MUMINA KO AZZALUMA

Chapter 16

by @sadisakhna

⚫ *MUMINAH DA AZZALUMA*⚫

 Available on:wattpad&arewabook



⚫ _SADISAKHNA_⚫




⚫ *BOOK 1*⚫



⚫ _PART 16_⚫



"Alfarma nakeso kiyimin,wannan matar zaki nemomin,a ina take wanne hali take ciki?
Tana gama maganar ta miƙamata wani hoto,hannu tasaka ta karba tareda yin murmushi.
"Wannan ai......."
"Ehh itace inaya,nayi mata wani abun da bana tunanin zan iya mantawa,bayan mun rabu a bakin makaranta kince idan inada wata alfarma na ƙiraki zakiyimin to ga wanann ki taimaka ki nemomin inda dake dan Allah,kafin ki tafi wajen mijinnaki"
"To shikenan bari zan duba a nahiyar nan da kewaye ki bani nan da kwana biyu,tunda bansan inda take ba saina duba"
Tashi tayi tabi wata hanya a gidan,jimm kaɗan sai gata ta fito da tire a hannunta. Ajiyewa tayi a gaban Surayyah,kayan marmari ne masu kyau sau kuma wani jug da ruwan inibi a cikinsa.
Kallon abubuwan Surayyah tayi kaman mai tantama,duk da a fuska tana nuna jarumta amma kallo ɗaya mutum zai mata ya tabbatar a tsorace take da inda taken.
Ƴar dariya Inaya tayi tasake tura mata tiren gabanta a hankali.
"Habadai Ƙawata da alama har yanzu kin kasa gasgata cewar ni bamai cutarwa bace a gareki,koda wani zaiji tsoron zama kusadani a tunanina bandake ciki,kada ki manta tun aji ɗaya na makarantar boarding muke tare a matsayin aminai har muka gama. Duk da cewar ba jinsinmu ɗaya ba amma kinsan bazan cutar dake ba. Naga kinada cikine shiyasa naje gonarmu na yanko miki kayan marmarin dazasuyi miki amfani. Ni ban tambayeki bama hala kinyi aurene?"
"Uhmmm nayi aure,da bansan ke wacece ba shiyasa,amma danasani kinsan yanayin bazai zama kaman da ba"
"Ƴar hararar wasa inaya tayi mata kafin tace,hmmm kin manta a makaranta kaman bakece mai nuna kece shugaba ba,ba wanda kika raina kamanni,amma yanzu ni kike taoro?"
"Uhmmm rayuwar makaranta ba,inna tuna nakanyi dariya ni kaɗai,saidai nakanji wani iri idan nasake tunawa ashe ƙawata uda ɗaya tall danayi rayuwa da ita na shekara shida ba jinsi na bace,abin yana ɗauremin kai kaman a mafarki. To ma taya kika boyeminne ko kika boyewa kowa a makaranta har malamai?"
"Wannan ba sabon abu bane kuma ba kaina farau ba,domin ɗauke kewa ko kuma samun wata ƙaruwa mukanyi cuɗanya da mutane tsawon shekaru batareda sun sani ba. Ko a makarantar ma bani kaɗai bace akwai wasu,saidai bama cutar da kowa,mukanyi har meeting na abinda yake faruwa damu da daddare idan kunyi bacci."
"Ina fatan dai yanxu kin daina hulɗa da wannan jinsinnamu wanda ba nagari ba dana sha gagargaɗinki ki rabu dasu"
Inaya tayi maganar tana ɗan ɗaure fuska.
Wani juyi da ido Surayyah tayi kafin ta ɗora da cewar.
"Haba no wonder ni sai yanzu ma abin ya dawomin,taya kikasan mai nake aikatawa,duk bankawo haka ba sai yanzu,ashe danke ba mutum bace. Karki damu Inaya wannan duk zai wuce,ke kanki shaidace da inda na fito,idan ba haka ba to da yanzu bana raye"
"Karkice haka Surayyah ita mutuwa ai lokaci ce,idan tazo ko ka kauce hanya domin kare kanka ko baka kauce ba to saita ɗaukeka"
"Uhmm to nagode Inaya ni zan tafi kar Ahmad ya nemeni,sai kuma yaushe zaki dawo?"
"Kiyi haƙuri a yau ne ganawarmu ta ƙarshe,inna tafi ba lallai nadawo yankinnan ba,yanzunnan ya aiko min saƙo kan na taho da komai nawa,saidai idan nazo yawo in Allah yaso zan nemeki. Saƙonki kuma inna bincika zan aika a kaimiki har gida"
Duk da cewar Allah Allah Surayyah take tabar wajen amma haka kawai taji wani iri datace mata wataƙila haɗuwar ƙarshe sukayi.
Har bakin wajen motar ta ta rakota,daganan sukayi sallama saida taga tafiyar Surayyah kafin tayi murmushi ta bace batttt😜 (nima na bace na daina rubutun?)
Ga wanda basu fahimta ba..... Inaya Aljana ce kuma ƙawa ga Surayyah dasukayi makarantar secondry ta kwana tare. Har suka gama gwagwarmayar su suka kwana tare suka tashi tare Surayyah batasan Inaya Aljana ce ba saida suka zo rabuwa a ranar yin candy take faɗamata ainihin ita wacece,sannan tayi mata kwatancen yanda zata sameta idan tanaso tayi mata wani abu. Duk da a tsorace Surayyah ta rabu da ƙawarta ta da taji cewar ita wacece? Hakan bai hana ta tuna kwatancen datayi mata,bata kuma taba nemanta ba ko tunawa da ita sai yau da buƙatar hakan ta taso mata.
Wayar tace tayi ringing tana cikin tafiya a motar bayan tashigo cikin gari. Tana ɗauka sunan bro ne ya fito akan wayar. Da kaman bazata ɗaga ba saikuma ta ɗauka batareda tace komai ba.
"Hello aunty Surayyah wai kina garinnan kuwa,Mama tace rabonki da kizo gida anfi wata huɗu,yanxu ma batada lafiya dawowarmu kenan daga asibiti hawan jininta ya tashi,kowa yaje amma babu wanda yaganki sai tambayarki ake,kowa yana cewa yanxu bakya ƙiransa a ƴan uwa gabaɗaya kin sauya"
"Kaga naji wannan ƙorafin,yanzu dai ina maman take ya jikinnata?"
"Da sauƙi sosai ta ɗan warware ma"
"Ohk bari na dawo daga wani wajene bari naje gida na shirya gani nan zuwa"
Bayan ta kashe wayar tabe baki tayi tareda juya ido.
"Ohh again mutum bashida hutu daga wannan sai wannan wai,ni marana ma ji nayi kaman ciwo take this irritating pregnancy wlh da baikai wannan girman ba zubar shi zanyi don ya isheni,to ma meyasa ma na yarda na barshine,a garin kwaɗayina na haɗa kaina da wuya,gashi yanxu it became useless mtsww"
Ita kaɗai take tafiya tana masifa harta isa gida.
Babu kowa a gidan data shigo alamar gogan bai dawo ba kenan. Watsa ruwa tayi ta sanja kaya,cikinta a cike yake da kayan marmarin datasha a gidan inaya dan haka hanyar ƙofa tayi zata fita.
Ta buɗe kenan sukaci karo da Nimrah zata shigo.
"Ahh aunty Surayyah fita zaki sake yi kenan?"
"Eh ko kin bani aikin wani abune banyi ba kike tuhumata"
"Ahah ba haka bane dama Hajiya Ummee ce take ƙiranki akan zakuyi magana,sannan sunga kin daɗe baki shigo ba sukace nazo na duba in jikinne suzo dubaki"
Ɗan juya ido tayi,ashe fah ita rabonta da shiga sashen mutanen gidan shima anyi wata huɗun,gabaɗaya ta manta da wasu sashenma a gidan bayan nasu.
"Kice musu ƙalau nake ni babu abinda yake damuna. Batun wama kikace sunan ta,hajiya waye? ......tajirani akwai inda zanje idan nadawo naga inada time ban gaji ba zanzo"
"Hajiya Ummeen ce zata jiraki?!!!......"
Nimrah ta faɗa tana zaro ido.
"To so what bazata jirani ba,nima wajen tawa uwar zanje batada lafiya,ko ganin tawa uwar zan ajiye naje ganin ta wani. Dan haka kaman yanda ta aikoki in kinaga zaki sake maida aiken kice da inda zani tajirani saina dawo"
Tana gama faɗin hakan tashiga mota tasake fita a gidan.
Sororo Nimrah tabita da kallo tana jijjiga kai kaman ƙadangare.
"Hmmm ba ina faɗamusu wannan matar ta kwance ba batada mutunci amma saisu hauni da masifa su hanani faɗa waisu ga dattijai iyayen dattaku,inama a gabansu tayi wannan tujarar naga ya zasuyi tabbb. Aike na kawo miki kam kema kika bani zan kuwa je na faɗamusu yanda kikace. Inkuma suka ƙi yarda zan zuba musu ido. Idan kere na yawo zabo ma na yawo ai dole zasu haɗu. Tunda kinayi ba ƙarya nake ba wataran dole zakiyi a gabansu su gani ai"
🥱🥱🥱 To nima sadi-sakhna nace zatayi kam.....ku jama'a aradu bacci nakeji,kafin sumayya ta tashi nima barina ɗan runtsa koh?"




Amin magana ta wannan layin 
***
Sadi-sakhna ce.