MUMINA KO AZZALUMA

Chapter 13

by @sadisakhna

⚫ *MUMINAH DA AZZALUMA*⚫



⚫ _SADISAKHNA_⚫




⚫ *BOOK 1*⚫



⚫ _PART 13_⚫



Buɗe idonta tayi kana ta sake lumshesu,wani irin nauyi da sukayi mata,a haka tayi ta ƙoƙari jikinta babu ƙarfi har ta samu damar tashi zaune a tsakiyar gadon.
Hango kanta tayi a madubin jikin wardrop yayi bitsi bitsi dashi kaman mahaukaciya sabon kamu. Idon kuma ya ɗan kumbura na alamun nauyayyen baccin daya dauketa.
Hannunta tasaka tareda bugun goshinta sannan taja dogon numfashi.
"Ohhh shitt nasan wannan aikin zeezah ne,na hanata sakamin Alcohol vipe amma bataji,i don't like this drowness"
Wayarta ce tayi ƙara tana cikin juye juyen
Dubata takeyi harta samota a ƙarshin gado,tana buɗewa zaro ido tayi ganin missed call sunfi goma na wata nurse ɗaya daga cikin mutanenta.
Message ɗin data turomata ganin bata ɗaga wayar ba tashiga karantawa.
"Hi madam na ƙiraki baki ɗaga ba,ɗazu Amjad yazo da wata leda ɗaukeda safar hannu a ciki da kuma wata riga dukka da jini a jikinsu,yabada anyi gwajin DNA dana wani majinyaci da suka kawo Rai a hannun Allah,kuma yayi matching jininsa ne. Likitan yace in yasan wanda ya aikata hakan yakamata a sanar da ƴan sanda,amma sai yace wai bayason kowa yasan zancen. Daya fito daga asibitin ya tada mota,nabi bayansa domin naga ina zayyi,saikuma naga ya nufo nan gidan inda kike. I think he figure something madam"
Wani abu ƙwaƙwalwarta tariyo mata,ta sauri ta sauƙo daga kan gadon tana jujjuya ido alamar mai tunani.
"Ahmad yashigo ɗakinnan jiya da daddare,kuma tabbas nayi magana dashi. Ohh god nasan daƙyar in ban faɗamasa abinda yafaru ba jiya,babbar tantama ta mutuminnan nasane,sannan munyi tracking ɗinsa bamu ganshi ba,da alamun sun samoshi kenan. Shikenan idan na faɗamasa to asirina in bai tonu bama yana dabb da shirin tonuwa........kai yama tonu zama bai kamani ba dole naje wajen zeezah,aiki baƙi ba ja ba ya ballo mana"

Tunda ya shigo ɗakin take binsa da kallo ko gaisuwar da yayi mata bata amsa ba,kwata kwata hankalinta ya shagala da kallon yanayinsa da kuma son gano mai yake damunsa.
Shima tsarguwa yayi da yanda ta kafeshi da ido,dan haka ya ɗago kansa dayake sunkuye suka haɗa ido. Kawar da nasa yayi tareda ƙwaƙwulo wani murmushin dole yayi.
"Ummee menene kiketa kallona haka,ƙalau fah nake babu abinda yake damuna"
"Babu abinda yake damunnaka ka kwana bakayi bacci ba,kowa ya kalli idonka ai yasan baka samu hutun da kowanne ɗan adam akeso ya samuba idan dare yayi"
"Ehh bansamu nayi bacci ba na tsaya duba wani aikine"
"Hmmmm shikenan Allah ya kyauta,koma menene ba laifinka bane laifinmu ne ya kamata a duba lamarin. Yanzu dai ba wannan ba,tunda ka gama karyawar maganace Babanku yabani na baka. Jiya Uwar taku Hunaiza taje ta Sameshi a falo sun tattauna,tace tana neman alfarma a wajensa kan ya haɗaku aure kaida Safeenah saboda ƙarin danƙon zumunci. Ka girmi auren dole,amma dai bai yada maganarta ta ba yabani saƙo na faɗamaka shin ya kake gani,saboda yasan tsakaninka da matarka yanda kuke son juna,kada ya amince kai kuma zuciyarka ba haka bane azo a samu wata matsala ta bullo. Shin ya kake gani zaka aureta ko kuma ......."
"A ɗaura auren kawai duk sanda suka shirya itama ta shirya kuma kuka shirya,ni zan wuce office ummi idan muka gaisa da Mama. Ina fatan ita ta kasance alkhairi"
"Tohh uhmm banace komai ba,to yaushe kake ganin zakaje wajenta kaji mai da mai take so saboda tunda ka amince yanzu a matsayin mai shirin zama matarka take ba ƙanwarka ba,dolene koda sau ɗayane ka tashi takanas kaje ka kuyi magana ta fahimtar juna.
Wata ƴar dariyar takaici yayi tareda kallon agogo.
"Hhhh haba ummee inje wajenta kuma,nace da ita me? Ba dama naji labarin ana cewa wannan ne burinta,to tunda ta samu ai murnar dazatayi ma ya isheta,banda bango ya tsage kinsan Ummee da bazan bar ƙadangare ya samu damar shigowa ba. Kawai kuyi komai yanda ya dace,infact ni inada tafiya abroad ma zuwa jibi,kuma zan iya yin Two month a can,kafin nadawo sai kuyi duk abinda ya dace"
Yana gama faɗin hakan ya ɗauki jakarsa tareda gyara rigarsa ya bar bangaren.
Ɗan murmushi Hajiya Ummee tayi tareda jijjiga kai. 
"Hmmm namiji dai idan bayason abu ko? Ina tausaya miki Hunaiza daga ke har Safeenah,wanann gurgun burin zuciyar taki babu abinda zai haifar maki sai ɗa marar ido. Ace kai bakada zabin kanka saina ƴaƴanka,kuma in antabasu kaman an soka maka mashi. Duk da ban taba haihuwa ba amma rashin kawaicin Hunaiza yayi yawa"
"Ummee dawa kike,Da maman Safeenah koh,hmmmm bakiga ma rawar kan da Safeenah take a makaranta ba,wai yau mamanta tayiwa Abba magana kan aurensu itada Yah Ahmad,wai tariga ta tabbatar ma dolene zai amince,har ta fara yiwa mutane burgar wai takusa zama Mrs Amjad,bakiga ba har sabin ƙawaye tayi. Kullum ina faɗamata ta amince da saurayinta Ridwan ta ƙyale batun ya Ahmad amma taƙi sam,ya Ahmad bazai taba amincewa ya aureta ba"
"Amincewa kuma na nawa,yariga ya amince ai"
Zaro ido tayi tareda dafe ƙirji kafin tace.
"Ehh ya amince Ummee,kuma Safeenah kaman ta sani tace tanada tabbacin dole zai amince.....mtsss ni Ummee anya kuwa Safeenah da Baaba Hunaiza ba Asiri sukeyiwa Yah Ahmad ba,domin daga yanayin confident ɗinta alamar saida ta shirya kafin ta......"
"Ke Nimrah to kuma surutunnaki yana shirin wuce gona da iri,zato ance zunubi ko ya kasance gaskiya,kuma kada ki manta Safeenah ƴar uwarki ce koma ya take,haka uwarta itama uwa take a gareki tunda cikinsu ɗaya da ubanki. Inma asiri suke Allah ya ganar dasu su daina,inkuma shi suka zaba zai basu nasara ba Allah ba nan ma ga wajennan mai fili da mai doki sau suyita sukuwa. Kedai kiyi shuru da bakinki ki zubawa sarautar Allah ido,na sanki da shegen surutu,da Zainab ce ba ruwanta,amma ke kam hmmmm"
Da haka Hajiya Ummee ta kwa'bi Nimrah daga 'barin zancen da takeyi zancen ya mutu a wajen.



Amin magana ta wannan layin 
***
Sadi-sakhna ce.