Kuncin zuci
by @bintuuu
A hankali Na'ima ta rinqa tafiya jin har sannan bata gama warwarewa ba har ta isa falon qasan, nan kuwa ta ga Husna a kwance kan kujera tana danna wayarta hankali kwance itama, sai Na'ima ta qarasa gareta tana murmushi tace "Sis yi hakuri bansan kinzo ba wallahi" sai Husna ta dago tana murmushi tace "Bakomai sis, nima fa baccin naji inaji shine na dan kwanta" Na'ima tace "Muje upstairs kiyi baccin toh" tace "A'a ai ya watse ma, kinsan can asibitin naje ashe jiyan kuka dawo" Na'ima tace "Eh, jiya da dare, Ina kwana sis" Husna tayi saurin cewa "Ina kwana" nan suka gaisa cikin raha, har Na'iman ta nemi kawo mata abincin tace a qoshe take, nan falon suka yi zamansu suna hira Na'ima ta kishingida jikin kujeran ta tankwashe kafafunta suna hiransu ahaka, zuwa tara da wasu mintuna aka danna masu door bell Husna ta je ta bude, wata nurse ce in her thirties ta shigo falon da fara'a sai Na'ima ta miqe ahankali tana mata iso, sai da ta zauna suka gaisa sannan tace mata tazo dubata ne Anty Amnah ce ta turota, a kunyace Na'ima ta amsa da toh, da haka ta miqe ahankali suka nufi stairs nurse din na biye da ita abayan, sai da sukaje falonta sannan tace da nurse din bari ta dubo ciki dan megidan yananan, nan falon nurse din me suna zainab ta zauna, Na'ima bata dade ba ta fito tace ta shiga baya nan ma...sai da zainab din ta bata kulawan da ya kamata sannan Na'iman tayi wanka ta shirya cikin kayanta me kyau suka fito tare har sannan Ahmad yana dakinsa, bayan nurse din ta tafi sai ta dawo gurin Husna ta zauna suka cigaba da hira jefi jefi, can zuwa goma da wasu mintuna kuma Ahmad ya sauqo cikin shirinsa na dark blue half jamfa zai fita yana kallonsu hannunsa riqe da wata qaramar baqar jaka me kyau, sai tashin qamshi yake ya qaraso falon kauda kai Na'ima tayi ganin yanda yake kallonta, anutse yace "Zan fita" ya kalli Husna yace "ki gaishesu" ta amsa da "toh Yaya adawo lafiya" ya gyada kai sai Na'ima ta dan dago ta kallesa itama tace "Adawo lafiya" qaramin murmushi yayi tareda amsawa da "Amin" sannan ya fita daga falon, fitansa a motarsa sai ya dauki hanyar babban office dinsu dake nan Abujan, dan yanzu ayyukansa yawanci sun dawo nan din, ahanya ya kira Adam ko yana office a lokacin sai ya fada masa yaje duba tank farm dinsu but yana hanyar komawa office din ma, da haka sukayi sallama Ahmad ya kashe wayan, bai fi 40 minutes ba ya isa dogon building din mai dauke da glasses tun daga samansa har qasa, a parking din da ya kasance na sa da daidaikun manyan gurin yayi parking sai securities guda biyu suka qaraso suna gaishe, amsawa yayi fuska a sake sai suka fara congratulating dinsa na auren da yayi, yana murmushi ya amsa sannan ya shige cikin building din, nan kuma ma'aikatan suka fara tayasa murna, duk inda ya wuce zaiji sunce "congratulations sir" "Happy married life sir" wasu ya amsa wasu ya daga hannu kawai, ahaka ya shige elevator ya wuce main office dinsa dake hawa na can sama wanda dagashi sai penthouse, Office din nasa tas yake ko ina neat kamar yananan, sai ya nufi fridge ya dauki drink me sanyi sannan ya qarasa ga executive chair dinsa ya zauna tareda jawo files din da aka masa submitting akan table din, sai da ya dauki almost 30 minutes yana aiki a desktop dinsa sannan yaji anyi knocking kofansa sau biyu kuma aka bude Adam ya shigo, suna hada ido Adam yayi dan dariya yace "Straight zan kai mata gulman office kazo yau" sai Ahmad ya kishingida a kujerar tasa anutse yace "Kuma gashi mintuna qalilan tabani da zan fito" Adam na murmushin ya qaraso yace "Ai ni bazaka taba oppressing dina ba Ahmad, in na biyeka sai in kamu da ciwon zuciya abanza" sai sannan Ahmad yayi murmushi me fadi tareda miqa masa hannu sukayi shake, Adam yace "How far Man, ya amarya" Ahmad ya amsa da "Alhamdulillah" sai Adam ya juya ya nufi fridge ya dauki ruwa me sanyi sannan ya zauna a lounge area na office din suna magana akan inda yaje din, sai da ya gama updating din Ahmad akan komai regarding tank farms dinsu sannan Ahmad ya miqe ya dauki qaramar jakan dake gabansa ya qaraso gurin Adam din, zama yayi yana facing dinsa sannan yace "Magana nakeson muyi" Adam yace "Akan menene?" sai Ahmad ya bude jakar ya cire folder'n dake ciki ya zuba takardun akan glass table dinda ke tsakiyarsu, miqa hannu Adam yayi ya fara daukan hotunan yana dubawa da daddaya Ahmad na kallonsa, sai Adam da yazo kan na Laila da Saddam din kawai ya zare idanu yana kallon Ahmad din yace "Me nake gani Ahmad, mahaukaciyar yarinyar nan nada hannu cikin aikin Saddam?" Ahmad ya gyada kai, anutse yace "I told you it takes two in a situation like that....ita ta aika takardun gurin Baba" Adam dake cike mamaki yace "Shit...amma sai na tattaka yarinyar nan" Ahmad ya sauqe numfashi yace "zanso nayi hakan nima, amma ba a halin da take ciki ba yanzu, kuma tayi claiming dan ni tayi" rai abace Adam yace "ka ajiye wannan batun ka koya mata hankali Ahmad, she's our sister so duk lokacin da tayi ba daidai ba dole mu koya mata hankali" Ahmad yace "shiyasa na bar maka hukuncinta a hannunka yanzu, speak with daddy akan wannan huldan da takeyi da mazan, it'll destroy her, ni role din da zanyi playing daban ne da naka" Adam ya sauqe numfashi har sannan bacin rai bayyane a fuskarsa, can yace "what about Saddam?" kafin Ahmad ya amsa aka kwankwasa kofarsa sannan aka sake turota Lamin ya shigo, fuska a sake ya qaraso ciki shima yace "Mijin princess" sai Ahmad ya dan hararesa, dan dariya Lamin yayi sannan ya nufi fridge shima sai da ya dauki coke me sanyi sannan ya zauna a kujera daya, Ahmad ne ya tura masa takardun gabansa shima ya miqa hannu ya dauka yana ganin cike da mamaki, Adam ya sake tambayan Ahmad ya zeyi da Saddam sai Lamin yace "G ga abunda yayi da Saddam a papers din ai" ya qarasa maganan yana miqawa Adam paper'n dake riqe a hannunsa, karba Adam yayi yana gani dan hankalinsa ya tafi kan na qanwarsa gaba daya, sai da ya karanta ya dago kai yana kallon Ahmad dake kallonsa shima, sai yace "Man you did him dirty" da dan bacin rai Lamin ya fara magana "Don't go there Adam, ka manta billions din da yasashi asara ne last year, kasani har mu da mukayi investing wasu kudaden mu a tanks dinnan sai da muka rasa, Saddam is a f*ck boy, I should've break his spine when i got the chance too" Ahmad yace "Na barsa ne da farko shiyasa ya sake taboni, and by Allah sai na kaishi qasa tunda ya cigaba da shiga harkata" Adam yace "Eh na yarda kanada gaskiya amma duk ranan da ka samu Tiyagah ka miqashi ga hukuma, banason ka riqe yaron nan a hannunka, it will be the best way in ka bari hukuma sukayi handling komai" Lamin yace "Ta nan ne kowa zai san wa'enda suka sashi aikin, hakan shi yafi" Ahmad ya gyada kai sannan yace "I'll see to that in sha Allah..thank you" da haka ya miqa musu hannu duk sukayi shakes yana qara fadin "Thanks" sai suka hau wata hiran daban regarding their businesses, basu bar office din Ahmad ba sai da suka share almost awa daya da rabi sannan suka koma na su aikin, da haka Ahmad ya sake tattare takardun ya maida jakan ya barta nan kan table din sannan ya koma work station dinsa ya zauna, sai da secretary dinsa ya kawo masa wasu takardun ya duba sannan ya maida hankalinsa kan desktop din gabansa, nan ya hau duba office mails dinsa da suka taru sosai sai can ya jawo wayarsa ya danna kira ga sahibar tasa, yana fara ringing ya saka a handsfree tareda kishingida bayansa a kujeran, a bugu na biyar ta dauka, cikin sanyinta tayi sallama sai yace "How are you feeling Babe?" ta amsa da "I'm fine" shiru sukayi sai can yace "Na barki ke kadai ko, sorry" tace "No ai Husna tana nan, bacci takeyi ma" sai yayi qasa da murya yace "kin sake shiga ruwan dumin?" shiru tayi sai ya sake cewa "Babe" ta amsa da "Uhm" yayi murmushi yace "I'll be back soon kinji, na zo duba wasu ayyuka ne a office bazan dade ba zan dawo" tace "Allah ya dawo dakai lafiya" ya amsa da "Amin jewel" Na'ima na murmushi ta jira ya kashe wayan sannan ta miqe zaune daga kwancen da take akan kujera, Kiran Alhaji ne ya shigo wayanta ta dauka, cike da ladabi ta gaishesa ya amsa da "Lafiya Na'ima, ya kuke, ya maigidan naki?" anutse ta amsa da "Alhamdulillah" sai yace "Ya jikin naki, Abbanki ya fadamin bakiji dadi ba ashe, ya kikejin numfashin naki yanzu?" tace "Alhamdulillah ya daina Abba" yace "Ma Sha Allah, irin haka ki rinqa kirana ki sanarmun, duk abunda yake damunki ki fadamin I'm always here for you kinji Mamana" murmushi Na'ima tayi tace "Toh Abba, in sha Allah" yace "Yauwa..Allah ya baku zaman lafiya, zan shigo Abujan next month, me kikeson in taho miki dashi?" nan ma tana murmushi tace "komai ma Abba, nagode Allah ya qara girma" yace "Amin ki gaisheda megidan naki" akunyace ta amsa da toh sannan sukayi sallama har sannan murmushin be bar fuskanta ba, tashi tayi asannu ta leqa dakinta dan dubo Husna daketa bacci a gado, sai ta wuce bandaki tayo uzurinta sannan ta fice zuwa downstairs, kitchen ta shiga nan ta fara cooking lunch, tayi nisa da aikin tajiyo knocking a kofa, dauraye hannunta tayi a famfo sannan ta fice zuwa falon, tana budewa taga Mami da Nafisa a tsaye, da saurinta ta qarasa garesu Mami tace "Habibti na jiki yayi sauqi kenan" sai tayi murmushi suka shige ciki, anan falon suka yada zango Na'ima ta zauna a gefen Mamin ta gaisheta, sai da suka gama gaisawa Husna ta sauqo fuskanta da alamun bacci, Nafisa tace "Ke kuma daga Ina?" Na'ima tayi dariya sai Husna tace "Daga aikoni na kama bacci" sai ta zauna a qasan carpet ta gaishe da Mami, ta amsa da "Lafiya Husna, yasu Mamma?" Kwanciya ta sakeyi a qasan sannan tace "Lafiyansu..ita ta aikonin ma"...Bayan Nafisa ta taya Na'iman ta kawo musu ruwa sai suka cigaba da dafa abincin itada Husna while Mami ta kira Na'iman, zama tayi wani kujeran sai Mami tayi patting din gefenta tace "zo nan Habibti" cikin sanyin jiki ta zauna a gurbin, Mami na kallonta tace "ki fadamin me ya faru abayan, meya faru da Bilal din har kuka rabu ahaka" idon Na'ima an duqe tace "Wallahi bansani ba Mami" tace "Bangane baki sani ba, haka kurum kuka zauna a gidan kenan?" sai Na'ima ta girgiza kai tace "Bansani ba wallahi, da budurwarsa yake zuwa gidan, kuma ta hanasa kulani" shiru Mami tayi tana kallonta sai can tace "Kuma ko da wasa bai taba zuwa gareki ba" sai Na'ima tayi shiru cike da kunya, Mami ta kamo hannunta tace "Tell me everything daughter, I'm your mother, karki ji kunyata" ahankali Na'ima ta share hawayen da suka zo mata tace "Cemin yake mayya, kullum in yazo sai ya rinqa riqe kansa wai ina saka masa ciwon kai shine yake dukana in beyi ba" Mami na kallonta da mamaki tace "Kuma yar Ina ce budurwa tasa?" Na'ima ta amsa da "Bansani ba, bansan daga ina suke dawowa tare ba" sai Mami ta gyada kai tace "Hakan shi ya zamo alkhairy a gareki daughter, Allah ba azzalumin bawansa bane, Allah ya baki zaman lafiya da mijinki, ki riqe gidan ki kinji Na'ima, kiyi biyayya ga mijinki, duk abunda yace yanaso indai be saba shari'a ba kimasa cikin biyayya, nasanki da hakuri, toh inason ki linkashi yafi na da, Ahmad yana sonki kowa ya shaida dan haka karkiyi wautan amfani da hakan gurin cutar dashi kinji, mace me hankali da wayo amfani take da hakan gurin kame mijinta a jikinta bawai tayi using soyayyar nan against him ba, kiyi amfani da hakan gurin faranta masa da biya masa duk buqatunsa, in sha Allah zakiga daidai a rayuwanki" Na'ima a gyada kai ahankali ta amsa da "toh Mami" har sannan kanta a duqe, Nasiha sosai Mami ta mata mai ratsa jiki suna zaunen, sai da su Nafisa suka gama girkin gaba daya Mami ta sa suka taya Na'iman mopping din gidan da qara kintsa ko Ina sannan suka fara shirin tafiya..