Chapter 2
*PAGE2️⃣*
Tunda motar mu ta ɗauki hanya, bamu tsaya ba sai a garin Mina sakamakon lokacin sallah da ya yi. Bayan munyi sallah muka ci abinci a wani haɗaɗɗen Hotel, duk yadda naso noƙewa bisa dole na sake naci abincin, dan bana mantawa rabona da abinci tun daren jiya bayan dawowar mu daga walima.
Yanzu na ji nayi kamar zan faɗi, da ya ke su ma sun zo da mata ƴan daukar amarya su biyu.
Ɗayar wadda tafi kama da Al'amen ce ta lura dani, ta matso kujerar da muke kai tawa Aunty Zulai maganar a sa naci wani abu,
Shi yasa har na iya ci ɗin.
Ban san Al'amen a ido na ba tun bayan ɗaurin auren, sai da muka zo komawa mota zamu cigaba da tafiya.
Daidai lokacin da Aunty Zulai ta kama hannuna ta buɗe motar, ɗagowar da nayi idanuna ya faɗa nashi.
Sanye ya ke ciki shadda sky blue, sai hular da ya sa wadda tayi daidai da kalar kayan.
Muna haɗa ido ya washe min baki, tare da ɗage min gira harda wani kashe min ido.
Da sauri na kauda kaina, zuciyata cikin wani irin Yanayi, madadin ya burgeni sai naji kamar raina na son ɓaci.
Bayan mun zauna Aunty Zulai ta rufe motar, sai na runtse idanuna a hankali, ina tariyo yadda Al'amen ya ke min a duk lokacin da muka haɗa ido.
Shi yana yi ne dan ya burge ni, Ni kuma bai fahimci hakan ɓata min rai ya ke ba. Shi tashi salon soyayyar kenan?na tambayi kaina.
A zuciyata na bawa kaina da kaina amsa, Eh haka ya iya, tunda tun haɗuwar mu ban taɓa ganin sabon abu daga gare shi ba, bayan ina son ki Rahamah, zan aure ki zaki zauna dani Rahamah? Sai kuma in mun haɗa ido ya kashe min ido, ko ya washe min baki, ko kuma ya ɗage min gira irin ta ƴan duniyar nan.
Badan ya samu kyakkyawar shaida daga bakunan mutane ba, sannan bai taɓa furta min wata kalma mara kyau ba tun haɗuwar mu, tabbas da na sashi a wani bigire na daban.
Daga wani ɓangare na zuciyata yace _Ki masa uzuri, in kika duba shi ba yaro bane, wataƙil yawan shekarun sa zai sa ya yi tunanin haka shike burge ku ƴammatan zamani._
Ji nayi nayi na'am da wannan batu na zuciyata, a hankali na maida kaina na jingina da jikin kujerar motar, na faɗa duniyar tunani.
Sai na fara wassafa
kamannin Al'amen.
Al'amen Muhammad kenan, kuma mijina.
A ƙalla zai iya kaiwa shekaru arba'in da takwas zuwa da tara, Kakkaura ne yana da tsayi da jiki, dan harda wani uban tumbi a gaban sa, wanda har yau nake yawan tambayar kaina dama zan iya auren miji mai tumbi? Banda amsar tambayar, tunda gashi har na aure shi za'a kaini gidan sa.
Sai dai a sanina tun tasowa ta, bana shiri da mutum mai tumbi kwata kwata namiji mai tumbi ko mai ƙiba baya taɓa burgeni, sai gashi cikin hukuncin Ubangiji yau Ni Rahamah na auri namiji mai ƙiba har ma da tumbi.
Lamarin Allah kenan, babu yadda baya juya lamarin sa.
Al'amen Muhammad ba wani Kyakykyawa bane, babu laifi yana da ɗan kyansa dai-dai yadda ba za'a sashi a layin munana ba, fuskar shi nada faɗi da tsayi, yana da hancin shi tubarkallah Masha Allah ɗan madaidaici, kasan hancin ɗauke ya ke da bakin mai faɗi da kaurin la'bɓa, yana da saje da gemun sa wanda bai cika yawa ba, sai furfura kaɗan kaɗan data fara fitowa.
Yana da ɗan hasken fata, ba za'a sashi a layin farare ba, haka ba za'a sa shi a layin baƙaƙen ba.
Duka da haɗuwa ta dashi da auren mu, bai fi sati Uku ba. A sati na huɗun ne aka ɗaura auren mu dashi.
Bana manta farkon haɗuwar mu dashi, na kai ziyara wajen Aunty Fati Yayata daga Kaduna, zuwa wajen ta Lagos.
Ranar ta aike ni kasuwa na amso mata saƙo wajen Abban Mubarak, mijin ta kenan.
Bayan na dawo ne, dai-dai lokacin da mashin ya sauke ni a bakin get, ina ƙoƙarin ƙwank'wasa ƙofar dan a buɗe min.
Shi kuma Al'amen ya sawo kan motar shi, da niyar shiga nasu gidan.
Ganina yasa ya dakata, ya buɗe motar ya fito ya nufo inda nake.
Dai-dai lokacin har an buɗe min ƙofar ina shirin shiga, jin anmin magana ana faɗin "Ƴammata. Hakan yasa na juyo, nayi tozali dashi cikin shigar farar shadda irin ɗin kin babbar rigar nan, daga kallon farko naji sam bai min ba, in ba ƙarya idanuna suka min ba, zai iya haifar kamata, saboda duka na banfi shekara ashirin ba.
Cikin raina nake faɗin _Shi kuma wannan bai duba shekarun sa ba, ya ke wani kirana da ƴammatan._ ina mai Allah wadai da hali irin na wasu mazan, nayi shigewata na ƙyale shi.
Ina jin yana magana da Sani me gadin su Aunty Fati, bansan ya suka ƙare ba na shiga farlon Aunty Fati ina mita.
Aunty Fati dake gyaran farce, ta ɗago ta kalle ni tace "Ke kuma dawa kike faɗa haka?."
Tsaki naja na shiga ƙoƙarin aje ledar hannuna, ina faɗin "Wani tsoho ne ya biyo ni, kai duk farin gashi amma tsabar son zuciya, shine harda wani ce min ƴammata, bayan nasan a haife ya haifi kamata."
Dariya Aunty Fati tayi tace "Kar kiga laifin sa, yaga ƴar duma-duma ne shi yasa, ki ka sani ko shine mijin, tunda anyi anyi dake ki fito da miji kin ƙi."
Haushi naji, cikin ɗan ɓata rai nace "Allah ya kiyaye ke kin ganshi, har da wani uban tumbin fa."
Cigaba tayi da jana da wasa, har sai da nayi fushi taga raina ya ɓaci, ina shirin sakar mata kuka sannan ta ƙyale ni.
Kamar da wasa da dare, sai ga Sani me gadi ya zo ƙofar farlon Aunty Fati, wai ana sallama da Rahamah.
Cikin mamakin wake sallama na kalli Aunty Fati, sai naga tayi murmushi ta kalli malam Sani tace "Wake kiran ta?."
Washe baki ya yi yana wani irin sosa kai yace "Hajiya ai ba wani ke kiran ta ba, sai Jagaba."
Da sauri naga Aunty Fati ta zabura, ta kalle shi da sauri tace "Ka je kace gata nan zuwa."
Ganin ya juya ya tafi, na kalle ta ina ɓata rai nace "Me yasa kika ce ina zuwa?."
"Dallah tashi ki je, ke kinsan waye Jagaba kuwa?."
Ba tare da damuwar komai ba nace "Ban sani ba, waye shi kuma a ina ya ke?."
"Dallah ta shi ki je, in kin dawo zan miki bayani, fatana Allah ya tabbatar mana da alkhairin sa."
Duk yadda naso na kaucewa zuwan, bisa dole Aunty Fati ta tilasta min fitar, haka nasa Hijabina cikin k'uncin na fita.
Koda na fita bakin get na tarda mota, ganin banga kowa ba yasa na juya dan komawa ciki.
Gani nayi an buɗe ƙofar motar an fito, cikin mamaki nake kallon mutumin. Wannan dai na ɗazun nan ne daya tsaida ni.
Ji nayi raina ya ɓaci, na daure na amsa sallamar shi, ganin har ya ƙaraso wajena.
Cewa ya yi na shiga motar muyi magana, nace masa bana shiga motar mutane, ya faɗi komai zai faɗa anan.
Haka ya shiga min bayanin kansa, shi ɗane ga maƙocin su Aunty, ya ganni ya ga na masa a matsayin matar aure da sauran duk bayanai dai.
Jin shi kawai nake, sai dai abinda ya girgiza ni jin cewa da ya yi bai taɓa aure ba, cikin mamaki nake kallon shi, sam na kasa yarda ace mutum kamar wannan wai bai taɓa aure ba.
Shima dariya ya yi ganin ina kallon shi, ya gyara tsayuwar shi yace "Zan faɗa miki dalili amma sai nan gaba, nasan kin shiga kokonto yanzu ko?."
Danne mamaki na nayi nace "A'a" dan Allah-Allah nake na tafi, yoh Ni ina ma zan bari mu ƙara haɗuwa, da har zai wani ce zai min bayani.
Haka ya ƙaraci surutun shi, da nagaji nace zan shiga gida. Yace Sai na faɗa masa ya min ko kuwa? Dan Allah in faɗa.
Ganin yana shirin ɓata min lokaci, gashi tsaiwar duk ta gundure ni, sai kawai nace masa "Eh" dan ya ƙyale ni.
Koda na juya zan tafi, haka ya zaro kuɗi, damin ƴan dubu guda, wato dubu ɗari kenan, ya miƙo min wai na amsa.
Zagaye shi nayi na tafi abina, ko juyowa banyi ba duk irin kiran da ya ke min, a zuciyata ina cewa _Haka kawai ya wani bani kuɗi, ko ance masa kuɗi nake so._
Koda na koma cikin farin ciki, Aunty Fati ta shiga bani labari akan shi.
Wai ɗan maƙocin su ne, mahaifin sa mai kuɗi ne, yana da mata huɗu ɗaya ce kawai bahaushiya sauran duk yarabawa ne.
Mahaifiyar Al'amen ita ce babba, shine ɗan ta na biyu.
Suna da arziƙi sosai dan shi Al'amen ma ana zaton ya gado mahaifin sa ne a dukiya, dan duk yafi sauran kuɗi waye-waye, duk dai ta dinga koɗa shi.
Harda cewa yana da kirki, ga kyauta kowacce rana cikin rabawa mabuƙata kuɗi da abinci ya ke, yana da mu'amala me kyau tsakanin sa da mutane.
Kowa na yaba kyawawan halayen sa, aure ne dai bai yi ba har yanzu, sakamakon duk yarinyar da ya nema sai an ci kuɗin sa, daga baya a hana shi auren ta.
Ya daɗe yana neman matar aure, har addu'a ake masa a masallatan unguwar akan Allah ya bashi mace ta gari, saboda yadda ya ke kai taimako makarantu da masallatai.
Duk maganganun ta, iya inda tace yana taimakon
Mabuƙata ne kawai ya burgeni, har ma na ɗan ji tausayin sa akan rashin auren da aka ce ba'a bashi.
Tashi nayi na nufi ɗakin dake farlon, wanda anan na sauka nace "Allah ya bashi mace ta gari Aunty."
Sallamar Sani me gadi dana ji yana faɗin "Ga saƙo ance a bawa Rahamah, ita ta dakatar dani daga shiga ɗakin.
Na juya na kalli Aunty Fati wadda idanun ta ke kallon ƙofar farlon.
Kuɗin dai dana ƙi amsa, shine ya bawa sani ya biyo ni da shi.
Ita kanta Aunty Fati na fahimci bata so ya aiko kuɗin ba, dan haka na cewa Malam Sani ya maida yace an gode.
Kafin ma ya dawo na rufe ƙofar farlon, dan bana son damuwa, dama mijin Aunty Fati baya gari, yaranta kuma sun je gidan ƙanin mijinta hutu.
Washe gari sai ga shi ya zo, ƙiri-ƙiri naƙi fita.
Aunty Fati ganin bana son lamari, dole ta haƙura da tilasta min ɗin da take akan fitar.
Kwana biyu tsakani na shirya na koma Kaduna gida, dan dama sati biyu nayi niyar yi mata kuma nayi.
Komawata gida da sati ɗaya, wata ranar juma'a ina zaune ina wa Mama Hajara tsifa, naga ana kirana da baƙuwar number.
Ina ɗagawa na gane Muryar me maganar, dan yana da irin saurin maganar nan.
Mutumin dai da na baro a Lagos ne, sai da nayi dana sanin ɗaga kiran.
Wallahi dana san shine ba zan ɗauka ba.
Ce min ya yi zai shigo Kaduna satin nan, yana son zuwa Kano sarin wasu kaya, in na bashi dama zai zo ya ganni ya gaida su Abbannmu.
Kai tsaye nace bana so, ya riƙe gaisuwar shi Nagode sosai.
Mama Hajara da taji abinda nace ne, bayan na yanke wayar. Ta shiga tambayata waye ya kira yace zai zo nace Ban yarda ba? Dan sun san halina na ƙin kula samari duk da na wuce ace ina hakan.
Ƙarya ba halina bace, dan haka na bata labarin komai. Cikin sanyin ta tace "Ki bari ya zo ku gaisa mana, gaisuwa ai ba komai bace Rahamah.
Me son ka shi ne kaɗai zai damu da kai, har ya so ganin ka haka."
Bamu gama magana ba, sai ga wani kiran nashi ya shigo. Bisa dole na ɗauki kiran, maganar ce dai ta zai zo wai akwai wani kaya da ya ke so ya siya a Kano, in yana zuwa zai sauka a Kaduna mu gaisa sai ya wuce, da dai sauran surutun sa.
Gudun Mama Hajara ta yi fushi nace Allah ya kawo shi lafiya.
Wallahi na manta da munyi magana da shi, bayan kwana biyu sai ga kira a wayata wai in faɗa masa sunan unguwar mu, gashi yana cikin garin Kaduna.
Kuma in sanarwa da su Abba zai zo ya gaida su, sosai na kaɗu da jin batun sa.
Taya zan cewa su Abba zan yi baƙi zasu gaida shi, bayan ƙa'idar gidan mu yarinya bata tsayawa sa saurayi sai da izinin mahaifanmu.
Kuma Ni ba son shi nake ba, bare nace wai ko zai zo ne saboda ni ɗin.
Dan haka sai nace masa, ba sai ya gaida su Abba ba ni zan fito mu gaisa, duk da nasan hakan laifi ne a gidan mu .
Amma a ganina gwara hakan, in yaso faɗa kawai za'a min Shikenan an wuce wajen.
Cewa ya yi shikenan, na kwatanta masa unguwar tamu kawai.
Haka na faɗa masa sunan, na shirya na nufi gidan Aunty Baraka matar Yayan ƙawata Binta, dan akwai wata walima da zamu je da yamma, ina son na kai mata Hijabina ta goge min tunda mu wutar gidanmu ta samu matsala.
Kwata-kwata na manta da wani batun Al'amen tun da naje na samu fira,wayata ma na cikin jakata kuma na sata a silent, munfi awa biyu muna shan firar mu da ita, ita ta rako ni har wajen ƙofar gidan mu sannan ta koma, ina ce mata in na shirya zan kirata a waya.
Sai da na na zo shiga gida, ganin baƙin motoci ya tuna min da maganar Al'amen.
Hannu nasa na ɗan dafe kaina ina faɗin "Kash nama manta da mutumin nan."
Nasa hannu a jakata tare da ciro wayata, ganin miss call nayi rututu sun fi ashirin, kuma duk shi ya kira ni.
Tsaki naja na tura k'yauren gidan mu na shiga, tun daga bakin zauren na fahimci gidan namu akwai baƙi.
Dan ƙofar farlon Abbanmu takalma ne na maza da yawa.
Zagayawa nayi ta bayan ɗakin Abban dan shiga ainahin cikin gidan, dan bana son wucewa ta gaban farlon dan sai an ganni.
Ganin mutanen gidanmu nayi kusan baki ɗaya a farlon Mama Hajara, cikin mamaki naga gaba ɗaya ni suke kallo.
Na cire hijabina na zauna kusa da Aminatu ƙanwata, ina faɗin "Lafiya naga duk kun taru anan?."
Ummi ce tayi caraf tace "Ba dole ki ganmu anan zaune ba, tunda kin bamu mamaki Aunty Rahamah, Ashe dai tuni ke kin yi miji abinki na nunawa Sa'a."
Da sauri Mama Hajara ta kai hannu ta doke bakin ta, cikin zare mata ido tace "An tambaye ki rasai? Dan ƙaniyar ki tashi ki bawa mutane waje."
Sum-sum ta tashi hannun ta dafe da bakinta, ta fita daga farlon.
Kaina ne ya ɗaure baki ɗaya, dan haka na kasa daurewa na kalli Mama Hajara da ke magana da Ummanmu ƙasa-ƙasa nace "Wai Mama ban gane ba, baƙi muka yi a gidan ne yau?."
Yakubu ne da ya sawo kai ɗakin, ya bani amsa "Ki ji yarinyar nan da rainin hankali, tambaya ki ke baƙi aka yi bayan ke kika turo su?."
Amminmu ce tace "Barta ina ga yanzun ma raina mana hankali za ta yi."
Gaba ɗaya sun ɗaure min kai da maganganun su. Sai daga baya nake ji wai ashe Al'amen ne ya zo harda wasu manyan mutane, wai Ni na turo su sun zo da shirin komai harda sadaki ya shirya aure na.
Mun riga da mun yi magana da shi tuni.
Sosai na kaɗu da jin batun, na rasa me zance musu sai kuka dana fashe da shi, ina rantsuwar wallahi bani na turo shi ba, cewa ya yi kawai zamu gaisa nace ya zo.
Duk irin yadda na so su fahimce ni, sun ƙi fahimta ta.
Bayan tafiyar su Al'amen ɗin ne Abba da Baba Usman suka kira ni suma.
Nasha faɗa sosai kafin ma su faɗa min Maƙasudin kiran nawa, nan suka maimaita min abinda su Ammi suka ce min, na Al'amen ya ce mun gama magana tuni. Ni na bashi izinin ya zo ya nemi aurena, in da Baba Usman ya hau faɗa a ina aka taɓa haka, kai tsaye a zo neman aure.
Amma tunda Ni na turo shi da kaina, su sun ce ya basu kwana biyu za su yi bincike akan shi, tunda abin ya zo da sauƙi ance maƙocin su Aunty Fati ne.
In yaso sai su bashi auren nawa, tunda dama sunyi-sunyi dani akan na fito da miji naƙi ina musu yawo da hankali.
Na fuskanci abin ya ɓata ran Abbanmu sosai, na zuwan Al'amen kai tsaye.
Hankalina ya matuƙar tashi da wannan batun, Allah ya sani ban sa a raina zan yi aure kusa ba, ga kuma wannan mutumin me tulelen ciki da ya zo ya haɗa Ni da iyayena.
Kwana nayi kuka zuciyata cike da k'uncin, wayar Aunty Fati ce ta tashe ni daga barci.
Cikin magagin barci na ɗaga. Nan ta hauni da faɗa akan na munafunce ta ashe ina son Al'amen har mun gama shirya komai, gashi har ya zo Kaduna neman aurena, shine ko na faɗa mata tsabar gulma na nuna bana son shi. Su Abba ne suka kira ta da mijin ta jiya da dare, suka ce a musu bincike akan halayen Al'amen da yadda ya ke gudanar da mu'amalar sa da jama'a, da duk wani bincike da ya kamata ayi kafin a bada aure.
Sosai maganar ta bugeni, ya tabbata dai mutumin nan ya ɗaure ni da jijiyoyin jikina, ta ko'ina ya gama sawa sun yarda Ni na tura shi neman aurena.
Duk yadda naso nawa Aunty Fati bayani, ƙin yarda ta yi da batuna.
Ga shi shegen duk kiran da nake masa yaƙi ɗauka kwata-kwata, ina son tambayar shi yaushe muka yi haka da shi ne kawai, sannan na roƙe shi ya janye maganar aurena ni bana son shi.
Sai da aka shafe kwana uku a gidan mu, ina ƙoƙarin wajen ganin na fahimtar da su bani na turo shi ba. Amma kowa cewa ya ke na sani, tunda Aunty Fati ta bada shaidar na san shi, kuma ita bata san yadda aka muka shirya junan mu ba.
Ganin na tashi hankalina, yasa Baba Usman cewa in har da gaske bana son shi, kuma bani na turo shi ba, to na fito da wanda na ke so kafin su gama bincike akan shi. Su kuma zasu fasa bashi ni, dan sun gaji Da yadda nake musu wasa da hankali akan fito da miji, gashi har Ummi da Aminatu sun kusa taddo ni ban fito da miji ba.
Hankalina ya tashi, saboda ban da wani tsayayyen saurayi, ba kuma dan banda samarin bane.
Ina da masu sona sosai, amma ban bawa Kowa damar zuwa gidan mu ba, saboda nasan in har aka bawa mutum izinin zuwa zance wajen mace, to fa in aka yi bincike aka tabbatar dana kirki ne, ƙa'idar gidanmu ba bu ke babu tsayawa da wani muddin shi wannan ya shirya auren ki.
Ina ji ina gani aka ce an gama bincike akan Al'amen, an kuma tabbatar mutumin kirki ne zai riƙe ni amana.
Cikin binciken harda wasu kyawawan halayen daban waɗanda Aunty Fati bata faɗa min su ba.
Ni dai ina jin yadda ƴan gidanmu ke koɗa mutumcin Al'amen ɗin, harda masu cewa zai riƙe ni amana, tunda bai taɓa aure ba dama da dai sauran su.
Ina ji ina gani, aka tsaida ranar auren mu sati biyu, kamar yadda ya buƙata.
Har mamaki na dinga yi sai kace wanda ya asirce iyayena da dangina, dan kowa ya bon shi ya ke babu wanda na ji yace ya min tsufa ko duba lamarina, akan cewar da nayi bana son shi.
Bisa dole na rungumi hakan a matsayin biyayya ga iyayena, tunda banda hanyar bijirewa auren tunda har sun amshi sadaki, dan dangin sa dake Lagos su suka zo neman aurena.
Ina jin yadda ake yaba karamcin su da mutumcin su.
Haka aka shiga shirye-shiryen aurena, sai da auren ya rage sati ɗaya Sannan Al'amen ya bari muka haɗu.
Na shirya in na ganshi sai na ci masa mutumci.
Sai dai abin mamaki muna haɗa ido na nemi kowacce kalma a bakina na rasa, Wallahi ban iya masa ko tari ba da sunan rashin kunya.
Sai dai ina jin wani zafi a ƙasan raina, ina jin kamar tsaiwar da nayi wajen shi ma tilasta ni aka yi.
Haka ya ƙaraci maganganun sa yana wani kashe min ido, wanda ya cika shi da wani uban kwalli kamar irin tsohon ɗan duniyar nan.
Cikin jin haushi na koma cikin gida, bayan shiga ta sai ga shi an aiko manyan ledoji cike da kayan maƙulashe, da su turaruka da kayan kwalliya wai yace a bani.
Ni dai ina zaune, ƙannene suka dinga ɗaga kayan suna santin kyansu, kayan ƙwalamar suna ta watandar su ina zaune ko kallo basu ishe ni ba.
A haka har ranar auren ta zo aka ɗaura auren mu. Wannan shine ainahin abinda ya faru.
***
*_DAWOWA LABARI._*
Bamu shiga garin Lagos ba, sai wajen ƙarfe biyu da rabi na dare.
Kai tsaye muka wuce ainahin family hause ɗin su Al'amen kamar yadda aka tsara, an ce anan zamu zauna na kwana biyu. Daga baya zamu koma ainahin gidan shi Al'amen ɗin dake can wata unguwa daban.
Tunda motar mu ta tsaya a farfajiyar gidan, wajen gaba ɗaya ya cika da hayaniyar mutane ta ko'ina, babu mai cewa dare ya yi sakamakon hasken da ya cika harabar gidan.
Maganganun jama'a ke tashi na Barka da zuwa, wasu da Hausa wasu da Yaren yarabanci kowa na faɗin Barka da zuwa amaryar mu.
Da ƙyar suka bari aka fito dani daga mota, saboda yadda wajen ya cika kowa na faɗin yana so yaga amaryar Jagaba.
Muna fitowa naji wajen ya cika da hayaniya da tashin guɗa, naji an fara min feshin turare ta ko'ina.
Ba tare da nasan waye mai fesa min ɗin ba, hannun Aunty Zulai na ƙara damƙewa, na kwantar da kaina a jikin Umma Safiya tare da rufe fuskata gudun kar su fesa min turaren a ido.
A haka har muka shiga wani ƙaton farlo, wanda daga shigar mu sanyin AC ya mamaye jikina har wani sanyi sanyi nake ji.
Ba zan iya tantance mutanen dake farlon ba, sakamakon fuskata dake rufe, amma tabbas farlon a cike ya ke da jama'a masu yawa har bakin ƙofa.
Zaunar dani suka yi gaban wasu mutane, waɗanda ban tantance su waye ba, sai da naji an dafa kaina ana min addu'a cikin Yaren Yarabanci.
Mace ce me addu'ar, sauran na amsawa da Amen.
Ɗaya bayan ɗaya suka dinga min addu'a, wasu su rungume Ni, wasu su dafa kaina duk da sunan sa albarka.
Gaba ɗaya ji na nayi cikin wata sabuwar duniya ta daban, dan duk wannan abin ba al'adar mu bace ban taɓa ganin. Irin hakan ba.
Daga nan bayan sun gama min duk wasu addu'o'in su, haka aka dinga bi dani sashi zuwa sashi, wai ashe wajen kishiyoyin maman sane.
Ta farkon ita ce mamar sa da ƴan uwan ta.
Ta ƙarshen da aka kaini wajen ta ce, naji hankalina yafi kwanciya da ita, dan Hausa naji ta mana kuma cikin nutsuwa ta tarbe mu.
Da wasu dake farlon nata da suma na ji suna Hausar.
Daga nan sai farlon mahaifin sa, in da shima albarka yasa da addu'a.
Da muka fito aka wuce dani sashin da aka ce nan zan zauna kafin mu koma namu gidan.
Babban sashi ne, me ɗauke da ɗakuna biyu, da toilet ɗaya a farlo kowanne ɗaki da nashi, kuma duk wasu kaya na amfani akwai a ciki kama daga gado da sauran kayan amfani.
Haka aka cika mu da kayan ciye-ciye kala-kala.
Ni dai ina kallon yadda su Binta da Ummi ƙawata, da su Aunty Fati suka dinga cin abincin su.
Ban iya ko kallon abincin ba, haka bayan sun gama suka dinga rige-rigen shiga wanka.
Kowa na son huta gajiya kafin asuba.
Ina naɗe akan gadon, zuciyata cike da tunani kala-kala, ina ganin komai kamar a mafarki.
Sai na ji wayata na ƙara.
A hankali na duba sunan mai kiran (Al'amen) na gani kamar yadda nayi sv ɗin number.
Kamar ba zan ɗauka ba ganin ƙarfe uku harda minti ashirin na dare,sai kuma na ɗauka tare da yin shiru ina sauraren sa.
Daga can naji Muryar shi "Rahamah ki fito ina bakin ƙofar farlo mu wuce sashina mu kwanta."
Shine kawai abinda kunnuwana suka jiye min.