BAƘAR ZUCIYA!.

Chapter 6

by @mamananalbarkace777

    *PAGE6️⃣*

 A Hankali nake bin su da kallo dukan su, ina sauraren bayanin da mutumin da ya kira kan shi da Malam ya ke.

"Kina jina Amarya. Yanzu tunda kin riga da kin ɓata mana cikin rashin sani, ki tashi ki yi alwala ki zo ki yi sallar a gaban mu, dan karki yi kuskure komai zai yi daidai."

Jinjina kai Al'amen ya yi, ya kalle ni ganin ban motsa ba har lokacin. Ya kama hannaye na duka biyun, yana bin fuskata da kallo cikin son na kalle shi yace "Rahamah ki tashi ki je ki yi alwala ki zo ki yi sallar kin ji."

Kauda kaina nayi ba tare dana kalle shi ba, so nake na buɗe baki na na ci musu mutumci, na faɗa musu su ji tsoron Allah amma na kasa hakan. 
 Bana jin duk abinda zai faru, zasu iya rinjayata na biye musu na aikata shirka, dan ni iya fahimta ta kenan shirka Al'amen ya ke aikatawa saboda neman duniya.

Cigaba ya yi da magana cikin lallashina "Rahamatah ki tashi ki je Please, ko ba kya son ki cigaba da more rayuwa ne?."

Yi nayi kamar ba da ni ya ke magana ba, a zuciyata nace _More rayuwa a ina? Mugu kawai cutar da rayuwa dai._
Daga ƙarshe da naga sun min rubdugu akan na tashi na yo alwala, sai na zare hannuna cikin nashi, na miƙe tsaye ba tare dana kalle su ba nace "Babu alwalar da zan yi na zo, ku cire rai zaku iya dilmiyar dani ni Rahamah bana haɗa Allah da kowa."
Ina gama faɗin haka na wuce bedroom na kulle ƙofar na bar mukullin a jiki, bakin gado na zauna ina sauke ajiyar zuciya.
Iya wannan maganar da na faɗa musu, ba ƙaramin ƙoƙari nayi ba wajen dakewa, ina faɗar maganar zuciyata na wani irin bugawar tsoron su duka biyun. Ni kaina nasan Allah ne ya bani iko kawai na iya faɗa.

Al'amen cike da tashin hankali ya fara kiran "Rahamah Rahamah! Ki dawo fa." Ya tashi da ƙyar ya bi bayan ta kafin ya ƙarasa ta rufe ƙofar.

Bugun ƙofar ya shiga kamar zai ɓalla ta, yana faɗin na zo na buɗe ko raina ya ɓaci.
Ina ji nayi shiru na ƙyale shi, ko me zai yi sai dai ya yi amma ba zan buɗe ƙofar nan ba Wallahi.

Ina jin lokacin da Mustapha ya zo bakin ƙofar, yana faɗin "Jagaba ƙyale ta, mu mata uzuri a bita a sannu watarana da kanta za ta yi ba sai ka sata ba, kaga taho mu tafi ka ji."

Da ƙyar ya janye Al'amen wanda ranshi ya kai ƙololuwar wajen ɓaci.
Ina jin shi yana faɗin "Za ki san ni kika wa gardama ai ba'a ɗakin za ki dauwama."

Tsaki naja a zuciyata ina neman tsari daga sharrin su. Dai-dai nan na ji kiran sallar magriba, tashi nayi na ɗauro alwala na tada Sallah.
Na daɗe ina addu'o'i akan Allah ya tsare ni daga kaidin Al'amen.

Dan na fuskanci dole sai na tashi tsaye da addu'a, wannan abin nashi ba lafiya ba, dole akwai wata ƙullalliya a ƙasa.
Amma nasan Allah shine kaɗai zai yi maganin duk wani shirin su. 
A fahimta ta kenan Aurena ma da Al'amen ya yi, bisa umarnin wannan mushrikin ne kenan? Danƙari ashe akwai matsala kenan da jan aiki a gabana.

Na daɗe zaune ina kaiwa Allah mai kowa mai komai kukana, har sai da aka kira sallar Isha'i na yi tare da shafa'i da wuturi. Ina jin yunwa amma naƙi fita saboda bana son ko ganin shi nayi bare wani abu ya haɗa mu.
Haka nayi wanka na ɗaura alwala tare da shirin barci, nayi duk addu'o'in da annabinmu (S,a,w) ya koyar na shafe jikina na kwanta ina jin zuciyata cikin wani irin yanayi.

*****

  *AL'AMEN*

Ranshi a matuƙar ɓace ya ke da abinda Rahamah ta masa, da ƙyar Malam Mustapha ya rarrashe shi suka fita.
Dama da motar Al'amen ɗin suka zo, dan haka suka shiga dan ya maida Malam gida.

A hanya Al'amen dake tuƙi cikin fushi ya kalli Malam Mustapha yace "Na rantse da Allah kai ka dakatar dani, da sai yarinyar nan ta gane kuren ta."

Dafa kafaɗar shi Mustapha ya yi yace "Kai matsalata da kai baka bin komai a sannu, karka manta ni ne wanda na shawo kan komai har ka samu ka auri yarinyar nan. Ko dai ka manta aikina ne, kar ka bari fushi ya jagoranci lamarin ka da yarinyar nan. Dan na fuskanci tana da ɗan motsi a kanta, dan yadda ta mana yanzu alamu sun nuna ba ita kaɗai bace. Zai iya yiwuwa tana da aljanu dan wannan kwallin dana sa a idona, babu halittar da zan kalla da shi bayan aljanu in basu umarni su take.
Dan haka yanzu mu je ga aiki na gaba, ita zamu dawo kanta."

Sai lokacin Al'amen ya ɗan ji dama-dama. Ajiyar zuciya ya sauke ya kalli Malam Mustapha yace "Amma kana ganin in aljanu ne da ita ba zasu dinga ɓata mana aiki ba?."

Jinjina kai malam Mustapha ya yi yace "Eh to gaskiya ban tabbatar su ɗin bane, dan zargi nake ka bari na gama tabbatarwa tukun in ya so sai na duba naga waɗanne irin aljanu ne kafin na tantance komai."

Maida kan shi ya yi ya cigaba da tuƙin yana faɗin "Shikenan in ka yi binciken maji. Maganar ɗaya aikin na riga da na samu yarinyar tuni, yanzu haka anjima zan je sabon gida dan mun yi da Bukar zai kawo ta anjima, matsala ɗaya ce kawai bana son nayi dare a waje tunda kaga yarinyar nan na nan.
Gasu Hajiyar mu, bana so su zargi wani abu suga ban dawo da wuri ba."

Gyara zaman shi Mustapha ya yi yace "To me zai hana zuwa gobe ka tattara ta ku koma sabon gidan, kaga sai ka fi samun sakewa, tunda can a kwai ɗakuna da sashin da ba kowa ma.
Dan gaskiya aikin mu na buƙatar lokaci."

Nan da nan ya yi na'am da wannan shawarar, ya amsa da "Hakan ya yi." Daidai lokacin da suka iso ƙofar gidan Malam Mustapha, gidane ƙarami irin na masu ƙaramin karfi, yana sauke shi ya buɗe ƴar ƙaramar ƙofar gidan ya shige. Al'amen ya juya kan motar ya ɗauki hanyar sabon gidan shi.

Koda ya shigar da motar, bayan sun gaisa da me gadin shi. Kai tsaye ya nufi ƙofar babban farlon shi. 

Zaune ya tarda wani mutumi baƙi dogo,bashi da jiki kwata kwata irin siraran mutanen nan ne.
Gefen kujerar da ya ke kai, wata mace ce zaune tana da ɗan jiki kaɗan a ƙalla zata kai shekara talatin, fara ce amma daga gani farin mai ne.
Idanun ta a tsatstsaye suke daga gani irin marasa kunyar matan nan ne, sai faman taunar cingum take tana wani kwarkwasa.
Sanye take da wasu irin riga da sket na atamfa, waɗan da aka musu wani shegen ɗinki duk kusan jikin ta a waje ya ke.

Hannu Al'amen ya miƙawa mutumin, wanda na ji ya kira da Bukar. Idanun shi akan yarinyar da ita ma ta ƙure shi da ido.

Bayan sun gaisa, Bukar ya miƙe yana nuna yarinyar yace "Gata nan dai Jagaba, nasan duk wani abu da kake buƙata  zaka samu a gare ta, dan Sa'a bata da matsala ƙwararriya ce ta gaske."

Dariya Al'amen ya yi yana wani bin matar da kallon ƙasan ido, ya kalli Bukar tare da miƙa masa hannu suka ƙara gaisawa yace "To ka kyauta sosai, ta yi min nima kuma yadda nake so." Yasa hannu a aljihun sa ya ƙirga kuɗi dubu ashirin ya bawa Bukar.

Amsa ya yi yana washe baki, ya yi godiya ya juya tare da cewa yarinyar sai sun haɗu, ya fice daga farlon.

Al'amen kam nufar ta ya yi ya miƙa mata hannu, babu musu ta bashi nata  tana wani irin kwarkwasa.
Kai tsaye saman bene suka nufa, ɗakin farko ya kaita ya rufe ƙofar.

***

   *RAHAMAH.*

Can cikin barci na ji kamar ana shafa ni, zabura na yi na tashi zaune ina zazzare ido cikin duhun ɗakin.
Ji nayi an ƙara kamo ni, ba sai an faɗa min ba, nasan Al'amen ne.
Sai dai ina mamakin yadda ya ke shigo min ɗaki, koda kuwa na rufe ƙofar na bar makullin.

Ture shi na shiga yi ina faɗin "Dan Allah sake ni, wai me ma ya kawo ka ɗakina, ta ina ka shigo min ma?."

Kunna fitilar gefen gadon ya yi, ina iya ganin shi shima yana gani na.
Ya wani kafe ni da ido cikin wata irin murya yace "Ke ki ke da gidan Da za ki na tambayar yadda na shigo?."

Ya ƙara yowa wajena da nufin kama ni, kaucewa na yi da sauri dan gaba ɗaya wani irin wari ya ke min, kuma ba warin komai bane sai warin zufa. Irin mutum ya wuni a ranar nan ya sha aikin wahala ya yi zufa ɗin nan.
Ga bakin shi da in ya yi magana kusa dani, da nake jin yana tashi.
Har ga Allah har wani amai-amai nake ji. Saboda a rayuwata na tsani wari, haka hancina yana da saurin jin wari ko ƙamshi ko ya ya ne kuwa. 

Ina ja baya ina komai, haka ya haɗe ni da fuskar gadon.
Yau ma abinda ya min jiya ya maimaita, sai dai yau cikin hayyacina nake. Nasha azaba ba kaɗan ba. Yana komawa gefe na tashi da ƙyar na nufi toilet na fara sheƙa amai kamar zan amayar da ƴaƴan hanjina.
Saboda uban warin da na shaƙa a jikin shi, gaba ɗaya cikina ya hautsine.

Ban fito daga toilet ɗin ba, sai da nayi wanka na haɗa da wankan tsarki na ɗauro alwala, ina bin bango na fito na sa kaya na tada Sallah. 
Raka'a biyu nayi na daɗe a sujjadar ƙarshe ina kaiwa Allah kukana.
 Na zauna tare da yin addu'o'i na, akan neman mafita wajen Allah akan wannan auren nawa.
Anan barci ya kwashe ni.

Jin motsin mutum kusa da ni yasa na buɗe idanuna dake cike da barci, cikin mamaki na ƙara ware idona akan shi.

Al'amen ne tsaye yana Sallah a gefe na, cikin shigar jallabiya.
Cikin nutsuwa ya ke sallar tashi, kuma gabas ya kalla saɓanin jiya.
Kallona na kai ga agogon ɗakin, sai naga ƙarfe ukun dare 3:0am.
A zuciyata nace _Ikon Allah shima  nafila ya ke yi kenan?_ gaba ɗaya na rasa in da ya kamata na aje Al'amen.
Dan abubuwan da ya ke ƙara sani cikin ruɗani suke baki ɗaya.

Yana idar wa naga ya ɗauki Alqur'ani, ya shiga karatu kamar yadda ya yi a safiyar yau.
Tun ina kallon shi har barci ya ƙara ɗauka ta.

Da safe koda na farka ban ganshi a ɗakin ba.
Dan haka na tashi na tattara ɗakin na gyara, na fita farlon shima na gyare shi tsaf rana ta farko dana ji sha'awar in sa turaren wuta a gidan.
Dan haka na koma ɗakin, cikin kayana da suka rage anan, saboda duk sauran dama ba'a kawo su nan ba, kai tsaye wancan gidan da yace zamu zauna aka kai har kayan gadona da komai an gama min jere na. Zuwa kaɗai ya rage.
Nan iya abubuwan da zan yi amfani dasu ne kawai.

Ina cikin zuba turaren sai ga sallamar shi ya shigo,  sanye dai ya ke da jallabiyar da zan iya cewa ta gado ce. Dan tunda nazo ita naga yana sawa. Hannun shi riƙe da carbi alamar daga masallaci ya ke.

Tunda na kalle shi sau ɗaya na ɗauke kaina, sai ya ƙaraso kusa dani yana ƙoƙarin riƙo hannu na na kauce.

Ya ɗan ɓata rai yace "Gaida ki zan yi tunda naga ke baki iya gaisuwar ba, duk da nasan ba tarbiyyar da aka baki kenan ba kin tsirowa kan ki ne."

Bance masa komai ba, na ƙara ja baya.
 Ya  kalle ni tare da taɓe baki yace "Ki riƙe jikin ki, Ni yanzu abinda nake son faɗa miki, ki kasance cikin shiri yau zamu koma sabon gidan mu. Saboda haka ki wuce ki fara shiryawa. Sannan ki je wajen Hajiyar mu ku gaisa, dan tace dama bakya zuwa kina gaida kowa a gidan nan tun ranar da aka kawo ki.
Ki kula bana son rashin mutumcin ki ya shafi iyayena, duk abinda za ki yi ki yi ƙoƙarin kaucewa ɓata musu, karki bari a dinga kawo min ƙarar ki."
Yana gama faɗin haka, ya juya ya nufi bedroom.

Ganin ya kusa shiga yasa na ɗaga murya nace "Babu in da zani na gaida waɗan da ba jin Yaren su nake ba, Iya gidan Aunty Fati kawai zan je na mata sallama."

Har ya kama mariƙin ƙofar zai shiga, jin maganata yasa ya fasa ya dawo da baya.
Ya ƙaraso wajena ya nuna ni da hannu cikin kashedi yace "In kin cika mara kunya karki je, in har baki je ba ko gidan Aunty Fati ɗin ba zaki je ba."
Ya juya ya tafi ya barni tsaye.

Tsaki naja na bi bayan shi da kallo, kamar nayi dariya ganin yadda ya ke tafiya a wani barbaje kamar buhun fulawa.
Na kauda kaina na zauna kan kujera ina shawara da zuciyata.

Allah ya sani bawai son shiga cikin gidan ne bana yi ba, kwata-kwata wannan hayaniyar tasu ce bana so. Basu iya komai a hankali ba, sai ihu da hayaniya ka rasa ma me suke cewa duka.
Nasan in ya hana ni zuwa gidan Aunty Fati, ban isa na je ba.
Dan sai me gadi ya buɗe min ƙofar zan fita, na kuma san cewa zai yi kar ya buɗe min.

Dan haka sai kawai na nufi ɗakin, zaune ba tarda shi ya baje a ƙasa babu ko riga a jikin shi.
Daga shi dai gajeren wando wanda ko cinyar shi bai gama rufewa ba.
Kuɗi ne dami-dami a gaban shi yana ta faman lissafi.

Yana ganina ya wani haɗe rai, na kauda kaina tare da taɓe baki na wuce wadrobe na ɗauki Hijabina har ƙasa nasa, na kalle shi nace "Na tafi wajen Hajiyar."

Bai min magana ba, sai jinjina kai da ya yi ya cigaba da lissafin sa.
A zuciyata nace _Ko ance masa kuɗin sa ya dame ni ne? Da ya wani haɗe rai dan ya ganni_

Da sallama na shiga farlon, wata mata na gani zaune da alamar ƴar aiki ce.
Tana ganina ta miƙe ta shiga gaida ni cikin gurbatacciyar hausar ta.

Amsawa nayi nace "Ina Hajiya?."
Nu ni ta min da saman bene tace "Ya shiga ciki."

Waje na nema na zaune a kan ɗaya daga cikin kujerun farlon, na ɗaga idanuna ina bin farlon da kallo a hankali.
Gani nayi matar ta doshi saman, alamar zata sanarwa Hajiyar da zuwana kenan.

Babu jimawa ta sakko tace min "Yace ka shiga."

Ba dan na so ba, na tashi na nufi saman ina bin ko'ina da kallo.
Ƙofa ɗaya ce kawai a saman, dan haka na tura na shiga da sallama a bakina.

Ɗan ƙaramin farlo ne, me ɗauke da setin kujeru ɗaya, da tv dake manne a bangon dake kallon ƙofa, sai wani ɗan tebur ƙarami dake tsakiyar farlon remote ne akan shi da wani ɗan kofi alamar Abu aka sha a ciki.

Daga ciki na ji ance "Ki shigo ina ciki."

Nufar ƙofar da na ji maganar na yi, na yi sallama aka amsa na shiga.
Tana zaune a bakin gado, gaban ta wasu takardu ne tana duddubawa idanun ta sanye da gilashi irin na ƙara ƙarfin gani ɗin nan.

A ƙasan carpet ɗin nake ƙoƙarin zama, ta ɗago ta nuna min gefen ta tace "Dawo nan ki zauna, ya za ki zauna a ƙasa."

Zama na yi nace "Ki barshi Hajiya nan ma ya isa, dan ina ganin yau dai ba zan iya zama kusa da ita ba, dan haka baya cikin kunyar da aka sanmu da ita ga surukai mu Hausawa kenan.

Ganin na riga dana zauna, sai bata ce komai ba ta aje takardun ta fuskance ni tana murrmushi.
Na gaida ta ta amsa, tare da tambayar lafiya ta, harda cewa fatan ina kula mata da yaron ta yadda ya kamata.
A bakinta ma nake ji, ashe Al'amen yana da yayu maza biyu da mata uku, sai ƙaramar ƙanwar shi tace tana aure a ibadan. Kuma tace gidan Yayan Al'amen ɗayan ma yana jikin gidan mu, matan sa biyu da yaran sa.

Ni dai jinta kawai nake, a raina nace _Sai kace na tambaye ta._
Ta daɗe tana bani labarin su, tare da min nasiha akan dai na kula mata da ɗan ta.
Ni kam nace _Ɗan ki kaɗai ki ka sani, ba ruwan ki da ƴar mutane da halin da take ciki._

Ban wani ɗauki lokaci ba nace mata zan tafi, nan ta tashi ta biyo bayana.
Kitchen ta shiga ta haɗo min wasu abubuwa a leda, tace "Gashi na ɗan yi aiki da su kwana biyu, Al'amen na son su shi yasa.
Ba tare dana san meye ba, na amsa na tafi.

Koda na koma na tarda ya fito a ɗakin, anyi Sa'a ya yi wanka ya canja kayan jikin sa.
Ko zama ban yi ba na aje ledar.

Nace masa zan je wajen Aunty Fati.
Miƙewa naga ya yi yace "Mu je na raka ki, dama ai ban je na mata ya gajiyar biki ba."

Kallon mamaki na shiga bin shi da shi nace "Ba sai ka bi ni ba, ina zaton ai in zaka gaisheta zaka iya zuwa daban ko?."

"To ni tare nake so mu je, in ba haka ba sai dai ki fasa tafiyar."

Bisa dole ina ji ina gani haka muka jera, duk da muna fita muka shiga gidan Aunty Fati ɗin, amma sai na tsinci kaina da jin kunyar yadda na jera da shi abu Ruguzaza haka.

Wajen me gadin Aunty Fati ya zauna, na wuce ciki na tarda yara ne kaɗai a farlon.
Suna ganina suka taso a guje suna min Oyoyo.
Iya Kamal kaɗai na ɗauka, na dungurewa Islam kai nace "Ke ba ruwana da ke, dan baki da kirki matsa ki bani waje dan Allah, wannan shi ne ɗana."

Matsawa ta yi tana ɓata rai, ban bi ta kanta ba na wuce bedroom ɗin Aunty Fati kai tsaye dan Kamal yace tana ciki.

Linkin kaya na tarar tana yi. Tana gani na ta fara fara'a tana kallona cikin murna tace "A'a Amarsusu ta angon ta mai abin mamaki, ku ne tafe kenan?."
Ta ƙarasa faɗar tare da miƙewa tsaye ta nufo ni.

Aje Kamal na yi muka  rungume juna, cikin dariyar farin ciki nace "Gamu kam Aunty Fati."
Taja hannuna muka zauna bakin gado, ta fita ta dawo hannun ta ɗauke da filet da ruwa da lemo me sanyi.

Bayan nasha ruwan na cire ɗankwalina ina gyara zama na kan gadon ta, ina bin ɗakin nata da kallo nace "Wai Aunty kayan ɗaki ki ka canja?."

Tana dariya tace "Wallahi kam ai tun kafin bikin ki, Abban Kamal ya canja min baki kula da kujerun farlon  ba kenan?."

Girgiza kai na yi ina jin daɗi a raina, haƙiƙa Aunty Fati ta yi sa'ar mijin aure. Yana matuƙar son ta yana kyautata mata sosai, baya barin ta ta yi kuka akan komai, duk wani abu na jin daɗin rayuwa yana ƙoƙari wajen ganin ya wadata su da shi.
Koda ina budurwa ina sha'awar rayuwar su, gwanin burgewa ba zaka taɓa jin kan su ba.
Sai na ji dama nima haka na yi sa'ar miji kamar ta, ai da na more bani ba kuka.

Cikin farin ciki nace "Allah ya sanya alkhairi, wallahi kuma naga farlon ya canja min fa, Allah dai bai bani ikon in lura da kujerun ba."

Tashi muka yi muka nufi farlon, na dudduba tsadaddun kujerun har Tvn bango Ya canja babba ce yanzu, na musu addu'ar Allah ƙara masa buɗi na alkhairi.
Ta amsa da Amen.

Sallamar me gadin ta ita tasa muka juya, sai lokacin na tuna da Al'amen nake tare.
Cewa ya yi wai Al'amen yace ya na neman iso.

Salati Aunty Fati ta fara tana tafa hannu idanun ta a kaina tace "Ke yanzu dama tare ku ke? Ki ka shanya bawan Allah a waje baki ce na shirya ya shigo ba."

Turo baki na yi gaba murya a shagwaɓe nace "Ni fa murnar ganin ki ce tasa na manta da shi."

Dungure min kai ta yi ta nufi ɗaki tana faɗin "Ina kin ga dama ki je ki shigo da shi."

Ina ɓata rai ina komai na fita, a bakin ƙofar farlo na tsaya na ɗaga muryata da ya ke ina hango su nace "Wai ka shigo."
Na juya na koma ciki abina, Aunty Fati ce ta fito sanye da hijabi.

Sai gashi shima ya shigo da sallama, hannun sa cikin na Kamal Yana wani sunne kai kamar na Allah.

Zama ya yi kan kujerar, ya gaida Aunty Fati harda yin ƙasa da kai a zuwan girmamawa, yana wasa da Kamal daya haye cinyar sa.
Shiru muka yi duka, Aunty Fati ta kalle ni ta banka min harara tace "Tashi ki kawo masa ruwa da lemo."

Ba dan bana so ta gane wani abu tsakanina da shi ba, da cewa zan yi ba zan kawo ba.
Haka na tashi na shiga kitchen na buɗe frij na ɗauko ruwa da lemon na kawo.
Haka ta maida ni na ɗauko kofi, sai da na zuba masa tukun ta ƙyale ni.

Ruwan yasha kawai, ana jimawa ya miƙe yace "Zamu tafi."

Kallon shi na yi nace "Ka je ni ma zan dawo."

Girgiza kai ya yi ba kunya yace "Kin san akwai shirin kayan da za ki yi, ki taso mu wuce tunda kun ga juna."

Mamaki ma nake ganin bai ji kunyar Aunty Fati ba, ina ƙoƙarin yin magana Aunty Fati tace "Ka je ka ɗan jira ta tana zuwa."

Kafin ya fita, ya zaro kuɗi dubu ɗai-ɗai ya bawa su Islam.
Ɗaki ta jani ta hauni da faɗan bata Sanni da halin musu ba, ya nake son ɓata wayona abinda bana yi shi zan nawa mijina.
Ganin ranta ya ɓaci na bata Haƙuri, nace mata yau zamu koma gidanmu tunda dama ban faɗa mata ba.

Addu'a ta bini da ita, tare da ƙara bani shawarwari.
Ta haɗo min kayan mata da su turaruka da abubuwan da baza'a rasa ba, tace ita ma zata shigo anjima kafin mu tafi.

Har waje ta rako mu, muka tura get muka shiga ina jin zuciyata duk ba daɗi.

*_🥰MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰✍🏻✍🏻_*