Chapter 8
*PAGE 8️⃣*
Tun da muka baro asibitin, kuka kawai nake kamar wadda aka sanarwa da saƙon mutuwa.
Na fara kukan ne tun sa'ar da likita ya faɗi kalmar data tafi da ɗan sauran farin cikin da ya rage min a rayuwa.
Ni Rahamah ni Rahamah, ace ina ɗauke da ciki cikin ma na wannan mugun azzalumin. "Ya Allah." Na furta hakan a fili.
Na fuskanci daga shi uban gayya, da tunda aka sanar da samuwar cikin ya ke washe baki.
Da ita Aunty Fati da ke ta faman aikin lallashi, babu wanda ya fahimci kukan baƙin ciki nake.
Duk tunanin su farin ciki yasa nake kuka, saboda Aunty Fati ta sanni da shegen son yara.
Eh tabbas ina son yara a rayuwata, sai dai duk da irin son da nake musu, ban yi fatan samun haihuwa da wannan mutumin ba.
Wanda nake wa kallon mugu kuma azzalu, me halin dabbobi.
Sai gashi ashe ni ina tawa ne, Allah kuma na nashi Allah ya riga daya ƙaddara sai na samu rabo da shi.
Tunda gashi ina ɗauke da cikin shi, har na tsawon sati biyu.
Ganin kukan yaƙi ƙarewa kamar ana daɗa tunzurani, Aunty Fati da ta fara zargin kukan ƙiyayyar cikin nake.
Ta ɗan ture kaina daga jikin ta tace "Wai ke Rahamah haka ake yi fisabilillahi, dama in mace ta samu ciki kuka take ba farin ciki da addu'ar su rabu lafiya ba take?."
Maida kaina na ƙara yi kafaɗar ta, na cigaba da kukana kamar ba dani take magana ba.
Al'amen dake tuƙi kam zuciyar sa fes take, tun sa'ar da likita ya sanar da samuwar ciki ga Rahamah, ya ji wani daɗi ya ratsa shi.
Allah ya sani yana son ace yau shima ga ɗan shi an nuna ance ɗan Jagaba ne, koba komai hakan ƙarin daraja ne da kima a gare shi a matsayin sa na mutum na mutane.
Jin da ya yi Aunty Fati nawa Rahamah magana, hakan yasa ya juyo ya kalle su yana murmushi yace "Ki bar ta ta yi kukan farin ciki ne, kin san dama tace min tana addu'ar Allah yasa ta samu ciki kusa. Ashe ma abin ya na tare da ita bamu Sani ba."
Ya ƙarasa faɗar hakan yana kallona, dai-dai lokacin da na ɗago ina kallon shi, cikin mamakin jin ƙaryar da
min ido-da ido ba kunya bare tsoron Allah.
Idanun shi fes a cikin nawa, babu ko alamar kunya a ciki ko nuna ba haka bane.
Ji nayi kamar na buɗe baki na danna masa zagi, sai dai hakan ba tarbiyyar da aka ɗora ni a kai bace.
Wani munafikin murmushi ya sakar min, ya ɗauke kan shi ya cigaba da tuƙi kamar wani na Allah.
Harara nabi bayan shi da shi, babu shiri na nemi kukan da nake na rasa.
A zuciyata nake faɗin _Lallai wannan mutumin lamarin sa ya wuce_ _tunina, wani abin in ya shirya ko ni da nake mace bana tunanin zan iya shiryawa._
Mun sha kwantar gidan Aunty Fati kenan, maganar shi ta ratso kunne na yace "Am yawwa Aunty Fati, ina son dan Allah kiwa Rahamah magana.
Kar ta dinga shan maltina madara, da yawan cin ƙwai, dan tana da jarabar son ƙwai kullum sai ta soya taci.
Ni kuma bana son abinda zai jawo yaron cikin ta ya yi girman da har sai an mata aiki, kin san abubuwan nan na kumbura yara su yi girman da ya wuce misali."
Tunda ya fara magana Aunty Fati take kallon shi, a ranta take faɗin
_Ikon Allah yau naga abinda ya fi karfina, Ni Fatima. Cikin da bai kai ko wata ɗaya bane ake sawa doka har haka? To Allah ya jiƙan mu mu da muke shan ta kullum_
Nan ta tuna cikin Islama kullum bata da wata cima sai ƙwai, maltina kuma ita ta zama kamar ruwan shanta.
Kuma babu abinda ya same ta ko babyn, asalima Islam ba tayi wani girman ku zo mu gani ba, lafiya ta haifi ƴar ta ba tare da komai ba.
Jin dukan mu mun yi shiru, hakan yasa ya juyo yace " Aunty ki yi haƙuri fa, na faɗi hakan ne dan ki mata magana ta rage, gani nayi bai dace ace tana ci kullum ba.
Tunda har likitoci sun ce suna hura yaro."
Murmushin yaƙe Aunty Fati ta yi, ta kalle shi tace "Karka damu zan mata magana, amma ni a ganina abubuwan da ka lissafa babu abinda suke sa yaro, sai ƙarin lafiya da kuzari ko a asibiti likitoci na cewa a yawaita cin dafaffen ƙwai."
Nan da nan ya haɗe rai, cikin cunkushashshiyar murya alamar ranshi bai so tace hakan ba yace "Ni dai abinda nace kenan, ki faɗa mata bana so ta jamin aiki dan ba son aiki nake ba.
Gwara ta haifa da kanta kawai."
Bansan lokacin da na ja tsaki ba, da sauri ya juyo ya kalle ni daidai lokacin da muka ƙaraso ƙofar gidan Aunty Fati.
A bakin get ya yi parking gaba ɗaya fuskar shi a haɗe, ba sai ji na yi Aunty Fati tace "Am Jagaba Ina so ka barta a nan ta ɗan huta, in yaso zuwa dare sai ka biyo ka ɗauke ta ku tafi."
Bata jira cewar shi ba, ta kama hannuna ta buɗe motar muka fita.
Raina fes, ji nake kamar an cire min ƙaya, dama ace in na shiga gidan ta ba zan ƙara komawa gidan shi.
Ganin har taja hannun ta, ba tare da ta jira izini daga gare shi ba, hakan ya ɓata masa rai.
Kamar yace bai yarda ba, ko me ya tuna sai ya washe baki yace "To shikenan Aunty, an jima dai daga anyi sallar Isha'i ta shiry, zan zo mu tafi.
Ban jira ya ƙarasa maganar shi ba, na zare hannuna ana Aunty Fati nayi gaba.
Ina jin su suna sallama, yana jaddada mata ta kula dani sosai, kar ta bari nayi abinda zai taɓa cikin jikina.
A zuciyata nace _Sarkin rashin kunya, ayi mutum babu ta ido ba kunya bare kara._
Shigowar Aunty Fati tuni na cire Hijabina, na baje a kan carpet ɗin dake malale a farlon, ina shan sanyin fankar dana ƙure.
Jina nake yau kamar na samu wani ƴancin kaina ne, kafin ya zo ya yanke min jin daɗi na ya maida ni cikin fursun ɗin gidan shi.
Zama Aunty Fati tayi a kan kujerar dake gefen inda na kwanta, ta kalle ni tare da aje jakar ta wajen ƙafata tace "A gaskiya Rahamah kina fama, wannan mijin naki na fuskanci sam bashi da kunya, ki ga daga samun ciki har ya fara rawar jiki abinka da ba saban ba. To an daɗe ba'a yi aure ba, yanzu har ga shi za'a samu ɗan kai, ko wane likita ne yace masa ba'a cin ƙwai da shan maltina da madara in an samu ciki?."
Ɗan kama ƙafar kujerar da take kai nayi, na miƙe zaune tare da faɗin "Wash, na gaji wallahi."
Na juyo gaba ɗaya na fuskance ta nace "Ke iya rashin kunya kika fahimta a tare da shi kenan?."
Jinjina min kai tayi tace "Ƙwarai Rahamah bashi da kunya, ko dan shi ɗin ba bahaushe bane oho?."
"Uhmm tunda abinda ki ka fahimta kenan, ina roƙon Allah ya bayyana sauran halayen shi, yadda kowa zai fahimce shi bama ke kaɗai ba."
Da sauri ta dafani, cikin nuna ƴar zaƙuwar ta da son in bata amsa tace "Waɗan ne irin halaye ya ke dasu Rahamah?."
Haka kawai naji na kasa ce mata komai, sai kawai na tsinci kaina da girgiza kai nace "Babu komai addu'a ce na yi, ina fatan kuma Allah ya amsa."
Ajiyar zuciya ta sauke, tare da jan tsaki tace "Har kin faɗar min da gaba wallahi, nayi zaton wani abunne daban.
Allah ya shirya ki Rahmah, na fuskanci har yanzu akwai wauta a tare dake."
Ban ce mata komai ba, na maida kaina na kwantar kawai.
Ni kaɗai nasan me meke damuna a zuciyata.
Har dare muna tare da Aunty Fati, haka ta dinga nan-nan dani tana kawo min abubuwan ƙwadayi irin na masu ciki.
Kusan har dare tana kitchen, ko da ya zo ɗauka ta haka ta cika min kula da dambun zogalen da nace mata ina so.
Tunda na shiga motar ko magana ban masa ba, shima bai ce min komai ba, sai motar da naga ya shigar gidan su.
Har ya buɗe ya fita ban motsa ba, ganin haka yasa ya leƙo fuska a haɗe yace "In kinga dama ki fito mu shiga ki gaida Hajiya."
Kamar kar na fita, tuna inda muke abu kaɗan zan yi ya sani a idon mutane.
Hakan yasa na fito ina ɓata rai nabi bayan shi. Farlon Hajiyar su muka nufa, kuma har yau ina mamakin me yasa baya kaini wajen sauran matan Baban shi, ko bai ɗauke su a matsayin iyaye bane ban sani ba.
Dan ko suma ƴan uwan nashi, basa wani damuwa da lamarin shi sai in buƙatar su ta kawo su, wasu daga cikin su kenan waɗan da ƙarfin su bai kai nashi ba.
Sai da muka shiga wajen Hajiyar na ƙara tabbatar da Al'amen baida kunya, dan ba wata damuwa yace mata, ina da cikin sati biyu.
Nayi zaton zata ji nauyi, sai naga ta hau murna tana addu'ar, Allah ya rabamu lafiya.
Ni dai gaba ɗaya a takure nake jina, daga ƙarshe sai ga Anisa ta fito wai zamu tafi tare da ita.
Ashe tunda ya fita da ita wajen Hajiyar ya kawo ta.
Ni sai naga kamar Hajiyar ma na wani harhaɗe min rai, dan bata wani sake min yadda ta saba ba.
A raina nace _Ke kika sani, daga ke har ɗan ki bakwa gabana._
Haka muka baro wajen ta, yace Anisa ta jira mu a mota muka shiga wajen Dadyn su ance baya jin daɗi.
Na tausayawa bawan Allah, ganin halin da ya ke ciki na ciwo.
Yana kwance a farlo akan katifa, an ɗaura masa ruwa, ciwon lokaci guda har ya rame.
Har ƙasa na tsugunna na gaida shi, da ƙyar ya amsa na masa addu'a akan Allah ya bashi lafiya.
Al'amen ya gyara masa kwanciya, muka masa sai da safe, ya bimu da addu'ar zaman lafiya muka tafi.
Muna isa gida na riga su fita a motar, kai tsaye wuce ɗakina, farkon abinda na fara shine fito da katifar Anisa daga ɗakina.
Daidai lokacin dana ɗire katifar ina ƙoƙarin juyawa ya sawo kai farlon.
Ban dakata ba na cigaba da tafiya, ina jin shi yana kiran sunana yana faɗin "Lafiya Rahamah ki ka fito mata da katifa?."
Ban kula shi ba, ya biyo Ni har cikin ɗakin cikin fushi yace "Wai ba dake nake magana ba?, ya ina tambayar ki zaki share Ni ki yi banza dani."
Ba tare dana kalle shi ba na ƙarasa bakin gado na zauna nace "Na rantse da Allah ka ji na rantse ko? Muddin kace Anisa zata cigaba da kwana a ɗakina, to sai dai ka zaɓi ɗaya. Ko Ni ko ita, dan in har kace ta cigaba da kwana daga yau na haramtawa kaina kwanan ɗakin, in yaso sai ku dinga kwana tare."
Na yi tunanin zai hayayyaƙo min, kamar yadda ya saba in maganar ta haɗa mu.
Cikin mamaki naga ya sassauta murya yace "Ki yi Haƙuri ba za'a yi haka ba, na yarda ta daina kwana a ɗakin, amma yanzu ki taso mu je ki taya ni mu gyara mata ɗakin farlo, tunda ba komai a cikin sa."
Tsaki naja na kauda kaina nace "Babu in da zan je, kai dai da ka ɗauko ta kaga zaka iya da hidimar ta ai sai ka je ka gyara mata."
Al'amen gaba ɗaya daurewa yake, yana Binta a hankalina ne kawai saboda sharaɗin da Malam Mustapha ya bashi, tun sa'ar da ya sanar da shi tana da ciki.
A waya ya kira shi.
Nan ne fa yace ya yi ƙoƙari wajen bin duk abinda take so, ko zasu samu ta saki jiki da shi ta dinga abinda suke so.
Tunda dai yanzu Allah yasa tana da ciki, me ciki na son kulawa ya dinga daurewa.
Wannan shine dalilin da yasa har ya sassauta muryar shi yanzu.
Ina jin shi ya fita yana kiciniyar sharar ɗakin, har ya gama ya dawo lokacin tuni nayi wanka na kwanta.
Ganin yana shirin hawa gadon ba tare daya yi wanka ba, nayi sauran tashi na zauna ina kallon shi nace "Kamar yaya zaka kwanta ba wanka?gaskiya in har ba kayi wanka ba, bana tunanin zan kwana a ɗakin nan sai na koma farlo abuna."
Ban yi zaton zai sauka ba, sai naga ya sauka tare da jan dogon tsaki ya nufi toilet.
Babu jimawa sai gashi ya fito ɗaure da zanina a ƙugun shi.
Cikin takaici na kalle shi, ban ma san yaushe ya buɗe Wardrobe ya ɗauki zanina ba, haka kuma ya nufo gadon jikin shi duk ruwa da niyar kwantawa.
Ƙara tashi nayi na dakatar da shi ta hanyar ɗaga masa hannu nace "Kaga dan Allah ka fara goge jikin ka, kuma ni karka ƙara ɗaura min zani na haka kawai akwai towel a toilet ba babu ba."
Bai ce min komai ba ya nufi wadrobe, cire zanin nayi ganin zai maida wadrobe nace "Karka sa dan Allah, baka ga ruwa a jikin ka ba.
Rataye zanin ya yi a kan katakon jakunkuna na, ya ɗauki gajeren wandon ya saka ya hawo gadon yana ta jan tsaki.
To ranar dai dama-dama zance, sunan ya yi wanka ne amma har lokacin jikin shi bai daina tashi ba.
Yau cikin Sa'a sai banyi amai ba.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, cikin ikon Allah na cigaba da rainon cikina, inda a halin yanzu har ya kai wata uku, kuma duk abinda nace Al'amen ya min yana ƙoƙarin yi sosai,
ba tare da musu ko cewa ba zai yi ba.
A hankali ƙaunar cikin jikina ta fara shiga raina, koba komai nima jinina ne kuma bashi da laifin komai a gare ni, tunda bai min komai ba.
Bai san me ke tafiya a duniya ba, addu'ar da nake kawai shine, Allah ya bani nagari ya tsare shi kar ya gado mahaifin sa ko karta gano mahaifinta.
Yau ina kitchen da rana, sai ga shi ya shigo hannun sa riƙe da wata leda.
Ajiye wa ya yi yace "Ga wannan ki yi min Farfesu, kan rago ne bana so a haɗa da harshen amma, ki cire shi daban tun daga tushiyar sa har ƙarshe.
Bayan nan ki dafa min faten wake, ina son raba sadakar su ne."
*_🥰MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰✍️✍️_*