Chapter 31
by @sadisakhna
⚫ *MUMINA KO AZZALUMA*⚫
Available on:wattpad&arewabook
⚫ _SADISAKHNA_⚫
⚫ *BOOK 1*⚫
⚫ _PART 31_⚫
A riƙe take gamm a gefen kafaɗarsa ta dama,tana rarraba ido tsakanin su inna,mamar jazuli,jazulin da kuma wanda ya riketan. Duk da cewar bata tunashi ba idan ma ta sanshin,amma haka kawai takejin ranta ya nutsu da kasancewarsa a kusada ita,ji takeyi kaman ta tsira daga dukkan rikita rikitar da take afkawa.
Jaxuli ne fankan fankan ya taho a zuciye ganin saleeharsa a jikin wani yana rike da ita. Saida ya taho yazo tabb da Ahmad amma sai yaga yayi masa gizo,sanadiyyar wani kallo dayake yimasa mai wuyar fassara.
"Kai waye dazaka zo ka riƙe matar dazan aura"
"Matar dazaka aura,kai wanne irin ɗan akuya ne kaga mace bakasan inda take ba da ciki kace zaka aureta,baka tunanin ko matar aure bace. Kuzo ku sakaminshi a mota,dole shari'ah ta koyamasa hankali tunda bai san shari'a ba"
Bai gama rufe baki ba bodyguard huɗu suka kama jazuli,cikin ƙanƙanin lokaci har an wullashi a booth ɗin mota. Ganin haka da sauri mahaifiyarsa tazo Tana bubbuga bayan motar tana a fito mata da danta.
"Kuɗi aiba hauka bane,kai waye daga zuwa danka riƙe matar dazai aura yayi magana ka sakashi a bayan mota,wlh ku bani ɗana ku fitomin da ɗana"
Ganin wajen ya kacame inna duk masifarta batayi ba,a tsaye take saida ta ƙarewa lamarin kallo kafin ta karisa inda ahmad yake riƙeda saleeha a hannunsa.
"Bawan Allah kai waye daga ina kake,sannan miye dangantakarka da saleeha. Karka damu da waccar mahaukaciyar kayimin bayani dallah dallah,ni nice na riƙe saleeha lokacin datazo garinnan batasan komai nata ba ciki harda ita wacece gashi tazo da ciki. Mutane kowa da abinda yake faɗa,amma ni har cikin zuciya ta inajin saleeha bazata aikata wani abu na ƙi ba,saboda kyawawan halayen dana gani a tattare da ita. Dan haka kai wanene a gareta?"
"Har sai kin tambayi waye,inma shine mazinacin dayayi mata cikin jikinta to yazo a makare,domin an riga an bada ita ga jazuli,in kishine ma yasa ka rufeshi anan to ka buɗemin ɗana"
Cikeda bacin rai da kuma mamakin ƙarfin halin matar ya kalle,maganganunsa ba ƙaramin zafi suka yi masa,ita wacece to dazata dunga yin wannan furucin?.
"Ke marka wannan wacce irin magana kikeyi,soyayyar ƴaƴa wasa ce zata saka ki dunga wannan shashancin,dama yarinyar nan bason ɗanki take ba,ni kaina fama nake daku a dole saikin aura danki ita,to dama ana hakane"
"Abubuwane dayawa suka faru yasa bamu je nemantaba,amma itaɗin ƴar adam ce mai muhimmanci a wajena,kuma uwar ƴaƴana dama wanda yake shirin zuwa nan gaba, matatace da mukayi shekara shida a tare kafin ƙaddara ta gibta a tsakani,sai yanzu Allah yasa na ganta. Tabbas kece nurul'ain,kodaga rikeki danayi da kuma nutsuwar danaji a jikina kece ta gasken kece ummul farhan da farhana,wanda suka aikatamiki wannan abun kaff cikinsu babu wanda zan ƙyale,saisun biya abinda sukayi miki hadda ruwa akai Masoyiyata"
Kowa sororo yayi yana sauraron yanda yake zuba mata kalamai masu tsuma zuciya don muryarsa a karye take ya ƙarisa maganar.
Ɗagata yayi ciɗak kamar salon ɗaukar amarya ya kaita cikin dankarerriyar motar daya fito a cikinta. Kaman mai lallaba ƙwai haka ya jawo belt ya saka mata,hannunta yakamo yana kallon yanda suka fuffurce babu laushinnan irin nada. Itadai duk abinda yakeyi kallonsa kawai takeyi domin inta buɗe bakimma batasan mai zata furta ba.
"Barina gama da wannan masu tsaurin idon saina kaiki asibiti a duba ki ko,ina babu inda yakeyi miki ciwo?"
Tashi yayi zai fita daga motar yaji tayi saurin riƙo hannunsa. Cikin sanyayyar muryarta tayi magana ƙasa ƙasa kaman mai tsoro.
"Kace kai mijina ne hadda wasu ƴaƴan a tsakanin mu bayan wannan,to miyasa ban tunaba ko banda lafiyane dama?"
"Ahah lafiyarki ƙalau,wani abun akayimiki yana warwarewa zaki tuna komai,karki damu da sai kinyi zurfin tunani kanki yayi ciwo,ki kwantar da hankalinki komai yazo ƙarshe da iznin Allah"
Ya ƙarisa maganar yana shafa kanta cikin kulawa.
"Dan Allah kayi haƙuri ka ƙyalesu basusan kai waye bane shiyasa,sannan abinka da uwa ya kwanta a asibitine wai saboda soyayyar dayakeyimin,ganin karta rasa Shine yasaka take wannan abun. Kuma ƙanwar inna ce,tayimin abubuwa da yawa da bazan iya misaltawa ba,idan kayimusu wani abun bazataji daɗi ba."
Haɗe rai yayi jin tace wani yanasonta,shi tunda yagansu kafin ma su faɗi mai sukayi yaji ya tsanesu itada ɗannata. Kallon kawai yayi kafin yafito daga cikin motar.
"Kayi haƙuri bawan Allah duk rashin sanine yajawo,naga ka sakata a mota ku shigo mana daga ciki"
"Ahah karki damu inna abinda kikayima mun gode,naso na hukuntasu saboda maganganun dasuke, amma Surayyah tace na ƙyalesu kodan saboda ke,zamuje asibiti a duba lafiyarta,bayannan akwai abubuwan da suke buƙatar a warwaresu,shiyasa bazamu bata lokaci ba ga wannan kiyi haƙuri bamu fito da kuɗi sosai ba in komai ya daidaita nayi miki alkawarin zamu dawo musake gaisawa."
Ya ƙarisa maganar yana miƙamata damin kuɗi yan dubu ɗari ɗari guda uku. Kallon kuɗin tayi ta jijjiga kanta.
"Ahah yaro bazan karba ba,ni ban riƙe Saliha Ba au naji kace Surayyah sunan domin wani yazo ya biyani ba,iya haɗuwa da tayi da ƴan uwanta ma naji dadi sosai Inayi mata fatan alkhairi,inzaka bari dai zan leƙa musake sallama da ita kafin ku sake dawowar kaman yanda kace,ko kuma idan ta haihu kasanar dani,don harga Allah kallon ƴar dana haifa a cikina nakeyi mata"
"Bazan hanaki yin sallama da itaba,daman hayaniyar da aka farane yasa nakaita mota,sannan karki damu wannan kuɗin dana baki bakomai bane, idan haihu kuma nayimiki alƙawarin zan turo mota a ɗaukeki"
Matsawa tayi zuwa bakin motar da Surayyah take ciki,hannu ta sako da riƙe na inna tana murmushi.
"Kinga ikon Allah ko,gashi rana ɗaya Allah ya turo ƴan uwanki,kuma ma mijinki ya wanke miki zargin da suke miki"
"Inna nagode da ɗawainiyar dakikayi dani Allah yasaka da alkhairi, Idan Mallam liman ƙaninkin nan daya kawoni wajenki yazo kice masa nagode sosai,su zulai ma kice musu a yayyafewa juna. Kuɗin daya baki dan Allah ki karba kinji inna.
"Toshikenan saleeha Allah yayimiki albarka,ki sanarmin ai kinada numberta akanki ki ƙirani inkin haihu Allah yasadamu da alkhairi"
Ma'aikatan ahmad saida suka kwaɗe jaxuli yana koke shida uwarsa haka sukaja mota suka tafi,yayinda inna ma tana matsar ƙwalla da kalmashe dubunta ɗari uku a gefen zaninta.
Baikai ga zuwa asibitin ba Surayyah tayi ta jaddada musu lallai karkowa yasan sun samota su taho inda take kawai domin babu ishashshen lokaci.
A yanda ya barta haka suka shigo ya sameta,saidai jikinnata yaƙara ɗan tsanani ba kaman da ba. Ɗagowa tayi ta kalli ainihin Surayyah itama danata tuƙeƙen cikin hannunta rikeda na Ahmad. Ɗan murmushi tayi kafin tamiƙa hannu akan tazo gareta. Itakuma mamakin ganin kamar dasuke da ita yasa tayi ƙoƙarin cire hannunta zataje. Gamm ya riƙe hannun ya hanata zuwa.
"Mai zakiyi mata,zaki sake cutar da itane kaman yanda kika cutar da ita a baya?"
"Ahah mai yayi zafi zan cire makullin dayake jikinta ne,kuma nagana da ƴar uwata dana dade ban ganta ba"
"Dan kinyi surkulle kinyi kama da ita,hakan bazai baki damar zama ƴar uwartaba,saboda abinda kika aikata mata ko maƙiyinta bazai mata kwatankwacinsa ba. Sace rayuwar mutum kuma gashi da ransa ba abune karami ba"
Bata yi masa magana ba sai wannan murmushinnata kawai da tayi,yunƙurawa tayi ta tashi lokacin da Surayyah ta ƙariso gabanta.
"Barkanki Surayyah sunana Jurayyah amma ina amfani da sunanki ne saboda wani abu daya faru,ki manta komai daya farune saboda rufe miki tunani da akayi,amma yanzu zan buɗe miki"
Tana gama faɗin hakan tasaka hannunta a bayan wuyanta,shafa wajen takeyi harta zaro wani abu fari mai ɗan tsayi kaman tsinke yana walwali a tsakanin wuyanta, yana shan iska ya bace batt babu shi. Luuuu tayi zata faɗi Ahmad yayi saurin rungumeta yanayiwa Surayyah (Jurayyah) kallon tuhuma.
"Maida wuƙar babu abinda nayi mata,abinda aka datse tunaninta na cire mata,yanzu duk tunaninta na baya zasu buɗe ta tuna komai. Shock na sauƙar tunaninne yasakata yin karamar suma yanzu zata tashi"
"Meyasa kika gusar mata tunani bayan abinda kikayi mata na ƙwace komai nata bai isheki ba"
"Mai kakeci na baka yana zuba ne,da sannu zan warware maka zare da abawa,bayan na warware daganan ruwanka kaga laifina ko akasin haka,amma a halin yanzu ka daina wannan kintaci faɗin. Sai an fayyace yanda raƙumi ya bata a ragaya tukunna"
Suna cikin magana Surayyah ta farka haɗeda yin atishawa tayi hamdala.
Kallon Ahmad tayi ta kalli Jurayyah saikuma ta fashe da kuka mai tsuma zuciya,ba wanda yayi yunƙurin hanata,saida tayi mai isarta kafin ta goge hawayen kana tace.
"Abban farhan ina ƴaƴana,nasan yanzu kam sun manta dani koh. Koda yake kinyimin alƙawarin zaki kareminsu kuma zaki kulada Abbansu yana ganki anan kuma da tsohon ciki"
"Tayi maganar tana kallon Jurayyah wacce ta sunkuyar da kanta,itama idonta cika yayi da kwallar,duk dakiyarta ƴau ɗaya surayyan ta bata tausayi sosai haƙiƙa an cutar da ita cutarwa iya cutarwa,duk da akwai hannun wasu amma itama tasan da nata hannunta,domin a lokacin kallon tsana takeyi mata,gani takeyi kaman itace silar abinda yafaru da ita. Gyaran zaman ta tayi akan tsakiyar gadon ɗakin,shi kuma yana zaune akan kujerar dake gefen gadon da Surayyah a gefensa wanda yanzu tabar kukan sai goge fuska da takeyi,so take taji mainene dalilin dayasaka baza'a maidata gida taga ƴaƴan ta da iyayenta ba,aka kawo wajen wannan wacce take kallon fuskarta a tata.
Amin magana ta wannan layin
***
Sadi-sakhna ce.