“SANADIN ƘADDARATA”

Page-65

by @zahratulqalam51

*FASAHA WRITER'S ASSOCIATION*
     (*F.W.A)*©✍️
     ⭐⭐⭐

Ƙungiya masu aiki cikin salon hikima da fasaha gurin juya tunanin al-umma, kaifin alƙalumansu ya zarta takobi ©✍
___________________________________________________



بسم الله الرحمن الرحيم.
اللهم صلي وسلم على نبينا محمد. 




❁ 𝐒𝐀𝐍𝐀𝐃𝐈𝐍 Ƙ𝐀𝐃𝐃𝐀𝐑𝐀𝐓𝐀 ❁ 




Free book📓



By: _*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_



Page6️⃣5️⃣





Da mamaki mu ke kallonta jin wai ta ganni à cikin TV, don haka daga ni har Haidar mu ka fara juyawa ta ɓangaren. 

Sai dai a lokacin da mu ka kai dubanmu ga TV wani labari daban ake nunawa, hotona da Khairat ta ce ta gani mu ba mu ganshi ba, da murmushi mu ka dawo da dubanmu ga Khairat, Haidar ya janyota ya ce, "My dear, soyayyar Anty ya yi yawa har kina ganinta a TV?" Murmushi ta yi tana kuma maimaita ai ta ga Anty Nuliya à EV, sannan ta juya da gudu wai bari ta je ta sanarwa da Ummee.

Da kallo na bi ta ina 'yar dariya, sannan na juyo ga Haidar na ce, "ina jinka yaya Haidar" sauke ajiyar zuciya ya yi, haɗi da gyara zama sannan ya ce, "Wani magana mai mahimmanci na ke son sanar da ke, kuma don Allah ina roƙonki, ki bi son ranki kada ki amsa min don wani abu daban, so na ke ki sanar da ni abun da ya ke daga zuciyarki".

Ni dai kallonsa kawai na ke ina girgiza kai, domin ni kawai maganar na ke jirar fitowarsa, saboda ba abun da na kawo a tunanina. Shi kuwa sai da ya kuma sauke numfashi, domin haka kawai ya ke jin nauyin maganar, "ranar na ce miki ina son ki ɗauki Khairat a matsayin 'yarki ko?" Na giɗa kai alamar haka ne, sannan ya kuma cewa, "abun da na ke nufi a wannan maganar shine...." kafin ya ƙare cewa Khairat ta kuma shigowa falon da gudu ta yo gurina, hannunta da hoto ƙato wanda aka gyarashi cikin wani gida mai kamar glass. Irin yadda za a iya maƙale shi jikin bango.

Da sauri na kama hannunta yayin da ta ke dariya, sai kuma ga Mu'azzam ya biyo bayanta yana cewa, "Bobbina ki kawo shi nan, kar ki fasa fa, in ba haka ba ke da Ummee ba ruwana" kallon Mu'azzam na yi ya tsaya yana sauke nishi wai shi ya yi gudu, na ce, "ya dai Mu'azzam? Yanzu Khairat ɗin da ka biyo shine ka ke uban nishin nan?" Na yi maganar ina dariya.

Haidar ya ce, "indai Mu'azzam ne za ki ga abun da ya fi haka. To kai me ka ke wa 'yata wannan bin? Idan ta faɗi fa?" Ya faɗi bayan ya kai dubansa kan Mu'azzam, Khairat sai dariya ta ke tana kuma shigewa jikina, tana ɓoye hoton wai don kar ya ƙwace, "yaya Haidar ni da Bobbina fa ba a shiga tsakninmu." Cewar Mu'azzam yana dariya, sannan ya ƙara da cewa Ummee ce ta ce ya amsi mata hoton. Haidar ya girgiza kai yana murmushi.

Ganin haka sai na fara lallaɓar Khairat ta ba shi hoton saboda kar ta fasa, sannan na ce da ita zan kawo mata na ta wanda ya fi kyau" murmushi ta yi min tana giɗa kai alamar ta amince za ta bashi, don haka ta ɗago hoton da ke kife ta baya tana miƙa masa" sai a sannan idona ya kai kan hoton duk da ba ganinsa da kyau na yi ba. Mu'azzam ya karɓa sannan ya juya.

Gefe na yi da kaina na haɗe girana wanda hakan ya ke nufin kamar akwai wani abu da na gani a jikin hoton, da sauri na tsayar da Mu'azzam sannan na miƙe na amshi hoton don na gansa da kyau.

Sai da hannuna ya kusa sakin hoton saboda tsabar yadda zuciyata ya harba, na zare ido ina ƙarewa hoton kallo, ganin haka yasa su Haidar mamaki, Khairat dai gaba ta kuma yi da guduta je ta ɗauki pillown kujera ta fara wasa da shi. Kafin kowa ya yi magana na juyo na kalli Mu'azzam sannan na maida kaina ha Haidar na ce, "yaya Haidar... me alaƙarku da na cikin hoton nan don Allah?!" Da tsananin mamaki Haidar ke kallona, kafin ya samu damar ba ni amsa da, "ke kin san na cikin hoton ne?!".

SADIYA.

Ba ta da wani matsala yanzu, saboda komai samunsa ta ke yi alhamdulillah, duk da idan ta tuna da ta rasa ɗanta guda ɗaya abun na yi mata ciwo sosai.

Faruq kuwa ya kasa mantawa da rashin ɗan na sa, musamman idan ya dubi cikinta da ya ɗan fara tasawa sai ya ji wani ƙuna a ransa, yana ganin da yanzu rai biyu ne a ciki. Sai da Sadiya ta taushesa bayan sakin da ya aikawa Nusaiba ta waya, don cewa ya yi sai ya sa ankulleta saboda ita che ta kashe masa ɗa.....

"Nagode sosai Sadiya, SANADIN ki ga shi zan koma gidan mijina, kin bani shawara kuma ya min amfani, na bi komai a hankali na ajje duk wani girman kaina na roƙi mijina akan ya yafe min laifukan da na yi masa, kuma na yi na dama na gaskiya. Sai ga shi da kansa ya ce zai mai da ni ɗakina. Duk da cewa ya riga da ya yi aure, amma wannan nasara ce agareni, kuma insha Allah zan yi amfani da haƙuri daidai gwargwardo gurin cigaba da yin zaman aurena. Bayan abubuwan da na sha yi miki a baya, kin manta da komai kin zauna tare da mu kamar ba abun da ya taɓa faruwa a tsekaninmu, ba kyara bare mummunar magana. Na gode miki Sadiya Allah ya saukeki lafiya, ya kuma cigaba da dawwamar da farin ciki a cikin rayuwarki".

Duk wa'yan nan kalaman Lantana ce ke yin sa wa Sadiya, yayin da su ke sashin Baaba zaune a tsakar gida. Murmushi Sadiya ta yi sannan ta ce, "ameen ya Allah Anty Lantana, addu'ar da ki ka yi min ya fiye min godiyar da ki ke ta yi min tun ɗazu. Ina son ki sani, Allah ne ya bani iko da har na baki shawar kuma ta yi amfani, ina so ki sani, duk wanda ya yi maka laifi sannan ya nemi yafiyarka, to abu mafi kyau shine ka zauna da shi kamar komai bai faru ba, ka manta da abun da ya wuce na baya, domin Allah yana ɗaga darajar duk wanda ya karɓi yafiyar wanda ya yi masa laifi, saboda haka ni ba na son ki rinƙa dawo da abun da ya faru, Abu na ƙarshe da zan iya ce miki à matsayin wacche ta ke ƙanwa a gareki shine, Allah ya tabbatar miki da alkhairansa".

Jinjina kai Lantana ta yi har da share 'yan ƙananan hawayenta, dai dai isowan Baaba riƙe da abinci rufe cikin plate, da kuma ruwan gora. fiskarta cike da fara'a, tana matuƙar ƙaunar surkanta Sadiya sosai, musamman saboda kyawawan halinta da sai yanzu ta gama ganosu, miƙawa lantana ta yi, sannan ta janyo bencin da ke kusa mara tsawo me faɗi, ta kai shi kusa da Sadiya, sannan ta amshe abincin daga hannun Lantana ta ɗaura da kai.

Lantana da har ta buɗe ta yi zaton ita ce Baaba ta kawowa ta ga an amshe, Sadiya dai ba ta ce komai ba har baba ta ɗaura abincin ka na ta ce, "to 'yata Sadiya ga dambun nan na yi miki, saboda na ji kin ce kina kwaɗayinsa, Allah yasa ya yi miki, son masu laulayi da dama ki ji suna kwaɗayin abu da an kawo musu kuma ya gunduresu".

Sai da kalaman Baaba su ka ba Sadiya kunya, wato ɗazu da ta ce wa Aisha kwaɗayin dambu ta ke zuwa ta yi ta sanarwa Baaba kenan?.

Amsa ta yi tana godiya, Lantana ta ce, "Baaba dama ba ni ki ka kawowa ba? To nima asa min dambun," hararta Baaba ta yi ta ce, "akan me zan kawo miki? 'Yata na kawowa ba ke ba, ba da sunanki na yi sa ba" ta faɗi sannan ta wuce, buɗewa Sadiya ta yi aikuwa ƙamshi ya dakar mata hanci, ji ta yi har miyau ya tsinke mata, ba shiri ta ɗauki cokalin da ke gefe ta fara afawa, gashi dambun ya ji komai ya yi daɗi. "Tun da Baaba ta hanani ke kya ba ni ko? Na ga alamar rowa za ki min, kin fara ci ba bismillah" cewar Lantana cikin sigar wasa.

Sai da Sadiya ta tsaya gudun kar ta ƙware sannan ta ce, "in ana sallah ba a magana, gwara ma ki je ki roƙi Baaba ta baki" ta faɗi tana dariya mara sauti. daidai lokacin Aisha da su Fatima su ka dawo daga islamiya, zuwa su ka yi suna gaishe da Lantana har aka juyo kan Anty Sadiya. Domin gaba ɗayansu yanzu sun koma kamar yadda Aisha ƙanwarsu ta ke gurin ladabi.

Bayan Sadiya ta kammala cin abincin ta sha ruwa, sannan ta miƙe haɗi da yi wa Baaba sallama sannan ta nufi sashinta.

Ko gama rufe ƙofar sashin Baaba ba ta yi ba ta ji ana ƙwanƙwasa na ta ƙofar, isa wurin ta yi tasa hannu ta buɗe, sai da ta yi baya baya ciki mamakin wanda ta gani, "Nusaiba!" Sadiya ta furta tana kallon Nusaiba da ta kutso kai cikin gidan, fiskarta kamar salaha.

Da ɗingishi kamar gurguwa ta iso gaban Sadiya, kasancewar wancan faɗuwar da su ka yi da Mairo ya yi sanadiyyar dawo mata da ƙafa haka. Nusaiba ta fashe da kuka, ganin ba ta da niyyar dakatawa yasa ta fara ba ta baki akan ta yi shiru me yasa ta ke yin kuka haka?" Sai a sannan Nusaiba ta dakata ta ɗago tana kallon Sadiya ta ce, "don Allah ki yafe min abun da na yi miki Sadiya, na yi nadama wallahi ki yafe min!".

Shiru Sadiya ta kasa cewa komai sai ganinta kawai ta ke yi. Nusaiba da yanzu burinta Sadiya ta yafe mata kawai ta ce, "na sani wallahi, na san cewa abun da na aikata yana da wahalar ace kin yafe min, ni ce wacche ta rabaki da mijinki, sannan na so kasheki, na salwantar miki da ɗanki ɗaya. A yanzu ba abun da ya rage mana a tsakani, tun da Faruq ya sakeni, ni dai kawai abun da na ke roƙonki shine ki yafe min, ki duba ƙafata yanzu na zama nakasashshiya, ƙafata ba zai taɓa dawowa daidai ba, kuma dama hakan ya kamata ya sameni, saboda na cutar da rai, amma ki yafe min".

Ita dai Sadiya ba ta iya cewa da ita ƙala ba, saboda har yanzu cikin rashin yarda ta ke, wannan Nusaiban da ta sani ne? Har ta ke neman yafiya agareta? Kafin ta ankara Nusaiba ta durƙushe tana ƙara fashewa da kuka. Kasancewar Sadiya mace ce mai zuciyar tausayi, hakan yasa ta ɗago Nusaiba tana faɗin, "shikenan... na yafe miki, ki daina kuka Allah ya yafe mana baki ɗaya".

Babban laifin da Nusaiba ta yi sai ga Sadiya ta yafe mata a lokaci guda. Ta ɗago tana share hawayenta sannan ta ce, "nagode Allah ya saka miki da alkhairi" ta faɗi sannan ta fito da wani leda ta ce, "ga wannan Sadiya, na siye shi ne musamman don na kawo miki, na san za ki ji daɗinsa".

Sadiya ba ta karɓa ba sai ƙarewa ledar kallo da ta ke yi, "shikenan, ba laifi Sadiya, don baki amshi abuna ba bai kamatana yi fushi ba, amma ina son san kin yafe min ne har cikin zuciyarki" Ta faɗi da fiskar tausayi, Sadiya ta ce, "me ki ke cewa ne Nusaiba? Idan ba da gaske na yafe miki ba ba zan faɗa ba". "Anty Sadiya me yasa ki ke magana da ita?" Cewar Aisha da ta shigo ta sashin Baaba haɗi da isowa kusa da su.

Cikin haushi da tsana ta fara cewa Nusaiba, "yanzu ke bayan duk abun da ki ka yi har kina da zarrar sake zuwa gidan nan?! Ki fice ba ma buƙatarki anan" hawaye Nusaiba ta cigaba da zubarwa haɗi da sadda kai ƙasa. Ganin haka yasa tausayi sake kama Sadiya, ta dafa Aisha tana cewa, "Aisha, Nusaiba ta yi nadama, kuma Allah na son duk wanda ya yi laifi ya gane kuskurensa".

"Kar ki yarda da ita, wa ya sani ma ko tuban ba na gaskiya ba ne?" Faɗin Aisha, Sadiya ta kuma cewa, "a ah Aisha, duk wanda yasan halin Nusaiba a baya, ya ganta yanzu zai gane tsantsar nadamarta" sannan ta juya ga Nusaiba ta ce, "karki damu, kamar yadda na ce na yafe miki ki je kawai".

Nusaiba ta ji matuƙar daɗin furucin Sadiya, wanda hakan ya ƙara nuna mata lallai Sadiya mutuniyar kirki ce. Kuma godiya ta yi mata sannan ta miƙo mata wannan ledar wanda cake ne a ciki, Sadiya ta amsa sannan Nusaiba ta kuma cewa don Allah ta ci shi ta ji, musamman don ita ta siya. Sadiya ta yi murmushi sannan ta ɗauki guda ɗaya, irin wanda ake yi ƙirar cycle haka cake ɗin ya ke, girmansa kuma daidai. Aisha dai kallon Nusaiba ta ke yi cikin rashin ganin daraja, don tun da ta auri Faruq ba ta yi mata ba tuntuni.

Bayan Sadiya ta ci cake Nusaiba ta juya za ta tafi, fiskarta cike da hawayen da ya ke nuna ta ji daɗin yafiyar da aka yi mata. Yatsunta ta fidda, ta fara irgawa, ɗaya.... seconds kaɗan tsakani ta kuma miƙar da wani, biyu.... sai kuma ta sake miƙar da na uku adaidai isanta ga ƙofa.

"A'uzubillahi!!!!" Ƙarar da Sadiya ta yi da ƙarfi, sanadin hakan Nusaiba ta tsaya cak, ta saki yatsun nan na ta gaba ɗaya biyar ɗin, wani irin fara'ar da ba na jin daɗi kaɗai ba ya bayyana a fiskarta, ta ɗaga idonta da ke kallon ƙasa zuwa sama kaɗan.

Sadiya tun bayan da ta saki salatin ta yi ƙasa haɗi da dafe cikinta, idonta ya fara juyawa kamar ba na ta ba, Aisha kuwa tashin hankali ta shiga tana rirrike Sadiya da kiran sunanta, da sauri ta kai dubanta gun Nusaiba da ta tsaya ba tare da ta juyo ba, Aisha ta ce, "me ki ka sa a cikin cake ɗin nan?! Na yi imani shine ya saka Anty Sadiya haka. Anty Sadiya ki tashi! Baaba! Baaba!!".

Sai a sannan Nusaiba ta juyo tana kai dubanta kan Sadiya da Aisha, idonta ya cika da wani hasken ɗaukar fansa da mugunta, ta sa hannu ta share hawayen da ta yi wanda ba na gaskiya ba ne, sannan ta fara takowa cikin cangala ƙafarta zuwa garesu. A sa'in ita kuma Aisha ta miƙe da gudu don zuwa kiransu Baaba.

Sunkuyowa Nusaiba ta yi kusa da Sadiya da ke kallonta cikin shan wahala, sannan ta saki dariyar mugunta ta ce, "shin kina kallona da kyau Sadiya? Ko gubar ta yi miki tsananin da ki ka kasa ganina?" Wani irin kallon mamaki Sadiya ta ke aikawa Nusaiba, yayin da ta ke yin juyi da nurƙususun ciwo mai tsanani. 

"Kin ruguza min rayuwa! Kin sa na zama nakasashshiya kamar wata almajira mai neman taimako, kece silar da mahaifiyata itama ta rasa ƙafarta guda ɗaya Sadiya! Shine ki ke tunanin ni Nusaiba zan bar ki? Never!! Wannan gubar ba ta kisa ba ce kaɗai, ta lalata duk abin da ke cikin mahaifarki ce!".

Ta faɗi idanuwanta ba sa tare sa tsoro ko kaɗan, sai zaryar rashin imani da ɗaukar fansa. Kallonta Sadiya ke ciga da yi da ƙwayar idonuwanta da ke shirin kullewa.

NURIYYAH.

Cikin rawar baki na ce, "yaya Haidar wannan na cikin hoton fa ba kowa ba ne illa yayana! Shi ɗin fa ɗan uwana ne, iyayenmu ɗaya da shi!" Na faɗi Idona na kan hoton yaron da ba zai wuce shekaru huɗu ba, kuma ba kowa ba ne sai wanda Abba ya sanar da ni shekaru da yawa da su ka gabata, alokacin da ya ke kan gadon jinya kafin ya amsa kiran mahaliccinsa, hoton nan shine wanda Abba ya bani labarin cewa, yayana ne wanda su ka nema su ka rasa!.

Haidar kallonna ya ke yi bakinsa a yanzu ya gaza furta wani harafi, haka Mu'azzam don bai da ta cewa. Alhaji da ya shigo falon ya ji maganar da na yi, ya kasa wucewa ya tsaya zuciyarsa ya bada wani irin bugu sosai, domin kuwa ya lura da yanayin hoton da ke hannuna, saboda shi ne ya kai aka gyara hotona da kansa. Gabansa ya yi mugun faɗi, a cikin zuciyarsa ya ce, "me Nuriyyah ta ke faɗi game da yaron cikin hoton nan? Kamar ya ɗan uwanta? Allah yasa dai abun da mu ka rufe lokaci da yawa ba zai buɗe yanzu ba, saboda fitar da sirrin inda yaron ya ke yanzu.....


Last page
___________________________________________________


Toh fah!!! Nusaiba kamar ta yi nadama ashe da wani shirin ta zo, shin za ta yi nasara akan Sadiya wannan karon? Me zai faruda Sadiya?. Shin su Baaba za su zo su sameta? Ya ma aka yi ƙafar ta ya koma haka duk da mun san abun da yasa hakan? Ya aka yi itama Mairo ta rasa ƙafarta?.

Ga Nuriyyah, ta ga hoton ɗan uwanta fa agidansu Haidar, waye ɗan uwan na ta? Sannan a ina ya ke? Wani sirri ne Alhaji ke tsoron a fitar? Shin akwai abun da ya faru acikin ahalin nan ne?. Wata sabuwa!!!.

Girmamawa ga ɗaukacin masoyana mutanen arziƙi masu bibiyar wannan tafiya tamu.

​Zan yi amfani da wannan dama domin isar da wani taƙaitaccen saƙo na ban-girma. Ina sane da cewa dakatar da wannan labari a wannan gaɓar ba zai yi muku daɗi ba, domin nima ba don lalura ba, ba zan so mu rabu da ku ba. Ina mai ba ku haƙuri ƙwarai da gaske. 🙏🏻

​Ina matuƙar godiya da yadda kuka nuna fahimta ga dalilaina kuka kuma amince da hakan; hakan ya nuna matsayina a wurinku. Allah ya bar ƙauna da amana. Insha Allah, littafin SANADIN ƘADDARATA zai dawo muku da wani sabon salo na musamman, mai cike da nishaɗi da darussa bayan watan Ramadan idan Ubangiji ya kai mu.

​Ina yi muku fatan alkhairi. Allah ya sa mu fara azumi lafiya, mu gudanar da shi cikin sa'a, kuma mu kammala shi cikin gafarar Ubangiji. Allah ya sa mu kasance cikin waɗanda za a 'yanta a wannan wata mai albarka. Ameen🙏🏻🥰





_*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_