Page 15
Sarac Stars R Pen...✍️
Nuratu ganin yaranta suma sun shiga damuwa a dalilin matsalarsu, basa walwala ga rashin cin abinci yadda ya kamata, hakan yasa ta dage wajen faɗawa Allah duk da tana cikin jini amma da yake na ciwo ne tana da damar yin ibadarta domin ya wuce adadin kwanakin hailarta da malamai suka yi magana akai, hakan yasa ta soma tashi sallar dare, tare da yin doguwar addu'a bayan sallar asubahi, sannan sallar walha baya wuta, ta dage da addu'a akan Allah ya sassauta mata halin da take ciki musamman akan zafin kishin Mahmood wanda shine ya hanata saƙat, da addu'ar Allah ya rage mata son Mahmood ya shirya mata yaranta ya haɗa su da alkhairin dake tattare da Zuhura ya kuma kare su daga sharrinta. Ita kanta tasan bai kamata ta bari matsalarsu da Mahmood ya shafi yaranta ba, dan wasu matan hantarar yaran suke yi da wofantar da lamarinsu duk dan za a yi musu kishiya saboda su baƙanta ran mijin, ansan kishi da zafi amma bai dace ta hukunta yaranta akan laifin da babu ruwansu ba. A dalilin babansu ta hana kanta sukuni yara sun daina ganin dariyarta, bata hira dasu balle yin wasa gashi har yanzu basu koma makaranta ba, gidan ya zama kamar ana zaman makoki.
Anya nayi muku adalci kuwa? Taya zan wofantar da farin cikinku akan matsalata.
Nuratu tayi maganar a cikin ranta tana mai jin hawaye yana sake zubo mata, bai kamata tayi wautar wasu matan ba wanda suke aikata abu cikin jahilci da son zuciya suna zaginsu a gaban ubansu ko su hanasu abinci suƙi yin girki dan su ƙuntata wa Mahaifinsu, tabbas wannan hanya ce na zubar da duk wata ɓarɓashin mutuncinta da ƙima, koda kuwa ace shi ɗin ya cutar da ita ne ko ya zalunce ta ai 'ya'yanta ba su da laifi, kamata yayi ta riƙa kauda haushinsa ko ɓacin ransa a gaban yaran dan ba tarbiyya bane tana zagin ubansu a gabansu ko nuna rashin mutunci wa ubansu a gaban su. A daure ayi abinda hankali zai ɗauka, dan kar nan gaba azo ana danasani domin uwa ita ce makarantar farko, duk abinda kike aikatawa lallai koyi ne ga 'ya'yanki.
Babban tashin hankali ne ki zauna da yaranki kina zagin babansu kina aibata shi dan akan wani laifi da ya yi miki. Wai shin ke ba kya ɓata masa ne? Wata ƙila ma sakacinki ne zai sa ya ƙara auren. Kina nunawa yaranki su daina ganin ƙimarsa ne da kuma rushe duk wata daraja na uba da Allah ya bashi a idon yaran. Amma ki sani idan har kin kasance haka gaba kece zaki yi kuka.
Nuratu ta nisa tana mai ƙara zurfafa nazarinta ga dogon tunanin da ta shafe lokaci tana yi wanda ta gano zallar wautar da take shirin aikatawa, duk da tana ƙoƙarin yin dauriya amma wani irin sabon son Mahmood ne yake taso mata yana kai komo daga ƙirjinta zuwa zuciyarta, duk yadda zata iya bayyana yadda take ji ba wanda zai gane halin da take ciki sai macen da ta samu kanta a irin matsalarta ko kuma wacce mijinta zai ƙara aure bayan tsayin lokacin da suka kwashe a tare amma lokaci guda wata zata zo ta raɓi inuwar da take sha, babu wanda yasan wahalar data sha har zuwa yanzu a cikin gidanta, da daɗi ba daɗi zafi da sanyi har na zuwa shekarun da ta kwashe da Mahmood, shiyasa take jin zafin wata zata same shi a kyauta bayan tarin ƙalubalen da ta fuskanta har kawo ya zama mutum, har yanzu bata iya jure hana zugar hawayenta ba domin hakan yana sama mata rangwame da zafin da take ji a cikin ranta, dan umma a koda yaushe in ta kira a waya cewa take yi.
Nuratu idan kuka ya zo miki kiyi shi karki riƙa danne shi kina yin dauriyar dole, sai dai zan baki shawara in za kiyi ki kasance ke kaɗai ko kuma a gaban mijinki ta yadda zai lallasheki hakan zaisa kina samun rangame daga ƙullin daya tokare miki maƙoshi, saboda danne kukan ba zai taɓa kawo miki sauƙi ba face hauhawan ƙullin baƙin ciki da asa-asan da zai iya sanya wa jininki ya hau, amma kukan ka iya sawa ki samu gaggwaɓar salama. Ba jarumta bane dan za ayi miki kishiya ana cewa ki ɗaure kiyi kamar bai dameki ba (pretending) wlh wahalar da zuciyarki kawai zaki yi, gwara ki fitar da kishin naki da zafin da kike ji amma ta sigar kuka bata sigar hauka ba, in kinyi haka wannan shine jarumtar.
Ire iren wannan maganganun kesa Nuratu bata rabuwa da yin waya da Umma dan bayaninta suna ƙara kwantar mata da hankali da ƙara juriya saboda rarrashin da take yi mata, ta yarda abokin kuka shi ake faɗawa mutuwa! Dan Umma ita kaɗai ce ta zame mata ƙawarta kuma abokiyar shawararta, saboda tasan ba zata taɓa ɗaurata akan kuskure ba duba da yadda take ƙara mata ƙarfin guiwa da tunatar da ita miƙa lamarinta ga Allah. Shiyasa ma ta daina waya da Beena da sauran wasu daga cikin 'yan uwansu da suka samu labari, to babu amfani yin magana da waɗanda ba zasu tallafa mata ba wajen karɓan ƙaddararta ba, wasu matan da dama a irin wannan gaɓar suke barin duk wata damarsu a gurin miji, saboda zugan ƙawaye ko 'yan uwa ko ma wata uwar da kanta, domin idonsu ya rufe kawai suna nuna mata ita ce kawai mutum, su riƙa zugata suna ɗaurata akan keken ɓera wanda in ya kwaɓe mata babu wanda zai agaza mata face kowa zamewa zai yi ya nuna ba ruwansa, shiyasa a wannan gaɓar sai mace tayi karatun tanutsu tasan su waye ke gewaye da ita kafin ta zauna tana tattauna matsalarta, idan kin san ba shawarar ƙawar zasu baki ba karma ki furta damuwarki gwara ki raba dare kina faɗawa Ubangiji sarkin da baya gyangyaɗi, shine zai yi miki maganin komai har ki samu yardarsa ya baki mafita mai kyau. Ki daina tunanin dan zai ƙara aure mijinki ya daina sonki ne, a'a kina nan a matsayinki sai dai kuma a yadda kika tarbi maganar auren shine zai ƙara miki matsayi da jin kunyarki da nauyinki a zuciyarsa. Mijinki yana sonki dan babu yadda za ayi ku shafe shekaru a tare sannan dan zai auro wata yaji baya sonki, duk kuwa da rashin kyautata masa da bakya yi wlh yana sonki ne ya jure zama dake har kuka kawo yanzu. A wannan gaɓar ke ce zaki cigaba da yin wasu ayyuka da zaki ƙara kusanci a zuciyarsa ya ƙara jin ke tashi ce, ya ƙara sanin darajarki da ƙimarki tun kafin zuwan amaryar, kin kashe duk wata hanya da zaki samu naƙasu koda tazo tana a bayanki. Ki kyautata ibadar ki, kiyi Addu'a wa kanki akan Allah ya ƙara masa soyayyarki a zuciyarsa. Domin ance so so ne amma son kai yafi. Tsaftar jiki, gida, da ko ina tare da riƙe ƙamshi. Sai kula da abincinsa, ki mayar da hankali wajen koyan girkin zamani dana gargajiya, kina sarrafa hatsi yadda ya kamata wanda ko da amarya tazo da nata salon to tabbas yasan kema dai ba baya ba. Kyautata kwanciyar aure, idan har mijinki ba irin mai gujewa mace bane in zai ƙara aure, to sai riƙe wuta kina bashi farin ciki kina yi masa salo salo na kwanciya ta yadda zaki bar masa wani fresh tunaninki a lokacin da baya tare dake. Koda amarya tazo tofa kin riga kin iya allonki. Idan kuma mijinki yaja baya dake karki damu domin kin samu damar gyara kanki ne sosai, ta yadda duk lokacin da ya dawo hannunki zaki rikitashi da wani irin amon daɗin da zai fara lissafin amaryar ce ko uwargidan. Sannan idan amarya ta zo to ke kuma kina da damar gyara jikinki kina shan abubuwan da zasu inganta n'imarki tare da kuzarinki, da kuma zama kina tunanin irin tarbar daya dace kiyi masa a duk sadda ya dawo hannunku, sannan fa kiyi ta addu'a akan Allah ya ɗauraki akansa da soyayyarki, dama ita amaryar kanta.
Nuratu tasan tabbas Mahmood yana mugun sonta kamar yadda itama take sonsa, shiyasa tun farko tayi masa uzuri akan abinda ya faru ta ɗauki laifin ta ɗaurewa kanta dalilin matsalar ya samu ne daga lalurarta, shiyasa ta dage sai ya auri Zuhura domin bata fata a sanadinta mijinta ya fara aikata zina, a kullun addu'arta su faɗi tare su tsira tare, gwara ta aje duk wani son zuciyarta ta bashi goyon baya domin su rabauta a tare, kawai ta gujewa auren Malika ne gudun kar su mama su matsawa rayuwarta a dalilin Malikar, ta kuma yarda ya auri Zuhura ne duba da yadda ta fara karantar sauyawa daga halinta, domin ta ƙara gogewa tana haɗuwa da samari kala kala wanda a ƙaramin tunanin Nuratu har take ganin Zuhura ta fara cuɗanya da maza shiyasa ma harta iya yarda ta bawa Mahmood kanta, saboda ta ɗinke wannan ɓarakar yasa ta dage sai ya aureta. Sai ta nisa tana mai jin kwarin guiwa akan In Sha Allah ba zata taɓa yin Nadama ba a bisa wannan kyakkyawar hukunta data yanke musu, domin alkhairi ta ƙulla kuma tabbas Allah yana tare da ita, sai ta saki guntun murmushi ta miƙe daga daddumar da ta gabatar da sallar walha tana mai jin kwarin guiwa a zuciyarta, kana ta ninke ta aje shi ta cire hijab ta fito falo tana kwalawa Yasmeen kira, da sauri duka yaran suka fito daga ɗakinsu Anwar, duk suka zuba mata ido cikin rashin walwala suna jiran me zata ce musu, buɗe musu hannu tayi alamar su je, da sauri dukansu suka ruga wanda Ashraf ya riga su ya rungumeta sai duk ta haɗa yaran ta rugume tana mai sauke ajiyar zuciya tare da Hamdala ga Allah daya dawo da hankalinta jikinta ya kuma sanya mata dangana a zuciyarta, har wani sanyi ne ta ji yana ratsa zuciyarta, sai ta sake su tana dubansa fuska cike da yalwataccen murmushi.
'Ya'yana alfaharina yau wani abinci zan girka mana mai daɗi.?
Mami kiyi mana birabisko da miyar ganye.
Cewar Anwar yana dariya, Ashraf yace tayi musu tuwo Naufal kuma tace shinkafa da miya, Yasmin ce daga ƙarshe tace.
Mami kiyi mana waina ko sinasir, kin san favorite ɗin abbanmu ne tare da juice ɗin kwakwa da abarba.
A'a kunun aya za kiyi mana mai daɗi kisa madara.
Cewar Ashraf. Nuratu ta saki murmushi wanda haƙoranta sai da suka bayyana.
Yasmin kin ci gari domin abinda Abba yake so shi zamu yi, kai kuma Ashraf za muyi kunun aya saboda duka muna so, mu tafa.
Sai ta miƙe musu hannu ɗaya bayan ɗaya suna tafawa, kana tace Ashraf da Naufal su zauna a falo suyi kallo ita da su Anwar zasu yi girkin. Da yake tana da sauran ƙullun waina tun lokacin bikin sallah da ta niƙa ta aje abinda a freezer, kuma baiyi komai ba sai ta saka masa yeast da baking powder sai ta saka a rana dan ya tashi, da ta gama haɗin kullun sai ta ɗauko kan ragonsu na layya da basu ci ba ta wanke ta haɗa farfesun kai mai mugun daɗi da ƙamshi kana ta zuba arish a ciki ta yanka su manya manya wato ta raba ko wani ɗaya gida biyu, wanda ya ƙarawa farfesun ɗanɗano ya saka shi ya ɗanyi kauri kaɗan, baya ta gama suka haɗa kunun aya da yake blender ɗinta yana niƙa komai, zuwa la'asar sun gama komai hatta suyan sinasir ɗin, suka gyara gida suka sakawa gidan turare mai ƙamshi ko wani lungu da ƙusurwa yasan tabbas mai gidan ta dawo duty ɗinta, sai suka yi wanka suka caba ado suka fito cikin shirin fita, Nuratu shadda ta saka Brown daya sha stone work ta saka mayafi cream color kana ta ɗauki jaka da takalmi baki sai ta ƙara feshe jikinta da turare mara ƙarfi sai suka fito ta rufe ƙofar falo suka shiga mota zuwa kasuwa shagon Mahmood dan kai masa ziyarar bazata.
****
Mahmood.
Tun safe Zaliha take damunsa akan yazo su tsara maganar aurensu yadda zai kasance, ana maganar saura kwanaki amma bai taɓa zuwa sunyi zance ba, duk da ya tabbatar mata da shi fa ba zai yi wani taron bidi'a ba kuma baya so yayi abinda zai ɓata ran Nuratu dan haka ɗaurin aure kawai ya isa, sai tayi nata taron a gidansu sai washe gari za a kawo ta gidansa, Zuhura ta nuna bata gamsu ba shi kuma yace to sai dai a fasa kawai dan ba zai yi abinda zai taɓa zuciyar Nuratu ba saboda lallaɓata yake yi, taji mugun haushin maganarsa amma sai ta daure tace ta amince ayi yadda yake so, sai yace mata zancen inda zata zauna zai kama mata haya sef contain wato ciki da falo haɗe da bayi da kitchen, nan fa Zuhura ta yi tsalle tace ita sai dai ya haɗata gida ɗaya da Nuratu, ita bata ga aibun haka ba tunda gidansa ne kuma akwai ɗakuna a wadace, yace to sai yayi shawara da mama duk abinda tace shi zai yi. Daga haka suka koma maganar kayan lefe dan mama tace kyalle ba zata bashi ba cikin wanda ta tara da sunan Malika, shiyasa ya ce zai haɗa mata iya abinda zai iya, Zuhura tace sai dai ya bata kuɗi ta haɗa da kanta, ya tabbatar mata da bayi da kuɗi tayi haƙuri da abinda zai bata. Can zuwa rana yana shago bayan ya sallami customers sai ya tura mata dubu hamsin akan ta siya atamfa kala biyu da gyale ɗaya da ɗan kunne da sarƙa, sannan yace zai tura mata na takalmi da jaka dubu ashirin ta siya set ɗaya da warin extra takalmi guda ɗaya, tana ganin bayaninsa da shaidar kuɗin daya tura mata a WhatsApp ta ƙunduma wani ashar tana cewa ba zai saɓu ba, nan ta nunawa Salame itama ta shiga mita tana Allah waɗai tare da cewar.
Ai wannan ko Bazawara tsohuwar ƙauye ba za ayi mata irin wannan kaya ba mai cike da kƙaskanci. Ai wlh arziki yayi! Da kin amincewa Fahad da ba wannan zancen ake yi ba, me akayi da talauci banda tarin takaici, kinga ai tun yanzu ya nuna miki ba kida wata daraja, ace mace kamarki zankaɗeɗiya son kowa ƙin wanda ya rasa itace za a yiwa kayan lefe haka, ina ce mijinki na farko mai kuɗi ne kin saba da arziki gashi zaki koma gidan ƙamas.
Ta ƙare maganar tana jan dogon tsaki.
Ai wlh bai isa ba taya ina ganin matarsa tana da shagon kaya ai ko anan yasan ƙudin manyan atamfofi, rqaina mini hankali kawai zaiyi, to in yasan wata bai san wata ba har shagonsa zanje na tirke shi tunda shagon ba baƙona bane, dole a sauya lissafi dan ba zai cuceni ba a banza.
Ai muna barin nan ki shirya kawai kije ki same shi ayi yacce za a yi.
Cewar Salame cikin takaici, haka ta cigaba da zugata har zuwa lokacin barinsu gurin aiki, wajen ƙarfe biyu da rabi Zuhura ta wuce kasuwa wajen Mahmood.
_To jams'a ga Zuhura ta tafi shagon Mahmood ko zasu haɗu da Nuratu da yara da suka kama hanyar shagon yanzu.? Ya lamarin zai karƙe ne?_
Zaku iya fara biyan kuɗinku na cigaban wannan littafin MIJIN ARO zango na biyu domin saura pages ƙadan mu gama zango na ɗaya mu tsunduma a zango na biyu wanda sai kun biya kuɗinsa kafin zaku samu cigaban wannan labarin ɗoɗar har zuwa ƙarshensa In Sha Allah. ₦700 ne kuɗin, dan Allah ku mara mini baya, domin kunsan akwai tarin darussa dana tanadar muku cikin wannan hikayar.
Pay ₦700 to 9034940106 RAMATU KABIR MONIEPOINT. Sai a tura shaidar biya a WhatsApp ta number nan ***.
Rahma Kabir ce Matar MG. [5/12, 8:44 PM] Rahma Kabir: *MIJIN ARO*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.