Chapter 25
by @sadisakhna
⚫ *MUMINA KO AZZALUMA*⚫
Available on:wattpad&arewabook
⚫ _SADISAKHNA_⚫
⚫ *BOOK 1*⚫
⚫ _PART 25_⚫
Harara ya zabgawa nimra kafin ya matsa ta gefenta ya wuce zuwa nasa sashen. Kashe wayar tayi tareda ja da baya tabar gidan,domin a irin wannan chakwakiyar bai kamata ta shiga gidan ba.
A bangaren Surayyah kuwa suna barin wajen komawa kujera tayi tana nazari na ɗan wani lokaci kafin ta tashi tashiga cikin ɗakinta.
A gaban kayanta da tsaya da zungereren ciki wanda yakusa taba wardrope ɗin,ɗan murmushi tayi wanda kana gani kasan abubuwan dasuke cikin ranta suna dayawan dabazasu iya fassara murmushin ba. Kaya kala bakwai wanda yawanci duk dogayen riguna ne tasaka a cikin akwatin,dan yanzu sune suke isarta. Gyalen abayar kanta ta yafa kafin ta jawo akwatin zuwa falo. Saida ta ƙarewa gidan kallo kafin tace .
"To bari kuma aje gidan can shima aga ya yake na ɗan wani lokaci,da nayi niyyar sauƙaƙa maka lamarin amma ahmad da alama bakasan sauƙin"
A hankali tafito har bakin harabar sashen ta,kicibis sukayi da Safeenah wanda tafito itama zata ɗauki motarta,duk tayi baƙi da rame tayi ƙuraje,alamar rashin nutsuwa da rashin bacci duk sun bayyana akan fuskarta. Har zata shiga motarta saikuma tatsaya kallon Surayyah wacce ke shirin saka akwati a gidan baya na motarta. Takowa tayi har wajen tareda da tattaro ƙarfin halinta tace.
"Me nake gani,matar gwal yau kece zaki tafi gida har da akwati,incedai ba abinda nake tunani bane,inkuwa hakane abun yabani mamaki"
Duk maganar da take Surayyah bata baata hankalinta ba saida tagama abinda take tukunna. Bayan ta buɗe murfin motar kaman zata shiga saikuma ta riƙeshi tana kallon Safeenah,ƙareta tayi da kallo kafin tasaki murmushin ganin abin tausayi.
"Da wannan fitar da zakiyi zaifi kyau kifara garzayawa asibiti tukunna,domin alamun ciki dakuma cutar zamani dukka sun bayyana a jikinki. Sannan idan kinason neman hanyar zakibi abin jikinki ya karye kina iya tuntubata daga baya. Domin mace mai ciki ,ga rashin lafiya sannan ga rashin bacci saboda jarabar mai cikin abin akwai damuwa sosai cacacaca kaiii gaskiya ina tausaya miki sosai"
Tana gama faɗin hakan ta ƙoƙarta tashiga motarta tareda janta tabar arear wajen.
Ba suman tsaye ba har mutuwar tsaye saida safeena tayi,inaga har Surayyah takusa rabin zuwa gidansu bata motsaba,sannan kunnuwanta basu daina yin ringing na amsa kuwwar abubuwan da suka jiyo ba .
Kai tsaye maigadi yana kallon motarta ya buɗe mata tashigo,washe baki yake yana gaisheta lokacin data fito daga cikin motar,amma ganin kaman yanda take masa kwannnan kota kan abinda yake bata bi ba,harta kusa shiga part ɗin ummansu ne ta juyo ta kalleshi,da sauri yamatso yana washe baki. Wurga masa key ɗin motar tayi tareda cewa.
"Ka buɗe gidan baya akwai akwatina ka shigomin dashi"
Daga haka tajuya ta barshi kasake a tsaye yana kallon bayanta,kokaɗan yakasa tantance wai wannan Surayyah ce,ta tun kafin yayi magana take saka masa gaisuwa,sannan kuma ta ciro ɗan ihsani tayi masa duk lokacin data zo gidan.
Lokacin data shiga falon waya takeyi,da alama kuma mai muhimmanci,sai kawai tasamu ƙasa a carpet ta zauna,domin ɗan iya wannan tafiyar da tayi duk gajiya ta kamata.
Bayan tagama wayar gaisheta tayi ta amsa cikeda kulawa da kuma tambayar ta nauyin jiki,suna cikin maganar ne mai gadi yashigo da akwatinnata,kallon akwatin ummannasu tayi da mamaki kafin tace.
"Ahhh ko kingaji da rashin dawowar mijinnaki kai shiyasa kikazo kiyi mana kwana biyu"
"Ahah ummah"
"To haihuwa zakiyi a gida wannan karon kuma kaman haihuwar fari?"
"Shima ba haka bane,yadawo jiya da daddare to sai yace natafi gidanmu yau da safe,wai ko sakina bazayi ba tunda bai yarda da aure a tsakanina dashi ba,sannan cikin jikina bashi bashi..........."
"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun ƴar nan mai kike cewa haka,kiyi shuru da bayaninnan haka babu daɗin ji ko kaɗan. Nikuwa da yarintata ban haɗu da wannan mummunan abuba sai yanzu. To kodai yasamu tabine a can ɗin. Banda haka mai zaisa yayi wannan ɗanyen aiki haka iyee"
Karyar dakai Surayyah tayi cikin sigar abin tausayi kafin tacigaba da cewa.
"Nima bansani ba ummah,amma inada tabbacin lafiyansa ƙalau,domin tun samun cikinnan haka nake fama dashi,ko yaushe sai yace niba matarsa bace,shi ba ɗansa bane,su farhana ma ya rabani dasu tun ba yauba ko inda nake basa zuwa"
"Innalillahi lallai ƴar nan kinanan da kawaicinki yanzu tsawon lokacin nan duk abinda yake faruwa kenan,amma kike ta shanye shi baki taba faɗawa kowa ba. Haba shiyasa duk naga kin sauya kin zama wata iri mana ba yanda nasanki da ba. Saina barshi kawai a matsayin cikinne yazomiki da haka,ashe duk ba haka bane shine ya sauya miki yake cutar dake. Ki kwanta ki huta barina kawomiki abinci akwatin kuma sai a kaimiki akin Saudat"
Bacin rai tulus hajiyarsu ta nuna akan fusakarta,har yamma tana aikin jajanta abin, Allah Allah take babansu ya dawa ta shaida masa.
Bangaren Surayyah kuwa kwanciyarta tayi hankalinta kwance kaman tsumma a randa.
Tun daga bakin ƙofa ta cire Takalminta ta faɗa wuff kaman an jefo ta. A zaune suke su uku hadda deedee sunata hira,
A gefen hajiya ummi ta zauna domin tasan itace zatafi yarda da abinda zatace ɗin batareda an samu matsala ba.
Wuri wuri take da ido tana kallonsu ido ɗaya bayan ido,dukkansu shuru sukayi da taɗin da sukeyi suka zuba mata suma nasu idon.
Hajiya mama ce takasa haƙuri tayi mata mata a hasale.
"To ke kuma lafiya kikazo kika sakamu a gaba kina rarraba mana ido,ko wani abune ya samu yayannaki,naga safiya ta ɗaga ma ko sashen umminnasa bai shigo ba"
"Uhmmm uhmm ƙalau yake,yanzu na shiga nake ji yana cewa Aunty Surayyah ta tafi gidansu,wai babu aure a tsakaninsu ballantana ma ya saketa"
"Wanne irin ba aure a tsananinsu tunda kenan ya saketa take zaune komai,sannan daga dawowarsa mai tayi masa da tsohon ciki da bazai iya haƙuriba ya korata gidansu. Mai sunan manya yanada mutunci kuwa. Yanzu dama tun wannan kakale kakalen dayayi kwanaki bai mutu ba har yanzu"
Hajiya mamace tafara masifa da takaicin abinda nimran tace. Itama Deedee nata albarkacin bakin tafara tofawa akan ɗayan aikin da ahmad ɗin yayi.
Hajiya ummi shuru tayi tana jinsu,bata tofaba kana kuma fuskarta babu yabo babu fallasa.
"To yanzu baza'a komai sai a jira yadawo aji ta bakinsa menene yahaɗasu,amma wannan yaro akwai ja'iri,kawai kace mata ta tafi gidansu,kuma ko saki bazakayi mata tunda ba aure a tsakani,to shi auren daakaje aka ɗaura masa a baya menene sunansa kenan"
Sababi dai tacigaba dayi da haka har suka watse akan dole za'aji ta bakinsa.
"Haba hajiya yanzu wannan yaron harni zai yiwa wannan cin mutuncin,wai tazo gida ko aure babu tsakaninsu,kuɗi haukane kenan,da har zayyimin haka ya turomin yarinya gida da tsohon ciki wai ba aure tsakaninsu,to wlh in yasan wata bai san wata ba,shari'a ce zata rabani dashi wlh"
"Ahah ahah alhaji kar ayi haka tukunna ita shari'a idan annemeta ai sai abu yabaci,abinda yayi kam bai kyauta ba babu daɗi,amma kamata yayi kafara zuwa ka samu mahaifinsa tukunna ka tattauna dashi muji ba'asin zancen"
Cika baban su Surayyah yake yana batsewa,kana kallo kasan ransa ba ƙaramin baci yayi ba da dawowarta gidan.
Kallon maman su Surayyah yayi bayan wani ɗan lokaci da shuru ya gilma a tsakaninsu.
"Inaa ita Surayyah ya dai yanayinnata,ince dai bata shiga cikin wani yanayi na damuwa ba ko?"
"Ahah ƙalau take babu abin yake damunta,ni nakaina nayi mamakin yanda abin ko kaɗan bai daketa ba,ina yawan tambayanta ko akwai abinda yake damunta amma sai tace min babu komai"
"To kodai kai akwai abinda yashiga tsakaninsu,gaskiyar ki ce kar kuma muyi garajen ɗaukar mataki batareda munsan abinda yake faruwa ba kuma aga rashin dattakonmu.
Ko kuma yadaɗe dama yana gallazamata har yafita ta kanta,kinsan ita ba mai yawan magana bace ba lallai ta faɗawa wani ba"
"Hakane kam kuma nima alhaji sai yanzu abin yake dawomin daki daki,kafin karo mata abokiyar zamannan fah haka yayi tafiya babu sanarwar ranar dawowa,kwatsam daga dawowarsa kuma wai ta tafi gidansu"
"Hmmm wato yara da kuɗi ko, wato yaro da kuɗi hatsarinsa yanada wuyar shaani,wannan kuɗi sakamusu yakeyi basa ganin kowa da mutunci sai abinda suka saka a gaba,babu komai zanje wajen mahaifinnasa gobe mu zanta bari naje na ɗan kwanta hajiya na gaji daga tafiyar danayi. Kodai zakiyimin wannan tausar taki danake jin daɗinta."
Ya ƙarisa maganar yana ɗan murmushin jin daɗi,Allah sarki tsohuwar zuma,hala yafara mantawa da halin da yake ciki.
Bayan Mahaifinsu Surayyah yaje gidanu Ahmad ba ƙaramin bacin ransa ya nuna ba,daga ƙarshen jin abinda yafaru bai wuce sanadiyyar sauya masa da tayi ba na cikin dayake jikinta yasaka ransa ƙara baci fiyeda da. Har yafara iƙirarin kaiwa kotu,hakanne yasa baban su ahmad dannarsa kuma ya shaida masa cewar Ahmad ɗin yana nan zuwa ya ɗauki matarsa ta dawo.
Saidai yin hakan sati biyu kenan amma ba Ahmad babu alamarsa,saima bincike da ya cigaba dayi na abinda ya fara a kadunan. Wanda hakan yasa ko tunawa da Safeenah bayayi ballana yayi hanyar sashenta.
Yauma kaman kullum bacci ƙalilan ne yasamu damar jiyartar gangar jikinsa,fitowa yayi da file a hannunsa wanda yaraba dare yana nazartarsu na bayanan da'aka turomasa na Surayyah wanda tayi a kaduna,haka kuma dana wanda tayi anan abujan. Tun da abubuwan da suka afkuwa dashi masu kaman mafarki bai taba ganin wata hujja dta fito fili kuma ta bashi tabbacin cewar ba mafarki yakeyi ba kaman wannan ɗin. Sannan an sanar masa da cewar Agent kamal ya farfaɗo daga comar dayashiga,duk da cewar har yanzu baya cewa komai sai kallom mutane da ido kawai. Sannan iyalansa suna buƙatar kasancewa dashi,bayason yazama yafara tuna masa da abinda yasakashi halinda yake ciki tun yanzu.
Kicibis sukayi da mutum,hakanne yasaka ya ɗago yaga wanene,Safeenah ce wacce tayi baƙi ta rame abin duniya ya dameta. A lokacin baya kafin wani abu ya haɗata da Safwan babu abinda datake buri kaman dawowar angonnata,amma yanzu makasudin rashin haɗuwar tasu itace. Domin duk wata hanya datasan zasu haɗu saida ta datseta. Saidai kashh gashi yanzu sunyi kicibis tafito zataje asibiti. Satinta biyu kenan batada lafiya tun tafiyar Surayyah, dannewa takeyi amma yau kam abu yaci tura,dole zataje taga likita,komai za'a cemata ma saidai yace. Tashirya kunnuwanta jin duk wani abu da zai biyo bayan sakamakon abinda ta aikata.
Zaro ido Ahmad yayi daya kalleta,domin sakanni na farko dasuka haɗa ido bai taba kawo cewar itace ba. Saboda tayi baƙi ta rame,ga wadu ƙuraje da suka fito mata kana kallonta kasan tana cikin halin jinya. Shi saida ya kalleta yanzu ma ya tuna da ita,tun ranar da abban su yaƙirashi yayi masa faɗa akan yaje ya dawo da Surayyah ya haɗa matansa ya riƙesu tsakani da Allah. Jikinsa ya ɗanyi sanyi dan haka yaje sashennata amma sai yaga a kulle,tundaga sannan bai sake bin hanyar ba.
Nazartarta yayi na wasu ƴan lokuta kafin yace.
"Safeenah bakida lafiyane, mai yake damunki?"
Wasu ƴan hawayene suke cikowa daga idonta tayi saurin maidasu tareda girgiza masa kai.
"Ehh wlh bana ɗanjin daɗine yanxu ma asibiti zanje naga likita"
"Ayyah to muje na kaiki mana don nima akwai wanda nakeson ganowa a asibitin kum........."
"Ahah daka barshi kawai zanje dakaina kuma naga ai sauri kakeyi"
"Ehh amma ai nacemiki nima zan zanje........"
Ƙirane yashigo wayarta,tana dubawa taga Safwan ne,don dama tun asuba yake zabga mata ƙira dashi tayi karin kumallo,saurin ɗaukar wayar tayi tareda da ɗanyin murmushin waskewa tayi wajen motarta tana rarraba ido alamar marar gaskiya. Shima tsaye yayi yana kallonta da mamaki akan fuskarsa,saurin basarwa yayi domin shima akwai tarin abubuwan dake jiransa,dan haka yafaɗa motarsa yabar gidan.
A zaune take tayi jugum kaman marainiya tana jira taji sakamakon da gwajin da akayi mata zai nuna,ita kanta tasan dole ace wani abu yana damunta dole ne ma.
Muryar nurse ɗin taji akanta bayan tashiga cikin zurfaffafan tunani. Wanda hakan yasakata firgita ta ɗaga idonta.
"Safeenah Ahmad"
"Ehh nice"
By *sadi-sakhna*