MUMINA KO AZZALUMA

Chapter 14

by @sadisakhna

⚫ *MUMINAH DA AZZALUMA*⚫



⚫ _SADISAKHNA_⚫




⚫ *BOOK 1*⚫



⚫ _PART 14_⚫


Tunda yaje Office ɗin kaman abin arziƙi ya wuce kansa tsaye ya zauna akan kujerar amma ya zubawa wasu takardu ido ya gagara rubuta komai a cikinsu,gabaɗaya ma tunaninsa baya cikin office ɗin yana wata duniya daban.
Ƙarar wayar security line ne ta firgitoshi ya kalli wajen tareda miƙa hannu ya ɗauka.Gaisheshi akayi daga ɗaya bangaren ya amsa a taƙaice tareda nunawa wanda ya ƙirashin yatafi kai tsaye da bayaninsa kada ya bata masa lokaci.
"Am sir batun bincike dakace muyine gameda hoton daka turo mana,maganar gaskiya abin ya ɗauremana kai,mai wannan sunan mutane dayawa sunce tayi aiki har anan companyn  a kaduna,amma kuma sam babu wani record nata a cikin bayananmu,kuma ance bata daɗe ba ta daina,sannan zancen ya jima zaikai shekara shida haka. Toh amma yallabai wannan ba hoton madam bane,mai yakawota yin aiki anan companyn to kafin ku haɗu,dama kasan tayi aiki anan ne kafin ka aureta?"
"Kaga bincike nasa kayimin ba tambaya nace kayimin ba Naseer,kawai na baka nan da wasu lokuta ka ganomin menene dalilin dayasa taje can ɗin aiki,wanne aiki tayi,adadin wanne lokaci ta ɗauka a garin. Babban ma'aikacina mai wannan aikin yanzu haka bashida lafiya amma bari zan haɗaka da wani anan wanda zai tayaka. Zan tafi germany akan wani aiki idan nadawo zan nemeka gameda ƙarin bayani. Kafin sannan please focus and found reasonable things"
Bayan sunyi sallama wayar office ɗin Saleem yaƙira ko yana nan,haka kawai yaji yanaso suyi magana koda kuwa na faɗane da suka saba wani lokacin. Bata gama ringing ba ya katse tareda tashi ya nufi office ɗinnasa da kansa.
Da sauri ta fito daga cikin gidan da makullin mota a hannunta,duk da tana Ƙoƙarin saita kanta amma kallo ɗaya mai hankali zayyi mata ya tabbatar hankalin ta ba'a saiti yake ba.
"Sauri kike ina zuwa haka,ko labarin zan shigo cikin gidan kai kikaji har kin fara birkicewa"
Harta riƙe maruƙar ƙofar zata buɗe sai kuma ta tsaya tareda juyowa ta kalli mai maganar.
Safeenah ce sanye da riga da wando na palazo tayi rolling ɗan ƙaramin gyale a wuyanta,farace amma sam Safeenah batada jiki,haka zalika kyau na fuska ma saidai muce alhamdulillah kawai.
Ƙaremata kallo Surayyah tayi daga sama har ƙasa kafin tace.
"Wanne gidan zaki shigo?"
"Cikin gidanki mana,hala to bakida labari Yah Ahmad ya amince da aurenmu,ki shiryar tarbata a matsayin kishiyarki nan da wasu watanni masu zuwa,bake kina sunkuyar dakai wai ke ga mutuniyar kirki kingama sace zuciyarsa baya ganin kowa saike ba? Tun ba'aje ko ina ba gashi ya dawo daga rakiyarki akalar hankalin sa ya dawo kaina. Ki zuba ido kiga yanda zan shigo gidan kallo ma sai yagagareki samu daga wajensa"
Tana maganar ne tana jujjuya ido tareda rangwaɗa kaman an ciro tarwaɗa daga cikin ruwa.
Wata arniyar dariya da Surayyah ta sheqe da itane yasa Safeenah tsayawa da maganar tayi sororo tana kallonta.
"Dama keɗin kina maganane,ai bansani ba sai yau. To in gidane waya hanaki shiga,yanzu ma gashinan kije ki ɗauko kayanki ki shiga mana.Kinga in bama nan mun samu mai gyaran gidan dayin abinci. Dama yace bayacin abincin ƴan aiki,faɗuwa tazo daidai da zama,naji ance ke ƴar uwarsace maybe zaici naki musamman in kika zama matar tasa."
Buɗe motarta tayi tashiga,har tayi ribas zata fita ta leƙo da kanta inda Safeenah take daskare tace.
"Amm idan mai gadi yazo kice yabaki key guda ɗayane wajena,inkin masa abincin ki ajiyemin,amma kinsan cikine dani bana cin curry dan haka kada kisaka"
Ɗan murmushi tayi bayan ta mayar dakan tareda cewa.
"Nice mutuniyar kirkin ko? Zaki kuwa gane kuranki,zakuna suna faɗa kina ƴar ƙaramar akuya zaki shigo tsakani.  Ina tausaya miki sosai,i swear you may suffer girl"
Waƙar davido tasake a motar,sautin yana tashi da ƙarfi tana ni tana karkaɗa kai,kaman ba dambun cakwakiyane a gabanta ba.
 Bayan ta bar wajen Safeenah ta daɗe kafin ta rufe bakinta wanda tasakeshi batareda tasani ba,kanta ta ɗauke daga kallon inda motar tabi kafin ta nufi sashensu,a ranta banda saƙe saƙe babu abinda takeyi.
Babu sallama tashiga falon,Hajiya Hunaiza ce zaune itada wata ƙawarta Wai ita Madam Aliya babbar matace amma daga ganinta kasan wayewa tayi wani abu waishi zama a jikinta.
"Tana saida duk wani nau'i na kayan mata,mallaka dakuma na kaucewa hanya. Sannan tana haɗa kayan kitchen kayan ɗaki da dukkan abinda yashafi amare in mutum yanaso. A online suka haɗu,tace zatazo Abuja Hajiya Hunaiza taroqi akan tazo su gaisa"
Baki a kumbure tashigo falon,kai tsaye inda hajiya Hunaiza ke zaune ta nufa tareda kwanciya akan cinyarta.
"Ohh ke kuma daga ina haka,hala kun sake faɗa keda Nimrah,domin nasan haka kuke saikace ƙananun yara"
"Ahah ni banganta bama yau balle muyi faɗa,daga sashen yah Ahmad nake,naje na tabattarwa Surayyah zan zama kishiyarta,amma saikuma naga kaman abun bai dameta na,har cewa tayi idan inaso yauma na dawo sashen bai dameta ba"
"Hhhhhh ke har yanzu yarinya ce,ya dameta kenan tunda har tatsaya ta saurareki kuma ta faɗamiki haka, babu wata mace da zata samu miji kamar Ahmad za'ayi mata kishiya tace kuma bai dameta ba,musamman ma ta yake bata kulawa taga ya sauya ya daina bata,ƙarshe yace zai ƙara aure kuma bataji komai ba? Wannan ai zancene. Shakuruminki ƴar nan ai watan damu damarne ya kama. Zan haɗamiki magunguna masu kyau da tsada,ai tunda ya amince shine farkon babbar nasararmu,wani abun saima kin shiga daga ciki. Inta kama ma waje kawai zamuyi da ita. Kiyi zamanki keda yayanki,gaba in kika tara zuri'a kuma mu fara tunanin malllakar campanoni"
Duk abinda suke madam Aliya tana kallonsu banda murmushi babu abinda takeyi.
"Hmmm ai kisha kuruminki yarinya daminki ne ya tsinke a gindin kaba,indai mallakarsane kuma kuna tareda ni kaman kunyine,ke iyayensa ma saikinga dama yaje inda suke"
Kallonta Safeenah tayi saikuma ta kalli hajiya Hunaiza akan ta gaskata mata zancen matar. Ɗaga mata kai tayi alamar eh,wanda hakan yasakata sakin murmushin daɗi.



Amin magana ta wannan layin 
***
Sadi-sakhna ce.