kamar dama Mama na jiran shigowarta,nan tai mata tatas akan rashin shigowar da bata yi sai in ta samu labarin su Muniba sun zo,Safwa da su Baniynah sai dariya suke ganin yanda Mama ta haƙiƙance ta ɓata rai,Muniba tace "Mama wallahi ba kya nan amma Allah'nki na nan,kafin mu shigo sai da ta faɗa itama da bakinta,har Umma tace in itace korata za tayi" Mama tayi ƴar dariya tace "ehh toh yanzu dai bazan koretan ba,zo ki zauna a kusa dani muyi shawara" Safwa ta zauna tana dariya tace "toh Mamana.." Mama tace "kawo kunnenki muyi sirri kada suji" Safwa ta matsar da kunnenta,Mama ta kama kunnen ta riƙe da kyau tace "ja'ira! Dama jira nake kizo mu yi ta dake a gidan nan,tun yaushe rabon da kizo min mu gaisa? Ehh?" Ƴar ƙara Safwa ta saki tace "i'm sorry Mama,Allah ban ƙara ƙin shigowa" Mama tace "alƙawari!" Safwa tace "ehh promise" Mama ta saketa tana faɗin "ai in baki zo bama zan kira Hjy Murja ta turo min ke,alhamdulillah mun ji abun alkhairi Allah yasa damu za'a yi" Safwa na dariya tace "kaiii Mama.. Kunyarki nake ji fa" Mama tace "auu! Yau ni ake jin kunya kuma? Tohhh ai shi kenan,yanzu yaushe za'a kawo min In-law ɗin nawa ya gaisheni?" Safwa tace "anytime soon Mama,idan bai zo ya gaisheku an sa masa albarka ba wa zai gaisar?" Mama tayi ɗan murmushi tace "toh Allah ya kawo shi lafiya" Safwa tace "ameen.." Kiran da ya shigo wayar Muniba yasa ta kalli Baniynah tace "darling get set za mu tafi ina jin sun taho" Baniynah tace "alright!" Muniba ta tashi ta wuce upstairs tana kai wayar kunnenta tace "assalamu alaikum warahmatullah wabarkatuh!" Lieut Abuu Turab ya amsa maganarsa can ƙasa yace "we are outside" Muniba ta ɗan fiddo idanunta kaɗan fuskarta na faɗaɗa da murmushi tace "ok! Amma da za muyi sallah ne fa,amma dai gamu nan fitowa" yace "ok! A gaisar da Mama" cikin wasa tace "ni bazan faɗa ba,sai dai ka shigo ka gaisar da ita da kanka" yace "ki sanar mata za mu shigo" tana buɗa idanunta tace "ni da wasa nake maka" yace "ni kuma da gaske nake,just come out ki rakamu" tana gyaɗa kanta tace "it's ok!" Yana katse kiran ta sauko da ɗan hanzarinta,Baniynah na miƙewa tsaye tace "Mama za mu tafi" Mama tace "toh ku gaida gida da Mamin naku" Muniba ta ɗauki veil ɗinta tana yafawa tace "Mama za su shigo ku gaisa wai" Mama tace "tohhh amma baki sanar min an yi musu wani abu ba kuma,sai dai su shigo haka?" Muniba tace "nima bai faɗa min ba sai yanzu" Mama tace "toh babu laifi" Muniba ta kalli Safwa dake waya tace "Babe bari na dawo muyi sallama" Safwa ta gyaɗa mata kai,tare Muniba suka fita da Baniynah,basu jima ba suka shigo tare da su Lieut dake ta zuba ƙamshi kamar sabon angon da bai jima da aure ba,a gurguje suka gaisa da Mama cikin mutunci da girmamawa,then suka yi mata sallama,Mama tai musu godiya sosai tare da addu'ar tsarewar Allah tunda ta ji maganar zai yi tafiya a daren,ya yi mata godiya tare da ajiye kuɗin da shi kansa bai san nawa bane yana bata haƙuri bai zo da shiri ba,Mama tana ta sa musu albarka,suna fita babu jimawa Mama ta tashi ta wuce kitchen,dambun naman kaji da chops da bata rabuwa da su da basu ci ba tayi packaging ta bawa Baniynah ta fitar musu da shi,Safwa na ganin za su tafi ta katse wayar da take tare da tashi,sukaiwa Mama sallama dukansu suka wuce.
*SAFWA*
Da safe bayan ta yi wanka though ba fita za tayi ba don ba ta da lectures yau,tana saukowa downstairs ta samu Baba tsaye suna magana da Umma,ɗan jim tayi a saman matakalar da take tana kallon cikin parlon,Umma tace "Engr baku aika fa an sanar musu an basu ba,kuma abunda suke jira kenan kafin suyi maganar tsayar da ranar biki,yanzu haka fa maganar da nake maka shi Hamood a son ransa ayi bikin nan da 2-4 weeks" Baba yana gyara zaman hannun rigarsa yace "yau za muje Fada in sha Allah mu sanar musu an basu" Umma ta saki wani murmushi tace "tohh amma ya kake ganin za'ayi idan suka zo da maganar bikin a gaggauce kamar na kawo kuɗin auren?" Baba ya sauke numfashi yace "zai yi wahala a barshi a yadda suka zo da shi,tunda dole sai mun yi shiri muma a namu ɓangaren,bayan haka ke kanki kin san ba wai na shirya aurar da Safwa bane yanzu,besides she's the only female child da Allah ya bamu,baza mu ɗauketa haka mu aurar da ita kai tsaye babu wani shirin da za muyi ba ko?" Umma tace "haka ne.. Amma ni sai nake ganin ko an bar shi a yanda suka sa babu abunda zai gagara,don in an ƙara ma ɗin abunda dai Allah ya tsaga rabonta shi za muyi mata,babu daɗi bare ragi" Baba yace "haka ne,amma ko can gida kin san idan mun yi magana da su za su buƙaci a ɗan ƙara lokacin" Umma ta ɗan taɓe baki kaɗan underneath tace "tohh Allah ya kaimu dai lafiya" Baba yace "ameen.. Tohh ni zan fita,akwai wani abu ne da babu?" Umma tace "a'a babu.. Sai dai ina son dama zuwa gidan Dr Aminatu na sanar mata zancen kawo kuɗin,amma sai can yamma nake jin ko ma bayan magreeba" Baba yace "toh Allah ya tsare hanya" tace "ameen.." Suna wucewa ita da Baba tayi masa rakiya bakin motarsa. Safwa na zaune parlour da wayarta a hannunta bayan Baba ya wuce,chat take da Radhiya tana sanar mata abunda ke shirin faruwa,sai ga kiran Hamood Waziri ya shigo mata,amsawa tayi tana sakin murmushin da ita kanta bata san na mene ne ba,cike da kissa suka gaisa tana kashe murya,yace "yau babu lectures right?" Ta gyaɗa kanta kamar tana gabansa tace "sure!" Yace "ok! Kina wani abu ne yanzu? I would like to talk to u,and magana ne me girma.." Girgiza kanta tayi tace "um'um! Babu abunda nake yi" yace "u know what?" Safwa tace "um'um sai idan ka sanar min" yana sakin murmushi yace "yanzun nan na samu saƙon kira daga Abba" Safwa tace "akan mene ne?" Yace "su Baba sun je fada sun sanar da Mai martaba sun bani ke,har an tsayar da aurenmu nan da 2 weeks in sha Allah" waro idanunta Safwa tayi cike da shock tace "whatt!?" Hamood ya saki murmushi yace "yessss! In the next couple of weeks za ki zama mata ta,mallakin Muhammad Aliyu Waziri.." Wani irin murna ne ya cika Safwa tace "amma Baba sun amince da bikin a haka?" Yace "in sha Allah.. Family'nmu ba'a sa mana rana da yawa,kawai lokacin biki ake yankewa" dogon numfashi Safwa ta sauke tana jinjina yanda aka yi Baba bai nemi a ƙara lokacin kamar yadda ya faɗawa Umma ba,Hamood yace "so maganar duk wani abu da shiri ta nan ɓangarenki ba sai su Baba sun sha wahala ba,na ɗauke musu komai,ke kaɗai kawai nake buƙatar su kawo min.. And i mean everything,saboda haka make a list na komai da kike so daga yanzun zuwa dare,zan zo yau in sha Allah sai mu ƙarasa tattauna maganar ko?" Safwa data rasa bakin magana saboda mamaki tace "ok²! In sha Allah" yace "so ki yi magana da Umma kuyi shawara kafin nazo,ok?" Da sauri ta gyaɗa kanta tace "tohh!" Yace "hope babu matsala?" Tace "babu" yace "kin tabbatar?" Ta sake gyaɗa masa kai tace "ehh" yace "ok! Akwai wani abu da zan aiko kafin nazo" ɗan jim tayi kafin tace "aiken mene ne?" Yayi murmushi yace "it's a little surprise.. Sai kin ji ni" yana faɗan haka bai jira ba ya katse kiran. Da kallo Safwa tabi wayar tana tunanin aiken mene ne Hamood Waziri zai mata? Ganin bai bata damar ta sani ba,sannan ga maganar da suka fara yi da yace tayi shawara da Umma and maganar na cinta,yasa da sauri ta bar tunanin da take ta tashi tana ƙwalawa Umma dake kitchen kira "Umma!!" Umma tace "ya aka yi? Ta samu ne?" Safwa na shigowa kitchen ta tsaya tace "kin san me ya faru kuwa Umma?" Umma tace "a'a sai kin faɗa" Safwa tace "duk ba wannan ba ma dai,albishirinki?" Umma tace "goro fari tas" Safwa tace "yanzun nan ya kirani yake sanar min Baba ya je fada ya faɗi sun bashi ni" Umma tayi murmushi tace "ehh na san zai je dama tunda mun yi maganar,sai dai bai sanar min da wuri zai je ba haka,thought ko sai can da yamma idan ya tashi a aiki" Safwa ta gyara tsaiwarta tace "kuma ya ce min ma wai an tsayar da ranar in the next coming couple of weeks" Umma tace "what? Sati nawa kenan?" Safwa tace "2 weeks yace.. And kuma kin san me yace?" Umma tace "toh bai sanar miki an ƙara ba?" Safwa ta girgiza mata kai tace "a'a bai ce min ba,sai dai maganar kayan da za ku min,da ya ce bai buƙatar ku wahalar da kanku da aljihunku,ni kawai yake so a kai masa" Umma tace "tohh! Ka ji masu yi da gaske,yanzu haka yace miki?" Safwa tace "wallahi haka yace,amma ni ina ganin duk don kada a ƙara lokacin ne,sannan idan akwai wani abu ya ce na sanar miki muyi shawara kafin yazo" Umma tace "toh bari na kammala abunda nake,sai muyi maganar a nutse zai fi" Safwa tace "tohh! Yanzu me zan iya taimaka miki da shi?" Umma tace "gyara min albasar nan ki yanka" Safwa ta amsa tare da ƙarasawa ta ɗauki albasar da Umma ta ajiye,tana fitowa tace "Umma ƙanana ko manya?" Umma tace "ke yanda kawai ki bani" Safwa tace "haka yayi?" Umma tace "ehh barshi haka,yi ki yanka mu gama da wuri sai mu samu lokaci sosai" Safwa tayi ƴar dariya kawai tace "amma ya ce zai zo yau fa" Umma tace "Allah ya kawoshi lafiya" Safwa ta amsa tana cewa "me ya kamata ayi masa toh?" Umma tace "nima na so na tambayeki babu ɗan wani abunda za ayi masa haka zai zo ƙamas?" Safwa tace "a'a za'a yi,me dame ya dace?" Umma ta shiga lissafa abunda take ganin zai yi. Sanda suka kammala suna fitowa kitchen Umma tace "ya kamata in kira Malama Gaaji ayi mana roƙon Allah,yanda aka sa ranar nan kada a ɗaga,sai zancen bikin yazo mana a yadda bamu yi zato ba,duk abunda mukai fatansa ya kasance haka ko ma fiye ko?" Safwa tayi dariya tace "ehh wallahi" Umma tace "muje kiga ke dai,ai ya kamata ma ace tun farko nayi tunanin nan na sanar mata ayi mana istihara aga idan akwai matsalar da zai taso ko ta nan ko can ɓangarensa,ba sai yanzu da magana ya gama yin nisa ba" Safwa ya tace "to ai ni na zata ma kinsa an yi shi yasa ban tambaya ba" Umma tace "uhumn! Ina kuwa sai dai yanzun ayi,ai sai mu godewa Allah ma da tunanin hakan yazo raina lokaci bai riga ya ƙure ba" Safwa tace "yawwa! Umma don Allah kice mata idan akwai abunda za ayi kome nace ina so ya yi min kawai zai amsa ne kamar uwar shi" Umma tace "a'a akwai mana.. Ai wannan ba wani abun wahala bane a gurinta,sha yanzu ne magani yanzu,bari na kirata sai ki mata magana da kanki" Safwa tace "tohhh! Ni in ta kama inje ma sai in tafi yanzun nan,kafin sanda zai zo in shirya komai ko?" Umma tace "haka ne.." Kiran Malama Gaaji Umma tayi suna gaisawa tace "Malama ya aiki da jama'a?" Malama Gaaji tace "Alhamdulillah Hjy Murja.. Ya yaran da rayuwa?" Umma tace "lafiyarsu lau wallahi" Malama Gaaji tace "maa sha Allah.." Umma tace "Malama dama na kiraki ne akan wani ɗan issue daya taso" Malama Gaaji tace "toh ina saurarenki" filla² Umma ta sanar mata komai,Malama Gaaji tace "Hjy Murja duk na ji bayaninki,kuma in sha Allahu na miki alƙawarin zan yi duk wani ƙoƙarin da zan iya akai naga na fitar dake kunya" Umma ta saki murmushi tace "na gode ƙwarai Malama,Allah ya saka da alkhairi ya ƙara hasken makaranta" Malama Gaaji ta amsa,sun yi maganganu sosai har da batun ɗaga bikin da ba ta so ayi kafin Umma tace "ga Safwa tana son magana da ke" Malama Gaaji tace "toh ina take ƴar tawa?" Safwa ta karɓi wayar tana ƴar dariya tace "hello Aunty ina kwana?" Malama Gaaji tace "lafiya lau Safwa,ya gida da shirye²?" Safwa tace "alhmdllh" Malama Gaaji tace "ya aka yi Ummanki ta ce kina da magana,akwai matsala ne?" Safwa na ɗan dai²ta muryarta tace "ehh Aunty" nan tayi mata bayanin komai har da maganar tsakaninta da Aley,Malama Gaaji tace "yanzu me kike so ayi masa?" Safwa tace "a rabani da shi Aunty,yaje can ya ƙarata tunda ni dai aure zan yi" Aunty Gaaji tace "haka ne.. To shi kenan,idan za ki iya zuwa ko zuwa da yamma kizo sai ki karɓi abubuwan da zan haɗa miki" Safwa tace "toh Aunty,na gode sosai.." Daga haka sukai sallama,tana katse wayar ta fasa wani uban ihun murna tace "wayyoo Allah ni Safwa,Allah ya kashe ya bani mijin wata" kamar zararriya ta waigo tace "Umma kin san irin kayan ɗakin da nake mafarki?" Umma tace "a'a" Safwa tace "dama can wallahi ba na son ƴan ƙasar nan,amma yanzu tunda Allah yasa ya min maganar zan faɗa masa" Umma na dariya tace "duk yadda kika so haka zai faru,matuƙar dai Malama Gaaji na nan a doron duniya kuma muna tare.." Safwa tace "Umma kin san me kuma?" Umma dai kallon ƴarta take da alfahari tana dariya cike da farin ciki tace "a'a sai kin faɗa min" Safwa tace "na daɗe ina mafarki da burin bikina sai an yi sati ana eventskuma wallahi sai anyi tunda Allah yasa na samu Hamood Waziri,bikina ba irin na kowa bane,sai an yi irin hidimar da ba'a taɓa yi ba a garin nan" Umma tace "za'ayi kam in sha Allahu,Allah dai ya ara mana nisan kwana" Safwa tace "uhumn!" Suka ci gaba da hirar su.
*HAMOOD WAZIRI*
Da dare after ishaa ya kamo hanyar gidan su Safwa,ka kalli yanda yake cikin farin ciki da giyar kuɗi dake fizgarsa,sam baza ka taɓa cewa ya haifi kamar Wazeer ba,jin daɗi gaba ɗaya ya ɓoye shekarunsa,idan ba ka sanshi ba za ka iya cewa bai fi Yayan Wazeer ba,zaune yake bayan toks range rover motarsa driver ɗinsa yana driving,abubuwa da yawa yake tunani kuma yake son zartar da hukunci akansu,ciki har da sauya gurin zama shi da iyalinsa,a yanzu ko muce a rayuwarsa bai son hayaniya sam,sannan a ganinsa ma Safwa bata dace da zama a family house ba,a matsayinta na ƙaramar yarinyar da baza ta wuce sa'ar ƴarsa ba sannan da tsananin son da yake mata akwai buƙatar ace an killace ta a guri daban,sai dai abu biyu da suke damunsa kuma yake zurfi cikin tunaninsu shi ne,ya ya su Abba za su ɗauki maganarsa? Shin za su amince ya bar zama cikin gidan ko a'a? Tunda Daada tace masa babu ruwanta da maganar aurensa ya yanke hukuncin nan,sai dai da wasa babu wanda ya sanarwa,shi dai yana ta shirinsa ne a gefe,a son ransa kuma sai lokaci ya yi daf sannan zai fito da maganar...
'''Alhamdulillah alaa kulli halin.. Cikin hukunci da ƙaddarawar Ubangiji gani na dawo da ƙarfina in sha Allah,ina sake bada haƙurin shirun da aka jini tsayin lokaci,yanzu za mu ci gaba daga inda muka tsaya,masu tambayar cigaban MAƘUNSHIN GISHIRI! Kuyi haƙuri³ a yanzu bazan iya muku alƙawarin samunsa ba,har sai Allah ya kaimu mun kammala littafin WAZEER,dama shi muke yi muka ajiye muka faɗa gasa,so alhamdulillah komai ya zama tarihi in sha Allah,saboda haka yanzu mun dawo gidanmu na tsamiya.. Sannan don Allah ina cigiya,idan akwai wanda Allah yasa take/yake da littafin WAZEER pages ba document ba,ya taimaka ya turo min shi ta wannan account ɗin *** ko nan *** Na gode.'''
#Follow
#Comment
#Vote
#Share fisabilillah!
#ASLI-SMASHER.