Page 8
Sarac Stars R Pen...✍️
Asalin Mahaifinsu Muhammad ɗan Yobe state ne, matarsa ta farko Hajara 'yar uwarsa ce da aka yi musu auren zumunci, ita ce Mahaifiyar Hafiz wanda a wajen haihuwarsa ne Allah yayi mata rasuwa, sai kulawar Hafiz ya dawo gurin Mahaifiyar mamanshi. A lokacin da Hafiz ya shekara ɗaya Muhammad yana Kaduna cikin NDA dan ya samu aikin soja short service har Allah yasa ya kammala ya fito a officer, bayan an kammala bikin passing out ɗinsu ne ya tsaya a Kaduna yayi siyayyar kayan sawa domin komawa Taraba inda aka yi posting ɗinsa, a hanya cikin napep ya haɗu da Halima lokacin tana karatunta na midwifery dake asibitin Yusuf ɗan Tsoho, tunda ya ɗaura idonsa akanta yaji ta kwanta masa duba da ya ga tana yi masa kama da marigayiya Hajara matarsa, shiyasa bai yi ƙasa a guiwa ba ya bita har gidansu dake Badarawa kuriga road. Tun daga wannan lokacin soyayya ya ƙullu mai ƙarfi, da yake Umma tana matakin farko ne a karatunta shiyasa sai da aka ɗauki shekara huɗu kafin suka yi aure bayan ta kammala makarantar, a lokacin Hafiz yana da shekara biyar sannan Abba yana Lagos an mayar da shi can. Bayan shekara ɗaya da rabbi da aurensu Halima ta haifi Nuratu wacce taci sunan yayar Abba da ta riƙe shi domin tun yana ƙarami iyayensa suka rasu shine ƙarami a gidansu yana da manyan yayyi, namiji ɗaya Aliyu sai mata biyu Nuratu da Amina sannan shi da yake auta, Nuratu ita ce yayarsa ta biyu saboda irin riƙon data yi mishi tamkar Mahaifiyarsu yasa shi sanya sunanta ga 'yarsa, a zuwan mutanen Yobe sunan Nuratu nan Lagos, sai Hafiz ya maƙalewa Umma saboda yaga sabuwar baby, wanda hakan ya sa da suka tashi tafiya suka barwa Umma shi, ita kuma ta riƙe shi da amana kamar ɗan cikinta, dan in ba ta faɗa ba babu wanda zai ce ba ita ce ta haifi Hafiz ba, Shima da farko ya ɗauka itace ta haifeshi sai daga baya ne suka sanar dashi dan ya riƙa yiwa mahaifiyarsa addu'a saboda dacewa da Rahmar Allah. Shekarun Nuratu uku Umma ta haifi Mubeena lokacin sun koma Adamawa da zama, wanda ba daɗewa aka mayar da Abba Enugu, a can aka haifi Jalila, bayan wasu shekaru ne aka dawo da shi nan Kaduna bisa dalilin yana son ya yi wani course na shekara ɗaya a nan, da yake yana riƙe da babban mukami shiyasa suke zaune a cikin jerin gidaje filat masu kyau wanda suke zaune su kaɗai. Kasantuwar Abba shi mutum ne da yake burin yaransa su samu ilimin addini mai kyau shiyasa ya sama musu makarantar Hudallahil Islam dake tsakanin Badarawa da SMC Unguwar dosa, lokacin Hafiz yana sacondary a JS 3 Nuratu tana primary 4 a makarantar dake cikin bariki, Beena Kuma tana primary 1, Jalila an sakata a nursery, a lokacin Umma tana ɗauke da cikin Munir. A nan makarantar islamiyya Nuratu ta haɗu da Zuhura ajinsu ɗaya kuma aka yi sa'a wajen zamansu ɗaya, a hankali suka fara sabawa da juna tare da wata Kulsum, Amma da yake Zuhura ta fi baki tuni ta shigewa Nuratu har suka yi mugun sabo sosai.
A wata rana Abba ya je Abuja yin wani aiki sai da ya kwana biyu acan kafin ya kamo hanya, yana gabda shigowa Kaduna yayi hatsari da motarta wanda ya samu matsala a ƙafarsa na hagu yayi dogon jinya daga bisani sai dai aka yanke masa ƙafar sanadin yana da ciwon sugar bai sani ba sai da wannan hatsari ya auku, saboda tashin hankalin da suka samu kansu a ciki Umma ta soma naƙudar cikinta ɗan wata takwas da kwanaki, ganin za a iya rasa ta ne aka yi mata aiki aka ciro yaro namiji wanda da kyar likitoci suka ceto rayuwarsa bayan an saka shi a incubator. Sai da suka yi wata suna jinya daga bisani aka sallame su suka dawo gida, basu yi taron suna ba aka sanya masa sunan Mahaifin Abba wato Muhammad Munir.
Bayan wani lokaci Abba ya aje aikinsa, sai ya siya musu gida anan SMC mai kyau suka bar cikin bariki, Umma kuma ta nima aiki bata sha wuya ba ta samu anan secondary health care dake kawo da yake Abba yana da hanya, haka ta soma aiki ta cikin nasara, Abba ya sauya wa yaran makarantar boko suka cigaba da zuwa islamiyan Hudallah, ashe kusa da gidansu Zuhura suka dawo saboda daga gidansu Nuratu sai wani fili da ake noman rani a ciki sannan sai gidansu Zuhura, a dalilin yawan zuwa da Zuhura keyi gidan yasa Nuratu ta sake da ita har hakan yasa iyayensu suka saba da juna, dan baban Zuhura har ƙofar gida yake samun Abba in ya fita shan iska su zauna su yi hira, Umma kuma da mama suka zama kawaye dan in zata je aiki gidansu Zuhura take kai Munir wajen mama ya zauna a gunta har sai ta dawo.
Lokacin da Nuratu ta gama primary Abba ya saka ta a Dilet Barrack wacce ake kira day kawo, saboda yana daraja makarantun gwamnati dan a wancan lokacin ana karatu sosai, shiyasa itama Zuhura tace nan zata shiga dan mate ɗin Nuratu ce sai dai ta bawa Zuhura shekara guda, haka suka taso tare ya zamana hatta kayan sallah iyayensu iri guda suke yi musu kamar 'yan biyu saboda shaƙuwarsu, Nuratu sai ta kwana a gidansu Zuhura haka itama take kwana, in ba an faɗa ba babu mai cewa Abba da Baba ba dangin juna bane.
Bayan kammala secondary ɗinsu sai Nuratu ta fara Business ɗin siyar da turaren wuta da Humra, wanda a dalilin wannan sana'ar ne wasu ke kira ta da Nuratu Ƙamshi, sosai take kama kuɗi shiyasa taƙi mayar da hankali wajen niman makarantar gaba da secondary, wanda a lokacin yaya Hafiz ya kusa gama karatunsa da yake yi a ABU Zaria yana karanta Business Administration.
Wata rana Nuratu ta shiga kasuwar Central market yin siyayyan kayan Humra da kuma kwalabe, saboda zata aika kaya Abuja da wasu family ɗinsu suka ce ta haɗa musu turaruka na Amare biyu, har ta gama siyayyarta ta ɗaurawa ɗan dako ta zo wucewa ta ƙofar wani ƙaton shago da ake sayar da kayan kitchen da robobi, sai ta hango wata farar roba mai murfi babba sai ta tsaya tana sallama a bakin shagon dake kan babban titi, Mahmood dake ciki ya fito ya tsaya yana amsa sallamar, nan ta tambayi kuɗin robar sai ya sanar da ita dubu biyu da ɗari biyar, Nuratu ta waro ido waje alamun yayi mata tsada, Mahmood ya tabbatar mata da sabon design ne shiyasa kuɗinsa yake a haka amma ta bada dubu biyu da ɗari uku, Nuratu tace ita kam ya mata tsada dama robar ya burgeta ne ta siyawa Umma dake sana'ar dambun nama sai ta riƙa zubawa a ciki, ta nisa tana cewa.
Nima Umma zan siya mawa da take sana'ar dambun nama ka bar mini dubu biyu mana saboda na gama kashe kuɗin a siyayyata. In Sha Allah naga guri zan dinga zuwa Ina tsintar kayan kitchen.
Mahmood yayi murmushi bai yi magana ba ya juya cikin shagon da nufin ya ɗauko leda, ita kuma Nuratu ganin kamar ba siyar mata zai yi ba sai ta cewa ɗan dako su wuce, lokacin da Mahmmod ya dawo ya hangeta sun wuce ya rasa ya zai yi ya kira ta sai ya aika yaron shagonsa da robar yace ya je ya kai mata, ba musu yaron ya bisu da gudu ya cimmusu ya miƙa mata robar tare da bayanin ogansa ne yace ya bata, Nuratu ta juyo ta hangi Mahmood wanda shima su yake kallo fuskarsa cike da murmushi, sai kawai ta juya ta koma shagon bata amsa robar ba, koda suka isa Mahmood ya rigata da cewa.
Nima na bada gudunmawa a cikin sana'ar Umma, ki kai mata kice wani ɗanta yana gaisheta.
Murmushi tayi ta nuna ba zata amsa ba, yace ci saboda Allah ya bata Kuma shaiɗan shike mayar da hannunta kyauta baya, jin haka yasa ta yi masa godiya ta amsa suka wuce cike da mamakin Mahmood tare da yaba kirkinsa a cikin zuciyarta. Har ta tari mashin zata hau sai ta amsa kayanta a hannunta ɗan dako ta ciro biro da takarda ta miƙa masa akan ya je ya amso mata number ɗin mai kayan kitchen yace masa Umma zata kira ne tayi masa godiya, ba musu ya je ya amso shima yace ya bashi nata a wata paper ba musu ta rubuta ta bawa ɗan dako tare da kuɗin aikinsa sai tahau mashin da kayanta suka wuce.
Wannan dalilin ne yasa soyayya ta ƙullu a tsakanin Muhmood da Nuratu, wanda sekara guda suka ɗauka aka ɗaura musu aure lokacin Nuratu tana da shekara sha tara, ta tare a family house ɗinsu Mahmood dake kawo, ta zauna asalin sashin da mama ta bari tun da dama yana rufe tun bayan barinsu gidan, lokacin babansu ya gina sabon gidansa a rafi guza suka tare.
A lokacin Kuma Zuhura ta samu makarantar kiwon lafiya dake garin Makarfi zata karanta Environmental health. Zuhura su shida ne a gidansu, yayarsu Salima tana aure a unguwar rimi yaranta uku, sannan Haisam shi kuma yana gama secondary ya faɗa harkar kasuwanci bai samu yin karatu mai zurfi ba amma kuma ya san kan juya kuɗi tun yana ƙaramin sa, sai Zuhura ke bi masa sannan ƙannenta maza biyu sai autar su mace.
Yaya Hafiz kuma ya kammala degree ɗinsa ya tafi Service a Maiduguri. Nuratu bayan haihuwarta na farko yaronta mai sunan Mansur ɗaya ci sunan Mahaifin Mahmmod da suke kiransa da Anwar, a lokacin ne ta samu gurbin karatun NCE dake nan cikin makarantar SMC tana karanta English.
***
Abbansu Nuratu ya rasu lokacin tana da cikin Yasmeen, sakamon ciwon sugar ɗinsa daya tashi daga ƙarshe rai yayi halinsa, wanda shine sanadin barin umma SMC ta koma gidan iyayenta dake Badarawa sakamakon fama da hawan jini da ta yi sanadin rasuwar Abba, sai dai duk da sun bar gidan amma zumuncinsu yana nan da iyayen Zuhura, dan bayan dawowar Hafiz daga Yobe ya haɗo kan dukiyar Abbansu ya siya musu gida can cikin unguwar dosa a 'yan majalisa duk saboda su samu hankalin umma ya kwanta ta dawo kamar da, shiyasa ma suka saka ta aje aikinta ta dawo gida tana sana'ar turaren wuta da Nuratu ta bar mata. Sauran kuɗin kuma aka raba musu gado, Hafiz ya soma juya nashi kuɗin yana ɗauko kaya daga ƙasar Dubai ya buɗe katon shago anan cikin gari kasuwa yana sayar da atamfofi, leshi da kayan yara da takalma. Bayan Nuratu ta kammala diploma taso yin aiki amma Mahmmod ya hanata yace sai dai in zata yi business ba zai hanata ba, wannan yasa ta yiwa Yaya Hafiz magana ya bata kaya sari da kuɗin gadonta dake ajiye a asusun banki, ta soma business anan cikin gidanta kuma cikin ikon Allah Allah ya saka mata albarka, kuma a lokacin ne Mahmood ya siya musu gidan da suke ciki a yanzu, ba jimawa kuma ya tafi Makka ya sauke farali, wanda duk a lokacin aka yi bikin Beena ta auri wani lecturer dake Zaria itama ta ɗaura karatun Biology anan ABU.
Zuhura itama akayi bikinta da wani Alhaji Taju yana da mata biyu itace ta uku, sai dai gidanta daban kuma da ita yake yawo kasashe dan yana mugun sonta, haihuwarta biyu dashi duka mata ta farko Aisha da suke kira Mimi sannan Murjana wacce take da sickler, Alhaji Taju ya rasu Zuhura tana ɗauke da ƙaramin ciki sai dai ruɗanin da ta shiga na rasuwar yasa ta yi ɓari, bayan an raba musu gado ta soma business da kuɗin tana kashe su duk yadda taso, ba jimawa komai ya ƙare ta dawo zero, Mimi tana hannunta inda Murjana take hannun yayar Mijinta wanda shekara biyu da rasuwar Babanta ita ma ta rasu dalilin ciwonta daya tashi. Zuhura ba ƙaramin shiga damuwa tayi ba ga babu komai a hannunta ba aiki kuma babansu shima yayi retire dan malamin makarantar primary ne, abubuwa sun ja baya sai Haisam ne ke riƙe da gidan shima abubuwa sunyi masa yawa dan ya yi aure da matarsa guda, shiyasa Zuhura ta fara fafutukar niman aiki sai dai da kyar ta samu aikin a asibitin primary health care dake rafin guza ɓangaren masu bada kati, shima saida Ummansu Nuratu ta samu hanya kafin Zuhura ta samu aiki, haka ta soma zuwa tana amsar albashi mai kauri ba laifi, tun daga lokacin kuma ta soma buga rayuwa tana kula samari wanda da yawa ba aure ke kawo su ba sai dan su watse, tun Zuhura tana ki har tazo ta saki jiki tana kama kuɗi a hannun samarin, a hankali ta zama taxi no garej, sai dai tana yin komai cikin hikima dan babu wanda ya ankara da tayi nisa da lalacewa, saboda Zuhura irin matan nan ne da suke da kamewa ba zaka taɓa cewa zata aikata ba, duk da ana yi mata maganar aure a gida amma taƙi nuna ma zata yi dan bata yarda samarin suna zuwa gidansu ba.
Bayan wani lokaci matar Haisam ta rasu a wajen haihuwa, shima ya dawo ba mata yaronsu ɗaya Sanusi da suke kiransa Abba dan sunan mahifinsu ya saka, raɗaɗin mutuwar matarsa ya sashi niman sojan ruwa wanda yana samu ya tafi, yana passing out aka tura shi Ibadan sai dai ya ke yiwa iyayensa aike, wanda a wani zuwa ne da yi yaje gidan ummansu Nuratu dan ya gaisheta sai ya ga Jalila ta girma sosai, shine ya fara kamun aurenta tun tana ƙi har ta yarda dashi suka fara soyayya, daga baya iyaye suka tsayar da maganar auresu akan saita kammala karatunta da take yi a KASU wanda take 300 level.
***
Gidan Nuratu.
Sun gida rayuwar aurensu ne bisa soyayya da tausayin juna, duk da arzikin Mahmood yaja baya ya daina kawo kayan kitchen ya tsaya a iya siyar da robobi, amma hakan bai kawo tasgaro ga zaman lafiyarsu ba duk da Nuratu keyin wasu ɗawainiyar gidan, ko haihuwarta na huɗu ma itace ta yiwa kanta kayan fita suna hatta ragon suna sai da tayi masa ciko, tun daga lokacin kuma kusan cefane itace keyi shi yana kula da biyan kuɗin makarantar yara da siyawa su Mama abinci, ga kuma nauyin da mama ta ɗaura masa na biyawa yaran Hassana kuɗin makaranta, shiyasa Nuratu take haɗa hannu da shi wajen cefanen gida, tasha siyan kayan abinci, kayan tea da sauran kayan masarufi, hatta kayan sallah daga ita har yara tasha ɗinka musu, shima ganin tana yi sai ya sakar mata wasu abubuwan shi yana ji da hidimar su mama, Dan nauyin da mama ta ke ɗaura masa yana ɗaya daga cikin abinda ya karya jarin Mahmood, Nuratu bata taɓa fallasa wannan sirrin ba illa takan yi wani hirar da Umma wacce ita kuma ke ƙarfafa mata guiwa akan haka, har take nuna mata itama bayan Abbansu ya aje aikinsa itace ta cigaba da kula da gidan lokacin da ta fara aiki, dan haka ta cigaba da yi lada take samu domin sun riga sun zama ɗaya da mijinta, kuma duk taimakon da tayi masa bata faɗi ba, wannan yasa Nuratu bata taɓa jin damuwa ba dan tana hidimar gidanta.
Rahma ce matar MG. [5/3, 5:03 PM] Rahma Kabir: *MIJIN ARO*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.