Wasan Sarƙaƙiya

Chapter 19

by @aryaahriyad

Wasan sarƙaƙiya.

By Aryaah Riyad..

Book one 1…

       Chapter 19…

Stars talented writers……



Mayarda kallonta tayi ka daddy batareda ta kalli kuyangar ba, a hankali muryanta nadan rawa tace “ No daddy ban ganiba gaskiya, sanda na shiga tariga ta fita daga palourn”. 



Wani kallo da kuyangar tayi mata saida taji kanta ya sara. Irin kallon da tamakasa gane wani irin kallo ne take binta dashi. Idanunta sun kada sunyi ja ta bude baki muryanta na rawa wani kukan bakin ciki na fita tundaga makwogwaronta tace “ Princess Yazrin kiji tsoron Allah, ki fada musu gaskiya hukuntani za’ayi dan bani da shaida, gaskiya duk inda take zata fito kuma….”. 



Katseta daddy yayi dacewa “ Ke mekike nufi? Sokike ki kirata makaryaciya kokuwa? Tashi ki wuce maganar ta wuce. Amma idanhar nakarajin wani abu kamar haka daga gurinki dole ki ansa hukunci mai tsanani”. 



Jiki a sanyaye ta tashi tabar palourn kanta a kasa. Yazrin da takasa motsi tunani kawai takeyi irin cutuwar da yarinyar zata shiga saboda karyar datayi. Nadama tafarayi inama kawai ta fadi gaskiya. Wata zuciyan na fada mata ai yanzuma bata baci bah, saidai chan kasan ranta tasan bazata iyaba. Tunda dai bai lalatata ba ai babu komai, itama kuyangar ai bazataso mutun kamar Ridwan ya aureta ba, dan haka idan abubuwa suka daidaita komi yayi yanda yakamata zata je tabata hakuri sannan tabata kudade masu yawa dazaisa tamanta.



Dan sauke ajiyan zuciya tayi sannan ta mike ta fice daga dakin tanajin idanunsu a kanta. Daddy ne ya kira sunanta saidai tayi kamar batajiba, dan ji takeyi ta tsaneshi yanzu bata tabajin irin haka a akansu bah saidai yanzu jitake bamatason ko hada guri dasu.



Kara sauri tayi sannan ta koma dakinta ta ajiye wayarta tareda shiga toilet tay wanka sharp sharp ta fito ta shirya cikin blue alkyabba mara kyalli sosai sannan ta dauki bag da flat shoes tasaka ta dauki waya dakuma book din tasa a bag ta fita.



Parking lot taje ta danna ma bodyguard dinta kira ya fito ya bude mata mota suka fita. Wasu motoci ne guda biyu black jeeps suke binsu a baya tunda suka fito. Tunani tafara toh waye ke binsu, saikuma ta tuna da cewa ai daddy dole zai kara mata security saboda abunda ya faru. 



Message ne ya shigo wayarta da kamar bazata duba bah saikuma ta dauko. Daga Library ne tana gani tasan waye tunda shi kadai keda numbernta. An rubuta “ Yazrin nanda kwana uku ki dawo da book dinnan. Ki kawoshi da sassafe karfe 10 za’a ansa indai har bakison asan kin dauka”. 



Tashin hankali. Kara karanta message din tayi bakomai ya tashi hankalinta ba sai ganin wai kwana uku gareta. Kwana uku kadai takedashi tareda littafin. Tasan indai takai littafin koda kwana biyu yayi mutanenda masarauta zata dauka domin suyi aiki akanshi bata tsanmanin zasuyi kwanaki sunayi, dan so ake sosai Amrah tazama princess da kowa a duniya zaisan yes taci sunanta dakuma title dinta. 



Kasa typing tayi tamai reply kawai ta kashe wayar ta ajiye a gefe. Rufe idanunta tayi tana jinginar da kanta jikin kujera tareda fuzar da nunfashi. Jitake kanta na wani kullewa kamar ana daureshi da igiya. 



A haka suka isa school dinsu usual inda yake ajiyeta ya tsaya. Bude idanunta dasukayi nauyi tayi jin motar ta tsaya. Dan tabe baki tayi tunawa batace mishi library zai kaita banan ba. Kamar batason magana tace “ A library zan sauka, digital art library ba ba main library bah”. Da ok bodyguard din ya amsa mata sannan yatashi motar yanufi library din, har a lokacin wayannan motocin na binsu dayasa ta gasgata yes daddy ne yasa su.



library ne mai girman gaske hawa hudu, library of digital art. Shine magi girman library a makarantar banda Main library dasuke dashi. Sauka tayi bayan sun karaso ta dauki bag dinta tana bin gurin da kallo ganin babu wasu students dayawa tana jin dadin hakan dan abundayasa tazo nan din kenan. Babu students sosai dake zuwa, infact inba dasafe bane toh ba lallai kaga mutun sunfi goma a ciki ba.



A bakin entrance door din ta tsaya sannan ta ciro student ID dinta tayi swiping kofar ta bude ta shiga. Cikin yafi wajen rashin mutane ga art collections nan ta ko ina. Babu books sosai sai computers da screens and displays kawai a tako ina. Dan runtse ido tai tanajin hasken screens din da displays na shiga mata ido. Its so radiant and colorful, itakuma bawai tanason bright colors bane.



Chan ciki ta shiga ta wani door study room ne babu kowa a ciki sai tables da chairs dake a jere a jere da juna. 



Na chan lungu ta nufa ta zauna tana kai idanunta kan cameras din saida ta saiti yanda bayanta na kallon cameras din yanda koda na cikin control room din naganinta da abunda takeyi bazai iya ganin wani littafi take anfani dashi ba.



Ciro book kin tayi tana murza gefe da gefen goshinta jin kanta na sara mata. Babu abunda take tunawa sai wai kwana uku gareta. Yanzu batama yi pages 10 a cikin littafin dakeida wajen 70 pages. 



Ganin tunane tunanin kara dagula mata lissafi yakeyi yasa kawai ta bude book din inda ta tsaya tafara bi. Kwata kwata puzzle din baya mata kan gado. Tama rasa ina ya dosa. Sai tayi kamar tagane saikuma taga abu a gaba dazai rusa na bayan gabadaya. Wani note book ta ciro tafara rubuta a ciki abunda tasamu a cikin book din saita rubuta. Ga desktop dake libraryn akan table din shima ta kunna shi tana research akai.



Sosai ta dukufa tana solving wajen 3hours amma still bata samu komai dazatace gashi takamaimai answern ba, question dinma bata gama ganeshi ba wato littafin anyishi ne yanda duk kwazonka dauk kaifin kwakwalwarka sai an wahalar dakai zaka gane. Wasa da kwakwalwa akeyi saika ga kamar kagano inda littafin ya dosa saika kara gaba zaka gane bakasan komai ba, sarkakiya ce aka nadeta cikin littafin da warware daya baya nufin cewa zaka iya warware nagabanshi, sannan idan ka warware guda daya shima hakan baya nufin zai baka wata kafa dazaka yi anfani da ita wajen warware nagabanshi.



Wani Gumi ke keto mata dukda sanyin AC dake tashi. Mayafin datasa ya warware ya sauko har zuwa kafadunta. Scarf data daura ya jike gabadaya da gumi shima yayi baya saboda tsansin gashin kanta. Hannunta datake typing ne yafara rawa gashi yayi wasu tabo tabo kamar an daketa a gurin yayi wani pink pink purple purple. 



Dan tsayawa tayi tana kallon hannun nata datakejinshi kamar ba’a jikinta ba dan dakyar take motsa shi. Sai a lokacin idonta yakai kan window taga waje yayi duhu sosai alaman magrib tawuce. Mamaki ne ya kamata kenan tayi fiyeda hour 4 anan? Duba time tayi taga har 8 tayi. Da sauri ta mike tana mayarda book din cikin bag tareda goge dik wani abu datayi searching a desktop din sannan ta dauki wayarta ta nufi waje tanajin zuciyanta na harbawa dum dum. Yanzu mezatace tazauna tanayi a school har dare haka?.



Gashi bata samu tayi wani abun arziki ba a cikin awannin data kwashe babu wani abu dazatace tasamu dazai mata anfani. Tunani take anya zata iya kuwa? Lokaci yayi kadan koda wata aka bata dakyar zata iya samu tayi shima bawai tanada tabbacin zata samu answern daidai bane, amma kwana uku fah, no ta furta tana tariyo abunda yafaru dazu. Ina dole ta nemi mafita, bazata taba bari ace Ta auri Ridwan ba. Dole tayi solving littafin nan komene ne a cikinsa kuwa. 



Dukda tasa labarin kanzan kurege take fadawa kanta amma tasan dole tayi hakan. Idan tabari tafara tunanin mezaije ya dawo bazata iya samu tayi abunda yakamata bah. Takawa tafarayi saidai jitake kamar an daura mata dutse dake janta baya. Dakyar take daga kafanta ga hannunta dake rike da bag yana yunkurin sakin bag din dan jitayi yamata wani nauyi gashi takasa sa karfi ta damki bag din. 



Qatar….





A bangaren Alina kuwa burki taja a tsakiyan titi tareda parking a gaban wata mota da kiris suyi karo dawani mai Bike.



Ajiyan zuciya ta sauke tana kara sako karanta message din tagani kodai bata karanta daidai bane, saidai no daidai ta karanta. Kara duba caller id din tayi still dai unknown number ne koba’a fada mataba tasan waye. Message ne aka rubuto mata kamar haka cikin yaren turanci. “ My Reina fuego, idan ban fada miki ada ba bari nafada miki yanzu, am an extremely jealous man, bana son woman dina tana tarayya da maza har yakai kiui shiga specially for wani kato. Idan har kinason zamanshi lafiya a duniya karda kikara koda wasa ne kisake zuwa inda yake da niyya irin nayau a zuciyarki. If you need anything ganinan ki tambayeni zanyi miki abunda bai isa yayi miki shi ba, kome kikeso ki tambayeni duk girmanshi kuwa, idan yau kinaso nasa a saki Abbinki a daure Hussain sannan a mayar mishi da kujerarshi ku koma gida just say the word”. 



Bata tsaya tunanin wani abu ba kawai ta danna mishi reply “Au haba? Kace zaka iyayin komai mezai hana ka fadamun waye kai? As for abubuwa na babu wanda ya isa yace mun ga abunda zanyi ko ga abunda bazanyi ba, dan haka kaida jealousy dinka kuje kusasanta. Babu wanda zai juyani”. Ta danna send tana huci. 



Wai har ita yau wani zai fada mata maganganu haka. Toh ina ruwanta da wani kishi? Abun ma dabata san waye ba. Saidai abunda ya daure mata kai shine ya akayi yasan menene dalilinta nazuwa chan din? Koda bibiyarta yakeyi bai kamata yasan wayannan details dinba. Besides bayau tasanshi ba yadade yana turo mata sako saidai baitaba turo mata sako kamar haka ba. Bai taba nuna wai ga manufarshi akanta ba. Saidai yaturo mata birthday wishes da gifts, dakuma idan taci wani gasa ko irin haka dai yana turo mata da congrats. Saidai kota mishi reply dan tambayar waye shi baya mata reply. Yanzun ma batasa ran yayi mata reply ba saidai tasan zaiga reply dinta. , hakan ma ya isar.



Unexpectedly taga reply dinshi ya shigo an rubuta “ Suit yourself, also idan time yayi zakisan waye ni, ayanzu bakya bana bukatar kisan waye ni”. Jitayi kamar tay ihu ganin reply din. Wato ma lallai ya raina mata hankali bakadan ba. Yarasa abunda zai ce mata sai ita tasani? Matsalarta nema wato ko tanaso kobataso. Lallai baisan dawa yakeyi bah. Ko waye keson sanin waye shi din ma oho. 

( niko nace ai kekika tambaya ba wani bah).



Sosai take huci tawai wurga wayar gidan baya ta tada motar ta fige ta tanajin wani bacin rai na dibanta. Buga steering motar tayi kamar ita tayi mata laifin tana danne accelerator kamar zata tashi sama motoci sai matsa mata sukeyi suna horn ganin yanda take figar motar kamar a filin tsere.



Bata dau lokaci ba ta kai gida tay horn gate ya bude ta shiga tay wani wawan parking ta sauka batareda ta kashe motar kota cire key dinba ta fice ta shige cikin gidan.