Chapter 11
by @zahrabmrs02
Page 11💬⌨️
AK ya Kira ni sau biyu daga yanayin yadda yaji ina amsawa be qara kira naba .gskiar zee tace bazai jure wulakanchi ba Alhamduillah mun rabu lfy ,mun gama exams wannan karan tare da Hamma zamu tafi inda yayi rantsuwar wallahi baza mubi precious ba ,na rasa yadda zanyi na fada mata haka dai na same ta Ana gobe zamu tafi nace kiyi hakuri motar kasuwa zamu bi ,Hamma sajid yaki yarda it’s ok tace ba damuwa farhana .munyi sallama cike da kewar juna nida su nusaiba . tasha muka nufa motar da ke layi aka saka kayanmu .Hamma ya biya kudin motar ina shiga naga precious a sit din baya ,da mamaki na kalleta me kike yi a nan ?naga driver yazo daukar ki na tambaya ?eh cewa nayi ya kawo ni park ban ma taba zuwa ba sai Yau tare zamu tafi shigo ki zauna ,turus Hamma yayi bayan ya hango ta .Ka biya mun kudin motar sajid kai nake jira Dama .daure fuska yayi yace fito ki wuce precious .bazan fita ba ay ba motar ka bace ta fada Tana gyara zama ,yan cikin mota Sharon sai Kallon ikon Allah suke haka ya biya mata kudin motar muka Kama hanya .
Mun iso abuja lafiya ,inda muka dauki taxi zuwa gida yayinda precious ta Kira drivern gidan su ya qarasa da ita.
Bayan mun huta Adda taja ni gefe ina Kallon Kayan lefen ta boxes 8 cike da Kaya latest masha Allah sai son Barka .yanmatana ya kk isa gida farooq ya fada cike da nishadi a duk sanda yake jin nishadi yanmatana yake ce mun,lfy Alhamduillah na furta ciki da Jin dadin muryasa,Indai kamala ce da nitsuwa farooq 💯
Muka dan taba hira tare da sallama yayi alkawarin zuwa daurin auren Adda inshaAllah.dayke ma a abujan zata zauna Tinda a nan uncle Salim yake aiki a union bank .
Tin a waya na ba Adda Sabrina labarin abinda jafar yayi min kuma na tabbatar ta fadawa abbi Tinda gashi be taso min da maganar sa ba.
Kiran AK naga yana shigowa wayata da mamaki na qara Kallon screen din ,kiran me yake mun kuma ?na dauka tare da sallama ,ya hanya sweetheart ya fada Bayan ya amsa sallamar.Alhamduillah na amsa da mamaki .abokina ke fada min Kunyi hutu,kiran da kika ga
bana miki kwana biyu Sabida naga Kina exams ne kar na raba miki hankali .Uhmm Toh kawai na iya furtawa. Send me your full address Zan zo mu gaisa ,to ubana na fada a Raina ,Uhmm ni mijin kine ba uban ki ba farhana ya fada ina jiyo sautin murmushin sa Ashe a fili na fada ya rabb.
"House 432 Lugbe Extension, Off Abuja-Leke Road, Lugbe ga address din nan nan , na tura masa via sms
Bayan minti 40 sai ga kiran sa ina Kofar gida,gabana ya fadi Ashe da gaske yake ,Ina zuwa nace tare da kashe wayar ,diddi Zan gaisa da wani a waje na leka dakin ta ,Kallona tayi tare da cewa idan kin dawo ina da magana da ke.
Ni ban San sunan motoci ba amma dai wannan ta gaban kofar Gidanmu ta hadu ,AK ne ya fito daga cikin motar sau biyu muka taba haduwa duk kananan kaya ne a jikinsa ,Yau yana sanye da yadi milk color da matching hula ,sai kalle kalle yake a unguwar ,Sannu da zuwa nace ina jingina jikin motar ,Yauwa sweetheart ya gida ? lfy Lou, Dama nan ne lubge din da ake fada yace yana cigaba da Kallona .eh Baka taba zuwa bane ?na tambaya ?me zai kawo ni arean nan Banda abinki .da Sauri na kalle shi ban gane me yake nufi ba,ya Raina mana unguwa ko mai?ko mai na zama Ina alfahari da lugbe ,Tinda a nan aka haifeni kuma Alhamduillah ba haya muke ba ,abbi fili ya siya ya fara gininsa a hankali .diddi tace farkon zuwansu abuja a gidan haya suka zauna Bayan unguwarmu .daf da haihuwata abbi ya kammala gini muka dawo.Dik ba wani babbban gida bane karamin flat ne da dakuna uku ,sai boys quarter daga gefe mai daki ciki da falo Guda daya ,da ciki daya Guda daya Alhamduillah baa takure muke ba.maganar sa ce ta dawo Dani daga tunanina,tunanin mai kk haka farhana tin dazu ina magana kinyi shiru.Kafin na bashi amsa sai ga abbi ,Hamma fahad da Hamma Muhammad Sun qaraso ,Sannu da zuwa abbi na fada tare da sunkuyar da kai ,dan rusunawa AK yayi tare da gaisawa da abbi,shiga ciki farhana cewar abbi.
A falo na tarar da diddi Adda Sabrina da sameena ,ina zama su Hamma suka shigo ,wa kika samu haka farhana ,cewar Hamma fahad yana gyara zama ban gane ba ?mun gaisa Bayan kin shigo Kinga agogon hannusa ?kin San nawa ne agogon nan kuwa ?ay zai kai 20 million cewar Hamma Muhammad what ?muka fada nida Adda a tare ,wallahi da gaske Rolex ne latest .shigowar abbi ne ya kaste mana zancen .gyara zama yayi inda ya fara da cewa farhana ,Abdulkadir yace Neman auren ki yazo kuma yana so zuwa next week zai turo iyayensa.to Kai kuma mai kace masa abbi?cewar diddi yaron da baa San komai a Kansa ba ?saurin me yake ?
Yace shi dan gidan Tahir tambuwal ne ,governor sokoto. ikon Allah ke farhana an gama da dan senator yanzu kuma dan Gwamna kika jajibo mana ?diddi ta fada ta na Kallona .ni wallahi ban San dan waye ba ,yanzu nake ji .hasalima sau biyu na taba ganinsa .
Abbi Akwai farooq yace zai zo ya gabbatar da Kansa inshaAllah,na fada da Sauri ,to yanzu dai naba Abdulkadir izini Tinda ni ban San da zancen wani farooq ba,amma dai Allah ya zaba abinda yafi zama alkairi .
Farooq na Kira a waya . Dama abbi yace na fada maka ka turo idan da gaske kake . cike da murna ya furta da gaske farhana ?Kinga dai ban shirya ba sosai yanzu Zan fara service amma inshaAllah Wajan zama da abinda zaki ci bazai gagara ba ,sai mu zauna da mamma ita kadai ce a gidan kuma yana da Yalwa bazaki takura ba,Kinga ma kaduna zai fi miki sauki .Zan Kama miki off campus ki bar hostel ,idan yaso weekend sai ki dinga zuwa kd koni na zo Zaria ,hakan ma yayi na fada cike da kunya .nagode yanmatana ya
fada cike da Farinciki .