MIJIN ARO

Page 6

by @rahmakabir13

Sarac Stars R Pen...✍️

Daga Mahmood har Nuratu babu wanda ya taɓa kawo zuwanta da manufa, shiyasa da zai tafi Makka ta zo ta zauna tare da Nuratu, a nan ne fa ta zama tamkar 'yar gida Nuratu ta sakar mata kayanta hatta suturarta wanda ya ɗauki jikin Malika sakawa take yi tayi amfani da takalminta da gyale tasa ta fita, komai take yi tamkar Jalila ƙanwar Nuratu da suke ciki guda, wani lokacin Beena har haushin ta take ji a yadda ta sakewa Malika, Umma ce ke goyon bayanta tace ta so masu sonta tunda suma 'yan uwan Mahmood suna sonta basu taɓa nuna mata wani abu ba to karta sake wani abu ya fara ɓullowa ta ɓangarenta har su fara ganin baƙinta, kuma Malika ai ba zama tazo yi ba da zarar ya dawo zata kama kanta, ire iren wannan maganganun da Umma ke yi mata yasa bata ɗauki komai a ranta ba ta cigaba da hulɗa da su, duk da wani lokacin ƙannensa suna nuna mata cewar Mahmood ne nasu, musamman lokacin haihuwarta na biyu haka suka fito da asalin halinsu suka dinga ɗibar mata kayan kitchen suna tafiya da shi da sunan sun ɗauki rabonsu ai yayansu ne ya siya, hatta tukunya sai da ta nima wasu ta rasa, kayan abinci shima sun ɗiba a cewarsu ai zata samu gara, Nuratu bata taɓa nuna musu bata so ba ko ƙorafi sannan bata taɓa sanar da Mahmood ba domin ta san shi zai tsawatar kuma tana gudun hakan ya zama rikici a tsakaninsu tunda suna zaman lafiya karta jawowa kanta baƙin jini, shiyasa da Malika ta zo ta zauna sai ta zuba mata ido ta sakar mata komai dan tasan na lokaci ne da ta tafi shikenan. Lokacin da Mahmood ya dawo haka Malika ta yi kane kane taƙi tafiya, wankan safe da kwalliya daban haka na yamma daban iyayi dai kala kala, Nuratu da kawo ido ta zuba mata dan har ta fara ƙosawa da ta tafi saboda bata samu tana sakewa da Mahmood wajen gudanar da soyayyarsu, har sai da Mahmood yace ta shirya ya mayar da ita daga nan ya gaishe da mamanta tunda yaga bata ƙaunar makaranta dan lokacin ta gama secondry ne, ya kuma ce dole ta cigaba da karatu in ba aure take so ba ayi mata, ba dan taso ba ta tafi. Lokaci zuwa lokaci inta bushi iska haka take zuwa gidan ta kwana musu biyu ko ta yini. A shekara biyu da ta wuce ne taga ta ja baya da zuwa bata san dalili ba, sai ta bayar da ƙila karatu ne yasha kanta dan tana karatun NCE a nan Zaria kafin ɗaga bisani ta watsar taƙi karatun.

Nuratu ta sauke ajiyar zuciya lokacin da ta dawo daga tunani ta haɗa hankalinta guri guda sai ta tsayar da amsa guda akan dama tuntuni zuwan Malika gidanta da akwai manufa, ƙila suna turo ta ne domin Mahmood ko zai yaba ya sota sai kuma suka fahimci hankalinsa bai kai kanta ba, shiyasa yanzu suka fito da abin ƙiri ƙiri akan sun haɗa su aure ko yana so ko baya so, sai yanzu ne ta kuma fahimtar Malika irin yadda ta dinga nuna wasu abubuwa ta gane son Mahmood take yi, ta sauke gwauron numfashi mai nauyi wanda yasa Jalila tashi daga kujerar da take zaune ta isa gadon tana faɗar.

Anty lafiya? jikin ne?

U-um kira mini likita.

Cewar Nuratu, ba musu Jalila ta fita kiransa, bata daɗe ba sai gashi ta dawo ita da likita ya tsaya a gaban gadon yana duban Nuratu.

Madam ya jikin?

Ya faɗa yana aje injin gwajin BP, ya soma shirin saka mata abin hannu da ake sawa dan gwajin jinin, Nuratu ta dakatar da shi da cewa.

Ba wata matsala ba ce yasa nace a kiraka, naji sauƙi Alhamdulillahi so nake ka bani sallama.

Ya ɗago tare da barin abinda yake shirin yi.

Amma jikinki bai nuna alamun sauƙin da zan sallame ki ba.

Likita ka sallame ni zan iya kula da kaina, ko ka manta kune kuke ƙarfafa mini guiwa akan na riƙa cire damuwa a raina da kuma jurewa lalurar da nake ciki, tun da nace ka sallame ni nasan zan iya kula da kaina.

Gaskiya ne tunda kince haka zan baki sallama amma ki kula da shan magani, bayan kwana biyu kisa maigidanki ya kawo ki a kuma duba jikinki da kuma bp ɗinki, yanzu ma zan gwada na gani.

To tace masa ta daga hannun rigarta zuwa kafaɗa ya saka abin gwajin ya soma aikinsa, bayan ya gama ya ɗago yana cewa.

Bp ɗinki har yanzu bai gama sauka ba yana ɗari da hamsin dan haka ki kula sosai ki daina cin abinci mai gishiri, ki kula da yin barci akan lokaci da kuma rage tunani, In Sha Allah in kika kiyaye jininki zai daina hawa dan har yanzu bamu fara ɗauraki akan maganin hawan jini ba duba da yanzu ne abin ya same ki, a yanzu shawarwarin dana baki dasu zaki yi amfani dan ya sauka.

Nagode likita.

Nuratu ta ambata sai ya yi rubutu akan farar takarda kana ya ɗauki abin gwajin bp ya fita yana cewa ya rubuta musu sallama, Nuratu ta ƙara yi masa godiya kana Jalila ta ce.

Anty da kin bari kin ƙara jin sauƙi.

Sauƙi na Allah ne a gurinsa nake nima, kuma ai ba daina shan magani zanyi ba, zan cigaba da amfani dasu bisa ƙa'idar da likita ya ambata.

Gyaɗa kai Jalila tayi alamar gamsuwa kana ta miƙe tana haɗa kayansu, nan Nuratu tasa ta kira Beena akan an sallame su zasu koma gida ta sanar da umma, bayan ta gama haɗa komai tace.

Na gama amma wannan abinci da su Surayya suka kawo ya za muyi da shi.?

Ki tafi dashi gida su Ashraf zasu ci. Ki kira mini yaya Hafiz yazo ya mayar damu gida in yaso sai ya wuce dake gida.

To tace sai ta kirashi yace gasu nan zuwa sun kamo hanya, Nuratu ta lumshe ido tana addu'a akan Allah ya bata ƙarfin zuciya da dangana, tana jin ma zata iya jure komai tunda Mahmood ma data yarda dashi yaci amanarta dan haka ƙarin aurensa ba zai wani ɗaga mata hankali ba dan zuciyarta zuwa yanzu ya bushe.

******

Gidan mama.

Suna isa suka tadda Mahmood a falo yana jiran dawowarsu, yana ganin sun shigo ya miƙe yana jerawa mama sannu da dawowa, bata amsa ba sai ta ɗage kai ta isa Cushing ta zauna tare da aje mayafinta a gefe, su Hassana suka wuce ciki suka basu guri dan sun gama iza mama akan lamarin, tun a hanya suka bata labarin kuɗin sarkar Nuratu da yadda zata matsawa Mahmood ya auri Malika, sun gama yi mata famfo kuma da hau sosai. Mahmood ya zauna a carpet ya risina kai ƙasa ya soma gaisheta cike da girmamawa, ta amsa a daƙile tare da ambaton sunansa, Mahmood ya ɗago kai yaga fuskarta ba alamar wasa kana ya sunne kai yana amsawa da.

Naam Mama.

Ka ce mini ba kada kuɗin sadakin Malika amma kana da kuɗin da zaka siyawa Nuratu sarƙa mai tsada ko, to ina so yanzu ba sai anjima ba kaje ka ɗauko mini sarƙar gwal ɗinta ni da kaina zan je kasuwa na sayar, sai na cire kuɗin sadakin sauran kuɗin mu ƙarasa akwati.

Gwal kuma Mama?

Eh gwal ɗin da ta saka ranar da suka zo yinin sallah.

Wlh mama bani na siya mata ba nima ganinta nayi dashi tace mini ta siya ne lokacin da aka yi musu wani rabon gadon kuɗin Mahaifinsu daya fito, shine Ummansu tace sai su siya kadara, su Beena suka siya fili itace ta siya gwal da nata kuɗin, kinga kuwa bani da hurumin da zan amsar mata sarka.

Ya faɗa yana kara sunne kai cike da biyayya, Mama ta ƙare masa kallo ta san gaskiya ya faɗa dan tasan halinsa in dai zai gurfana a gabanta to tabbas ba zai faɗi mata abinda ba shine ba, sai ta taɓe baki tana cewa.

Idan sarƙa kuɗin gadonsu ne duk da ni ban yarda ba to motar ta fa.

Wallahi tallahi da kuɗinta ta siya...

Kai dalla miye na rantse rantse ai ciki da gaskiya wuƙa bata huda shi, idan duk jikina kunne na bazan taɓa yarda da wannan maganar naka ba, ko ka kawo mini sarƙa na siyar mu rufawa kanmu asiri ko ka kai motarta a siyar muyi amfani da kuɗin.

Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, wlh babu kuɗina a cikin sarkarta da mota, zan je na nima bashin kuɗi na kawo miki.

Ya faɗa cikin tashin hankali, mama ta ƙara haɗe fuska.

Aiko sai an siyar da ɗaya daga ciki ko naje har gidan naku na nuna mata na fita iko da kai, Mamuda ka bini a hankali wlh in ba haka ba zan saɓa maka fiye da yadda kake tunani.

Kiyi haƙuri mama amma wlh bazan iya sayar da ɗaya daga abinda kika ce ba, ki yafe ni.

Mama da zuciyarta ta kawo wuya ta miƙe ta iso inda yake ta zabga masa mari yayi saurin dafe kuncinsa, mama ta shiga nuna shi da tsaya.

Ka nuna mini kai ɗin mai kunnen ƙashi ne, dan iskan yaro dan kaga ina lallaɓaka duk ka sake mace ta susuta ka ka zama jani talau, banda ina tsaye a kanka da ko gaishe ni ba zaka riƙa zuwa yi ba, daga yanzu na aje duk wani kawaici tsakanina da Nuratu zanyi fito na fito da ita naga ni da ita waye yafi iko da kai, albarkacin iyayenta take ci nake kawar da ido amma....

Ta tsaya da maganar tana girgiza kai tare da yin kwafa sai ta koma ta zauna tana huci, idanun Mahmood suka kawo kwalla yasa hannu ya share yama kasa kwakkwaran motsi balle yayi magana, yana nan a zaune tamkar gunki dan gabaɗaya ya rasa waƙar farawa, itama mama bata ƙara cewa komai ba sai karkaɗa ƙafa da take yi, Hassana ce ta shigo riƙe da kofin ruwa a hannunta ta zauna tana cewa.

Mahmood maganar kuɗin makarantar yarana nake yi maka tuni kasan da an koma makaranta zasu fara magana tunda har yanzu rabi aka biya da term ɗin baya ba'a ciki ba ga wani term ɗin ya zo. Sai kuma maganar kujeru da nace maka nawa sun lalace ina so zanyi sabo, to jiya mama take sanar dani an sayar da gonar gadonsu babanmu ta ɓangaren Mahaifiyarsu da tuntuni 'yan uwanta suka ƙi yarda a siyar, to shine aka ce naka dubu ɗari biyu da ashirin namu kuma ɗari da goma an raba baffa Halilu zai tura a account ɗina, to gaskiya naka kuɗin zan haɗa da nawa na yi sabbin kujeru.

Ta ƙare maganar tana jan fasali da jin me zai faɗa, Mahmood yace cikin rauni.

Babu damuwa ki yi amfani da shi.

Nagode ƙanina Allah ya saka da alkhairi ya nuna mana aurenka da Malika.

Ameen, amma da alama bai amsa auren ba tunda gashi yana yi mini tutsu da zancen sayar da sarƙar Nuratu ko motarta.

Cewar mama fuska a haɗe, Mahmood ya ɗago kai a hankali yace.

Zanyi yadda kike so Mama kiyi haƙuri.

Hmmm mama tace kana daga bisani ta miƙe ta wuce zuwa bedroom ɗinta, sai a lokacin Mahmood ya samu damar shaƙar numfashi mai daɗi yana ƙoƙarin miƙewa kira ya shigo wayarsa ya ciro shi daga aljihu ya duba sai yaga likita ne da sauri ya ɗaga ya shiga fargaban me likita zai ce masa, nan ya sanar dashi ya sallami Nuratu itace ta buƙaci hakan, ya tabbatar masa da jininta ya ɗan sauka dan haka in wata matsala ta taso su garzayo asibiti kuma ya saka mata ido sosai wajen shan magani, sannan yace zai iya zuwa ya biya kuɗin magunguna da aka bata, Mahmood yayi masa godiya kana suka yi sallama ya kashe wayar yana cewa Hassana.

Dan Allah ki ƙara bawa Mama haƙuri zanyi abinda take so.

Hmmm ai kai ne ka fiye gardama kuma kasan halin mama bata son jayayya, kayi ƙoƙari ka yi mata biyayya dan mu rabu da ita lafiya.

In Sha Allah, ni zan tafi ki sanar da ita na wuce.

Babu ruwana kaje ka sameta a ɗaki ka yi mata sallama kasan dai in ka tafi zata yi zaton rashin ɗa'a ne.

Ta ƙare maganar tana miƙewa zuwa gurin tv ta kunna Mahmood sanin abinda ta faɗa haka mama zata ce sai ya miƙe ya je ɗakinta ya yi sallama ya shiga ya sameta kwance a gado da alama waya ta gama yi ya zauna yana cewa.

Mama zan tafi an bawa Nuratu sallama zanje asibitin.

Hmmm Allah ya bata lafiya. Kuma kayi ƙoƙari ka kira Malika a waya ku fara fahimtar juna.

To ki fito lafiya.

Ya ambata yana miƙewa kana ya fita, bai ɓata lokaci ba ya wuce asibiti wanda lokacin har su Umma sun dawo sun fitar da kaya an saka a mota zasu wuce, Mahmood ya ƙaraso da sauri ya ƙara gaishe da Umma ya bawa Hafiz hannu suka gaisa yace cikin kulawa.

Nuratu ya jikin, gida zaki wuce ne ko can gidan umma?

Rabu da ita Baban yara gidanta zata tafi, yanzu Hafizu zai kaimu daga can mu wuce gida.

To madalla bari naga likita.

Cewar Mahmood sai ya wuce ciki su kuma suka shiga mota suka wuce gidan Nuratu. Koda suka isa ba bata lokaci suka juya dan Jalila taso ta zauna mata amma Nuratu tace tabi su Umma Abban Ashraf zai kula da ita dan kar a barsu umma da hidimar yara, jin abinda tace yasa suka barta suka tafi, ita kuma ta wuce ɗakinta sai dai tana tura ƙofa abinda ta gani tsakanin Mahmood da Zuhura ya shiga dawo mata, ambaton Allah ta shiga yi a fili tana koro addu'a tare da dafe gefen zuciyarta, a hankali ta samu natsuwa sai ta wuce toilet ta haɗa ruwan zafi kana ta yi wanka, ko da ta fito taji ƙarfi a jikinta sosai ta saka doguwar rigar material mara nauyi ta shafa mai da turare sai ta isa gado ta cire zani gadon ta ɗauko wani ta saka, sauri sauri ta gyara dan jikinta ba ƙarfi nan da nan taji ta gaji, sai ta hau gadon ta kwanta ta rufe ido, tsayuwar mashin ɗin Mahmood yasa ta buɗe idon ta sauko daga gadon ta fito falo wanda a lokacin shima ya shigo suka yiwa juna kallon kallo, Mahmood ya kasa ɗaga ƙafarsa balle ya ƙarasa shiga ciki.

Rahma ce matar MG. [5/1, 6:22 PM] Rahma Kabir: *MIJIN ARO*

Na

©®Rahma Kabir MrsMG.