KUNCIN ZUCI

Kuncin zuci

by @bintuuu

Washegari ya kasance Friday guraren 8:00 o'clock Na'ima na tsaye a kitchen tana hada musu breakfast, sanye take cikin riga da ya wuce gwiwanta yellow color daya haskata sosai, ga gashinta nan ta kulleshi in a bun, sai kai kawo takeyi a kitchen din Simba na biye da ita dan sai yanzu take ji ajikinta ba qaramin debe mata kewa zeyi ba in kadaici ya kamata a gidan, tana cikin fere dankali Ahmad ya shigo cikin singlet da dogon wando baqi, hannunsa riqe da waya yana duba abu sai Simba ya taho garesa nan Ahmad ya miqa kafansa daya yana masa wasa, Na'ima ta dan juyo tace "Good morning" sai ya qaraso gareta yayi pecking kanta yace "Morning wife" "how was your day going" sai ta nuna frying fan din gabanta tace "it goes like this" nan suka dan yi dariya dukansu, Ahmad yace "Sannu, da wanne zan tayaki" ya qarasa maganan tareda saka wayarsa aljihu sai ta turasa baya tace "ka tayani da zama" baya Ahmad yayi yana kallon rigan jikinta da kyau, sai ta kai hannu ta rufe fuskanta tace "Namanta, a falo zaka tayani zaman" nan ya fara dariya qasa qasa yana kallonta in a naughty way, kunya ce ta rufeta sai ta fara buga kafanta kadan kadan tace "Ni dai ka tafi" sai ya matso ya riqo waist dinta da dukkan hannayensa yace "in tafi gurinki kenan?" ta dan bugi qirjinsa tana murmushi tace "ka tafi can falo" sai ya girgiza kai, duqowa yayi tareda kwantar da muryarsa yace "Muje toh mu gaisa a falon" ta dago tace "mun gaisa yanzu fa" yana kallon idonta yace "Dayan gaisuwan" sai ta hau turasa baya yana dariya qasa qasa kawai ya dagata ya dorata akan kitchen island din, nan suka lalace ajikin juna kuma..Simba na ganin ikon Allah beyi breakfast ba, haka suka kama wata badakalen anan kitchen din, sai ga Na'ima riga ta sauqa har qasa Ahmad na yanda yaso da ita, qamshin tafasan shayin dake kan gas ne ya dawo da Na'ima hayyacinta tayi saurin riqe hannunsa dake qasanta ahankali tace "Zai qone fa" muryan Ahmad a daddafe yace "Barina kashe to" tace "Da ka bari na qarasa" sai ya girgiza kai ya nufi gas din ya kashe nan ya dawo ya sureta sai main falon nasu, hautsinata ya shiga yi son ransa itama tana biyesa, kissing dinta yake da dukkanin zuciyarsa, wani irin abu yakeji akanta kamar ya hadiyeta ma ya huta, Na'ima na hautsina masa tunani baya iya kama kanshi in anzo batun ta, yana kissing dinta ya dago kadan, cikin wata iriyar murya yace "My luscious" sai ta rufe ido tana murmushi, ya sake kissing dinta yace "I love u with everything in me" bai jira amsar ta ba yafara qoqarin rabata da lingeries din jikinta kawai suka Jiyo qarar shigowan mota a can compound, da sauri Na'ima tayi stiff nan ta fara qoqarin miqewa sai ta duqa zata jawo riganta ya rigata dauka yafara kokarin saka mata, sai da ya gyara mata rigan ajikinta sannan ya miqe ya nufi upstairs, bai dade ba yadawo hannunsa riqe da hijab dinta sannan t-shirt dinsa, nan ma saka mata yayi taki kallon idonsa sai kauda kai take, yana saka rigansa ajiki ya nufi kofa ya bude suka dawo falon tareda Anty Amnah tana gaba yana biye da ita, miqewa Na'ima tayi tafara mata sannu da zuwa sai ta karbi basket din hannunta, nan falon suka zauna Anty Amnah tace "Sannu daughter...ya jikin naki?" sai Na'ima ta duqar dakai cike da kunya, Ahmad ne ya gyara zama a kujera a nutse yace "Good morning Momma" ta amsa da "Lafiya Ahmad, ya ayyuka kuma?" yace "Alhamdulillah" Na'ima ce ta miqe duk a tsarge ta fara takawa ahankali ta nufi kitchen, bata dade ba ta dawo riqe da refreshments sai Anty tace ta dauko plate ga abinci nan ta kawo musu, nan ma ta sake komawa ta dauko ta zuba farfesun naman shanun da Antyn tayo musu, da bread ta hada musu sai ta zubo juye musu tea dinda suka katse tafasansa dazun, nan falon ta zauna a qasan carpet zataci abincin sai Anty Amnah ta miqa mata pillow ta zauna akai while Ahmad yana zaune bisa kujera ga breakfast din nan a gabansa bisa glass table yanaci anutse, hira suka rinqayi jefi jefi da Anty wanda shirun Ahmad yafi amsarsa yawa, suna cikin maganan ne Na'ima tace "Anty ya twins?" Anty Amnah tace "sunanan lafiya, zan koma next week in Allah ya yarda, dan jiya muna zoom call dasu Jafar yayi ta kuka wai in dawo" ta qarasa maganan tana murmushi, Na'ima tace "da an taho dasu ai Anty" tace "Ai time din zan tsaya a Dubai ne shiyasa, kinga kuma tafiya dasu din zai zama mun wani nauyin" sai sannan Ahmad yace "Then let me send for them, sai akawosu gobe" Anty Amnah ta juya garesa "A'a son, nima inada ayyukan da nakeso in koma nayi, my surgery appointments are piling up, i need to go back as soon as possible" Ahmad ya gyada kai cikin fahimta, sai da ya gama breakfast din sannan ya miqe anutse ya wuce part dinsa, nan Anty Amnah ta dan yi tambaoyinta ga Na'iman sannan sukaje dakinta ta dan duddubata, sai da Anty Amnah ta babbata shawarwari sosai game da yanda zata kula da kanta sannan ta fara shirin barin gidan, har compound suka rakata itada Ahmad tayi side hug ma Na'ima tace "toh Daughter Allah ya qara lafiya, in na tafi kuma may be sai wani lokacin" Na'ima na Jin hawaye na zuwa mata tace "zanzo Anty" tace "A'a badamuwa Na'ima, kar kiyi kuka ai muna tare, it's just a few hours flight fa" sai ta gyada kai tana share idanunta Ahmad ya riqo hannunta yana murmushi, Anty Amnah na murmushi ta shige mota tace "Son sai munyi waya" Ahmad yayi mata wave da hannu yace "take care Momma" da haka taja motanta zuwa gate suna kallonta, sai da ta fice Na'ima ta fara kukan kewa kadan kadan Ahmad na murmushi ya duqo ya hade goshinsu yace "My cry cry baby" nan ta dan qara sautin kukan nata sai ya fara dariya qasa qasa ya dauketa ajikinsa suka koma ciki.....

Misalin 11:30 na ranan Ahmad yana zaune a falonsa, laptop ce bisa lap dinsa ya dora feets dinsa kan glass table yana aiki da ita, time ya dauka sosai yana building wani App dinsa da ya fara developing tun kwanaki kuma bai samu nutsuwan cigaba da aiki akai ba, yananan zaune shiru sai ya dan dakata da typing din da yakeyin, anutse ya ajiye laptop din a gefensa ya miqe tareda ficewa daga side dinsa, falon Na'iman ya shiga nan ya sameta kwance a sofa tana bacci hankali kwance, ga Simba a dayan edge na kujeran shima yana tayata baccin, murmushi yayi sannan ya qarasa gareta yana kallonta, sai can kuma ya juya ya fita daga part din nata ya koma nasa, wanka yayi ya shirya cikin black half jamfa da ta fito da haibarsa sosai, yana tashin qamshi ya koma gurin Na'iman dan ganin ko da ta tashi amma har sannan baccinta takeyi sosai, bai tabata ba sanin zai iya tada ita sai ya sake ficewa ya nufi parking space....
A windscare Hospital yakai destination dinsa, ya fito yana taku a nutse ya shige cikin asibitin bai zarce ko ina ba sai dakin da Laila take, cikin sa'a ya sameta tareda Anty Ummi kadai a dakin, dago kai Laila tayi daga zaunen da taken sai ta fara murmushin ganinsa, Ummi ce ta fara gaishesa ya amsa casually sannan ya qarasa gurin gadon Lailan, kallonsa kawai take har ya jawo qaramin stool dinda ake zama kusa da gadon nata ya zauna shima, sai da ya dago ya kalleta sannan tayi saurin cewa "Ina kwana Yaya" yace "Lafiya" sai ta sake cewa "Yau ma Anty Amnah tace zata sallame ni, naji sauqi sosai" sai ta gyada kai, ta sake cewa "Yaya kayi hakuri da maganan da na fada ranan can, I was angry ne" sai sannan ya sake kallonta yace "saboda kin rainani ko?" tayi saurin girgiza kai tace "Wallahi A'a yaya" sai ya juya gurin Ummi yace "fita" ta miqe da dan hanzari ta fice daga dakin, nan ya maida hankalinsa gurin Laila yace "Yaushe na taba maganan aure dake?" tayi tsuru tsuru ya sake cewa "Jira kike ince ki amsa min?" tayi saurin cewa "Wallahi ba laifina bane Yaya...sonka nake shiy...." Katseta yayi da "Baki da hankali ne Laila? Haka akeyin son, wane irin tunani gareki ne?" sai ta duqar da kanta tafara kuka, rai abace Ahmad yace "wannan ba so bane Laila, wani ciwon ne kikeson dorawa kanki..this is purely madness, wani irin hali ne wannan? ki tuna ke mace ce fa" sai ta dago tace "Amma Yaya laifi ne dan nayi hakan don ka aureni?" mamaki ma ta basa ganin tayi nisa a tabarbarewa har bata gane abunda ba daidai ba, anutse yace "laifi ne, it is purely hypocrite of you to do that, sannan after that..Meye hadin ki da Saddam?" Sai ta dago kai a firgice tana kallonsa, kasa magana Laila tayi a wannan lokacin tanajin zuciyarta na bugawa sosai, cikin bacin rai Ahmad yace "You're claiming kina sona kuma kina son aurena and then kin qulla irin wannan alaqan da Saddam, Then.. wane irin so ne hakan? Anya kinada tunani Laila?" sai ta fashe da kuka tafara bashi hakuri, rai abace "Shut up...kar in sake ganinki tareda Saddam, I'm telling you this as your brother, idan na sakejin ko da labarin an ganki da wani namijin a waje Billahi sai na karyaki" kasa dago kai tayi, rai abace yace "Stupid girl, tarbiyar da zaki kai gidan mijinki kenan, kina tunanin in kin tafi a hakan akwai me iya zaman aure dake?...By Allah I'm giving you a final warning kar ki kuskura in sake jin wani rashin hankalin ya bullo daga gurinki dan bansan iya hukuncin da zan miki ba nima" sai sannan ta amsa da "Toh Yaya" da haka ya miqe ya fice daga dakin ransa abace...

Fitan Ahmad daga Asibitin ya dauki hanyar zuwa central mosque domin samun sallahn juma'a, bai samu fita ba sai misalin karfe biyu da wasu mintuna, yana driving ahanya ya kira Na'ima, jin bata dauka ba ya ajiye wayan sannan nufi hanyar zuwa gida gurin iyayensa, time dinda ya isa gidan ya samu Baba ya dawo daga masallacin tareda baqi sai be shiga gurinsu direct ba ya wuce part din mahaifiyarsa, samunta yayi a falonta tareda su Fatima da ta kawo musu ziyara itama, nan ya samu guri bisa kujeran ya zauna sannan ya gaisheda Mamma a nutse, amsawa tayi da fara'a tace "Ya Habibti? tana lafiya?" Ya amsa da "lafiyanta" sai tace "kayi magana da ita sai in sa akai mata me tayata aiki, gidan nan ya mata girma tayi aikinsa ita kadai" amsawa yayi da "toh" da haka kuma ya kishingida jikin kujeran sai Fatima da Ummi suka gaishe ya amsa da "lafiya" tareda miqa hannu zuwa ga hamra dake kusa da mamanta, da saurinta ta tako garesa tana murmushi sannan ta haye jikinsa kamar wanda dama can ta sanshi, Fatima tace "Yaya ya anty Na'ima" anutse ya amsa da "tana lafiya" sai ya kalli Ummi yace "sai nace kuje kenan?" da sauri tace "A'a Yaya, jiya mukayi maganan da su sumayya akan sai Sunday zamuje mu gaisheta" Mamma tace "Yakamata" da haka tasa ummin ta kawo masa abinci da drinks masu sanyi ya sauqo qasa kusada mahaifiyar tashi yanaci suna magana jefi jefi, cin abincin yake anutse at the same time yana feeding hamra dake kusa dashi tanaci kadan kadan, acikin hiran ne suka iso kan maganar abunda Lailan tayi sai ummi ta miqe asannu ta fita daga dakin while Fatima ta dake ta zauna dan itama bakinta cike yake da maganganu, Mamma na kallon Ahmad din tace "Banaso ko da wasa ka amincewa mahaifinka da batun auren yarinyar nan, babanta sai sintiri yake a gidan nan kwanannan kuma duk munsan menene musabbabin hakan, dan jiya mahaifinka saida ya sakomin maganar ta" Ahmad ya dakata da cin abincin sa anutse yace "Ban taba kawo aurenta araina ba Mamma" tace "wai ko da zeyi convincing dinka ne ai, yarinya kwata kwata babu kintsi a lamuranta, ace wai iyayen ma sun zuba mata idanu tana abunda taga dama kamar ba mace ba, toh banaso...kar in sake inji ka amince da batun zaka aureta dan duk uwa ta gari bazata so ta hada zuriya da me irin halinta ba, muna mata fatan shiriya tunda muma ba wayon mu bane ya kintsa mana namu 'ya'yan, Kuma da ace iyayen nata suna qoqarin gyaran tarbiyar nata ne ma, toh da lamarin zaizo da sauqi, amma ace kome yarinya tayi kuna gani ba daidai ba amma ku bita da idanu, wannan ba daidai bane kwata kwata" Fatima ta gyada kai cikin gamsuwa, sai Ahmad ya sauqe numfashi yace "Duk yanda kika ce din haka za'ayi" anutse tace "Allah yayi albarka" ya amsa da "Amin" da haka ya zuba ruwa me sanyi a cup yakai bakinsa, aransa yana tunanin ta ina daman zai fara auren Laila, yarinyar da ko da wasa bai taba jin sha'awan dogon magana da ita ba balle har batun aure....