Chapter 17
by @sadisakhna
⚫ *MUMINAH DA AZZALUMA*⚫
Available on:wattpad&arewabook
⚫ _SADISAKHNA_⚫
⚫ *BOOK 1*⚫
⚫ _PART 17_⚫
"Yeee ga aunty Surayyah tazo,Granny kinga aunty Surayyah tazo"
Ƴar yarinyace take maganar wacce bazata wuce shekara shida ba,kyakkyawa ce anyi mata kitso a dogon gashinta ta sha riga ƴar kanti pink mai kyau.
Da gudu ta tafi ta rungume Surayyah data fito a cikin mota.
"Aunty Surayyah inasu Farhana baki taho dasu ba,kullum fah dasu kike zuwa amma yau bakizo dasu ba. Aunty ina chacolate ɗina,ina yau kam zaki ɗanani a mota kaman yanda kikace jiyaaa?"
Duk wannan surutun tana riƙeda ƙafar Surayyah takeyinsa,ko ɗaya bata bata amsa ba amma hakan bashi ya hanata yin shuru ta daina tambayar ba.
Wani tabe baki Surayyah tayi ta juya ido kafin ta matsar da yarinyar gefe a hankali cikin dabara.
Ɗan murmushi tayi mata tareda cewa.
"Intisar ina mamanki?"
"Uhmmm tana part ɗinmu"
"Yawwa to maza jeki kice mata nazo ko?"
Ɗan bata rai tayi alamar batason tafiyar tareda noƙe kafaɗa,jakar hannun Surayyah take kalla,da alama wani abun take tunanin samu a ciki. A bangaren Surayyah kuma gabaɗaya yarinyar ta dameta.
Muryar Mama sukaji tanayiwa Intisar magana.
"Inti jeki maza wajen mommy ko,kinga yau auntynnaki batajin daɗin biyeki kuyi tayi kamar kullum kinji"
Badan taso ba ta nufi hanyar sashennasu,Mama tabita da ido tana murmushi. Ƴar yayansu Surayyah ne na fari,anan cikin gidan yayi aure a nasa part ɗin. Intisar itace babbar ƴarsa saikuma Saddiq shikuma ƙaramine bai wuce shekara uku ba.
Juyawa Mama tayi zuwa sashennata yayinta itama Surayyah tabita.
A falo suka zauna dukkansu,saidai suna shigowa Mama tasaka ƴar aikinta ta kawowa Surayyah ruwa.
"Mama na sameku lafiya ya jikin,haka Faisal yace bakiji daɗi ba harda asibiti"
"Eh wlh amma dai ba mai tsanani bane sosai kwana na ɗaya,har yayanku yafara faɗa akan ya bakizo ba nace su barki kema ba daɗi kikejiba,wanda bashi kaɗai ba baya rabuwa da laulayi dole a dunga yi masa uzuri. Ya can wajennaku dai ƙalau ko,su hajiya mama da Ummee,ina cewa dai zansaka Faisal ya kaini mu gaisa to kinga lafiyarce gabaɗaya taƙi daɗi sam.
"Hmm hakane kam,to Allah yaƙara sauƙi"
"Ameen ya Allah,ni ya zancen fara kasuwancinnaki kinfara ne ko har yanzu kina nan dai zaune a gidan. Ba'a haka Surayyah,gwara kiɗan samu wani abun ki dungayi,duk da cewa miji yanada rufin asiri amma iya juya taro zuwa sisin shima wani abune,zaki dungayiwa kanki wani abun batareda miji yasani ba"
Shuru Surayyah tayi tana sunkuyar dakai daga baya kuma tace.
"Ehh yanzun kam banayi amma zaije ƙasar waje bari inya dawo zanyi masa maganar naga mai zan fara"
"Kin fasa yin harka Kayan sakawar kenan. Shikenan duk yanda kukayi dai Allah yasaka albarka ya inganta,baki tambayi mutuniyar taki ba,dazu kuwa tagama ƙorafin kin daɗe bakizo ba,itama bata daɗe da fita ba"
"Ohhh Ameera? Ni sungama makarantar ne"
"Ahah da dan saura dai,set ɗinsu ɗaya dasu zainab ai ƙanwar taki. Ana ta fama dai aski yazo gaban goshi. Kije ku gaisa da Babannku yana ɗakinsa,da kuma hajiyan Su Faisal kafin nan bari nima nayi sallar la'asar"
"To shikenan bari na shiga sashen su intisar mu gaisa nima"
Daga haka Surayyah ta tashi ta nufi wani bangare na gidan.
Bayan ta fita Tashi mommy tayi tai sallah,daga nan da kanta tashiga kitchen yimata abin ƙwalama na masu ciki.
Ɗan na sululu tayi mata yasha kayan vegitable da kuma manja da yaji. Mai aikinsu tana cikin jerawa Surayyah tashigo falon,abinka da dama masu ciki lokaci guda yawunta ya tsinke tana lelleƙawa taga ta inda ƙamshin yake tashi.
Bismillah mommy tayi mata ta juice na ginger shima an ɗan matsa masa lemon tsami.
Tana ci tana lumshe ido tana kora lemon saida ta kusa ganin bayan kwanon kafin ta sarara. Duk da AC dake falon amma ta haɗa gumi sai shishutu take saboda yanda take barbaɗa yaji.
"Kai Mommy amma abinnan akwai daɗi,anya kuwa na taba ci?,gaskiya inaga rabon danayi ƙoshi irin wannan harna manta,nake cewa ni bana laulayi na zaben abinci ashe bansamu bane. Dan Allah mommy a ina zan dunga samun irin waɗannan abubuwan?"
Dariya mommy tayi tareda jijjiga kai,jin yanda Surayyah ta baje a kan carpet ɗin falon tana zuba santin abincin.
"Kai Surayyah kema dai da shiririta kike,wanne irin baki taba ci ba,daman wannan ai abinda kike so ne tun kina gidama,saidai kice kin manta dai saboda santi, mesunan babannawa ne zaizo ya daukeki ne,naga kinyi dare?"
"Wanne mesunan baban kuma waye haka?"
Harara wasa mommyn tabi Surayyah da ita,kafin tace.
"Ke lafiyarki kuwa ko cikinne yamaidaki haka,mijinnaki kika manta wayeshi.....wai naga in kikayi dare shike zuwa ɗaukanki,ko yayi ta ƙira in bayanan akan ki koma gida da wuri,naga harkin fara tuƙi da kanki ina umarin?......uhmm girma mai saka mutum ya sauya,gabaɗaya ɗabi'unki sun sauya yanxu babu wannan lankwasar dakan da kalar abin tausayin kinfara zama mace mai kwarjini"
"Ehh wlh kuwa Mommy,gabaɗaya aunty Surayyah ta sauya,kinaga wai yau itace tazo da gida da gyale kuma tana tuƙa mota ba driver,kiga wayar hannunta ma fah.....kai Mommy gaskiya dole na zama business man sosai,kuɗi fa ba wasa ba yana sauya mutum sosai"
"Kaga sarkin surutu to ya isa karka dameta,ɗan shige muje in kaji ana faɗa ka shige gaba"
Ɗan jimm Surayyah tayi kafin tayi dariya,can kuma sai tace.
"Mtss gaskiya inaga dai yanayin cikinee danni kaina naga na sauya dayawa,Abban su Farhana Bazaizo ɗaukana ba yana wasu ayyuka. Abba bai dawoba ko bamu gaisaba"
"Ahah bai dawoba sun tafi wani Ƙauye shida Malam Hashim akan wani ambaliyar ruwa da akayi,zasuyi jaje ba lalle ya dawo da wuri ba.kije dai cikin gidan kuyi sallama to kizo ki tafi"
Amsawa tayi da to kafin ta miƙe tafita,itakuma Mommy ta hau tattaramata ɗan abinda zata tafi dasu wanda baza'a rasaba.
Sai wajen misalin ƙarfe tara Surayyah ta danno hancin motarta cikin etate ɗin,waƙar Viviano takeji tana rausayar da kai,gabaɗaya tama manta da zancen wai zasuyi magana dasu Hajiya mama dan haka kai tsaye sashensu ta nufa tana yatsine fuska alamar ta gaji.
Ahmad tagani a bakin ƙofar shiga cikin falonsu ya kama kunkumi yana kallonta,ɗan tabe baki tayi kafin ta fito daga motar ta nufeshi tana tura ciki wanda yafara fitowa.
"Daga ina kike?"
"Miye damuwarka da inda nake,ka damu ka dunga sanin wannan ne,ko kuma yau wani abun kakeji dashi,to daga gidanmu nake"
"Nimra tacemin ta faɗamiki zakuyi magana dasu Ummee kikace mata wai su jiraki,su jiraki fah kikace? Surayyah kin sauyamin tun ina tantanmar cewar anya kuwa kece yanzu kam na fara gaskatawa,ki faɗamin gaskiya anya kuwa kece wacce nayi soyayya da ita harna aureta,kokuma dama waɗannan sune halayyarki kika boyemin,to in haka kike ko kuma koya kikayi yanzu menene dalilinki na boyewa sai yanxu ki nuna,wani abu nayi miki kike ƙoƙarin ɗaukar fansa akaina?.....
"Hhhhhhh haba ahmad gaskiya na raina wayonka,menene ya ɗaukeka tsawon lokaci kafin ka gano hakan...........
Amin magana ta wannan layin
***
Sadi-sakhna ce.