Chapter: 16
by @zmchubado
BAFULATANA
Zm~Chubaɗo
016
Kallonta yake sosai, jin ta ƙi magana ne ya sa ya dawo gefen gadon ya zauna, sannan ya kamo hannunta cikin nasa ya ce,“What exactly is the problem between you and Ummie? wllh har cikin raina bana jin daɗin wannan dabin dake tsakanin ku mom”
Tunda ya fara magana mom ke binsa da wani irin kallo cikin alamun ɗaure fuska ta janye hannunta daga nasa ta ce,"Don’t you ever call her Ummie in my presence,If you do it again, na rantse da Allah I will show you my anger dan wallahi zanci maka mutunci tunda haka kake so."
Shiru ya yi a ransa, yana girmama rashin jituwar da ke tsakaninsu. Amma koma mene ne, yana roƙon Allah ya kawo ƙarshensa. Miƙewa ya yi yana kallon agogon da ke ɗaure a tsintsiyar hannunsa cikin girmamawa da mutuntawa yace, “Mom ni zan wuce, sai mun yi waya.”
“Allah ya ba da sa’a da nasara akan abinda zakaje nema, Ubangiji ya tsare mini kai daga dukkan sharri.” Mom ta faɗi hakan tana miƙewa a hankali ta nufi toilet ba tareda ta sake kallonsa ba.
Murmushi ya saki mai sauti sannan yayi mata rakiya da idanunsa har ta shige ta rufe ƙofar, sannan ya janye isanunsa ya sauke ajiyar zuciyar data maƙale masa a ƙirjinsa tunda suka fara magana da Mom. Goshinsa ya kai hannu ya mirza tare da ƙudurtawa kansa cewa koma mene ne a tsakaninsu sai ya tono shi kuma ya dedaita tsakanin su da izinin Allah.
Juyawa ya yi walking slowly ya fita daga ɗakin. A falo suka ci karo da Zainab wadda ta fito daga kitchen hannunta ɗauke da faranti ta zuba chips da plantain a ciki, saboda ita da wuri take yin breakfast ba kamar sauran mutanen gidan da sai 11 ko 12 ba.
Tsayawa ya yi a inda yake yana kallonta fuskarsa ɗauke da murmushi.
Maƙalewa ta yi daga inda take tsaye tana kallonsa tare da marairaice fuska ta ce, “don girman Allah Bro kayi haƙuri, wallahi takura mini tayi shi yasa na nuna mata part ɗinka.”
Still kallonta yake with a smile on his face hannunsa ya harɗe a ƙirjinsa ya ce,“ naji takura miki tayi amma zo mana muyi magana.” ya faɗi hakan cikin ɓatar da murmushin dake shimfiɗe a kyakkyawar fuskarsa.
Da sauri ta maƙe kafaɗa ta ce, “Umm, ni ba zan zo ba fa, na san dukana za ka yi.”
“Haba ke kuwa, ta yaya zan dake ki? Ke dai kawai kizo ki ji,” ya faɗa yana takawa a hankali zuwa inda take tsaye.
Da sauri ta ajiye farantin dake hannunta akan dining, ta naɗe doguwar rigar atamfar dake jikinta fita da gudu za ta haura sama, shi kuma yabi bayan ta. Zagaya falo sika shigayi Zainab na ihu, har Abie ya shigo falon.
Murmushi ya yi ganin yanda muzaffar ya biye mata suna tabka ƙuruciya, sannan ya nemi guri ya zauna ya ce,“za ku makara fa, time ɗin tafiyarka ya kusa, saura 40 minutes.”
Tsayawa Zainab ta yi jin yayanta zai yi tafiya kuma bata sani ba. tsayawar da tayi ne yasa har ya zo inda take ya kama kunnenta na hagu da ƙarfi ya matsa sannan ya ce, “Wallahi this is the last warning da zan miki a kan nunawa wata ƙatuwa hanyar part ɗina.”
Ƙara Zainab tayi tana roƙonsa, sannan ya saki kunnen ya kama hannunta suka dawo tsakiyar falon inda Abie ke zaune. Taɓe baki Fadilah ta yi ta ƙara maida hankalinta ga TV.
Murmushi Abie ya yi, sannan suka gaisa da Muzaffar cikin girmamawa, sannan Zainab ma ta gaida shi. Cike da soyayya yake amsa mata gaisuwar tare da shafa gefen fuskarta. Kamar za ta yi kuka ta ce, “Abie! wai ina Bro zai tafi daga dawowarsa cikin family?"
"wannan tafiyar kasuwanci ce Mamana, kuma ba nisa zaiyi ba India zaije." cewar Abie.
Juyawa tayi a sanyaye tace,"Bro dama india zakaje amma ko labari babu? Ni kam, Abie, ina son zuwa India saboda Ummie ta iya miyar gyada sosai, sannan kuma tana ba wa mutum lokacinta su yi hira fiye da yadda Mom ke bamu time ɗinta. Please Abie, don Allah idan na gama school ka nema mini admission a Imperial College of Engineering da ke Mumbai, kaga sai na dinga zama tare da ita ta koya mini girkinta mai daɗi…”
“Har abada wannan ranar ba zata zo ba!. Saboda bana fatan Allah ya haɗa Aisha da ƴaƴan dana haifa a ƙarƙashin inuwa ɗaya, wllhi Wannan shine kashedi na ƙarshe da zan miki akan alaƙanta kanki da waccan matar mai baƙar zuciya. Idan kuma kika sake, to wallahi zan nuna miki nina haifeki bake kika haifeni ba dan iyayenki!”
Mom ta katse wa Zainab magana ta hanyar faɗar hakan cikin ɓacin rai.
Daga Abie har Zainab kallonta suke yi, shi ko Muzaffar ya ma kasa cewa komai, saboda inda sabo ya saba ganin wannan abin a gidan tun yana ɗan ƙarami. Abinda ya lura dashi Mom ta tsani ta ji ana ambaton sunan Hajiya Aisha a gabanta, ji take kamar zuciyarta za ta fashe saboda baƙin ciki, musamman idan ta ji yaranta na kiranta da suna Ummie.
A haka mom ta ƙarasa cikin falon fuskarta a ɗaure, sai dai hakan bai kashe tasirin shigar alfarmar dake jikinta baiyana kanta ba.
doguwar rigar shaddace ƴar ubansu anyi mata ɗinkin Senegal sai baza ƙyalli take, da alama dai rakiyar ba zata ta sakko tayiwa gudan jininta.
Janye idanunsa Abie yayi daga kanta a ransa yana mamakin ƙarfin hali irin nata. Saboda bai taɓa tunanin har yanzu zafin kishinta yana nan a yanda yake ba.
Abin takaici ma wai a kan Hajiya Aisha wadda sam ita ba ta gabanta. Hajiya Aisha irin matan nan ne masu shiga rai, ko ya ka yi mu’amala da ita sai kaji a ranka kana ƙaunarta. Wannan dalilin ne ya sa ta samu kaso mafi girma a zuciyar Abie, kuma yake ji da ita don soyayyar da yake mata ta musamman ce.
Girgiza kai ya yi sannan ya miƙe ya ce, “Oya mu je kar ka makara.”
Da ga yanayinsa mom ta fahimci ta ɓata masa rai, amma seta haɗe rai tabi bayansa
A haka suka fita gaba ɗayansu, except Fadilah wadda takaici ya ishe ta ta koma sama, ta buɗe ɗakinta ta haye gado.
Har sun fita harabar gidan Baba Hajara ta fito ɗauke da wata babbar leda tana faɗin, “Ƙaramin mai gida tsaya kar yi babbar mantuwa, na tagomashin da na yi maka tana daɗi.” Ta faɗi hakan cikin yanayin wasa.
Da sauri Muzaffar ya koma da baya zuwa inda take don ya sauƙaƙe mata yanayin tafiyar, saboda fama da ciwon ƙafa da take yi wasu lokuta. Yana son matar sosai saboda yadda take ba shi kulawa tare da nuna masa ƙauna. Ta sha rasa abubuwa da yawa saboda shi, shi ya sa yake kallonta a matsayin kaka a gare shi, ba mai aiki ba. Wasu lokuta idan yana kallonta yakan ji a ransa cewa ita ɗin tamkar madubi ce a rayuwarsa, shi ya sa tasu ta zo ɗaya.
Miƙa masa manyan ledodi guda biyu ta yi sannan ta ce, “Dambun nama ne na yi maka tun jiya, da na ji Abbanka yana faɗar zaka tafi India. Ɗaya naka ne, ɗayan kuma ka ba wa Hajiya Aisha, sannan ka gaya mata ina gaisheta gaisuwa mai tarin yawa, ko ma in ce mara adadi.”
Dariya ya yi sannan ya ce, “Nagode sosai, Mai ran ƙarfe. Allah ya ƙara miki lafiyar da ta fi wadda kike da ita a yanzu.”
Kafaɗarsa ta ɗan dafa sannan ta ce, “Kai ma haka Allah ya kaika lafiya ya kuma dawo da kai lafiya.”
Da Amin ya amsa mata, har bakin mota ta raka shi, sannan ta koma gida a ranta tana jin kewar Hajiya Aisha na ratsa duk wata gaɓa ta jikinta. Ita dai kam Allah ya sa mata ƙaunar wannan baiwar Allah tun ranar da ta fara ganinta har zuwa ranar da ta bar ƙasar Nigeria, duk rashin jituwarsu da Mom zaiyi wahala ita kam kullum cikin kyautata mata take.
Har ta shiga cikin gida ta zauna a ɗakinta ba ta bar tunanin Aisha ba. Nan take gabanta yay wata irin faɗuwa a lokacin da ta tuna wani baban al'amari da ya faru shekaru talatin da biyar da suka wuce. Nan take Baba Hajara ta miƙe ta fara zarya a ɗakin gumi yana yanko mata cikin maɗaukakin tashin hankali, tambaya ɗaya ce ke mata yawo a zuciyarta.
"yanzu ya zanyi idan sirrin da muka ɓoye ya baiyana?"
Komawa tayi ta zauna a bakin katifarta tana sauke numfashi a hankali, sai kuma ta ƙara yu ƙurawa ta mike tsaye dakyar ƙirjinta na bugawa da tsananin ƙarfi fiye da ko wace rana a rayuwarta.
Ɓangaren Su Abie kuwa ba su dawo gida ba har sai da suka ga tashin jirgin su Muzaffar. Nan ma kafin ya shiga jirgi sai da Mom ta yi masa kashedi kan cewa ya yi taka tsan-tsan da duk wani abu da zai kusanta shi da Aisha. Sannan suka dawo gida cike da kewarsa.
**************
DAJI
Tana zaune a saman bishiya, a haka bacci ya fara ƙoƙarin ɗaukarta. Jin kamar za ta faɗo daga bishiyar ne ya sa ta farka da sauri tare da kifar cikinta kan reshen bishiyar ta yadda za ta ji daɗin kwanciyar ba tare da fargabar faɗuwa ba. A haka wani gajiyayyen bacci ya ɗauketa mai cike da tarin muggan mafarkai iri-iri a kan mahaifinta. Firgigit ta miƙe hankalinta a tashe sai kawai ta fashe da kuka, kuka take sosai har sai da idanunta duk suka kumbura bacci ya ƙaurace mata. Ma’ana, yadda ta ga rana haka ta ga dare a wannan ranar. Sai da garin Allah ya waye ko ina ya yi haske sannan ta Sauko daga saman bishiyar cikinta na murɗawa saboda yunwa.
Jakar dake kafaɗarta ta gyara sannan ta fara tafiya a hankali tana kallon bishiyun su kaiwa jejin rumfa ko zata samu wani ɗan itaciyar da zata ci, sai da tayi tafiya mai nisa sannan ta riski bishiyar mangwaro, ajiye jakar tayi a ƙasa sannan ta naɗe zanin dake jikinta ta fara ƙoƙarin hawa bishiyar, cikin ƙanƙanin lokaci ta haye sannan ta fara tsinkar mangwaron tana jefawa ƙasa.
Sai da ta cira da yawa sannan ta sakko ta zauna a ƙasa ta fara sha, sai da ta sha mai yawa sannan ta ɗebi ragowar ta zuba a cikin jakar taci gaba da tafiya ba tareda ta san inda ta nufa ba.
*** **** *** *** ***
MUMBAI INDIA.
Hajiya Aisha ce tsaye cikin kitchen ɗinta na alfarma tana haɗa abinci na musamman wanda za ta tarbi Muzaffar da shi. Abinci kala-kala ta haɗa masa wanda ta san yana so, sannan ta fito da kanta ta jera su akan dining.
Duk yadda yan aikinta suka so su taimaka mata amma fir Hajiya Aisha ta ƙi amincewa; ta ce su bar shi ita da kanta za tayi masa komai, saboda yadda mijinta ke ji da ɗan nasa dole ne ta yi masa kara.
Bayan ta kammala ne ta ba da umarni a je a gyara masa part ɗinsa da zai sauka. Cikin mintuna kaɗan suka kammala gyaran gurin sannan aka feshe part ɗin da expensive air fresheners masu sanyin ƙamshi da daɗi. Bayan sun gama gyaran da awa ɗaya motocin da ke ƙarƙashin companynsu dake ƙasar suka tsaya a ƙofar gidan cikin jerin gwano. A nitse ya sanyo ƙafarsa waje wadda ke ɓoye cikin baƙin takalmin fata samfurin Batozi. Sai da ya shaƙi iska na mintuna kaɗan sannan ya saki murmushi don ya jima rabonsa da ƙasar.
Yana zaune cikin motar Ummie ta fito cikin shigar doguwar rigar Abaya maroon. Kallo ɗaya zakayi mata ka fahimci cewa ta fara manyanta, don a ƙalla shekarunta za su kai 52 geting to 55. Ta yi lulluɓi da wani babban mayafi mai kauri ruwan madara.
Fuskarta a sake cikin maɗaukakin farin ciki ta marabceshi ta ce, “barka da zuwa.”
Murmushi ya yi har sai da fararen haƙoransa suka bayyana ya ce, “Nagode, Ummie. Ai da kin bari na shigo da kaina ba sai kin fito ba.”
Ƙara murmusawa tayi ta ce, “Ai shekarun da yawa, Muzaffar, ba zan iya zaman jira ba sai na fito na tarɓe.”
Shiru ya yi yana kallonta yana jin ƙaunarta na ƙara huda tsokar zuciyarsa, kallonta yake sosai yana son gano baƙin halin da Mom ke yawan siffanta ta da shi. Shi dai kam ba zai ce ya san wani abu na sharri a tareda ita ba, don shi bata taɓa yi masa komai na mugunta ba, uwa uba kuma ba su taɓa yin dogon zama tare ba balle ya fahimci hakan. To ko dai akwai abin da take shirya masa a bayan fage ne wanda shi bai san da shi ba?
Thanks 4 d love fans 🙏
Comment
Nd
Share
ZMC 💋
***