KUNCIN ZUCI

Kuncin zuci

by @bintuuu

Safiyar ranan bayan Na'ima ta farka daga baccin ta miqe zaune ahankali tana miqa, sai da tadan jira ta warware a zaunen sannan ta sauqa daga gadon, sanye take cikin white t-shirt din Ahmad wanda ya zamo so baggy ajikinta dan jiyan da kansa ya dauko ya saka mata bayan ya gama badakalensa da ita, da asuba ma da itan tayi sallah a jikinta bayan ta saka dogon wando da babban hijab, downstairs ta nufa tana daure gashinta sannan ta saka hulan da ta riqo a hannunta, shiga kitchen tayi nan ta yi feeding Simba dake biye da ita kaman jela tana kallonsa, saida ta tabbatar ya qoshi sannan ta sake fita ta fara gyara gidan, da part din Ahmad ta fara, tana ta shige da ficen aikin Simba na biye da ita, har walk in closet dinsa ta shiga amma sai taga gurin a kimtse sai kamshi ma room din yake, nan ta debo daidaikun qananan kayansa da taga yayi hanging a gurin da yake ajiye kayan da ya riga ya saka sannan ta hau wanke masa su cikin washing machine dinsa dake nan cikin babban toilet din nasa, sai da ta tabbatar ta gyara duk inda ba'a kimtse ba agidan sannan ta nufi kitchen...
Ba ita ta nutsu ba sai around 9 o'clock, tana zaune a falonta suna waya da Mami tajiyo qaran shigowan mota agidan, ta daya bangaren Mami tace "Abu sun kiraki kuwa" tace "A'a Mami, wani abune?" tace "naji sunce zasuzo ne jiya" Nafisa dake gefe tayi maganan da Na'iman tajiyo ta "Mami it's a surprise visit fa, you ruin it....Habaaa" sai Mami ta danyi dariya while Na'ima na tayata, tace "toh Ina nasani bayan basu fadamin hakan ba" Na'ima na murmushi tace "Inaga anjima zasuzo" sai Nafisa ta sake matsowa jikin wayan tace "Bobo just act surprised when they come, they've been planning it" bata bar murmushin ba tace "toh, nima gobe zanzo" Mami tace "A'a Habibti kiyi zamanki yayi wuri fitan, gashi baki gama samun sauqi ba. Kibari ba yanzu ba kinji ko" ahankali ta amsa da "Yes Mami" sai suka hau maganan building din Nafisan da ake ta qoqarin qarasawa, bude kofan falon akayi Ahmad ya shigo sai ta dago kai tana kallonsa waya kare a kunnenta, miqewa tayi itama ta fara nufansa suka hade a tsakiyar falon yayi hugging dinta, Na'ima na sauraron Nafisa daga can bangaren tace "float glasses din zasu iso cikin satin nan, sai kinzo zaki nunamin ta inda yakamata asakaminsu cikin office din, inata chanja shawara ni kadai" Ahmad na saurarensu ya sake burying fuskansa a wuyan Na'iman, sai ta amsawa Nafisan da "toh sis bakomai, in nazo sai muyi shawaran yanda za'a sakasu din" Nafee tace "Alright take care...sai anjima" da haka sukayi ending call din sai Na'ima ta fara murmushi tareda wrapping hannunta a bayan da tace "Sannu da dawowa" dagowa yayi yace "kinyi baccin?" tana kallonsa tace "Eh saura kai, amma sai kayi breakfast tukun" yayi murmushi sannan yayi baya yana kallon rigan jikinta da ta kasance budaddiya daga sama, kauda kai Na'ima tayi tana murmushi sai ya sake riqota yace "Babe you look yummy" batasan lokacin da tadan bugi qirjinsa ba suka fara dariya qasa qasa, ya sake rada mata "So yummy and deliciously beautiful" tace "Abinci na zama kuma?" yana murmushi yakai bakinsa kunnenta "Abinci na, and I'll keep tasting every nook of you until you're breathless" da sauri ta rufe idonta tana dariya, cikin sanyinta tace "This is so dirty, baka kunya ta ma" yadan ware ido yace "Au kinzata ina kunyarki?....jewel the signs are there even before we get married fa" tace "uhm uhm nidai bakayin haka" sai ya duqo ahankali yace "I levelled up darling" ta kwantar da kanta a qirjinsa tana murmushi while shima haka...
Bayan ya fito daga wankan ya sameta acikin closet dinsa tana nema masa kayan da zai saka, qin kallonsa tayi tana duba wani shelve da yayi hanging kayan shan iskansa, ahankali ya qaraso gareta ya rungumota ta baya, sai tayi stiff batareda ta juyo ba tanajin damshin ruwan jikinsa yana sauqa a bayanta, ya kwantar da murya yace "Wife, let's explore this feelings together please" tayi shiru bata ce komai ba, ya sake hayo da hannunsa zuwa kirjinta yana shafawa a hankali, rufe idonta tayi sai yayi qanqan da murya "ki daina jin kunyata kinji Na'eemah" wani irin abu ta rinqa Jin yana bin jikinta gaba daya sai tayi saurin bude idanunta ta gyada kai kar hakan ya kaisu ruwa kuma, ahankali takai hannu tana nuna masa wani riga tace "wannan ya maka?" sai ya dago kai yace "shi kikeso in saka?" Ta gyada kai sai yace "toh Babe...shi zan saka" da haka ta miqa hannu ta zaro rigan daga jikin hanger, sai ta juyo tace "Muje ka shirya, bakaci abinci ba" ya gyada kai ta riqe hannunsa ya bita suka fita daga dakin bayan ta dauka masa kayan da zai saka, nan dakin ya saka kayan tana tsaye gabansa sai kauda ido take ganin yana yin komansa a gabanta hankali kwance yana kallonta shikuwa sai murmushi yake, sai da ya gama sakawa sannan ya duqo yayi kissing goshinta yace "thank you Babe, naga kin wanke min kaya, but ki bari kinji inada mai yimin zai rinqa zuwa yanayi every week" tace "zan iya ai" ya girgiza kai yace "No ban yarda ba, that's final" sai ta gyada kai batace komai ba ya sake cewa "Allah ya miki albarka" tana murmushi tace "Amin" suka fice daga dakin...A main falon gidan yasa ta kawo masa breakfast din nasa yanaci still yana bata a baki tana nonnokewa, bayan sun gama takai komai kitchen ta dauraye sai tayi tunanin fara wani girkin da zata tarbi su Abu dashi, tana cikin aikin nata Ahmad ya shigo kitchen din, yana kallonta yace "Babe wani aikin kike? Muje ki huta" ta girgiza kai tace "su Abu zasuzo may be nan bada jimawa ba" sai ya qaraso gareta yace "toh ki kawo wani abun in tayaki kinji" murmushi tayi tace "zaka iya matse lemon" ya wani gyara tsayuwa yace "ranan nan fa kawai Husna ta tayani ne" Na'ima ta hau dariya tace "A'a ka dai fara da wannan din sai ingani" sai ya amsa da "Yes your highness" da haka ya nufi fridge ya dauko fruits, saida ya wankesu tas a sink din kusa da ita sannan ya yanka Apple din ya jerasa a gefen berries da grapes din, kawo mata yayi kusa da ita yace "Babe kici wannan" ta amsa da toh amma ganin hannunta da mixer tana hadin cake sai ya dauka yana miqa mata baki tanaci a hankali yana kallon yanda machine din ke juya komai, anan kan island din ya fara tayata tana zubawa cikin cups dinsu zata kai oven, suna cikin yi ta juya ta kallesa ganin yanda yake zubawa ta fara murmushi tace "kana zuba dayawa fa" idonsa na kan abunda yakeyin yace "Kedai wait and see" sai ya daddage ya sake jibga wani acikin cup din, da sauri ta riqo hannunsa tana dariya tace "Boo..." dariyan ya fara yi shima yace "idonki neh yasa yayi yawa Babe, ki daina kallo" bata bar dariyan ba ta fara gyara wanda ya zuba din tace "barina sake kwatanta maka" sai ya gyada kai yana kallon yanda take sakawan a hankali, nan ya sake gyara tsayuwa shima yafara bin yanda takeyin, yanayi yana kallon nata har suka gama ta dauka babban tray din takai cikin oven sannan ta koma gurin girkin da takeyi, aikin takeyi yana dan taya ta hira jefi jefi, gashi komai yaga tana yi sai yace zai tayata amma daga ya fara sai komai ya tafi downhill har sai ta qara kwatanta masa, sauqin ta ma yanada saurin fahimta da koyan abu da wuri shiyasa in ta kwatanta masa zai dan tafi daidai in his second try, saida ta gama zuba abincin a flask sannan yana biye da ita abaya kaman jela suka nufi gurin oven din ta ciro cakes din da suke ta tashin qamshi, nan kan kitchen island din ta ajiye tray din ganin su so yummy yasa shi miqa hannu zai dauki daya tayi saurin cewa "Boo da zafi" da haka ta dauki daya ta bude tare da yankawa in pieces and the next thing she did yayi melting zuciyar Ahmad yana kallonta, daukan daya tayi ta ruha shi har ya huce sannan ta miqo masa a baki tana murmushi, and that little gesture melt his heart while he's smiling at her too...yana cin cake din sama sama ya bi kitchen din da kallo sannan yace "Babe you need a house help gaskiya, haka kikeyin ayyukan ke kadai" sai tayi murmushi tace "Ina iyawa ai babu komai" ya girgiza kai yace "No, it's too much for you, Mamma tamin maganan but na shafa'a ne ban fada miki ba" tace "Ai bana komai for now, chores din ba komai bane" yace "Please ki amince min Babe, this is your house, sai da amincewar ki za'a kawo miki mutum cikinsa" shiru tayi tana kallonsa sai ya sake cewa "kinji" gyada kai tayi ahankali sai yayi murmushi yace "Karki damu, zan debe miki kewa in kika rasa abunyi" da haka ya ajiye cake din ya matso, cikin kwantar da murya yace "Besides....we have so many unfinished businesses" sai ta fara dariya tana girgiza kai tace "Ya zanyi dakai  ne ma Ahmaad" yana dariya qasa qasa yace "Ki so ni kawai ya isheni, ni zanyi sauran ayyukan" kawai ta miqe tana murmushi ta nufi fita daga kitchen ya miqe shima yabi bayanta yana fadin "Lokacin business din yayi kenan" yana qoqarin cafkota ta dan yi qara tareda saurin guduwa daga kitchen din tana dariya yabi bayanta suka fice daga kitchen cikin annushuwan zuci....

Sai around 12:30 su Abu da Al'ameen suka iso gidan, zuwa lokacin Ahmad yana kwance a dakin Na'ima yana ta baccin da bai samu yayi da safiyar ranan ba, Kiran Na'iman sukayi lokacin da suke bakin gate din farko sai ta bada izini ga securities din suka barsu suka shigo, fita tayi daga dakin tabar Ahmad kwance ta nufi  compound din daidai lokacin da suke fitowa daga mota sai ta dan ware baki da mamaki ganin sun taho mata da motarta, Abu yayi driving aciki while Al'ameen ya taho a tasa, suna murmushi suka qaraso gareta Abu na fadin "Mami tace mu taho miki da ita ana ta ajiyanta babu mai hawa" sai Na'ima tayi murmushi tace "Meyasa bakayin amfani da ita ba toh?" yace "Tawa ta iso fa" ta dan ware idanu "Haba? yaushe?"  Al'ameen yace "Anty yanzu Kuma hankalina ya koma kan tasa, irinta zan iya" sai Na'ima tayi dariya tace "Kuma dai" Abu na murmushi ya miqa hannunsa ya dan tari ruwan dake flowing acikin fountain din compound din sannan ya kalleta yace "Ai bakyanan suka saka min ido har da Anty Nafisa, nima nace indai ta siya irinta zan kyautar da nawan ma ba siyarwa ba" nan sukayi dariya gaba daya Na'ima tace "ka rama kenan" da haka ta sake cewa "sannunku da zuwa, mu shiga ciki" da fara'a suka shige cikin gidan tana gaba suna biye da ita, a corridor Abu yaga Simba sai ga duqa ya daukesa yace "Anty wa ya kawo muku mage?" tace "Nasa ne, from England" sai ya shafa kansa yace "Yamin kyau" tayi murmushi batace komai b, sai da ta kawo musu refreshments sannan ta zauna suka gaisa tace "Nafee ta fita gurin aikin ne" Abu ya amsa da "Sai da mukayi dropping dinta sannan muka taho nan, Abba yanacan ma shida Yaya already, it's weekend sun samu time" Na'ima tace "Ma sha Allah, Allah ya sanya alkhairy" Al'ameen yace  "Anty dama business dinki kikayi akan bank dinnan, it's an exhausting work wallahi" Abu ya qara da "Be your own Boss Anty" muryan Ahmad sukaji yace "A boss with her own rules ba" duk suka juya suka kallesa yana sauqowa daga stairs din a nutse, da fara'a Abu yace "Yaya barka da rana" gyada kai yayi sannan ya qaraso tareda miqa hannu akowannen su sukayi musabaha, kujeran da Na'ima take kai ya zaune a gefenta tareda barin gap tsakaninsu sai ya kishingida kadan wanda hakan ya zame masa sabo, nan ya fara tambayansu ya gida suka amsa sannan yace "shawara me kyau kuka kawowa Antyn taku har gida kenan" sukayi murmushi Abu yace "Ai Yaya ayanda naga Yaya faruk yana fama da office work duk sai naji banaso" Ahmad yace "Ya fasa komawa kanon?" Al'ameen yace "sunyi maganan da Abba jiya, I think zeyi running office branch din Abba nacan" sai Ahmad ya gyada kai tareda juyawa ya karbi cool drink din da Na'ima ta miqo masa a cup yace "thank you"... Hira suka dan yi sannan suka tafi masjid yin sallah bayan sun dawo ta kawo musu abinci sukaci suna hiran, basu tashi tafiya ba sai bayan la'asar, time dinda suka fito compound din tare dasu zasu tafin sai Al'ameen yace "Anty zan koma school this coming Tuesday" sai fara'an Na'ima ya washe daga fuskarta, Abu na murmushi yace "shiyasa bai fada miki ba yace sai mun shirya komawa" sai tace "Kuma sai yaushe zaka dawo" da fara'a ya amsa da "I'll be attending a summit program in Cairo on 26th of next month, zan iya dawowa gida immediately after that" Ahmad yace "You mean A26?" ya amsa da "Yes shine, Aetherforge 26 in Zamalek ba?" sai Ahmad ya gyada kai tareda miqa masa hannu yace "Ma sha Allah, see you then" da haka suka sake musabahan , jiki a sanyaye  Na'ima tace "Allah ya taimaka" sai ta kalli Abu tace "Amma tafiyanka school ba yanzu ba ai ko" yace "Nima in the next three weeks zan tafi" nan taji jikinta ya qara yin sanyin tace "Ina ne?" yace "Heidelberg, Germany" Ahmad yace "Allah ya bada sa'a, I'll check on you someday" suka amsa da "toh Yaya mungode" da haka suka shige mota, Na'ima sai danne hawayenta take tana daga musu hannu har suka bar compound din, Ahmad ne ya kamo hannunta sai ta juyo idanunta cike da kwalla ta kallesa, dan kwanto da ita yayi a qirjinsa yace "zan fara hana baqi zuwa mana yanzu, suna saki kuka dear" ta girgiza kai tace "We'll miss them" yace "Zasu dawo fa, it's just school, kowa ma haka yayi" sai ta gyada kai batace komai ba, yana shafa bayanta yace "Toh ki shirya gobe Sunday mu fita muma, muje ki gaisa dasu Baba da Mamma" sai sannan taji ranta ya fara sauqa tace "Allah ya kaimu" da haka ya kama hannunta suka koma ciki.....