Bayan Murmushi

Chapter 18

by @zahrabmrs02

page 18💬⌨️

farooq pov

Na lura da canji a wajen Farhana waɗannan kwanaki. Yau kwana biyu kenan bata online. Mafi yawan lokaci wayarta bata shiga, koma menene ay Wednesday zan dawo Nigeria Na tabbata ta koma school kafin nan.Farooq a ransa ya ayyana: “Tunanin me kake yi haka Lamido?”

Safina yayar Farooq, ta tambaye shi cike da raha: “Ba komai sis, kawai dai bana samun Farhana a waya. Ina tunanin Allah yasa lafiya,” ya furta a sanyaye. “Maybe wayar ta sami matsala, beside mun kusa komawa Naija, sai kaje ka ganta.”

Kalmar Safina tayi tasiri a zuciyar Farooq. Shopping dinsu suka ci gaba da yi; duk abinda Farooq ya gani mai kyau sai ya É—aukar wa Farhana. Har Safina na tsokanar sa akan kar ya qarar wa mamma kudin ATM dinta.

Alhamdulillah, jikin mamma yayi kyau, ta warke sumul, hankula duk son kwanta.

Farooq da Safina sun koma hotel dinsu, inda suka tarar da Mamma da Husna, yayarsu  suna hira.

“Mamma, ga tsarabar Farhana,” Farooq ya fada yana mika wa Mamma ledar shopping bag ɗin.

“Ah, masha Allah! Ka iya zaÉ“e Lamido, sirakata zata ji daÉ—in kayan nan,” Mamma ta ce cike da annashuwa.Farooq ya amsa da murmushi, yayin da Husna ke dudduba kayan“Yanzu da gaske auren zaka yi lamido ?You’re just 25, kaine autan mu, kuma kai kadai ne na namiji a gidan mu ,ka bari nan gaba idan ka zama very steady sai  mu shirya gagarumin biki.”

A kyale mun Auta ya huta. Tunda auren yake so, gara a masa. Yaron da bai taba zancen buduwar ba, babanku zai je kai kudin gaisuwa gidansu Farhana next week, inshaAllah,” Mamma ta fada tana karɓar zancen.

“Kai Mamma, zan so naga Farhanan da ta sace muku zuciya keda Lamido,” cewar Husna tana murmushi. “Ina son duk abinda Auta ke so in ji, Mamma.”

“Nima na Ć™osa na ga Farhana da Lamido ya ishe mu da zancen ta.cewar  Safina.

Safina na aure Abuja da yaranta uku, yayinda Husna ke Kano da yara hudu. Su uku kadai Mamma ta haifa kafin rabuwar su da baban su Farooq.

WhatsApp call ne ya shigo wayar Farooq. Ya É—auka tare da sallama.

Adda Sabrina ta gabbatar da kanta, suka gaisa a mutunce.

“Farooq, akwai magana da zamuyi, dan Allah ka fahimce ni,” ta fara.

Daga nan Adda Sabrina ta ba Farooq cikakken bayani kan duk abinda ya faru da yadda auren Farhana ya kasance.

Jinsa daukewa yayi na É—an seconds, gif su Mamma su ji faduwar Farooq rike da waya.

A bangaren gidansu AK kuwa, Momy ta wakilta Safiyya da Fadila akan ragamar hada lefen farhana Dan kiri-kiri, Ramla ta rantse bazata shiga harkar biki ba, kasancewar tafi kusa da Hanadi tafi kowa daukar zafii

mommy Ta ce kuma su tabbatar komai daga aljihun AK ya fito.

Hanadi ta rage walwala, amma bata nuna damuwarta a fili. Ko ba komai, tayiwa Farhana nisa ta kowani fanni. Abuja zasu koma da AK saboda school É—in yara.

“Hello Anty Farhana, ina yini?” aka fada.Bayan Farhana  ta  dauki kiran  .Fadila Tahir Tambuwal ce ,qanwar yaya AK ce ta qara fada 

“Ya kk?” Fadila yaa gida, farhna ta amsa murya a sake.

“Am good, Alhamdulillah,” fadila tace,Dama yaya Safiyya ce tace na kira ki. Muna bukatar sizes dinki na shoes, undies, sai kuma favorite colors dinki,” Fadila ta fada cike da faar ah.

Zan miki text, Fadila,” ta qara fada a sanyaye.

“Yauwa, kuma ki bamu list ɗin friends dinki. Su nawa ne? Zamu turo da ankon su.

 sai da tayi maganar qawaye zee adetayo  ta fado min, “yau kwana 3 tana kirana da message na kasa dauka. Hellooo Anty Farhana, are there?”

Muryar Fadila ta dawo dani.

“Uhmm… anko kuma na tambaya?

“Eh, zamuyi dinner da Budar Kai,cewar fadila .Naso nace bana so amma na yi shiru.

“To, zan tura miki komai, Fadila. Idan akwai wacce zaki haɗani da ita a cikin friend ɗinki, sai ki bani number ta Fadila ta ƙara da cewa.

zan turo miki da number ta.

“To, sai anjima, Anty Farhana Fadila ta ce tana kashe wayar ta . tsaki yaya  Safiyya tayi Shiyasa nace ki kirata, Fadila, ji yadda take magana… ba alamar wayewa.local ce daga jinta wallahi 

“Idan ta turo miki details, ki yi mi forwarding, wallahi sai account AK yayi kuka,” cewar Yaya Safiyya, tana hayewa sama.

Rudewa Mamma tayi, suna ta shafawa Farooq ruwa a fuska.

“Lamido, tashi! Me ke faruwa? Waya kira?”

Bude ido yayi a hankali. Maganar Adda Sabrina ce ta dawo masa da hankali:

“Aure? Farhana?”

Bude baki yayi zai yi magana, amma ya kasa. Bai taɓa son abu kamar yadda yake son Farhana ba… ya zata masa haka?

Tashi ya fara ƙoƙari yin zai ɗauki wayarsa, jiri ne ya kwashe shi, tif! Ya ƙara faɗowa.

A gefe guda, Hanadi da AK sun yi sallama da Mummy, sun ɗau hanyar airport zasu koma Abuja, inda Mummy ta ƙara jaddawa wa Hanadi: suna tare da ita, komai rintsi. ramla da safiyya jibi zasu bi bayansu dan zuwa nanda 2 weeks zaa fara shirin tariyar amaraya da dinner .

zee kiyi hakuri naga messages dinki na misscalls bana cikin yanayin da zan iya daukar kiran ki ,farhana ke fada bayan zee ta dauki wayarta

ki bar komai idan kin shigo school zamu tattauna zee ta mayar da martani.bazan dawo school ba an min auren ranar friday na fada a sanyaye 

aure?how ?wat?saurin me farooq din yake haka farhana ?zee ta fada a razane,ba farooq na aura ba .na sake fada ,what the hell zee ta fada da karfi,kardai kice mun jafar ne ya dawo?

labarin abinda ya faru farhana ta kwashewa zee harda yarda AK ya mata makirci wajan abbi ,wanda abbi ya dauka soayyaya suke shiyasa ya bashi auren.sallalami zee ta fara mamaki ,aljabi. yanzu wani mataki kk dauka ?murmushi nayi me ciwo wani mataki zan dauka kuwa na rungume kaddara ta nayi kuka idona har zafi suke min ,adda ta amsa number farooq zata masa bayani Allah yasa ya fahimceni,zan taho abuja jibi farhana dik dazu nima na shigo school  zee tace sanyaye ,aa ki bari zee zasuyi biki sai kizo,zan turawa fadila qanwar Ak number ki sai kuyi maganar shirye shirye rauni sosai a cikin muryata ,yan room dinku son sani ?zee ta qara tambaya ,aa zan kirasu conference call ko zuwa gobe ne.to Allah yasa hakan ne mafi alkairi saida safe kuma ki kwnatar da hankalin ki dan Allah oremi

awa biyu kenan da tashin farooq banda kukan zuci ba abinda yake  ,mamma tayi tayi yaki magana .rufe ido yayi kamar mai bacci a hankali suka fice tare da rufo masa kofar,dazu husna ta kawo masa wayarsa bayan ta koma hotel.

kiran farhana yayi ta WhatsApp dinta cos tinda yazo ta WhatsApp suke waya. be siya sim din cairo ba ,a cewarsa ay ba dadewa zasuyi ba  .

luckily tana online ,duk ringing din wayar tare da zuciyarsa take bugawa

sunan farooq ta gani a saman screen dinta  rudewa tayi ,accepting call din tayi tare da wasti da Allah ya isan da AK ya mata ……..