MUMINA KO AZZALUMA

Chapter 34

by @sadisakhna

 ⚫ *MUMINA KO AZZALUMA*⚫

 Available on:wattpad&arewabook



⚫ _SADISAKHNA_⚫




🖤🖤🖤



⚫ _PART 34_⚫




Kallo da ƙaresu dashi kana ta jefamusu wannan murmushin nata,wanda na kula ko tana cikin mawuyacin hali bata gagara yinsa.

"Da alama labarin dana baku akwai abinda baku fahimta ba. Ahmad ko Surayyah da take matarka bata isa ta faɗamin lakantar halayenka ba,an saka min madubin rayuwarku na bibiyeta fiyeda yanda kuke zato. Sannan bangare ɗaya nima da nawa ra'ayin da har yanxu banga namijin dazan bashi kaina ba,musamman ma wanda bansan matsayina a wajensa ba,kuma mijin wacce take ƴar uwata da muka kwanta a ciki tare. Hmmmmm duk wannan shige maka dagaka nakeyi duk yana cikin acting ɗin dana kirƙira kuma nake gudanarwa,na zuba maka alamomi dayawa dazasu tabbatar maka dani ba Surayyah bace,ciki kuwa harda ƙin yarda danayi nayin rayuwa sakk irin tata,wanda kai kaɗai nake nunawa hakan idan ka kula. Shiyasa kowa inkayi masa maganar sai yaƙi yarda dakai. Ko wasi wasin dakake ji akaina duk aljani na nasaka yake saka maka su. Saboda nima a bangarena banida sha'awar yin zaman aure dakai na bogi. Duk da kuwa bazanyi muku karya ba zamana dakai naji na kamu da sonka,na kamu da son iyayena sannan kuma nakamu da tausayin Surayyah wanda a da banajin hakan saida nayi alaƙa daku a zahiri.

A yanzu nasan abinda kukeso kuji bai wuce matsayin cikin jikina ba. Hakane yanda na fara yimuku bayani,bamu tabayin wata mu'amala dakai ba,nasaka maka kaji kaman ka kwanta dani dai amma sam hakan bai faruba,ni budurwace cikakkiya ban taba kwanciya da kowanne na mijiba. Tun ranar dana gano babban burin hajiya zakiyya shine nayi karuwanci,kuma ƙiri da muzu take jin bacin rai idan taga ƴarta tana bin maza sai na ƙuduri niyyar nikuma bazan aikata abinda takeso ba. A lokacin bawai tsoron Allah na ne yakai yakawo ba,ko kuma son iyayena ba. Saidan inajin daɗin ƙinyin abinda wani yakeso,kuma na aikata abinda bayaso domin naga ya zayyi. A haka na taso tun inasawa a raina har yabi jikina, har takai takawo na daina ganin wani dalili dazai sa na buɗewa na miji cinyata samm"

"To cikin jikinki fa"

Ahmad ya katseta tareda watsa mata tambayar,zuciyarsa cikeda son sanin ya akayi hakan ta faru.

"Mai kakeci na baka yana zuba,karka damu komai a sannu zan fayyaceshi ku jishi tunda nayi niyyar hakan. Shin ina labarin extanal fertilization da akayiwa Surayyah a cikin su farhan,bayan aurenku da wata ɗaya tafara wani matsanancin ciwon ciki,bayan ka kaita a asibiti aka ce maka tanada matsala bazata haihu dakanta ba saidai ayi mata IVF. Abinka da ƴan boko kuma masu kuɗi sannan ba abine mai matsalaba sai Dr. Safwan ya lallabaka ka amince. Cikin nasara akayi fertilizing ƙwan Surayyah guda huɗu,Ɗaya  mace uku maza. Babu bata lokaci kika zabi mace da kuma na miji ɗaya,aka sakamiki kuma aka samu nasara suka zauna,yayinda sauran kuma akayi frozen ɗinsu saboda gaba.  Saidai sannu a hankali bayan kin haihu aka baki hutu mai tsayi tareda ɗoraki kan magani a india inda sukace da kunzo ma aka ɗoraki a magani zaki warke basai anyi IVF ba,cikin ikon kuwa kika warke suka tabbatar miki dazaki iya haihuwarki cikin sauƙi batareda matsala ba anan gaba. Wannan abu anyishi ne bada sanin mutane dayawa ba. Amma cikin ƙalilan dasuka sani hardani a ciki,saboda na faɗamuku na daɗe ina bibiyar rayuwarku. Allah sarki wannan ƴaƴa biyu da kuka manta dasu a cikin daskararriyar ƙanƙara batareda sanin matsayin gobensu ba,su ƴar uwar mamarsu taji tausayinsu ta ɗaukesu kuma ta dasasu a cikin mahaifarta ake shayar dasu da jininta kuma sukejin ɗuminta,sannan kuma takeyiwa ubansu barazana dasu"

Ƙarisawa maganar tayi tareda komawa ta kwanta saboda gajiyar da bayanta yayi a zaunen. A lokaci ɗaya kuma Surayyah da Ahmad suka Zaro ido dan sai bayan ta kwanta tukunna suka gano mai yake nufi. Kenan ƙwayoyin halittarsu da akayi frozen tazage taje aka dasa mata tashin hankali...

Ganin sun gane mai take nufi yasa tasaki ƙasaitaccen murmushi tareda shafa cikin a hankali.

"Karku damu fah zanzosu tamkar jinina,jinin wanda nakeso da ƴar uwata yaushe zan ƙisu,in Allah yasa sun kai da ransu zan kuladasu,idan kuma su sunkai ni bankai ba kunga nayi muku surrogation a kyauta kenan"

Maganganun nata sanyi yakamata susa mutum yayi koma yayi ta kuka,amma tsabar dakiya da takedashi na zuciya kaman ita abubuwan suke faruwa da ita ba ko suka faru da ita.

Itakam Surayyah banda hawaye dayake zuba a idonta kaman famfo babu komai,gabaɗaya labarin ya kiɗimata matuƙa,ga tausayin ƴar uwartata daya shigeta sosai har takasa cewa komai sai kallonta da kawai takeyi,yanzu in itace akace wannan abun ya faru dashi ya zataji kenan a ranta,lallai Jurayyah tacika mai dakyakykyiyar zuciya,a da tanayi mata kallon Azzaluma amma yanzu sam ba haka bane,dan ita a iya saninta bata taba ganin wanda akayiwa zalunci kamanta bama,ƙarin zalunci ne a ƙirata da wannan sunan.

Ahmad ne ya katse mata tunanin da takeyi ta hanyar jan hannunta zasu tafi.

Saurin fizge hannunta tayi tareda dafe mararta daya yanka mata wani azababben ciwo mai shiga har tsakar kai. Cikin kiɗima ya zauna akan kujerar yana leƙata domin yaga ko lafiya,itakuwa sai cije lebe take tana jujjuya kai lokacin guda.

"Kingani nidama naso na wuce dake gida na sanarwa kowa dawowarki dakuma fayyace abinda ya faru,kika sakamu tsayawa jin wani labari,zaki iya tashi ko na ɗaukeki muje asibiti"

"Karkayi garajen fitar da ita daga wajennan tunda kun riga kun shigo lafiya batareda an kashe baƙar wutar da takeci a wajen ba. Naƙuda tafara kuma da alama yazo mata da ƙarfi,ka ƙira Dr. Safwan yazo ka turamasa address ɗin wajen sannan kace yayi basaja kuma yataho shi kaɗai batareda yafaɗawa kowa ba a asibitin"

Wata harara Ahmad ya watsawa Jurayyah tareda cewa.

"Wannan wasan kwaikwayon ya isheni haka,komai ina binkine kafin na samu matata,amma tunda na sameta wannan matsalarki ce tsakaninki da ita kuje can ku ƙare"

"Hmmm Amjad kenan, a tunaninka  har naƙuda da kamani amma sauran ƙarfina duk yanaga yanda zan taimaki Surayyah duk inayine domin kaina,ka manta tsananin kamar da mukeyi da itane,to koda bama kama Hajiya zakiyya takalli Surayyah kuma ta tabbatar bani bace sai tariga saurin cutar da ita akanni,saboda tasan ba wanda salwantarta zatafi yiwa iyayenmu ciwo kaman ita. Shikuma dr. Safwan tabbas nasan ya yaudareka,amma akaf asibitin garinnan babu wanda yadace ka yarda dashi kamansa,saboda hajiya zakiyya tayi ƙaurin suna wajen siyan mutane su zama idanuwanta a inda batanan,shikuma soyayyar dayakemin bazata saka ya yaudareni ba nasan haka"

Duk da bayaninta hakan baisa Ahmad ya gamsu ba ɗari bisa ɗari,saima ƙoƙarin ɗaukar Surayyah dayake shirinyi subar asibitin,itakuma ganin hakan yasa ta ƙwace jikinta tareda cewa.

"Tsawon lokacinnan duk da tayi wani abu ba daidai ba amma munsan wani abun ba ita tayiba koba yin kanta bane,dan haka dama ta ƙarshe ka amince mu yarda da ita iya wannan kawai,kaje ka ƙirashin yazo .......dan Allah"

Ta ƙarisa maganar a galabaice cikin halin ciwo.

Hakan kuwa akayi badda kama yayi cikin kayan aikin gareji akan tsohon mashin yashigo layin wajen har zuwa gidan da akayi masa kwatance,babu bata lokaci suka shigo,amma tareda wata nurse guda ɗaya mai ɗan kama dashi"

Kallon tuhuma ahmad ya bishi dashi,hakan yasa yayi saurin kare kansa.

"Ayi haƙuri yallabai hakan bazata sake faruwa ba,nasan da alama gimbiya ta fayyace maka abinda ya faru. Wannan kuma ƙanwatace ba bare ba,bazata bada matsalaba,midwife ta karanta bana sukayi graduation,naji kace abinda yashafi haihuwane shiyasa nazo da ita"

Ahmad bai sake cewa komai ba yabasu wajen suka wuce,koba komai yaji daɗin zuwa da macen. Bayan sun wuce baibi bayansu ba,ɗakin daya ƙirada nasa anan aka shigar da Surayyan,itakuma Jurayyah tana guda ɗaya itama. Sai sagir wanda shike yin badda kama ya nemo wani abun,shima dr. Safwan ɗin yasanshi,shiyasa basu wani sha wahalar fahimtar juna ba.

Abin ya fara isar Ahmad ganin da matsayinsa da komai ga jami'an tsaro amma yazo yana rayuwa acikin kewayayyen waje saboda wata can,sannan ga matarsa na buƙatar ishashshiyar kulawa. Sai yayi niyyar yin wani abun saikuma zuciyarsa ta hanashi,ba dan komai ba sai lafiyar matar tasa yake jiyewa,kar yayi abu kai tsaye kuma axo a samu matsala,yazo yana daya sanin da yabi zancen jurayyan,tunda ance ba'a shiga ramin maƙiyi sai ansan mai zai'iya miye kuma bazai iyaba,sannan wanne irin salo da ƙarfi yakeda shi.

Gadan gadan naƙuda takama Surayyah,da taimakon ƙanwar dr. Safwan ta samu ta haihu,Allah yasa ma abin baizo da matsala wani lokaci dabaifi awanni uku na ta ɗanta na miji fari sol dashi, kyakyawa mai kamada Ahmad sak,dan har yafi su farhan kama dashi. Bayan an gyarashine Nusaiba ƙanwar safwan takawomasa shi a cikin tawul din data taho dashi daga asibitin. 

Karbarsa yayi cikin sanyin jiki yana kallonsa,gaba ɗaya baifi awa ashirin da huɗu da sanin samuwar cikinsa ba,sai gashi an kawo masa shi cikin tsumma har ya fito duniya kuma ɗansane ɗan matarsa abar sonsa. Hawayene ya taru a cikin idonsa,soyayyar yaron sosai tashigeshi kaman bai taba karbar ɗansa kaman haka ba. Lallai akace ƴayanka ko ɗarine to kowanne kana sonsa.

Har saida sukayi gyaran murya kafin yamiƙa yaron aka kaimata shi,tafito daga banɗaki za'a fara bashi nono.

Shida kansa ya wuce ya kaimata yaron,tana zaune a bakin gado harta sauya kaya,banda ƴar rama data ƙara na wahalar naƙuda babu mai cewa ta haihu,murmushi ta sakar masa ganin yashigo da jaririn a hannunsa. A inda take zaune shima ya zauna kafin yasaka mata yaron akan cinyarta. Gyara masa zama tayi cikin nutsuwa kafin taciro mama tasaka masa,yana wawure wawure kuwa har ya samoshi yasaka a bakinsa. 

"Kinga ikon Allah ko Nureetee, a lokacin dana yanke tsammani sai gashi Allah yadawomin dake harda tsarabar kyakykyawan saurayi mai kamata,babu abinda zance sai alhamdulillah ke ɗin rayuwata ce.

Dagowa tayi itama ta kalleshi,baza ta iya fayyace iya adadin kewar datayiwa mijinnata ba,wanda kullum bashida aiki idan suna zaune sai yabonta da kuma laƙana mata kalaman soyayya. Idan suna zaune gabaɗaya manta a wanne duniya suke itada shi.

Haka nima takasance a bangarena,jiya iyanzu ina nan a zaune bansan makamar yadda rayuwata zata kasanceba,shikansa ɗan dayake cikina taradaddin haifarsa nakeyi saboda bansan da wanne matsayi zai kasanceba. Sai gashi na haihu Allah yasada ɗana da mahaifinsa mai ƙaunarsa kuma abin alfahari a gareshi Alhamdulillah shine kaɗai abinda zance ga ubangijina mai yin yanda so"

Da sauri nusaiba ta shigo ɗakin hankalinta a tashe,ɗaga ido sukayi a tare suna kallonta cikeda son jin mai ya hankaɗota haka.

"Ranka ya daɗe ɗaya madam ɗin,tana cikin wani hali tana ƙiran Surayyah takeson gani da gaggawa"

Tun kafin Ahmad yace wani abu tuni Surayyah tayi gaba hannunta rikeda jaririnta,saida nusaiba ta tareta ta karbeshi, ta miƙamata shi da sauri ta nufi wajen ƴar uwartata,harta manta da wani ciwon mara da takeji wanda bai gama saketa ba.

Amin magana ta wannan layin 
***
Sadi-sakhna ce.