Page 5
Sarac Stars R Pen...✍️
*Masu cewa ko tsohon littafi ne da aka yi shi a zamanin baya, to ko ɗaya ba haɗi, wancen daban published book ne da aka yi shi a baya, wannan kuma labari ne sabo da yanzu nake rubuta shi, suna ne kawai yazo ɗaya.*
*Gargaɗi* _Ban yarda a juya mini labari ba ko ayi afmani da wani ɓangare na labarin, ko a ɗaura min shi a wata kafa ta media ba tare da izini na ba, sannan ina gargaɗi ga masu cire sunana a cikin labarina su saka nasu tare da sakinsa a shafinsu, a barmin sunana tare da barin rubutuna a yadda yake, da fatan za a kiyaye_
Hassana sosai ta ƙosa su bar asibiti dan ta samu damar amayarwa mama kuɗin sarkar Nuratu wanda tasan duk a jikin Ƙaninta ta samu, duk wani abu da zasu gani a jikinta ko a jikin 'ya'yanta tofa Mahmood ne yayi wannan wahalar, shiyasa lamarin ke ƙona musu zuciya suka shiga hassada sosai, domin duk cikinsu babu wacce take auren me kuɗi balle ta samu mijinta ya yi mata hidima haka, sannan a ganinsu bai yiwa mahaifiyarsu ba amma ya tare a gindin mace komai na sha'awa sai dai a gani a gunta, wannan yana ɗaya daga cikin dalilin da yasa mama ke son aura masa Malika domin da ita ce za suyi amfani dan fitar da Nuratu a gidan su samu damar cin dukiyar Mahmood da suke ganin Nuratu ce ta kasa ta tsare akansu. Bayan kuma duk hidimarsu in ta taso ko bai da kuɗi sai mama ta sashi dole yayi musu koda kuwa bashi zai ci, anty Hassana kuwa shi ke biyan kuɗin makarantar yaranta saboda mijinta bai da ƙarfi, sannan in hidimar kuɗi ya taso mata akansa take saukewa kuma dole yake yi mata, sannan duk sallah haka zai haɗa yaransu yayi musu kayan sallah wanda mama ta saka masa dole sai yayi musu domin ƙarfafa zumunci, haka dole yake yi mata biyayya domin su rabu lafiya, kuma Nuratu bata taɓa saka masa ido ba ko ta hanashi yayi wa 'yan uwansa hidima, wani lokacin ma in kuɗi ya kakare masa ita ce ke yi masa ciko duk dan a taru a rufawa kai asiri, sai dai a nasu ɓangaren gani suke ta mallake shi ne ta hau kan dukiyarsa tayi kane kane, shiyasa suka zaɓi ya auri Malika dan wannan tasu ce sai yadda suka yi da ita, sannan kuma burinsu su karya kadarin Nuratu a gurin Mahmood, zagon ƙasa suke haɗawa Nuratu dan basu taɓa nuna mata basa sonta ba ko a fuska, in suna tare da ita suyi ta shige mata suna yabonta, hakan yasa Nuratu ta sakankance musu ta kuma yarda da tayi dace da dangin miji.
Jalila data gama waya tazo zata koma cikin ta hangi Mama da Umma sun juya baya daga inda take da alama a lokacin suka tsaya a gurin sai ta isa da sassarfa ta ɓoye a bayan wani fulawa ta tsaya kamar mai jiran wani abu tana danna waya, haka nan ta saka a ranta wannan fitowa da suka yi magana za suyi mai mihimmanci daya sa ba za suyi a cikin ɗakin da Nuratu ke ciki ba. Mama ta kalli Umma cikin rashin jin daɗi a fuska tana cewa.
Ina tausayawa Nuratu halin da take ciki, ciwo dai baya jin magani ana ta fama, shiyasa naga dacewar ta samu mai tayata kula da yara da shi kan shi Mamudan, shi ne muka yanke shawarar haɗashi aure da 'yar uwarsa Malika ɗiyar Ƙanwata Hadiza, kuma duk sun amince har mun tsayar da rana wata guda mai zuwa, to tuntuni maganar take na hana Mamuda ya faɗawa Nuratu saboda halin da take ciki, shiyasa na zaɓi dana fara faɗa miki domin ki taya mu kwantar mata da hankali tare na nuna mata munyi ne ba dan mu muzguna mata ba sai dan ta samu sauƙin hidimar gidanta, kuma ita Malika ashe ta jima tana son Mamuda bamu sani ba sai da na nima haɗin auren ga mamanta shine take faɗa mini, cikin ikon Allah aka yi sa a shima yayi mini biyayya ya amince.
Ta ƙare maganar tana duban umma, wacce zuciyarta ta shiga yi mata zafi da maganganun mama, amma sai ta danne ta aro murmushi tana cewa.
Abu yayi kyau masha Allah kin ga tuwona maina zumunci zai ƙara ƙarfafa, ai Hajiya wannan abu ba wani abun tada hankali bane tunda ita Malika ba baƙuwar Nuratu bace dan an san halin juna, sannan zata samu sauƙin hidimar gidan kamar yadda kika faɗa, dan haka wannan abun farin ciki ne, Allah ya tabbatar da alkhairi ya sa ayi muna raye, kuma in dai nice na haifi Nuratu In Sha Allah ba zaku samu tawaya daga ɓangarenta ba, Allah ya haɗa kansu ya basu zaman lafiya.
Ameen ya rabbi, Ameen Ameen, gaskiya naji daɗin da kika fahimce ni Allah ya bar zumuncinmu.
Ameen Hajiya, sai mu koma ko, ni zan yi shirin tafiya naje gida na huta dan bamu samu barci mai kyau ba.
Hakane ai kin san zaman asibiti ba daɗi sai dole. Allah ya ƙara mata lafiya.
Umma ta amsa da amin wanda a lokacin Jalila tayi ƙoƙarin zamewa ta wuce ciki suma suka rufa mata baya ba tare da sun san tayi musu laɓe ba, jikin Jalila har rawa yake yi saboda taji gulma, Kuma tayi alƙawarin itace zata fara isar da maganar ga Nuratu kafin umma, sosai Maman Mahmood ta bata mamaki da irin son zuciyarta, ace Nuratu tana jinya a asibiti amma tana zancen Mahmood zai ƙara aure saboda bata san zafin taba, ƙiri ƙiri ta nuna bata haifi Nuratu ba babu kara sam. Koda suka shiga ciki Umma ta shirya ta fito dan tun ɗazu driver ke jiranta daya kawo Jalila, tayi sallama da su mama ta kai dubanta ga Nuratu cike da tausayinta tace.
Naratu ki tabbatar da kinci abinci kafin na dawo, ina ga ma ba zan jima ba a gidan zan dawo.
To Nuratu tace tana gyaɗa kai kana Umma ta ƙara yin sallama da mama sai ta fito suka wuce, zuciyarta cike da damuwar halin da Nuratu zata shiga in ta samu labarin auren da Mahmood zai ƙara. Su mama suma basu daɗe ba suka tafi wanda a lokacin ne Jalila ta samu damar magana tana cewa.
Anty Nury.
Na'am autar Umma.
Ta amsa tana tsure ta da kallo nan ta gane da akwai magana a bakinta amma sai Jalila tace tana sosa kai.
In zuba miki abincin.?
Jalila ki faɗi maganar dake bakinki karta kashe ki.
Ta ƙare maganar da ɗan murmushi, Jalila ta saki 'yar dariya.
Kai anty nifa ba komai kawai ki ci abinci, bari na saka miki.
Nafa san halinki kamar yunwar cikina, na tabbatar wani gulma kika guntso to gwara ki fesa mini kafin wani ya shigo bana son nuƙu nuƙu.
Uhum anty kenan, to kici abinci sai na faɗa miki.
Ai dama na san ba a rasa nono a riga, saka mini kaɗan, dama tun ɗazu nayi brush.
Cewar Nuratu da ta tashi zaune ta saka filo a jikin bango ta jingina, Jalila ta saka mata indomie wanda yake fari kwal ba komai a ciki daga maginsa sai mai, sai ta ɗauki robar yaji ta miƙawa Nuratu haɗe da plate ɗin abinci, Nuratu ta saki murmushi.
Yauwa autarmu nasan dama kin san abinda nafi so in ina jinya.
Hmmm cin wannan abincin sai ke, abu fari kwal kamar na masu ciwo.
To dama na mai ciwon ne, ya naga baki yi ta tayi romo sosai ba.
Tayi fa kafin mu zo ne ta soma tsotsewa.
Jalila ta faɗa tana murmushi, nan Nuratu ta fara cin indomie ta zabga yaji tana ci tana karɓan ruwa, haka ta cinye wanda ta saka mata tace Jalila ta ƙara mata domin daɗin da yajin yayi mata ne yasa ta ƙara, bayan kamar minti talatin ta gama ci ta kammala Jalila ta mayar da komai inda yake, Nuratu ta kalle ta tana cewa.
Uhum faɗa mini maganar.
Kai anty baki manta ba.
Taya zan manta bayan kunnena ƙaiƙayi yake yi mini na ƙosa na ji labari.
Ta ƙare maganar da guntun murmushi, Jalila ta gyara zama ta soma karanta masa hirar mama da Umma ba tare da tunani ba ko hangen abinda zai je ya dawo ba. Kan Nuratu ne yayi mummunar sarawa jin wai Malika ce mama zata aurawa Mahmood, wani irin tururin zafi taji yana rugugi a cikin kanta, fuskarta ta haɗe tamau da ɓacin rai idanunta a warwaje cike da azababben mamaki wanda ruwan hawaye ke kwance a ciki, ganin yanayinta ya sauya ya sanya Jalila gimtse sauran maganarta cike da damuwa.
Anty! Anty Nuratu! shiyasa fa kamar ba zan faɗa miki ba dan kar ki shiga damuwa, kuma ga halin da kike ciki, ki rufa mini asiri ki yi haƙuri kuma kar Umma ta san na faɗa miki nasan sai ta haɗani da yaya Hafiz.
Ta ƙare maganar tana tsure Nuratu da ido wacce ta yi shuru kamar ruwa ya cinyeta, da alamar kamar ma bata ji maganar Jalila ba dan ta shiga yin tunani, can ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi sai ta sauko daga gadon dan dama tuni aka cire mata ruwan, ta nufi hanyar bayin dake cikin ɗaki, Jalila ta miƙe tana kallonta hankalin ta a tashe tare da danasanin faɗa mata da tayi, sai yanzu ta gane ta tafka wauta bai kamata ta fara jin maganar a bakinta ba ita da take gadon jinya tana fama da jiki, jin an rufe ƙofar bayi yasa ta dawo daga guntun tunanin data shiga ta isa ƙofar da sauri tana cewa.
Anty wanka za kiyi ne?
Shuru bata bata amsa ba sai jin sassheƙar kukanta da tayi, Nuratu tun tana a tsaye ta soma rusa kuka ƙafafunta suka gaza ɗaukarta ta tsuguna kan guiwarta a cikin bayin ta dafe bango ta buɗe murya ta cigaba da kuka mai cin rai wanda yake fitowa tun daga zuciyarta, hankalin Jalila ya ƙara tashi ta tura ƙofar taji shi a rufe ashe ta saka masa key domin akwai key a jikinsa, ta soma bugawa a hankali tana magiya akan tayi haƙuri ta fito, Nuratu tana jinta amma baƙin cikin dake zuciyarta shi ne take fitarwa da wannan kukan, dan ji tayi shi ne kaɗai zaisa ta samu sauƙin nauyin da zuciyarta tayi mata, Mahmood ya kafa mata mugun tarihi da ba zai taɓa goguwa ba a ranta, ta yarda dashi ta so shi da duka zuciyarta, ta sadaukar da duk wani farin cikinta da jin daɗinta akansa, shi ne duniyar ta haka shima ta ɗauka itace duniyarsa ashe ba haka bane, ashe tayi wa lamarin fahimtar baibai, a tsawan zaman da tayi da shi sai yanzu ne ta fahimci asalin waye Mahmood, ta ɗauka ita ce kaɗai mallakinsa wacce ke mulkan zuciyarsa wanda koda mace zata yi yawo tsirara a gabansa ba zai ɗaga ido ya kalle ta ba balle zuciyarsa ta hasasho masa yin wani abu, irin wannan yarda tayi masa har yasa ta sallama masa duka zuciyarta da komai nata data mallaka, ashe tayi masa bahagon fahimta, kitse take yiwa kallon rogo! ya gama shayar da ita guba wanda dafinsa shine zai riƙa bin lungu da saƙo na jikinta da zai cigaba da azabtar da ruhinta har sai ta bar duniya, sai ta kuma rushe wa da wani sabon kuka, jin bugun ƙofar da Jalila ke tsananta yi yasa ta sausauta murya ta tashi ta isa famfo ta kunna ta soma wanke fuskarta, jin sanyin ruwan ya sa ta soma jin sanyi a zuciyarta, sai ta wanke ƙafa ta miƙe tana ambaton.
Laa'ihala illa anta subhanaka inni kuntu minazzalumin. Muhammadur Rasulullah Sallahu Alaihi Wasallam. Ya Rahman! Ya Rahim! Ya Zaljalalu Wal Ikram, Ya Hayyu Ya Ƙayyum bi Rahmatika astagis aslihli sha'ani kullahu walaa ta kilni ila nafsee ɗarfata ain.
Ta ƙare da sauke gauron numfashi kana ta riƙa jin sauƙin azabar bugun da zuciyarta ke yi, nauyin dake kanta shima ya ragu, sai ta ita ƙofar ta buɗe nan ta yi ido biyu da Jalila wacce taci kuka ta gode Allah idanun ta sunyi jajur, guntun murmushi Nuratu tayi mata sai Jalila ta matsa ta wuce ta koma gado ta kwanta rigingine kana tace a hankali.
Jalila ki kwantar da hankalinki, kukan da na yi ya rage mini zafin halin da nake ciki, sannan nayi Imani da ƙaddara mai kyau ko mara kyau, sannan ban fi ƙarfin zama da kishiya ba domin ƙila hakan yana daga cikin ƙaddarata, kawai dai nayi mamakin wai mama ce da kanta take so Mahmood ya ƙara aure, sai na soma tunanin ko akwai laifin dana taɓa yi mata ne da take niman hukunta ni da haka, a ganina ban gaza mata ba ban kuma gaza da kula da mijina ba, ina ƙoƙarin fita haƙƙinsu kamar yadda ban taɓa ganin ƙiyayyata a idonsu ba, sai kuma mutum tara yake bai cika goma ba wataƙila akwai in da na gaza shiyasa suke son alaƙanta ƙara auren a dalilin ciwon da nake yawan yi.
Ta ƙare maganar cikin rauni, Jalila ta share hawaye cike da tausayin 'yar uwarta tare da shan majina tace a sanyaye.
Shiyasa dangin miji suka yi ƙauri suna saboda irin son zuciya da wasu ke nunawa akan sunfi son nasu, duk da ina yarinya amma nima naga rashin kyautawar mama a wannan maganar, ace kina gadon asibiti kina jinya amma su ta Mahmood ya ƙara aure suke yi, kuma dan rashin kirki har ta iya taran umma da wannan maganar, Haba ana barin halal dan kunya, ai ta san dole abin zai bigi Umma tunda itace ta haifeki kuma kowa yana son nasa. Sannan a rasa wacce za a bashi sai Malika yarinya mara kamun kai da natsuwa.
Ta ƙare maganar tana turo maki cike da takaici, guntun mitumushi Nuratu tayi tama kasa magana, tunanin abinda ta aikatawa Mama take yi ko zata gano inda ta gaza da har ta cancanci ayi mata kishiya da Malika, koda yake biri yayi kama da mutum dan dama aka ce sassomin hauka zubda yau! ba zata mance lokacin baya ba da Malika take yawon zuwa gidanta ziyara ko yin hutu.
Nuratu mace ce mai son mutane shiyasa take haba-haba da dangin Mahmood in sun zo gurinta, duk ranar da Malika ta zo gidan yini tofa Nuratu sakar mata komai take yi tayi abinda ranta ke so, in ko yamma tayi musamman Malika take yin wanka ta caɓa ado kamar yadda taga Nuratu tayi sai tace mata.
Anty kar ki faɗawa yaya na zo, ina son bashi surprise ne.
Nuratu zata ce mata to kana ta cigaba da lamuranta dan a zatonta shirme ne Malika ke yi da yarinya. A lokacin da Mahmood ya dawo Malika zata fito falon da gudunta taje kamar zata rungumeshi sai ta tsaya gabda shi tana cewa.
Surprise! Oyoyo yayanmu, ya siyo mana tsaraba har da naman kaza, Yaaya baka son zuwa gidanmu ka manta dani ko.
Ta ƙare maganar cike da shagwaɓa, shi kuma Mahmood sai ya washe baki yana irin wow.
Yaushe kika zo.?
Fuskarsa cike da farin cikin ganinta, haka zata zauna su sha hira daga bisani in zata tafi sai tace shine zai mayar da ita gida mama a motarsa, suyi-suyi da ita ta kwana sai tace ita a'a haka zata yi Sallama da Nuratu sai su fita tare da Mahmood ya kaita gida, a nan zata cikashi da surutu tana yi masa ƙorafin baya son zuwa Zaria, idan shi baya kewarsu su suna kewarsa tunda baya son zumuncin, Mahmood sai dai yace ta bawa Inna Hadiza haƙuri zai zo, a haka zai sauketa bayan ya cikata da kayan ciye ciye, ya shiga ya gaida mama sai ya dawo gida.
Rahma ce matar MG. [4/29, 5:56 PM] Rahma Kabir: *MIJIN ARO*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.