Page 13
Sarac Stars R Pen...✍️
Umma taɓe baki tayi tana cewa.
Gwara ki tunatar daku dan yaran yanzu mugun son jikinku shi ke kaiku ya baro ga baƙar ƙazanta, da anyi magana ace yara sunyi yawa, to kun san ba zaku kula dasu ba zaku saki jiki kuta haihuwa, yaran nan dai kiwo aka bamu kuma ko wanne sai Allah ya tambayemu kiwon daya bamu, Kuma iyaye nagari ne sune silar samuwar 'ya'yana nagari, sannan ku sani kafin Allah ya tambayemu haƙƙin 'ya'ya to sai ya fara tambayar haƙƙin Miji.
Hakane Umma Shiyasa a kullun muke alfahari daku tare da yi muku addu'a da fatan gamawa lafiya da samun aljanna maɗaukakiya, Allah ya jiƙan Abbanmu.
Cewar Nuratu sannan duk suka amsa ta amin kana ta ɗaura maganarta ga Zulfa.
Kinga kina dawowa daga makaranta ki zauna ki huta na 'yan mintuna ki rama sallah in baki samu yi ba acan, sannan ki shiga kitchen ki ɗaura sanwa sai ki fito kiga me zaki gyara a gidan, wataƙila ya bar miki kayan breakfast a inda ya karya ya barsu, dan maza akwai mulki sai ki kwashe ki kai kitchen kiyi wanke wanke kina yi kina duba abincinki, ba dole sai kin tsaya kyale kyale ba kiyi girki mai kyau mai daɗi tunda yasan kina zuwa makaranta ba zai damu da wani kyale kyalen abinci ba shi dai kawai yaci yaji yayi daɗi, kina gamawa kiyi wanka ki shirya, da ya shigo yaji gida na ƙamshin turare gauraye dana abinci wanda zaisa yaji farin ciki da tunanin kin gama girki. Dan Allah in kina yin haka taya zaki samu matsala da yaya Hafiz? wata rana da ka shi zai ce kar kiyi girkin ki huta.
Nuratu ta ƙare maganar tana tsure ta da ido, Zulta ta saki murmushi tana sunne kai ganin umma a gurin saita kasa magana, Umma tace.
Ki yi maganarki domin ni ba ruwana da kunyar nan dan itace ke cutar ku yaran yanzu, abu yana damunku amma kuna zurfin ciki, gadai shi nan kinji Nuratu tana tuna miki dan mazanku na zamanin nan kin gyara ma ya aka ƙare balle kinyi wasarairai da shi.
Umma ga Beena nan kusa dake tana ji itama zanyi lokacinta anjima dan akwai tamu da ita.
Cewar Nuratu tana murmushi, Beena kuwa haɗe fuska tayi tana wani basarwa dan sarai ta gane inda maganar Nuratu ya dosa, Zulfa ta turawa Nuratu text da cewa.
Anty har fa da matsalar buƙatarsa da yake yawan yi mini, wlh wani lokacin a gajiye nake sai yazo ya takura mini.
Nuratu ta ɗan saki murmushi kana tace a bayyane.
Zulfa kin taɓa faɗa masa damuwarki?
Sai ta girgiza mata kai, Nuratu ta ƙara yin murmushi.
To kamata yayi ki zauna da shi ki sanar da shi damuwarki wataƙila ba zai fahimci halin da kike ciki ba har sai kin bayyana masa, a zaman aure yana da kyau a riƙa fitar da magana ana tattauna shi ta hakane za a riƙa ɗinke ko wani ɓaraka inta ɓullo.
Girgiza mata kai Zulfa tayi alamar gamsuwa tana cewa ta gode, Nuratu sai ta tura mata saƙon text da cewar.
Akwai lokutan da zai iya kusantarki ba lallai sai dare ba, kamar bayan sallar asubahi da ake kira kafi shayi amma fa sai kin kasance mai tsafta, sai da rana a cikin weekend ki bashi lokacinki tunda bakya zuwa makaranta, ga kuma tsakiyar dare bayan kinyi barci kin farka, sai ki wanko baki ki shafa turare a inda ya dace ki dawo ki lalubi mijinki, in har a matse yake zai kula ki, in kuma barci ya cika masa ido sai a barwa asubahi.
Zulfa da ta karanta murmushi tayi tana sunne kai Nuratu ta saki dariya, saboda Zulfa ƙaramar yarinya ce bata wuce tsarar Jalila ba. Umma ce ta katse hirar Jalila da Beena tana cewa.
Nuratu yana ganki da akwati in ce dai lafiya.?
Umma ta ƙare maganar a ɗan cikin damuwa da tsoron kar dai taji labarin auren da Mahmood zai yi ne har tayi yaji. A sannan ne damuwa ya sauka fuskar Nuratu kana ta shaida wa Umma, Mahmood ya sanar da ita zai ƙara aure da kuma labarin mama tace ya kai mata sakar gwal ɗinta ko motar ta a siyar, wani ashar Beena tayi tana cigaba da cewa.
Uban kuturu yayi kaɗan wato da kuɗinki ne zai ƙara auren, wannan ai rainin hankali ne, ai dama tunda mama ta iya mutstsuke ido ta sanar da umma ƙarin auren nan kina kwance a gadon asibiti nace sun tanadi rashin daraja, to idan da kuɗin ubansu a sarƙar da motarki sai su zo zu amsa 'yan iska marasa mutunci ai...
Dalla dakata mini shashasha, wannan tayar da jijiyoyin wiyar fa? sai ƙunduma zagi kike yi kamar wata bamagujiya, wai Mubeena ina kika bar hankalinki ne? gabaɗaya ke auren mara hankali ya mayar dake duk kin sauya daga tarbiyyarmu, to idan ba zaki faɗi alkhairi ba karna sake jin baki ki anan. Ke kuma shine kika haɗo kaya kika zo mini yaji ko me? Ya ina yi muku kallon kun mallaki hankalinku ashe ba haka bane, idan zuwa kika yi ki zauna to babu gurin zama a gidan nan ki ɗauki kayanki ki koma gidanki har yaranki dasu zaki tafi, ƙarin aure ba akanki aka fara ba kuma ba kanki zata zauna ba ya ƙaro uku to se me? Ko wacce halinta ne zai zaunar da ita...
Ummaaa!
Nuratu ta faɗa cikin katse mata magana cike da rauni, wanda hakan yasa umma tayi shuru tana kallonta, Nuratu ta ɗaura da cewa.
Ni ba dawowa gida nayi ba na kawo muku ajiyar atamfofina ne da sarƙoƙina a aje mini dan ina gudun Mahmood ya faki idona ya kwashesu, dan kinsan yana mugun tsoron mamansu zai iya yin komai gudun ɓacin ranta.
Ta ƙare maganar a gajiye tana mayar da hawayan daya kawo mata ido, Umma ta nisa.
Nuratu kiyi haƙuri Allah yana sane dake kuma shine zaiyi miki maganin komai, idan har zaki yi haƙuri ki kawar da ido wlh wata rana kowa sai ya kasance a ƙarƙashinki, ban zaci zai iya sanar dake auren ba duba da mamansu ta bani saƙo, to tunda ya rigani isar miki ni haƙuri zan baki kuma kinyi kyan kai da kika kwaso kayanki dan a wannan gaɓar yadda idon mamanshi ya rufe wlh zata iya saka shi ya aikata komai. Ke Jalila ɗauki akwatin ki kai ɗakina zan zo na adana mata har ƙurar ya lafa sannan motarki ma ki aje ta anan gida gudun rikici.
To umma, amma da naso komawa da motar saboda sauƙin zirga zirga in ya so zan riƙa adana makullin yadda ba zai gani ba.
Haka yayi Allah ya tabbatar da abinda yake alkhairi ya ɗauraki akan duk wani sharri ya ƙara miki juriya da haƙuri, yanzu ne zaki fara zaman aure da duk wasan yara kika yi, saboda ƙalubalen dake cikin zama da kishiya abu ne mai yawa gashi kuma 'yar uwarsa ce, to lallai sai kin zama mai takatsantsan da kawar da kai akan komai.
In Sha Allah Umma.
Cewar Nuratu wanda yayi daidai da miƙewar Beena ta nufi ɗakinsu da take sauka kamar kububuwa cike da tsananin ɓacin rai, ji take yi kamar zata kama da wuta saboda zafin da take ji yana hawa mata kai, ita fa a yadda take ji da ta zauna da kishiya gwara mijin ya mutu ko su rabu, sosai take jin zafin kishiyar da za a yiwa yayarta hakan ne yasa ta ɗauki wayarta ta kira Mahmood, koda ya ɗaga wayar bata amsa sallamarsa ba ta shiga zazzaga masa maganganu masu zafi ta ƙara da cewa.
Idan ka gaji da ɗawainiyar ciwonta sai ka saketa, mu bamu gaji da ita ba kuma Allah ba zai hana mu kuɗin kula da ita ba, sannan kaje ka gayawa mamanku babu gadonku a cikin sarƙar Nuratu da Motarta baku isa kuce da dukiyarta zaka ƙara aure ba sannan...
Bata ƙarasa maganarta ba Nuratu ta fizge wayar wanda shigowarta kenan, tace cikin tsawa.
Me kike yi haka Mubeena? Mijin nawa kike yiwa cin mutunci haka, ke za a yiwa kishiyar ko ni? to ni na amince ya ƙaro aure akan mijina ya zama mazinaci, bani da lafiyar da zan ɗauke nauyinsa, bazan so kaina ba na danne gaskiya, daya zama MIJIN ARO ga matan banza a waje gwara yazama mijin aro ga Sunnar Ma'aikin s.a.w, nasan ko ba komai suna ƙarƙashin inuwar aure ne.
Ta ƙare maganar cikin kuka da rauni wanda duk Mahmood yana jin su sai a sannan ne ya kashe kiran yana mai sauke numfashi akai akai, idan yace bai zuciya da maganganun Beena ba yayi ƙarya amma jin maganar Nuratu ya saka masa rauni da damuwa, ya tabbatar tana son shi kuma ba zata fallasa sirrinsa ba, ji yake kamar ya fashe da kuka na tausayin Nuratu, itace suka yiwa laifi amma itace ke ƙarfin halin danne damuwar ta akan nashi farin cikin, shi ko da wani irin abu ya dace ya sakamata dan wlh ta cancanci duk wani kyautatawa dan farin cikinta, guntun hawaye ne daya sauka gefen idonsa yayi sauri ya goge yana mai jin kamar ya fasa auren amma ba yi da yadda zai yi domin yin auren shine zai kawo masa sauƙi a tsakaninsa da mama.
Beena itama kukan ta fashe da shi ta zauna gefen gado Nuratu kuma tana tsaye tana share hawaye, Umma, Zulfa da Jalila suma sun shigo ɗakin sun tsaya domin hayaniyar Nuratu da suka ji shine yasa suka shigo, ganin su suna kuka yasa suma suka tsaya zuciyarsu a karye, ko umma dauriya take yi dan ƙarfafa zuciyar Nuratu amma matuƙa tana tausaya mata musamman lalurar da yake damunta, ga kuma ƙarin damuwa da zama da kishiya kuma ga dukkan alamu maman Mahmood ba zata muna kara ba dan sai ta fi son Malika fiye da Nuratu, matsowa tayi ta shiga rarrashin Nuratu da maganganu masu kwantar da hankali, Nuratu ta share hawaye tana mai jan majina.
Wallahi Umma nayi imani da ƙaddara mai kyau ko mara kyau, Umma rashin lafiyata ya shafi zamantakewarmu domin bana iya sauke haƙƙin Mahmood shiyasa na goyi bayan auren ɗari bisa ɗari dan daya koma yana mu'amala da matan banza gwara na ƙarfafa masa guwa yayi aure domin ni da shi duk mu kuɓuta a gurin Allah, wannan kukan ma da kuka gani, ina yinsa ne domin samun rangwame daga nauyin kishi da zuciyata ke ciki, babban rauni na a duniyar nan shine son Mahmood ina jin kishinsa tamkar na kashe kaina, amma inna tuna kwanciyar kabari da hisabi sai naji rauni kuma naji komai na duniyar ma ya fice mini a rai, ina tsoron haƙƙi ina tsoron ranar da dukiya ko 'ya'ya basu da amfani face sai ayyukan alkhairin dana gudanar a duniyar shine zai cece ni, umma wlh na yarda Mahmood ya ƙara mata uku a kaina in har hakan zai kawo masa maslaha akan matsalarsa.
Allah ya rabaki da zafin kishi Nuratu Allah ya shiga lamarinki yayi miki albarka.
Umma ta ambata cikin kuka tare da jawo ta jikinta ta rungume tana bubbuga bayanta, wanda maganganun Nuratu sune suka karya zuciyar Beena ta shiga zubda hawayen damuwa. Bayan 'yan mintuna Jalila data gaji da lamarin dan itama har kwalla ta saki sai kawai ta soma waƙar.
_So kenan Sanadin labarina, so kenan Sanadin labarina, bayin kaina ne ba kaima bayin kanka ba tsarin Allah ba mai iya kauda shi, bawai matsayi ne ba sannan ba girma ne ba halitta ne ba mai iya canja shi, bai barni ba kaima bai barka ba a zuciya shine kesa rauni, soo..._
Kinci gidanku Jalila.
Cewar umma data katseta tana yi mata daƙuwa, sai Jalila ta kwashe da dariya tana cewa.
To haka kurin an dafa mana jiki da damuwa ai gwara mu kore shi mu yi farin ciki, duk sharrin so ne fa yaja aketa wannan koke koken.
Zulfa ce ta kaiwa bakin ta duka sai ta goce ta fice daga ɗakin tana dariya, itama Zulta tabi bayanta, umma ma haka aka bar Nuratu da Beena, a lokacin ne Nuratu ta yi mana nasiha akan ta shirya ta koma gidanta bai dace ta bar mijinta ba har na tsayin kwanaki, da farko taso ta tubure amma da ta ce mata zata kira Baffa Sunusi ta faɗa masa sai ta ce ba sai ta kai kararta ba zata tafi amma sai gobe In Allah ya kaimu, to a haka suka bar maganar suka fito falo aka cigaba da hira har tsayin lokaci. Koda Nuratu ta shirya zata tafi tare da yaranta ta wuce, Anwar shine babba mai sunan Mahaifin Mahmood wato Mansur shekararsa sha biyu, sai Yasmeen wacce taci sunan Ummansu Halima shekararta goma, sannan Naufal mai sunan Mamansu Mahmood wato Naja'atu 'yar shekara bakwai, sai mai sunan Baban Nuratu Muhammad suna kiransa da Ashraf dan shekara huɗu. Haka suka shiga mota da kayansu suka koma gida.
*****
Mahmood.
Da damuwa fal cikinsa yayi yinin ranar, haka jiki ba kwari ya nufi gidan mamansu dake rafin guza, ya tadda Hassana tazo amma su Surayya da Labiba basa nan, bayan ya gaisa da Hassana sai take ce masa.
Wlh babansu kasan tunda ya tafi kudu bai dawo ba shine nayi zamana anan har ya dawo, dan can gidan namu babu abinci.
To Allah ya dawo dashi lafiya.
Mahmood yace, da kamar zai ce mata a cikin kuɗin gadonsu data ce an tura mata meyasa bata siya abinci ba amma sai ya rabu da ita dan kar ya ɗauko magana, suna zaune sai ga mama ta fito falon riƙe da mayafi da jaka kamar fita ma zata yi da sauri Mahmood jiki yana rawa ya isa gareta ya amsa jakar cikin risinawa, ta bashi kana ta zauna a cushing ya aje mata jakar a gefenta ya samu kan carpet ya zauna a ƙasa ya shiga gaisheta kai a sunkuye cike da tsantsar biyayya dan ko ido baya yarda suna haɗawa da mama, ta amsa cike da ƙasaita kana ta ɗaura da cewa.
Ya jikin Nuratu in ce dai taji sauki.?
Eh Alhamdulillahi ta samu lafiya.
To Madalla ya batun sarƙar, ka kawo ne?
Umm umm ban kawo ba dan bansan in da ta ajiye ba.
To hakan kaga yafi maka ko, ke Hassai bamu guri.
Mama ta ƙare maganar da Hassana dan duk in zata yi magana da Mahmood bata cika so suna zaune a gurin ba tafi so daga ita sai shi, yadda koda yayi mata wargi ta ƙare masa tanadi ba mai goyon bayansa balle a bata haƙuri, Hassana tana fita tace.
Ehen ina jinka ya batun motar?
Mama na zo miki da wata magana ne tare da niman alfarma, a gaskiya a yanzu ba ni da kuɗin auren Malika kasantuwar ita budurwa ce tana buƙatar ayi mata komai na gata kamar yadda ake yi a al'ada, to akwai wata Bazawara da tuntuni muka fara daidaitawa dama na bari bayan sallah ne na tayar da maganar aurenta sai kuma kika rigani da zancen Malika, dan Allah mama ki bari na auri wancan dan na yi mata Alƙawari kuma karna zo bancika mata ba ta ganni a mutumin banza, kuma kinga aurenta babu tsada daga sadaki shikenan ko akwati tace ta yafe sai dai na ɗinka mata na fitar biki kawai, ba kashe kuɗi sosai.
Ya ƙare maganar yana jan fasali dan jin me zata ce, Mama sai da ta ɗauki kusan minti biyar bata ce komai ba har sai da Mahmood ya ɗago kai suka haɗa ido wanda yayi saurin mayar da kansa ƙasa, Mama ta ƙanƙance ido tana cewa.
To ban amince ba, bamu san me ya raba auren bazawarar ba da kake son aurowa kanka ƙamu ƙamu.
Wlh mama mijinta rasuwa yayi kuma tana da tarbiyya da kamun kai, dan Allah mama ki amince mini kamar yadda nake ƙoƙarin faranta miki, ki duba girman sirrinki dana haƙa rami na rufe wanda har gobe bana tsammani wani zai jishi, kuma..
Wani irin daka masa tsawa da mama tayi tana miƙewa tsaye, shi ya saka shi miƙewa da mugun sauri yayi baya jikinsa babu inda baya rawa saboda tsantsar tsoranta.
Rahma Kabir ce matar MG. [5/10, 6:42 PM] Rahma Kabir: *MIJIN ARO*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.