MUMINA KO AZZALUMA

Chapter 22

by @sadisakhna

⚫ *MUMINA KO AZZALUMA*⚫

 Available on:wattpad&arewabook



⚫ _SADISAKHNA_⚫




⚫ *BOOK 1*⚫



⚫ _PART 22_⚫



Tunda ya shiga part ɗin Safeenah ke kallonsa cikeda sha'awa,gaskiya itakam ta samu wajen zama daram.
Duk abubuwa data zaba shine aka sakamata a part ɗin babu ko kuskure ɗaya,gaskiya ta jinjinawa masu aikin tabbas sun cika ƙwararru.

Yanda sashen Surayyah yake itama haka nata yake,saidai tsari da kuma decoration har kan funitures ne kowa da irinnasa.

"Kai gaskiya gidan ya ƙayatar dani danma bashi na nuna inaso ba,wlh badan Abba yayi magana ba banga mahalukin daya isa yasa na barmata shiba ,kallon yarinya takeyimin ban kai ba,amma kota tsiya tsiya saina kwace ahmad a hannunta. Wai anty Aliya mai kuka tattauna da itane ɗazun dakika koma tambayarta wani abu,naji wai har sunan bokanki ma ta sani,da alama shike yimata aiki,miye aciki yanzu kam inda da kuɗi ake neman sa'a banga wanda zaiyimin cikas ɗin mallaka ba. Duk inda take taƙamar takawa da sannu nima yanzu saina takashi."

Sunkuyar dakai madam Aliya tayi tana ƙiƙƙifta ido,da alamar ita kaɗai tasan abinda tajiyo,sannan kotayi magana ma ba lallai su fahimceta ba ballantana kuma su gane,kawai abinda yafi shine tabisu ta uhmmm taja jikinta ta fece,domin wacce aka turota ta kara da ita babu makawa tafi ƙarfinta nesa ba kusa ba.

A haka suka gama yiwa Safeenah duk wani abu daya kamata suyi mata kana sukayi sallama da ita suka barta daga ita sai halinta da kuma ƴan aikinta.

Wasa wasa dama ance wuyar ayine in anyi shikenan,Safeenah tayi sati guda a ɗakin mijinta,kuma har yau babu abinda yahaɗa tsakaninsu itada Surayyah,domin tunda aka kawota bata taba fitowa daga sashenta ba,yayinda itama kwana uku kenan tunda tafita bata dawo ba har yau.

Kallo takeyi a falonta amma a ƴan mintuna ƙalilan tazuba tsuka sunfi sau a ƙirga,ganin hakan bazaiyi mata ba kashe tvn tayi tanufi banɗaki. Wani abu taji yana shirin zubo mata kamar period,hakan yasa ta buɗe drawer ta ɗauki part kafin ta ƙarisa banɗakin,saidai tacire wandonta wani abune mai yauƙi kamam majina yabiyo pant ɗin yalulu,zaro ido tayi cikeda tsoro,marmaza ta wanke ta sauya wasu kayan tafito ɗakinta.

A bakin gado ta zauna kanta yashiga wani tunani,
Tabbas abinnan yanada alaqa da videos ɗin data buɗe na nude a wayarta ɗazu,wannan yanayin data shiga shine ya haddasa mata wannan yoyon.

Wayanta ta ɗauka ta ƙira ummanta,bugu uku kuwa ta ɗauka.

"Ƴar albarka yanzu nake zancenki kuwa ya gidan"

"Waini umma da kuka aurarni wajen wa kuka kawoni ne,kunxo kun ajiyeni a gida yau kwana takwas kenan babu Yah ahmad babu alamunsa dagani sai halina. Tun kafin a ɗaura aure ake cewa za'ayi masa ƙira ya dawo gashi har yanzu ba labarinsa. Kuma ni gaskiya wannan magungunan danake sha duk sun dameni ni na daina sha ma"

"Kin daina sha fa kika ce,to idan ya dawo kuma fah kin daina sha yakikeso ayi,wlh nima abun yana raina,dan ko jiya nayita neman madam Aliya a waya amma bana samunta sam kedai ki zauna cikin shiri bari zanje wajen Ubannasa nayi masa magana yaƙirashi ya dawo,nasan ai wannan guzumawan iyayennasa ne suke ɗaure masa gindi"

"Toshikenan nidai kiyi wani abu dan wlh nagaji,har a makaranta fah mutane sun fara gulmata,nasan kuma wannan mara kunyar Nimrah ce take faɗamusu"

"Kedai ki kwantar da hankalinki zamusan abunyi"

Bayan ta kashe wayar Najwa taƙira babbar ƙawarta,jin wajen da hayaniya bata jinta yasa ta tambayeta inda take.

"Wai a ina kikene haka najwa inata magana amma kaman bakya jina"

"Ehh ina wani wajen party ne wlh ba'a ma faraba casu kawai akeyi,ke wlh wajennan ya haɗu,partyn farouq nefa abokin Safwan ɗinKi shima gashinan yazo naga har yafara warwarewa da rashinki"

"Partyn farouq ake wannan partyn da aketa maganar shirye shiryen yinsa,a ina akeyi?"

"Ehh shifa muna government house,ai wajen ya tsaru akwai manyan guys a wajen,.........."

"Ke tsaya kwatantamin wajen ganinan zuwa,wlh dama nagaji da wannan kaɗaicin,wanda na ƙunshe kaina dominshin ko keyarsa bangani ba,nasan shima mai yakeyi a ƙasar wajen. Dan haka bazan tsaya damuwa tayi ajalina ba kafin lokacina yayi"

Tana kashe wayar tafaɗa bayi tasake wanka sannan tafito zabar kayan dazata saka wanda duk wanda yaganta dasu yasan ta kece raini. Murmushi take tana shiryawa da rawar jikinta,ranta fari tass kaman sabon goro.

Cikin mintuna kaɗan ta tsuke da wasu arnan riga da wando golden da baƙi masu bala'in tsada amma sakasu bai kamata ba sai a iya turakar mijinta,domin sun fito da surar jikin ta sosai.

Key ɗin motarta ta ɗauka da wayarta sai baƙin glass kalar girma.

Dama tuni najwa da turamata da address ɗin,dan haka kai tsaye wajen ta nufa.

Tun daga parking ɗin motarta take jiyo sautin dayake tashi a wajen a har zuwa ciki.

Wajen ya kacame da hayaniya,kiɗa da kuma kala kalan dimm light dake haska wajen irinna club
.
A can ta hango Najwa zaune itada wasu ƴan mata da samari suna morewa duniyarsu,wasu da cup na giya,wasu da cigari wasu kuma da shisha.

Ƙarisawa tayi inda suke da zauna,sunyi mamakin ganinta saboda ance tayi aure,kuma sannan bata biyosu irin wannan wajen sosai.

Da tazo ɗinma saidai tayi tabin mutanen wajen da kallo,domin bata taba zuwa wajen casun dayakai wanann ba,iyakacinta na abokanta mata.

Kaman ance ta ɗaga idonta saikuwa ta sauqe akan safwan yana fesar da shisha kaman an kunce salansar mashin.

Ƙyam sukayi da ido nakusan minti ashirin kafin ta sauƙe nata idon,duk jikinta yayi sanyi kaman tsumma a randa.

Wayarta ce tayi ƙara tana dubawa taga ƙiransa ne sai kuma ya kashe. Tana ɗagowa taga yayi mata alamar tabiyoshi.

Kaman bazata jeba saikuma wata zuciyar tace tabishi.

A wani corrido ya tsaya yana jiyo takun takalminta harta iso gareshi. Juyowa yayi suka haɗa ido sai kuma ya tako kaɗan bai ƙaraso sosai ba zuwa gareta.
"Feeenah ya naganki anan bayan ance kinyi aure,ko nace kinyi aurenma guarantee"

Tsikar jikinta ne ya zuba jin sunan daya ƙirata dashi wanda yake ƙiranta dashi a baya,saidai a lokacin bayan baya tasiri akanta kaman yanda yayi a yanzun.
"Ehhh nayi aure amma ba irin auren da mace zatace tayi ba. Akwai muhalli,akwai abinci,akwai komai na dukkan more rayuwa,saidai babu mijin yin rayuwar,kaɗaici da damuwa sun isheni shiyasa na fito na magancewa kaina damuwar.....shin zaka iya magancemin?"

"Ehh to bansan wacce irin magancewa kike nufi ba,karki manta fa wanda kike aure........"

"Ba ruwana da waye idan bazaka iyaba ka faɗamin,saboda naji ance kana nan wajenne yasa naxo,sanin kanka ne ba shaye shaye nakeba dan haka bashine ya kawoni ba. Abinda muka saba yi nakeso mucigaba dayi harma fiyeda shi"

Taƙarisa maganar tana isa tabb da inda yake.

Da sumbata suka fara a haka harsuka kai ga ɗaya daga cikin ɗakin dayake gefensu. Sun lulula sun kuma lulawa tukunna suka saƙƙo,ba sambatu ba kuka wurjanjan Safwan ya tsugunna yana yiwa Safeenah a bakin gado bayan sungama abinda yakawosu ɗakin,sakayau taji mararta kamar anyi mata yasa,ga wata duniyar sama da tsohon saurayinnata ya jefata mai cikeda shauqi.

Kukan da taji yanayine yasakata saurin maida kayanta ta saƙƙo inda yake,domin tun ana zagayen farko yake shiɗemata yana sukuwa kaman dokin daya ƙwace ranar sallah.

Tana saƙƙowa daga kan gadon ya rungumeta da ƙarfi kaman zai maidata cikinsa,wani irin sambatu yake mata akan komai takeso zayyi mata shidai kawai tayimasa alƙawarin Bazata rabu dashi ba.

"Tunda nake bantabajin abinda naji yau ba feena,kin shayar dani zumar da bawacce zata iya bani,ki taimaka karki rabu dani,domin zan iya mutuwa akanki ke kome kikeso zanyi feena ina sonki inasonki sosai."

Cikin dabara da zare jikinta daga nasa suka zauna suna kallon juna,yanzu ya daina kukan yadawo cikin hankalinsa,amma da alamar koma miye yashiga jikinsa to ya samu waje ya zauna,domin soyayyarta take hangowa a ciki idanuwansa wanda haka siddan bazai iya yimata itaba saidai ta sanadiyyar siddabaru.
Gabanta ne ya faɗi sai a sannan da tuno abinda ya faru ana gobe ɗaurin aurenta,sunje wajen bokanya mai gurjiya tayimusu aiki.

Da jininta na al'ada akayi rubutu a allo aka wanke,sannan aka bata ruwan tayi tsarki dashi,kan cewar duk wani ɗa namijin dayayi tarayya da ita musamman idan bayyi addu'a ba anso ma kafin suyi aure saboda zaifi ci amma da aurenma zasu iya yi. To shida wata mace har abada,sannan komai takeso a duniyar nan shi zayyi mata. Kuma bugu da ƙari zai makance da zauce akan sonta.

Gaba ɗaya sharruɗan da kuma yin aikin wanda anyi shi ne domin Ahmad sun kwanta mata,burinta kawai wanda zai ɗauke mata bukatar ta takeyi. Saida muraran daga aikin yaci amma ba'a akan mijinta ba sai a kan tsohon saurayinta kafin ta dawo cikin hankalinta. Hannu tasa aka tana zaro ido,domin tasan ba iya shiga uku ba harta huɗu ma tayi mata sallama. Musamman dataji furucinsa na ƙarshe ganin halinda tashiga.

"Meyasa kike damuwa,indai wannan mijin naki ne a yanda nakeji zan iya gaba da gaba dashi ko kuma ma na kasheshi idan har hakan zaisa hankalinki ya kwanta kuma mu cigaba da soyayyarmu"

Wata harara ta watsamasa na alamar ya tabene komai.

"Ka kasheshi fah kace ko kuma yin gaba da gaba dashi,da haka kan ai gwara ka hau lasifika ka faɗi abinda mukayi. Ka shiga kayi wanka kafinnan zansan abunyi,domin ina cikin cakwakiya"

Bai mata musu ba yashiga bayi yin wanka,itakuma wayarta ta ɗauka taƙira hajiya Hunaiza.

Bayan ta ɗauka kai tsaye tambayarta tayi.
"Hello ummah ni wannan aikin da kika kaini akayimin a wajen wannan bokanyar tace zai iya karyewane idan anyishi?"

"Ehh to tace aikin yanada ƙarfi sosai,domin ita kanta shine babban aikinta na mallaka da takeyiwa manyan mutane wanda suka biyata maƙudan kuɗi,saboda ƙarfin sama bata iya yinsa sai bayan shekara biyu idan tayi,domin ruwan datake wanke rubutun dashi a wata rijiyar aljanu ake ɗeboshi,kuma sannan idan aka buɗe aka kowa ya ɗiba ya kaiwa ubangidansa ba'a sake buɗewa sai bayan wasu shekaru,shiyasa ruwan yakeda wuyar samu.

Batun karyawarsa kuma tace idan matar aure tayiwa baya ƙarfi sosai kaman in wanda tayiwa sunyi tarayyane ba aure,karyewar sa ga waɗanda sukayi zina sai wani tsananin ikon Allah. Amma meyasa kike tambayata,karki damu tace koda aurenma yanada matuƙar ƙarfi,ko wanda yafi ƙarfinta bai isa warware sihirin da akayi da ruwan zafeer ba"

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un shikenan nashiga uku na lalace"

Bayan takashe wayar tasaka hannu aka tana faɗa.
Ta gudu safwan yafito daga bayin dagashi sai tawul ɗaure a ƙugunsa,baza hannu yayi tareda hawa har tsakiyar gadon yana tambayarta lafiya. Banza tayi dashi saida tayi kuka mai isarta kafin itama tatashi tashiga bayin,ta barshi a nan cikeda damuwar dayake yinta ba a cikin hankalinsa ba.

Bayan tafito ko kallon inda Safwan yake zaune batayiba tashirya jikinta tafita daga ɗakin,baƙin cikin ta ɗaya shikenan ta rasa damar mallakar Ahmad gefe ɗaya kuma ya zatayi da wannan datasaka jan zare a tsakaninsu,wanda zayyi ta bibiyar rayuwarta ne ko taso ko kuma taƙi.

Bayan tafita bayanta yabi da sauri,kicibis sukayi da Farouq yana shirin shiga ɗakin shida budurwarsa zeezah.

Kallon safeena sukayi wadda tawushesu ko magana batayi musu ba,da kuma safwan wanda ya bita da gudu kaman tababbe.

Kallon Farouq zeezah tayi da mamaki kafin tace.

"Beb wannan ba mrs Amjad bace amaryarsa?"

"Ehh itace kinsanta ne,dama ex ɗin safwan ce ai,maybe har auren ya isheta ta dawo harka,ku mata ai dama bakuda amana aure ma da wuya yasakaku hankali idan kuka kauce hanya"

"Ahhh kaga karka zagi mata a gabana cos am also a woman,kuɗin ma wata amanarce daku,ba gwara matan bama idan aka tabo shafinku. Kaidai muje idan kanaso na kashe maka arna"




Amin magana ta wannan layin 
***
Sadi-sakhna ce.