MUMINA KO AZZALUMA

Chapter 35

by @sadisakhna

⚫ *MUMINA KO AZZALUMA*⚫

 Available on:wattpad&arewabook



⚫ _SADISAKHNA_⚫




🖤🖤🖤



⚫ _PART 35_⚫



A durƙushe ta sameta tana fitar da numfashi mai wahalar fitowa,nishi takeyi iya ƙarfinta,wanda duk wanda yayi ido biyu da halinda take ciki dole sai ya tausaya mata,mamakine yakama Surayyah wacce tayi mutuwar tsaye akanta. Yanzu duk wannan wahalar da takesha ta zabi tashata kawai domin ta haifo ɗanda ba nata ba kuma bana wanda take aure ba?.

Ɗagowa fuskarta tayi ta kalli Surayyah da take tsaye,wani jajirtaccen murmushi tasake mata kafin ta miƙa mata hannu alamar ta iso gareta,batayi musu ba kuwa taja sanyayyun ƙafafunta da jikinta marar ƙwari itama ta isa gareta. A gefenta ta zauna haɗe ta riƙe hannunata gamm a cikinnata. Cikin kalalliyar murya Jurayyah tafara yimata magana.

"Kina tunanin meyasa nakeshan wannan wahalar akan abinda nina ɗauki hannuna na jawowa kaina ko?. Hmmm ƴar uwata ko nadama banayi na abinda na aikata,sannan da dukkan zuciyata nakeson abinda zaizo duniya na ganshi. Sannan bana tunanin koda narayu na sake haihuwa a gaba zanzoshi kaman sa. Bazan miki ƙarya ba ina tsananin ƙaunarki sosai,duk abubuwan danakeyi miki badaga cikin zuciyata suke fitowa ba,sannan inason Mijinki Ahmad shine ɗa namiji na farko dana fara so a rayuwata,duk da banajin koda mun zama mu biyu nidashi a duniya zan iya zaman mace da namiji dashi saboda ke Surayyah,ko iyayen dasuka kawoni duniya banayi musu son da nakeyi miki,wani farinciki nakeji idan naga kamata akan fuskarki,a da nayi zaton banida kowa,amma idan na kalleki na tunada ke ƴar uwata ce sai naji zuciyata ta girgiza,ke da Ahmad kune maƙasudin gazawata a cigaba dayin aikin da Mommy tasakani,saboda zuciyata tazo gandun da bazata iya jurar cutar daku ba sam, to wannan jinin dayake cikina fah na waɗannan mutanenne, kuma har nayi nadamar ɗaukarsa koda zayyi silar fitar raina?"

Girgiza kai Surayyah tayi hawaye na fita daga idonta.

"Duk da haka da baki aikata hakaba Jurayyah,bai kamata mutum yadungabin zuciyarsa ba akan komai koda yasabawa mahaliccinsa, ubangiji maɗaukakin sarki shiyafi cancanta ki bashi muhimmanci fiyeda komai a rayuwarki,sannan kibi koyarwar shugaban halitta Annabi Muhammad (SAW). Ko a labarinki naji abubuwa da dama dakika aikata wanda basu dace ba,saidai nasan ba laifinki bane laifin yanayin tasowar dakikayi ne, na rashin sanin hukunce hukuncen addini. Zuciyata tayimin daɗin jin kaman yanda nakejin ki a raina kema kina jina,Insha'allah zaki haihu ki kalli ɗanki kuma kiyi rayuwa mai kyau ki haifi ƴaƴa ta hanyar da musulunci ya yarda da ita. Haihuwar taki da alama zatazo da matsala,bari na ƙira Dr yazo ya dubaki"

Cikin rawar murya mai ɗauke da damuwa take yi mata bayanan,yayinda itakuma take saka numfashi jefi jefi,amma maganganun Surayyah tabbas sun tsaya mata a rai,domin ita kanta tasan idan akwai abinda tarasa bai wuce ilimin addini ba,to waye zai koya mata,ɗan gwara ma Inayah tana kwabarta akan wani abun. 

Duk abinda suke faɗa Ahmad yana jinsu,yabiyo Surayyah tasauri amma jin kalaman Jurayyah yasa ya fasa shiga,shin yanayinta na ƙara zafi yasa yakoma ya ƙira Dr.Safwan.

Tsawon awa biyu kenan suna tsaye a bakin ɗakin,Dr.Safwan ne a ciki shida ƙanwarsa,sunata ƙoƙarin wajen ganin sun bawa Jurayyah duk taimakon daya dace. Sai bayan wasu lokuta ya fito hankalinsa a tashe.

Surayyah kuwa ko zama tagagara yi,duk yanda Ahmad yake fama da ita kan taje ta huta itama haihuwar tayi amma fir taƙi,danma jaririn nata bamai rigima bane,wajen tamkar ba ƙaramin jinjiri. 

"Ranka ya daɗe abin fah yana nema yafi ƙarfina,haihuwar tazo ta matsala sosai,da alama akwai abinda tasha  lokacin cikin yana ƙarami yabata matsala sosai,ko lokacin nayi mata magana akai banyi tunanin matsalar zata kai haka ba"

Cikeda damuwa Ahmad ya sunkuyar dakansa,dan shi kansa shaidane kuma yasha kamata da shisha.

"Hakane kam tana shaye shaye,amma kaman shisha take sha shima yanada matsalane har haka?"

"Ehh to maganar gaskiya ba shishar bace,kayan mayen da Zeezah take saka matane ya haifar da matsalar,kuma da alama dama cikin jikintan akayi attacking dashi."

"To yanzu dr. Miye abunyi,shikenan bazata haihu ba kenan?"

"Ahah ba haka bane,da alama bazata iya haihuwa da kanta bane,saboda bana tunanin yaran ma sunada rai,itakuma tayi laushi bazata iya fitowa dasu ba dan haka dole sai an fitada ita zuwa asibiti domin..........."

"Yaaya yaaya dr. Kazo kai yafara fitowa yanzunnan"

Asiya ce ta leƙo a firgice taƙira dr. Safwan ɗin, Shima jin abinda ta faɗa yasa yakoma ɗakin da sauri,Surayyah ma binsu tayi da sauri,wannan karon babu wanda yayi yunkurin hanata saboda ganin yanda ta damu kwarai.

Daidai shigarsu ne yayi daidai da ƙarisa fitowar jaririn cikin duniyar,hannu yasa ya tallafeshi,jikinshi lakab kaman marar rai. Ɗagashi sama yayi ai kuwa jin iskar duniya yasa yafara motsa hannunsa. Ganin haka yasa miƙawa Sister Asiya shi.
"Mashaallah yaron yanada rai, maza ki bashi taimakon gaggawa bari na cigaba da kulada ita,consious ɗinta na shirin ɗaukewa,Idan ta suma bata fitar dashi ba za'a samu matsala."

Jijjigata yakeyi yana yana danna cikin,lokaci bayan lokaci take fidda nishi a hankali,wanda kowa yagani yasan ba ƙaramin dauriya take ba wajen yinsa. Ƙarshe ganin za'ayi biyu babu yasa ya yatsagata(ephisiotemy) ya saka hannu ya jawo yaron,saboda ganin da tayi nishi ya taho,kuma yana ƙoƙarin komawa.

Jinine ya wanke wajen kaman an yanka dabba,gashi ya haɗa uban gumi shirkif,banda uwar gayyar da har yagama ɗinketa hankalin ta ya gushe batasan inda kanta yake,ga jininta yayi ƙasa sosai dole sai anyi mata ƙarin jini.

Jaririn daya ciro daga cikinnata na ƙarshe ya ɗaga,yayi Kalar jibi (purple) mutum yana gani ma yasan dama babu alamun rai a tattare dashi.
Lullubeshi yayi a gefe kafin ya kalli sister Asiya wacce tagama goge na farkon dayazo da rai ta naɗeshi a towel. Miƙawa surayya shi tayi wacce duk abinda ya faru akan idonta ko kiftawa batayi,jikinta yayi sanyi kalau ganin halinda ƴar uwartata tashiga.

Cikeda damuwa dr. Safwan ya kalli Jurayyah wacce take kwance kaman gawa kana yace.

"Tohh an tsallake wani mataki sai kuma na gaba,abubuwan da suke cikinta sun fita lafiya,sai kuma jini,wanda jininta yayi ƙasa dayawa,kuma ma cigaba dayin ƙasan yakeyi,idan ba'asaka mata jini ba zata iya rasa ranta.

Kallonta Surayyah tayi idonta ya sauƙa akan alamar da take jikinta,wanda tayi mata bayaninta jiya,wajen yayi jawur alamar ana shirin kaiwa jininta ga dodo kokuma ankai. Saurin karisawa wajen tayi tana jinjiga kai.

"Wannan matar bazata barta ba kokarin kasheta takeyi,bazata barta ko ɗan da ta haifa ta ganshi ba. Yazamuyi dr.?"

Kallon rashin fahimta dr. Safwan yakeyi mata kafin yace.

"Bangane mai kike faɗaba,waye zata kashetan,ai wanann shugabar tasu?"

Bayani tashiga yimasa na abinda yake faruwa,jijjiga kansa yayi alamar gamsuwa kafin yace.

"No wonder muna cikin wannan artabun sai weak takeyi jininta yana ƙarewa,ashe ba iya haihuwar bane yake barazanar ɗaukar rayuwarta harda wani abunma daban. To amma wannan lamarin baza'a ɗauko malami ba kuwa,tunda abune yahaɗa da shirka dakuma mutanen boye,to babu wani mai taimakonmu sai wanda zayyi aiki da Ayoyin Allah"

"Ehh hakane batun jini kuma inaga Ahmad zai iya bata tunda jininsa O ne,nima yabani a haihuwar su farhan.

"To Mashaallah tazo gidan sauƙi,akwai abubuwan ɗaukar jini a kit ɗina,Asiya idan kunyi magana dashi saiki ɗauka a saka mata,ni bari zanje akwai malamin Masallacin juma'ar mu zan taho dashi in nayi masa magana ya amince.

Da sauri ya ɗau key ɗin motarsa jikinsa yana rawa ya fita,dan ma almuru yafara gari yayi duhu saboda tsaro.

Duk abinda su Surayyah sukeyi Hajiya zakiyya tana kallonsu ta ƙofar da take suyan Jurayyah,wani shu'umin murmushi tayi ta murza zoben hannunta lokacin da Jurayyah tazo haihuwar ɗanta na biyu,hakanne yasa jikinta yasake takasa aikata komai,kuma dalilin kenan dayasa ta daina jin mai suke tattaunawa,saboda tajin Jurayyah take amfani wajen gane a ina suke mai suke,idan taso zama yin hakan. Yanzu dayake nemanta take ruwa a jallo shiyasa tayi wani siddabaru akanta,dodo yasaka aljanin dayake jikin hatimin wuyanta yana ɗiban jininta da kaɗan kaɗan,itakuma yana turomata duk wani abu dayake wakana a wajen.

Batasan mai suke faɗaba sai gani tayi kawai Dr. Safwan yafita daga cikin ɗakin,sannan wani abun takaicin ɗakin kawai take gani jurayyan bata fitaba ballantana tagano a inda suke,sannan abinda yasa ta sumarta saboda su razana su fitar da ita asibitine amma sam sunƙi yin hakan. Takaici ne ya isheta hakan yasa ta murza zoben hoton ya ɗauke,daidai shigowar zeesha kuma falon wacce take sanye da wani ɗan iskan wando shida babu duk ɗaya.

Kallon takaici Hajiya zakiyya tabita dashi kafin tace.

"A ina kika kwana da sai yanzu kikaga damar dawowa?"

"Ohhhsh mommy menene haka,saikace kin Turke ƙaramar yarinya,amm mature enough nayi rayuwata,kuma ke kanki kinsan bana zama for long time babu namiji,inason maza sosai so bazan iya rayuwa irin taku ba wai babu maza a lamurrana."

"Zancen banza a hakan zan damƙa miki ragamar komai kina yawo a titi kamar karya a ƙasan maza,dole saikin raba hulɗa dasu,na tsani naga mace tana bin namiji,ban yarda dasu ba samm tun tabon da namiji ɗaya yayi min na tsane su,na zabi su zama a ƙasana har abada na takasu amma badai na basu kaina a matsayin ƙarƙantacciya ba. Dan haka bazan taba zuba ido wajen ganin ƴata tazama baiwarsu ba,shiyasa dolene ki daina hulɗa dasu saidai a matsayin yaranki"

"Ahah bazai yiwuba ni bazan iya rayuwa basu ba,hakan ma ba ɗaya ko biyu ba. Inaso na dunga caccanjawa ina jin kala kala,shiyasa aure ma baya tsarina sam. To ni ya akayi ma kika haifeni in baki hulɗa da maza,a sanina dai baban rayyah ne yayimiki haka,toni nawa uban fah?"


Amin magana ta wannan layin 
***
Sadi-sakhna ce.