KUSKURE

KUSKURE 10

by @fatimaoumshaheed479

*KUSKURE*



By maman shaheed



shafi na goma



Cikin wasu mintuna suka Isa gida gaba d'ayan su, yayin d Haneef ya Jima d bacci a hannun INDO,  a kafaɗunta  ta shiga da shi gida. 


Momyn su Noor ,Noor ta ja kawai suka shiga gd ,su twins d su huzna ma sukayi ciki ,itama Indo t gama kici_kicin d'aukan Haneef tayi cikin Gidan da shi dan a ƙoshe suke. 


A palour ta ajiyeshi Kan kujera tayi d'akin ta , ta cire kayanta ,ta canja wasu zuwa, marasa nauyi dan waɗan can sun dame ta. 

Itama momyn su Noor nata d'akin t nufa , yayin d Noor take cemata "" mummy bacci zanyi" 

"OK je Kan kujera ki  kwanda kafin a karkad'e muku gado" bawai Dan yayi kura ko dati ba Sai ɗan koyarwan musulunci da indon ta sabar ma yaran d shi har ita uwar ta ara ta yafa ta mai da shi duk a cikin aikin indon ne. 


Su suhaima , Asmy, ussaina sunwuce ɗakin d suka kwanta jiya Dan sun gaji hutu d bacci kawai suke buƙata. 

Daga hassana sai huzna a palour suma suna shirin tafiya Dan su kwanta kowa jikin shi yayi la'asar. 


Can sukaji, karar mota ,sun tabata Yaya safwan ne dadyn su Noor ,Aiko mintuna uku suka shigo dashi palour ,Yana ganin su ya tmby su basuyi bacci ba , hassana ce tace "wlh Yaya yanzu muke shiri" itako huzna sai wani irin kallo take binshi dashi Wanda t gama shagala acikin son shi da birge ta da yake a koda yaushe. 


Sai da ta nisa kafin tace "ya S bamu ganka wajen kamu ba?" 

Yayi murmushi batare d y kaleta ba ,yace" kamu sai Mata ai ,naku ne ni me ya haɗani da wani kamu, badai Anyi nawa na aurena an wuce wajen ba? Ai shikenan"

ta wani kebe baki "Kai y s mazama ai suna zuwa kaga d munsha hotuna na yaushe gamo Naka kamun Ai Y zama tsoho n big broh ne sabo kafin..." sai kuma tayi shiru maganar ta maƙale mata. 


 Dariya yayi kafin ya firta  "haka dai kika ce any way ko gobe ma ai zamu Sha Amman yau Kam ta wuce" yayi gaba ma y barta Yana Kiran dear shi mummy Su noor, y barta d baki buɗe. 


Huzna kamar t bishi d duka Dan takaici ,besan cewa dadin Hira takeji dashi ba ,tayi tsaki siriri yadda hassana Bata ji ba t tashi ta nufi daki Dan kwanciya baccin da bata shirya mai ba. 


Yana shiga y Sami momyn su Noor n lalab'a Noor Kan tayi bacci dan taƙi kwanciya a falon. 


Tamai sannu d zuwa , y amsa da fara'a, yana tambayar su biki da gajiya, kafin ya fara ma Noor magana atunanin sa baccin be d'auketa b ina tuni tariga tayi bacci dan Bata d wuyan bacci. 


Yace" aje akaisu d'akin su amusu Addu'a nima kizo Ki shinfiɗe Ni kumin fiye da irin lalaɓawar da kika musu in ba haka ba na hana, kowa bacci a gidanan.. "

,be gama rufe baki ba momyn su Noor t Fara kwalawa indo Kira  to eleven 10:45pm alokacin Saboda tsabar lissafi. 


Shine y dakatar da ita d cewa" Dear me zata Miki Kuma a tsohon Daren Nan yarinyar nan a keɓen tacen waje irin wanan da, muke nida ke? "

Bud'an bakin sokuwar sai tace" D zuwa zatayi t d'auki Noor t kaita daki har Haneef t kwantar dasu wlh nagaji tilis kaima Sai dai kamin uzuri ka barma gobe in ban gaji ba"


Y wani buga tsaki ya girgiza Kai ,yace "haba wai sai yaushe Zaki bambance aikin Indo a gdn Nan d Wanda ba nata ba? Kuma ni kike cema sai de nayi haƙuri da hakki na?" 

"Nifa kai kake ɗaukan abun nan wani iri banga laifin hakan ba dadyn su noor" 

"Hmmm yanzu Ina cikin d'akin Ina tare d iyalina a cikin Daren Nan ,Amman Zaki Kira wata wacce b muharramata ba Kuma zuwa d'akin d nake bukatar na huta da iyali na aciki? ,Dan t d'auki yarinya taje t kwantar ,ai ko hassana d hussaina da suke muharamaina jini na ,in har kinada tunani acikin Daren Nan Kuma yadda nake k'ok'arin rage kayan jiki na d'inan , bakya kirasu ba kice su shigo ,bare baree wai Mai Aikin Ki wacce bani da alaƙa da ita ta kusa ko ta nesa"


Aiko ,ta harziko dan ita tunanin ta a tsaye yake cak "Wai akan indon kake wani tada jijiyoyin wuya kamar wata mace cikakiyar indon kake ɗauka wata  baliga wanan kucakar ? Kazamar? House girl? Da Bata cika mace ba har gobe har jibi ,duk wanan b Yana cikin aikin ta ba ,da har zaka kirani Mara hankali safwan?" ta kira sunan shi kai tsaye yau. 

Aiko dama kiris yake jira" ina hankalin naki yake nuna min shi? na kuma  kiraki din da, mara hankali ai har tunani ma baki da shi ki samin gas ko ki yankemin hukuncin d yadace Dani, NAWAL! "ya firta ranshi a ɓace

Ita kanta ta tsorata yadda taga ranshi y baci ,ta Jima rabon d taga bacin ranshi haka ,amman taurin Kai d kin d'aukan *KUSKURE* ta yasa tace" ai ba wani Abu bane Dan t shigo t ganka yarinyar d Bata karema mutum kallo ma ,wanan Yar tatsitsiyar yarinyar me ta sani a namiji d har zaka kirani d Mara hankali, sai dai ko in Kaine kake sa wani abu a ranka"Tana wani hucci  ya ke maganar. 

Yace "Kinga irin rashin tunani  d lissafin ba ,na baki gyara kin ki karban ,gyaran still kina min kalaman da Basu dace ba , in har kinada hankali Abin d kikayi yunkurin aikatawa me zurfin tunani Kuma mace wacce tasan kanta bazata aikata ba wlh, ki faɗi duk abin da kikaga dama na ɗau ɗamarar gyara miki KUSKUREn ki"


"SAFWAN! har da  wasu munanan kalaman sun biyo baya ,har da Mara tunani d lissafin ,Kuma nice Mara zurfin tunanin SAFWAN? Wai ko dama a wuya kake da nine? ta wani k'an k'ance ido Tana Mai tuhumar sa. 


Yace" yeess kece  ko kinada Abin yi ko karya nayi NAWAL? Kin fa fara kaini bango Ki kiyayi ɓacin raina a cikin gidanan"

rass! rass!! rass!!! Taji kirjin ta y amsa ,rabon d y ambaci sunan t har t manta tun tanada ciki y canja Mata suna zuwa mommyn unborn Amman yau Abin yasha bam_bam Sai Kiran ta yake ta manta da itama ta kira shi da sunan shi ita ma ta fara. 


Cikin bacin Rai d hucci y fice y bar Mata room d'in y koma nashi dama y biyotane dan ya samu keɓewa da ita a matsayin ta na matar shi gonar shi maybe yanaso y d'an kare yawa saboda halin buƙata, Amma haka ya haƙura ya bar mata ɗakin ,kunde gane ,toh t Bata Mai Rai y hadiye abinsa y koma nashi daki Yana shiga yasa key ma dan Ko Ganin ta baya son yi in y cigaba da zama kusa d ita kuma komai na iya faruwa. 



Haka aka barta d lissafi , cikin mutuwar jiki t tashi ,ta d'auki Noor takaishi d'akin su , sanan ta d'au Haneef taje t kwantar dashi kusa d Noor ,sbd ɓacin Rai Tama manta ko addu'a Bata musu ba dama bata saba ba  (sakaci d shirme ,kiyayewa ai yafi Allah na Nan) 


Yara under 5 yrs a d'aki su kadai babu nuna musu addu'a ko basu kariyar d addini y tanadar. 


Ranar kwanan bacin Rai tayi , gashi tanason Jin dumin mijin ta matuƙa Ko Bata yadda da shi ba yana dai bata kariya in tana tare da shi, ga girman Kai Yana addabarta , bare taje t nemi sulhu , Abin takaicin Taƙi yadda tayi *KUSKURE* haka t kwana cikin zullimi d tunani dakyar bacci y Dan dauketa harda mafarkai ta dingayi Gashi gani take shi ya fita laifi. 


Da safe , Indo d su twins suka tashi suka shirya komai na break , cikin ƙwarewa d birgewa , dake d wuri zasu fita zuwa gdn Ammy Dan yau acan zasu kwana ma ,Dan yau d'aurin AURE da dadare Kuma za Ayi dinner wacce ta gaji d had'uwa dan yau babu sauƙi Hijira zasu ma gidan. 

Da Asuba ko ta kan NAWAL be bi ba, itama taƙi bi ta kanshi a lissafin ta ko ta dalilin biki zasu shirya ze neme ta. 


Safwan d NAWAL dai sama _sama ake ,Amman sunki Bari jama'ar gdn su gane hakan musamman shi d ya fita tunani duk d huzna taso gano hakan Amman suka hana ta ƙofar da zata gane. 


Sunyi break lpy , Dady su Noor y koma bedroom d'inshi ya fesa wanka yaci wata d'anyar gezna Mai ruwan Zuma tanata kyali Riga d malummalun adon malum malun din iri d'aya d hular kanta takalmi d agogon sa masu tsada ne ga wani zoben azurfan sa  sheki yakeyi ayatsan sa ya feshe jikin sa d turaruka sunkai 4 Yana Shirin fita Dan barin gidan ba tare da ya nemi matar gidan ba. 


Momyn su Noor ta shigo d'akin , har y gotta ta ze wuce ta Sha gaban shi , ya tsaya , cikin narkarkiyar murya tace dadyn Noor wai meye haka?"


Y kalleta yace" kamar yaya da akayi me?"


Ta ce" Abin d kakemin Mana?"Ya sake cewa" me nayi Miki kuma? "

Cikin shagwaba tace" kafa sani kanata wani shareni hakama jiya kaki kwana..."
sai kuka y kwace Mata t fad'a jikin shi Tana shashekar kuka na ƙirsa da makirci. 


Abin ka d masoya ,duk yadda yaso fuzge ta ko ya ture ta zuciya da gangar jikin shi sun ƙi bashi haɗin kai tuni yaji kukan har cikin ranshi ,gashi y tsani kuka arayuwar shi musamman Nata, Dan haka besan San lokacin da ya matseta a cikin jikin shi Yana Dan dukan bayanta  d shafa Bayan ta ba Alamar rarashi. 

Jin taci gaba d narkewa kamar zata kule kirjin shi ,yasa y talabo ta Yana cemata tayi"toh Ai Kece da abin haushi dole sai kin ƙular da mutum ga Taurin kai kiyi laifi kiƙi karɓan kuskure Ki, yi shiru to"


 ta yadda tayi lefi ,haka t d'ago da kyar ta Fara bashi hakuri , cikin lokacin kankani , yace "y wuce ki gyara ki  dinga kula d kanki d hidiman iyalin Ki ba Komai zaki sakar ma mai aiki ba ni naki ne bana mai aiki ba ko nata ne kin bar mata ni?" 

Ta wani ɗago kai a firgice, tana mai wani kallon mugun kishin shi na taso mata. 

"to mai da wuƙar ni naki ne ke kaɗai til jannah Ki  gyara Rayuwar Auren mu pls Dan Allah sai mu sami daidai to bana so abin d ya faru jiya na sake jin shi, kuma ina binki bashi hakki na da kika hanani" 

Fuska ta rufe a ƙirji shi "toh kayi haƙuri Amman sai mun gama bikin yayan mu insha Allah zan gyara dadyn su Noor" 

"au SAFWAN dai" 

"a'a dadyn su noor dai" ta mai mai ta.

"au kin gyara?" 

"ba dole na ba ma" tana mai nuna mai wani musulmin so. 

Shikenan komai y canja ,ganin zata ɓata Mai kwaliya y dagota y Bata tissue yace t goge fuskar ta d guntun hawayen  dg baya ma y karba y goge Mata hawayen , gudun Kar t shagalar dashi gashi y gama shiri ,ya lalab'ata , yace" za muje wani waje ne daga can zamu wuce  gun d'aurin AURE Kar Ki ƙarya min alwala ki makarar dani "

" sai munn had'u gdn Ammy Kinji Ki kular min da kanki da yarana"cikin birgewa da matsanaicin kewar juna suka rabu tamai rakiya har bakin mota, ji tayi kamar ta bishi haka t dawo bedroom ɗinta dan ta gama nata Shirin yara kuma boyi_boyi ta shirya su. 


 Su ko su Noor d Haneef tuni Indo t gama musu wanka t gyara su tasan aikin tane , ussaina Kuma t sa musu Kaya t gyara su tsaf suka fito suna ta baza ƙamshi ana ta musu hoto d Jan su ajiki dan sun saba d kowa dake gidan yanzu banda huzna da bata jansu Sai taga dadyn su. 


Huzna,suhaima,Asmy,hassana,usaina,duk sun gama shiri sun tsantsara kwaliya t agani ayaba , kafin suje gdn Ammy me kwaliya t sake tatso musu kyan su in zasu canja Kaya. 


Indo ma tayi wanka ta saka material d'inta d'inkin bubu dinan tayi kyau b lefi kayan d su twins suka Dinka Mata Ankon dinner shiko ta sashi a Leda se a gdn Ammy zatasa .


Koda suka fito gaba ɗayan su Dan tafiya, momyn Noor d huzna d suka ga Indo seda sukayi mamaki ,suka San Ashe kwaliya d kowace mace dacewa yakeyi Amman Basu yaba Ba.


Suka nufi inda driver yake , suka shiga y jasu sai gdn Ammy uwar ango kakar su Noor uwa ga twins.