Kuncin zuci
by @bintuuu
Bayan Ahmad y fito daga part din mahaifiyarsa sai ya ga Anty zaune a main falon gidan itada twins dinta safiya da sumayya sannan ummi da tayi joining dinsu not long ago, a nutse ya sauqo daga stairs din ya qaraso gurinsu sai ya zauna a kujeran dake facing din Anty, calmly yace "Ina wuni" Anty na kallonsa tadanyi murmushi tace "Lafiya, ya mai jiki?" ya amsa da "Alhamdulillah" nan sukayi shiru sai qannen nasa suka gaishesa ya amsa, ganin ba sake wani maganan zeyi da Antyn ba yasashi miqewa tareda nufan bangaren mahaifinsa, shida ita hakan take tun fil azal, babu me shiga harkan dan'uwansa in ba gaisuwa ba kuma bawai dan suna gaba ko wani abu ba, yana gidan tana gidan suna iya sati basu hadu ba in ba dai anan falon ba ko in yaje side din mahaifinsa, shigarsa falon ya samu Baban zaune da wani amininsa sannan Abba cikon na ukunsu, nan qasa kan carpet din falon Ahmad ya zauna cikin ladabi ya gaishe da iyayen nasa suka amsa Baba yace "ya mai jiki, numfashin ya daidaita ko?" Ahmad ya amsa da "Alhamdulillah" Abba ma ya tambayesa ya jikin Na'iman nan ma ya amsa da Alhamdulillah, hira suka dan taba kadan game da batun ayyukan Ahmad din, Baba yace "Inason muyi magana kuma bansamu nutsuwa ba kwana biyun can" Ahmad ya gyada kai yana sauraron mahaifin nasa, sai can Baba yace "kaje dubo qanwar take a asibitin bayan nan?" Ahmad ya amsa da "Eh dazu na dubota" Baba yace "Ma sha Allah, ya jikin nata?" yace "Alhamdulillah" anutse Baba yace "Wane hukuncin ka yanke game da al'amarin nan?" sai Ahmad ya duqar dakansa bai ce komai ba, ganin haka sai Baba ya sake cewa "Baka tunanin auren ta ne Ahmad" nan ma ya qi dago kansa amma a hankali ya girgiza kansa, sai Baban yace "Magana nakeson muyi ta fahimta dakai" Ahmad yace "Ban taba ganinta a wani matsayin ba face qanwata" sai Baba yace "Bazaka iya aurenta ba kenan?" Ahmad ya amsa da "Bana mata so na aure" shiru sukayi har Abban suna kallonsa, sai Aminin baban yace "Ka gama magana son" Abba yace "Hakane" sai Baba yace "Amma inace in ka auretan zaka iya son ta ai" Ahmad be dago ba ya girgiza kai ahankali yace "Bani da tabbacin hakan Baba, inason matata banason ranan lahira in tashi da shanyayyen bari guda, bani da tabbacin zan iya yin adalci a tsakaninsu" Abba ya gyada kai cike da gamsuwa, Aminin Baba ya sake cewa "Kafa gama magana son, Allah yana gani ka fadi gaskiyarka" sai Baba ya sauqe numfashi yace "Toh..Allah yasa hakan shi yafi alkhairi" duk suka amsa da Amin har Ahmad din da har sannan bai dago ya kallesu ba, da haka ya miqe bayan sun sallameshi ya fice daga falon suna kallonsa, har ya bar gidan wani irin feelings yake ji aransa, ji yake kamar ya kauda storm dinda ke shirin tasowa ya masa kutse tsakaninsa da Na'imarsa wanda bayida tabbacin jure hakan a rayuwansa, zuciyarsa ce take ta tafiya zuwa gareta a wannan lokacin, har da azamansa na qara gudun motansa yana muradin isa gida gareta.....
Daren ranan Ahmad na zaune a falon qasa yana aiki bisa laptop dinsa Na'ima ta fito daga corridor'n kitchen hannunta riqe da tray dauke da tea kettle da cups, qarasowa tayi sai Ahmad yadan gyara kafarsa dake miqe akan glass table din sannan ta ajiye tray din ta zuba masa a cup ta miqa masa, ajiye computern yayi a gefe sannan ya karba yana murmushin kadan yace "Allah ya miki albarka" , murmushin tayi itama sai ta matso garesa ta dauke Simba dake zaune gefensa tayiwa kanta mazauni agurin, sai da Ahmad ya kurbi tea din sannan ya juyo gareta yace "Babe yayi dadi" tana kallonsa tace "it's just tea fa?" sai yadanyi dariya yace "I'm serious wife, kin iya sosai" tana murmushi tace "thank you" sai taga ya tsaya kallonta, dan ware masa idanunta tayi alamun "meya faru?" sai yace "Babe baki sake fadan sunan can ba...Ina sane fa" sai ta juya kai tana murmushi, can kuma tadan miqo masa tafin hannunta alamun yabata abu, yana kallon hannun yace "Mene?" ta juyo tace "Oya bribe me" sai yadan ware ido dariya na zuwa masa yace "what?" tana kallonsa ta juya idonta sukayi sama sannan tadawo dasu qasa ahankali, wani irin mamaki yayi harda bude baki yana dan dariya yace "yarinyar nan waya koya miki wannan abun" sai tayi dariya kadan tace "baka iya juya idanu ba kaddai" sai ya ajiye tea din ya fara matsowa yace "ki koyamin" sai Na'ima tayi baya bata bar dariyan ba tace "A'a basai ka matso ba, daga nan din ma yayi" bai fasa matsowan ba yayi qasa da murya "kusa da kusa zai fi" nan tayi baya sai taji ta kwanta kan kujeran shikuma ya mata rumfa tana murmushi duk yana kallonta, dan dakatawa tayi tana kallonsa at the same time zuciyar ta na sauya bugu, shiru sukayi ahakan sai Ahmad ya kwanto jikinta ahankali tareda dora kansa a qirjinta fuskarsa na kallon gefe, ahankali Na'ima takai hannu cikin lallausar sumar kansa tana shafawa asannu tana kallon sama sukayi shiru ahakan, sun dauki almost 15 minutes ahakan babu wanda ya sake cewa komai acikinsu, Ahmad ya rufe idonsa yana sauraron bugun zuciyarta, cikin sanyin murya Na'ima tace "Ahmad" sai ya bude idanunsa, ahankali ya amsa da "Na'eemah" tana kallon saman tace "duk sunan da zan kiraka dashi sai inji kafi qarfinsa a wajena" sai ya dan dago kansa yana kallonta, cikin kwantar da murya yace "da sunan, da babu sunan, you're still the world to me...." ya maida kansa ya kwantar a qirjinta, anutse ya sake cewa "You're my Home Na'eemah..." sai takai hannunta ahankali tayi wrapping bayansa tanajin soyayyarsa na sake mamaye duk jiki da bargonta, haka suka sakeyin wani shirun anan kwancen while zuciyoyinsu ne kawai ke magantuwa da juna.. Da sukazo kwanciya shima babu magana sai wanzar da soyayyar suke a aikace, kowa na muradin farantawa dan'uwansa, Na'ima da kanta ta rinqa welcoming din kowanne saqonsa gareta at the same time tana maida masa martanin dake sake haukatshi cikin soyayyarta, ba ya iya fadin komai a wannan lokacin sai sunanta, every touches and kisses yanayinsu ne cike da ambaton sunanta, da ya nemi shiga hanyarsa sai ta qanqame idanunta cikin qwarin gwiwa na sallama masa komai amma da Ahmad ya dago ya kalleta sai ya dakata, kallonta ya rinqa yin ganin yanda ta qanqame idanunta ga hawaye na bin gefen fuskarta suna isa kan pillon da take kwance akai, sai ya duqa ahankali yayi kissing goshinta, ya sake kissing din same place again, sannan ya mirgina zuwa gefenta yana dan maida numfashi, hannuwansa ya miqa tareda da rungumota jikinsa ya sake kissing goshinta tana jinsa, sai nan kuma hawayen suka fara zuba daga idonta babu qaqqautawa, cikin rawan murya tace "I'm sorry" sai ya sake qanqameta yace "Don't be...it's not your fault, and I'll wait....kinji" sai tayi shiru batace komai ba, nan ya sake rada mata "Nima bana iya riqe kaina ne shiyasa" sai ta damqe idonta cike da kunya, sai Ahmad ya sauqo da hannunsa kadan zuwa bayanta yafara shafa bare skin dinta ahankali, shiru sukayi ahakan na wani lokaci sannan ya kwantar da murya yace "tell me what happened?" "Meya faru a tsakaninki dashi bai sanki ba" bude idanunta tayi nan ma batace komai ba, sai ya rada mata "Tell me kinji, abun ya tsayamin arai na Babe" cikin sanyinta tace "kirana yake da mayya, bansan meyasa yake dafa kansa ba in yazo gurina" sai Ahmad ya dan dagota yace "And kuna hada shimfida kuma" sai ta kauda idonta ta gyada kai ahankali, kallonta ya rinqa yi baya kifta ido sai can kuma ya fara murmushi, Jin yayi shiru dayawa yasa Na'iman juyowa ta kallesa sai taga yana murmushi, sai ta samu kanta da cewa "karka fadi maganan dake bakinka please" nan kuwa ya fara dariya qasa qasa yace "Kuma kin tabbatar Namiji ne? Kin duba da kyau kuwa?" dasauri tajuya tace "Oh God...Ahmaaad" sai ya fara qoqarin juyo da ita bai bar dariyan ba yace "Like how can a full grown Man resist a woman like you...I wonder" sai yakai hannu yafara kokarin sauqe duvet dinda ta rufe qirjinta dashi, da sauri ta riqe duvet tace "Dan Allah kabari" yace "So nake in qara tabbatar da lafiyata nima" sai ta rufe idanunta tace "Ahmaaad" bai bar dariyan ba ya sake shigewa cikin duvet din ya mata rumfa, yace "then i'm glad you became the witch, take my soul instead" nan ya sake hade bakinsu akaro da ba adadi ya hau sake jagwalgwalata son ransa sannan sukayo wanka akayi baccin....
Washegari Ahmad bai dawo daga sallahn asuba da wuri ba sai da garin yadan fara haske, dawowarsa ya samu har Na'ima ta koma wani baccin hankali kwance, qarasawa yayi gareta yana kallonta sai can yayi murmushi ya nufi cikin closet dinsa bai dade ba yadawo sanye da qananan kaya wanda rigan ta kasance fara me laushi tareda black facing cap da tayi matching da baqin wandonsa, sannan ya sake dawowa gurin Na'iman ya cire cap ya duqo yayi pecking bakinta kadan, cikin baccin ta dan bude ido kadan tana kallonsa sai ya mata rada da "Sleep jewel, zan fita yanzu i won't take long kinji" sai ta gyada kai tace "Lafiya" yayi murmushi yana kallon idonta yace "Babu komai, bazan wani dade ba sosai" nan ma ta gyada kai sannan ya miqe ya maida cap dinsa ya nufi kofan fita tana kallonsa, da sauri securities din suka bude masa kofa ganin ya tada motan da haka ya fice suna gaishesa ya amsa shima, hanya ya dauka kamar ze bar cikin Abuja sannan ya bi titin da zai kaishi warehouse dinda packages dinsa suke ajiye tun tuni, a lokacin da yayi parking motarsa agaban babban gidan ko Ina yayi tar dan gari ya dade da wayewa, dago hannunsa yayi ya duba wristwatch dinsa ganin time yaja sosai kafin ya iso, anutse ya shiga gidan sai ya wuce direct main building din cikin makeken compound din madadin ya je inda su Bilal din suke, waya yaciro ya kira Mazzy, yana dagawa yace "I'm here" da haka ya qarasa ya kwankwasa wata makekiyar kofa, nan aka bude yaron Mazzy ya masa iso cikin wani daki babba dake dauke da komai na falo da Kuma working station dake can end din dakin, Mazzy ne ya taso daga kujera ya qaraso garesa sukayi shake sai Ahmad ya zauna kan leathers seat din dake kusa dashi sannan Mazzy ya zauna suka gaisa, sai da suka dan taba maganganunsu akan batun Tiyagah sannan Ahmad yace "bring him to me" sanin wayake nufi yasa Mazzy yin alamu ga yaransa guda biyu suka fice, sunanan zaune yaran suka dawo riqe da Bilal da ya rame duk ya lalace sai wani fari da ya sake yi, kansa a duqe suka zaunar dashi a qasa sai Ahmad yace su maidashi kan kujera, hakan sukayi sai yazamo Ahmad dashi din suna facing juna, anutse Ahmad ya juya yana kallon Mazzay, ganin haka sai ya miqe ahankali suka fice shiga yaran nasa aka bar Ahmad da Bilal din zaune adakin, anutse Ahmad yace "I married her" sai Bilal ya dago kai da sauri suka hada Ido, Ahmad na kallonsa cikin ido yace "And i won" "kuma nayi abunda kayi qaryan kayi, i did it with her" sai Bilal ya kai hannu ya dafa kansa duk Ahmad na kallonsa, can kuma ya dago kai fuskar nan tayi jaa, cikin rawan jiki yace "Ka barni in tafi Dan Allah, na yarda kayi nasara, daman tun can na fadi hakan ne dan in rama dukan da kamin, in kana qaunar iyayenka ka barni in tafi" sai ya sauqo daga kujeran yace "Dan Allah" da haka ya sauqe kansa saiga hawaye suna diga a qasa, Ahmad yace "Zaka tafi, Amma ka sani...Billahi ko dogon kallo kayi mata sai na ballaka Bilal, akan Na'eemah ni kaina i don't know what i'm capable of doing" Bilal ya dago kai idanunsa har sannan da ruwan hawaye yace "Qanwata ce fa" Ahmad yace "I don't care, in kuma so kake inyi extending zaman ka anan, then go ahead" da sauri Bilal ya girgiza kai "Dan Allah ka barni in tafi, iyayane sunacan hankalinsu ba'a kwance ba" Ahmad ya gyara zama yace "Daman kasan da hakan kake zamanka a wani qasar tareda wata baka nemansu?, kana da wannan hankalin daman, ban taba sanin kana dashi ba, scars din da nagani abayan matata beyi kama da kana da kwakwalwa ba Bilal" sai Bilal yafara kuka ahankali, Ahmad ya miqe batareda ya sake kallonsa ba ya fice yabarsa nan duqe a qasa yana kukan.....
Bintu Musa✍️