Chapter 26
by @sadisakhna
*MUMINA KO AZZALUMA*⚫
Available on:wattpad&arewabook
⚫ _SADISAKHNA_⚫
⚫ *BOOK 1*⚫
⚫ _PART 26_⚫
Shine abinda ta faɗa a sanyaye.
"Kishigo likita wai yana son magana dake,wai zaifi ma idan tare kukazo da mijinki ko kuma zaki ƙirashi"
Banza tayi da ita tareda yin hanyar inda ta nuna mata nanne office ɗin likitan.
Shiga tayi bakinta ɗaukeda sallama cikin sanyin jiki,shima amsawa yayi hankalinsa ɗauke da wasu takardu da files dake gabansa. Sai bayan ta zauna ne kafin ya ɗago ya kalleta cikeda tattara nutsuwarsa.
"Am you are Safeena Ahmad ba. Amma kaman nace mata zaifi kyau kuzo da mijinki,domin abubuwan dazan faɗamiki yanada kyau shima ya sauraresu sabo........."
"Dan Allah likita kawai ka faɗamin abinda yake faruwa,tunda na yanke shawara nazo asibiti gwaji,to na shirya jin duk wani abu da zai biyo baya"
"Okay to shikenan. a halin yanzu kina ɗauke da ciki na wata biyu,sannan kina ɗauke da ciwon sanyi matsananci wani yanada matuƙar illah a gareki dakuma barazana ga cikin dake jikinki. Sannan rashin bacci da zabura dakikeyi yanada alaƙa ne da Sexual abuse da akayiwa jikinki,wato baki samun hutu daga mijinki,wanda wannan rashin hutu shine yayi sanadiyyar ramar da kikayi. Abinda yasa kikaji mun buƙaci ganin mijinki yanada buƙatar yasan matsaloli guda biyun saboda zai iya yiwuwa shine yasaka miki ciwon sanyin,sannan kuma mu bashi shawara gameda tsarin zamantakewar ku,yanda vazai zamo barazana ga cikin jikinki ba da kuma lafiyarki.
Tun bayanin likitan na farko Safeenah tasaki ajiyar zuciya jin ba a faɗi abinda take tsammani ba kuma take matuƙar fargaba wato cutar zamani ta ƙanjamau,sauran duk masu sauƙine. Sakamakon ma ko karba batayi ba tayi hanyar waje tana haɗa hanya na yunwar dayake cinta.
Bayan tashiga cikin motarta kai ta haɗa da citiyari ta dunga rabzar kuka,saida tayi mai isanta kafin taja motar fuuu sai gidan su Surayyah. Domin ta san a halinda take ciki a yanzu ita kaɗai ce zata iya tayata shawo kan matsalar da take ciki.
****
Wanke wanke takeyiwa inna amma gabaɗaya hankalinta baya kan wanke wanken har ta gamashi.
Maganar da innan tayi matane ma yasakata ɗagowa ta zubar da sauran ruwan robar tareda tashi ta ɗauki kwandon wanke wanken ta kaishi inuwa.
"Haba saleeha ki haɗa kai da gwiwa kiyi ta tunani,na sakaki aiki ma ko zaki ware amma sam abu ya gagara,inaga kinyi awa biyu a gaban kwanu kannan kina wanke su. Rana har ta isoki baki tashi ba. In bazaki kulada kanki ba ai saiki kulada lafiyar abun jikinki ko haihuwa ko yau ko gobe."
Ɗan murmushi tayi domin inda sabo tasaba da mitar inna akan tunanin da take jefa kanta. Kuma babu yanda zatayi ne,kota saka a ranta bazatayi ba dole sai tayi. Kuma koma mai ta tsinci kanta ai waccar ƙawartata ce sila itada wannan jarabbabben ɗannata,gabaɗaya sun sakata a gaba wai saita aureshi,kwanaki har ƙaryar kwanciya a asibiti yayi wai ciwon sonta zai kasheshi,itama yanxu innan harta fara yarda. Kawai dan tanajin nauyin yimata maganane shiyasa batace komai ba. Ita kuma tanajin a jikinta tabbas duk inda uban ɗanta yake yana nan kuma zai nemeta Insha'allahu.
"Uhm toh inna na daina. Shikenan aikin ko akwai wani"
"Ke a halinda kike ciki har wani aikin kike sake nema,babu wani in akwai ma zanyi abuna ko shiga ɗaki ki kwanta"
Har ta wuce zata nufi ɗakinnata saikuma ta dawo a hankali tana kame kame kamar mai son faɗin wani abun.
"Menene kuma kike susar gefen fuska,uwar fulako in kinason abu sai kiyi ta kame kame,har yanzu tsawon lokacinnan ai yaci ki saki jikinki ko"
Innan ta faɗa tana murmushi,dan ita halin saleehar tun yana bada mamaki yanzu dariya yake bata.
"Uhmm uhmm dama inna nace ina idan na haihun ba auramin Zajuli za'ayi ba ko?"
Shuru Adda tayi kafin tace.
"Banda abinki salaha to koni na tsugunna na haifeki kina matsayin bazawara ai banida ikon yimiki dole akan saikin auri wani. Ballantana har yanzu bamuda cikyakykyen labarin shin mijinki yana raye ko kuma akasin haka. To kinga bazayyiwu nayimiki dole ba. Amma ni dubamiki nakeyi zaman hakan ba mafita bace,tunda kin samu mai yimiki irin wannan son mai zai hana ki bashi dama ko kaɗanne?"
Anzo wajen,ita daman tasan naka naka ne koda yana yimaka abinda bakaso ko kuma yana aikata ba daidai ba. Yanzu mutum irin zajuli har shi akecewa ta bashi dama? Ina gaskiya bazaiyiwu ba,tunda nan ɗinma zuwa tayi batada kowa. Inaga mafita shine kawai tasake guduwa taje wani wajen. Na Allah ai basa ƙarewa a duniya. Muryarsa tajiyo shine ya katseta daga tunaninta,gefe ɗaya kuma gabanta ya bada sautin dummm. A razane ta ɗago ido ta kalleshi sukayi musayar kallo,wani killer smile ya sheƙa mata har saida dafaffun haƙwaransa suka fito fili. Saurin ƙasa da kanta tayi,daidai lokacinne yake gaisheda Adda wadda tayi sheƙeƙe tana kallonsa baki buɗe. Domin shigowa yayi wuff kaman an jefoshi yana wani yayyada kai kaman gwadan ƙadangare.
"Daga ina haka ka faɗowa mutane gida babu ko sallama"
"Ehh wlh dama nazo ganin masoyiyar tawane,gabaɗaya kwana biyu ina asibiti daban sakata a idona ba duk na kasa sukuni,shine ba na iyo sammako domin nazo nayi tozali da kyakkyawar wannan fuskartata"
Ya ƙarisa maganar yana sake kallon inda salaha take zaune,wacce takeji kaman wajen ya buɗe tashige domin tsoro,jikinta sai rawa yake kaman an jona mata wutar lantarki,inaaa bataga ta zama a garinnan ba dole ta gudu. Don wannan yanda yake ɗinnan tsaff zai iya afka mata ko yayi mata illa idan taƙi aurensa. Wannan karon ma maganar Addah ne ta tsamota daga dogon tunanin da take shirin afkawa.
"Ganin kana neman aure ido rufe har na fara tunanin ƙila hankali ya soma zuwar maka,amma da alama kwana biyunnan sake sukurkucewa ma kakeyi, kai wai ko cikin jikinta baka kallone da kuma shin daga ina ta fito,kawai ka kwance sai abu kakeyi babu kai babi gindi?"
"Ni ina ruwana da cikin jikinta ko kuma daga inda ta fito,ko daga ramin aljanu take ni wlh addah ina sonta,kuma da gaske nake aurenta zanyi. Ni cikinma nace inaso,babu ruwana da waye yayishi nima inda lokaci zanyi nawa. Yanda take kyakyawar nan nasan ƴaƴanta ba karamin kyau zasuyi ba da kuma farin jini. Kai nifa naji nagani addah........."
Allah ne yabata iko ta miƙe tsaye tareda nufar hanya zata bar wajen,domin maganganunnasu bata tunanin kunnuwan ta zasu cigaba da jurar jinsu. To a yanda ya ɗauketa ko tunkiyace ai iya kaci kenan.
Hannu yakai zai shafi fuskarta ganin tazo zata wuce ta gefensa. A razane taja da baya tana kallonsa cikin kiɗima. Adda ce tayi masa tsawa ganin katobarar dayake shirin aikatawa a gaban idonta.
****
A bakin ƙofar gidan su surayya ta faka motarta haɗeda danna horn domin sanarwa da maigadi da mota take tafe,babu bata lokaci kuwa ya leƙo domin ganin wacece,bayani tayi masa a taƙaice,da farko bai gasgata ta ba,ganin yanayin ta kamar bayyi masa kama da wacce zatace matar Ahmad Amjad ba,amma kuma motarta ta bayyana hakan.
Bayan tayi parcking ta fito kwatancen part ɗin su Surayyah yayi mata,domin yaune karon farko zuwanta gidan,ko da ta haifi su farhana ma da Nimrah tayi tayi suzo tare ƙi tayi,kasancewar tun a lokacin tana mutuwar son Ahmad ɗin.
Sallama tayi a falon babu kowa sai tashar sunna tv da takeyi, tana tsaye ƙiƙam harta cire tsammani taga wata yarinya tafito ƙarama da kofi a hannunta tana shan golden morn da cokali. Tun kafin Safeenah tayi magana tayi caraf tace.
"Wakike nema ko Aunty Surayyah?"
Gyaɗa kai Safeenah tayi da sauri tareda bata amsar ehh.
"To jomuje na nuna miki,tana shan ɗakin"
Gaba tayi itama tabi bayanta har zuwa wani ɗaki dayake cikin part ɗin.
Ƙwanƙwasawa tayi amma shuru ba'a buɗeba,saidaga can ciki taji muryar Surayyah tana cewa.
"Come in ƙofar a buɗe yake banason tashi"
Murɗa ƙofar tayi da buɗe ta shiga,a tsakiyar gado ta ganta a cikin wani farkin bargo,da alama ɗan bacci tayi na rana. Koda suka haɗa ido da Safeenah babu alamar mamaki a kan fuskarta,saima nuna mata kujera tayi da ido akan ta zauna.
"Banason tashi,idan mutanen gidan basusan kin shigoba to kiyi haƙuri da samun ruwa kisha,don na ɗakin yakare kuma basu shigo dashi ba har yanzu."
Cikin sauri Safeenah ta ɗora murmushi akan fuskarta tareda yin yaƙe kana tace.
"Ahhhh bakomai nasha ruwa ma,kuma yanzu ni bashi nake buƙata ba. Dama maganar dakikayimin rannane shine........."
"Har kin gaji da masoyinnaki kenan kinaso ki rabu dashi?"
Jin abinda Surayyah ta faɗa yasa Safeenah sauƙa daga kan kujerar tana kuka take labarta mata duk abinda yafaru, tareda haɗata da magiyar ta taimaketa.
Biris Surayyah tayi da ita saida tayi mai isarta kafin taja ajiyar zuciya kana tace.
"A halin yanzu nima da tawa matsalar bana tunanin zan iya yimiki komai, ko ita kanta wacce tayimiki bazata warware miki ba. Mafi sauƙi shine kuyi aure dashi,shine kaɗai makarin. Tunda rashin aurene ya haɗaku to auren shizai karya shi,amma ana ɗaura aure madadin Tsananin so to tsananin ƙiyayyaya zai miki,kuma yana sakinki ko yin nesa dake,to zai sake jin nan duniya ba wacce yake so saike. Dan haka sai kije ki yanke shawara,in kuma kafin sannan na kawar da matsalar gabana na iya waiwayar taki. Amma kafin sannan ki koma gidanku ki sanar da uwarki komai. Domin halinda kika shiga bakiga komai ba indai akan asirin bita zaizai ne. Sannan yaƙi na farko dazakiyi shine na kusada ke susan mai kika aikata kinemi yafiya,domin da alama da wannan yake amfani akan zai faɗa kowa in bakizo gareshi ba. Kekuma saboda rufin asirinki saiki biyemasa. To ki bankaɗa asirin da kanki kisha kunyar ki more,in kin tafasa kin ƙone a ciki kinga bashida wani makamin yaƙar taki."
"Wlh Aunty Surayyah hakane nagode nagode amma dan Allah ki taimaka ki waiwayeni domin......."
Ganin taja bargo kanta ta juya mata baya yasakata yin shuru taja jikinta tabar ɗakin a sanyaye.
Kai tsaye gidansu ta nufa,har sannan ƙirjinta bai daina dukan tara tara ba,domin tasan ruwa data ƙira yake shirin dukanta ba ɗan ƙarami bane.
Da Hajiya Hunaiza suka fara yin ido huɗu tayi ɗaɗdaya a falon tana cin tufa(apple).
Lokacin da tayi arba da Safeenah zaro ido tayi tareda jifa da Tufar hannunta ta isa gareta,hannunta ta kama tana duddubawa kafin ta ɗaga ido ta kalleta,daidai lokacin kuma safeena ta kau da kanta alamar marar gaskiya. Don tun lokacin da Safwan yafara yi mata bibiyar ƴan bunsuru bata sake shigowa sashennasu ba. Sadai waya kawai da sukeyi,tasan wannan mamakin da mahaifiyar tata tayi bai wuce na mahaukaciyar ramar da tayi ba.
"Feenah lafiya mai ya sameki haka,bakida lafiyane haka na ganki kaman tsohon maye ya kafamiki haƙora?"
"Uhmmm ehh to amma ummu ai zaki bari na zauna ko, tundaga baƙin ƙofa ki tsareni da tambayoyi"
Cikin tsiwa da rashin tarbiyya haɗeda ƙosawa da tambayar da uwar take jefa mata tayi maganar,sai daga bisani ta wuce uwar tazo ta zauna akan ɗaya daga cikin kujerun da suke falon.
Itama bata daddaraba ko nuna damuwa da yanda safeenan tayi mata magana,saima biyota da tayi ta zauna a gefenta tanayi mata kallon abar tausayi,dakuma son sanin mai yake faruwa.
Kafin da sake buɗe baki tayi magana ta tsinkayo muryar safeenan tana furta wata kalmar da bata gane kanta ba ballantana gindinta.
"Umma cikine dani wata biyu yanxu haka daga asibiti nake"
"Cikiiii kai Mashaallah ayyyrrrrr.........ahah tsaya wata biyu naji kaman kince,kodai ahmad yazo ya tafi bamusani ba. Don Kaman ba shekaranjiya ya dawo ba?"
"Ahah bai dawo ba,shekaranjiyanne dai dawowar sa"
"To ubanwa yayi miki ciki na wata biyu keda mijinki bayanan,ko kuma a ruwa kika kurba kai?"
"Umma safwan ne safwanne ummah shikenan nikam nashiga uku,na cuci kaina kuma kema kin cuceni wlh ummah"
Tirƙashi.