04
ZAINAZAIN..!
(Is a love Story and Betrayal)
Wattpad:Jamilaumar351
Mallakar:Janaftyshakira❤️
BOOK 1
0️⃣4️⃣
#SHEKARUN BAYA..!
"A kowani Fanni na Rayuwa akwai Cigaba akwai akasinsa Haka Zalika kamar yadda akwai Samu akwai Rashi akwai Nasara akwai Faduwa,kuma Duk Allah Subuhanahu Wata"ala yake Tsara Abunshi kuma ya Tafi yadda ya Tsarashin.
In mukayi Duba da wannan Rayuwar Tamu ta yau da kullum,Allah ya Hallicemu Dabam Dabam ne kuma Rukuni Rukuni Akwai Kasa kasa a Duniya akwai mu kuma Jaha Jaha,Kana kuma sai yazo yayi mu al"adu da kuma Harsuna Dabam Dabam..Sai kuma ya bama wasu Daga Cikinmu ikon Tashi Cikin Addinin musulunci wasu kuma Daga Baya ya basu ikon Zamowa Musulmai akwai kuma Wadanda Yake son ganinsu Haka kuma ahaka ya barsu Tunda Shi din mai Fitar da matacce ne acikin Rayayye kuma mai Fitar da Rayayye acikin matattu.
Kamar yadda muka gani ko yatsun Hannunmu ba Daidai Suke ba Wasu sun Dara wasu Toh Haka Abun yake in mukayi Duba da Rayuwarmu ta yau da kullum,Acikin mu akwai masu Tarin Dukiya wadanda bazamu iya Gogan Kafada dasu ba kama Daga wasu yan Siyasa ne wasu kuma yan kasuwa ne masu Tarin Arziki wasu kuma Suna Kasansu ne ma"ana masu Rufin asiri Daidai Gwargwardo Wadanda Suke fin karfin Gidansu Har da Nauyin wasu akansu Wasu kuma iya Nauyin kansu ma Suke iya Dauka yayinda da wasu kuma ko Nauyin kan nasu bazasu iya Dauka ba saboda Halin yau da kullum Ammh Duk da Haka basu Gaza ba ba kuma Suce Allah baya sane dasu ba akowani Hali na Rayuwa Sai dai Su Furta kalmar Godiya Ga Allah ALHAMDULILLAH..!
Dr.Abubakar Bashir Saulawa Haifaffan Garin Katsina ta Dikko Dakin kara ne,Kuma Haifaffan anguwan nan ta Cikin katsina mai Suna Saulawa,Abubakar ya Taso Dan Gata Cikin Dangi Duk da Tun yana karami ya Tsinci kansa amatsayin maraya ta Bangaran uwa da Uba sakamakon Hadarin Mota sai Rikonsa ya koma Hannun Baffansa Ma"ana Yaya Wajen Mahaifinsa.
Shi ya Daukeshi ya Hadashi Cikin ya"yansa Ya inganta Rayuwarsa Tunda alokacin Yana da Halin yin Haka Tunda ma"aikacin gwannati kuma yana Cin Lokacinsa Sosai Abubakar Tun yana karaminsa yake da Burin Zama Likitan kwalkwalwa Sakamakon Labarin Daya samu Kakarsa wacce ta Haifi mahaifiyarsa da Ciwon Hauka Ta Rasu Sai Abun ya Shiga Ransa ya Saki Tasiri Tun Daga Lokacin Yayi ma kanshi alkawarin sai ya zama Likita Ta Bangaran kwakwalwa kodomin Taimakama Talakawa Maraasa karfi Wadanda Suke karewa a Hauka Har su mutu basu samu mai Tallafamusu.
Alokacin ba wanda ya Dakatar Dashi kan kudirinsa sai ma Goyon Baya Daya samu Ana Cikin Haka yagama Secondry School Dinsa anan garin na Katsina Lokaci kalilan Baffansa yayi masa Cuku Cukun Samun Gurbi Karatu Awata Medicine School Inda ya Shafi karatun Likitan Kwakwalwa Wato Psychiatric kenan Dake Birnin Delhi India Chan ya Tattara ya Tafi Inda ya Kwashe Shekara Goma achan kafin ya Dawo kasar sa ta Haihu Shima Din Rasuwar Baffansa ne ya Dawo Dashi Tunda Shekara Daya kenan Da kamallah karatunsa da kuma kananun Cosa cosan Dayai ta Hallata Saboda Cikar Burinsa ya Fara aiki da wani Asibitin kwakwalwa Dake Bangcof a matsayin Psychiatric Doctor,duk da bashi da Burin aiki a ko"ina sai a kasar sa ta Haihu bai Hanashi Fara aiki Dasu ba Ba domin komai ba Sai Domin yana Bukatar Tsayuwa da Kafafunsa kafin ya koma kasar sa ta Haihu yaga kuma ta ina Zai Bullo Domin Cikar Burinsa na Taimakawa Talakawa ya Tabbata.
Ana yin Sadakan Bakwai ya Tattara ya koma Dama Bashi da gado Tunda Da iyayensa Suka Rasu da Abunda ya Gada aka Dinga mai Hidima koda ma Ragowa bai Damu Daya Nema ba alokacin Hankalinshi ya Karkata kan neman Halas Dinsa da kuma yadda Burinsa zai Cika.
Yayi gwargwarmaya Sosai kafin Cikar Burin nashi Tunda Sai da ya kara kwashe Shekaru wajen uku achan Bangcof kana ya Dawo Gida Nigeria ya yada Zango a Lagos inda ya Fara da Wani asibitin a Bangaran Masu Laluran kwalkwalwa,bayan nan yayi Tafiye Tafiye zuwa kashashen ketare da bai san iyaka ba Wajen kara sanin kam Abunda ya Shafi masu Laluran kwakwalwa yana Da Shekara 28 a Duniya komai na Bukatar Rayuwa ya mallaka Motar Hawa da Gidan kansa da kuma Wasu kadarori gefe Daya kuma yana Kokarin Taimakama yan"uwan da Dangi.
Sai da ya Shekara Talatin Yan"uwa suka Taso mai kan Mganar Aure Alokacin Shima bai kiba sai ya amince ya Fara Neman Aure sai dai Dayake Tun Farko ba"anan Hankalinsa ya karkata ba Sai ya kasa kawai Daga karshe sai ya basu Zabi Su kuma Suka Zabamai Aminatu Diyar Baffansa Wanda ya Rikesa bai yi gaddama ba ya karba,Duk da Amina itace auta Bai wani Wayeta sosai ba,Saboda Tana karama ya Daga Zuwa Delhi ammh bazai Taba kinta ba ba"a saka Lokacin Bikin da Tsawo ba Tunda Itana Aminar ta gama Secondry School Dinta kenan Mganar Tataso kuma bata ki Dan"uwanta ba Duk da Lokacin ana Ta so a Hure mata kunne ganin Abubakar din ya Riga ya Tazurance bai yi Aure ba ammh Taki Jin kowa Tunda dai Mahaifiyarta ta yarda da mganar kuma yan"uwanta Sun bata Goyon baya Sanin Dr Saulawan Samun kamarsa a wannan Marran sai an Tona.
Wata Biyu Tsakani aka Daura Auran Amina da Dr.Abubakar Saulawa,Direct kuma Gidansa Dake Lagos ya wuce da matarsa Tunda ba wani Sha"ani akayi ba Ta Samu Rakiyan yan"uwa da basu gaza Biyar ba,sukaje suka ga Inda Take suka kwana Biyu suka Dawo Suna Musu Fatan zama Lafiya na Har Abada.
Alhamdulillah Zamansu na Gudana Cikin kwanciyar Hankali Amina nada matukar Hankali da Natsuwa Shi ma Haka sai suke kokarin Sauke Nauyin Juna Dake kansu,Watansu Biyar da Aure ya Sakata a makaranta Tayi Diploma Dinta Shikuma alokacin yana taCikun Cikun Dawowa Arewa da zama Gabadaya Hakan bai samu ba sai da Suka Shekara Biyu kana Ya samu Babban matsayi a Asibitinn General Hospital Bauchi Ya Tattaro Amina Suka Dawo Garin Bauchi da zama Wanda ya zama kamar garinsu Ciki yayi ya"ya da Jikoki har kuma Babban Burinsa na mallakan Asibitin kansa ya Tabbata.
Suna Dawowa Amina ta Fara Laulayin Shigar Ciki Murna Wajen Dr.Saulawa Ba"a mgana yan"uwaa Suna Ta Murna Sosai Dama Ta gama Diplomanta Dayayi mata mganar Cigaban karatunta sai tace ya bari sai ta Haihu Shikuma sai ya kyaleta ganin Tana Fama da Lailayi.
Watan Cikin Amina na Shiga Wata Tara ta Haifo Santalelen yaronta Sak mai kama da Dr.Saulawa,Ranar Suna ya Ci Sunan Mahaifin Abubakar Wato BASHIR kuma basu mai wata alkunya da Bashir dinsa Suke Kiransa,Haihuwan Bashir kamar Tazo da wani Budi ne Tuni Sunan Dr Saulawa yayi Fice agarin Bauchi Da kewaye Duk inda ake nenan Likitan kwakwalwa Wanda ya kware a aikinsa Shi ake nema kuma yana Taimakawa gwargwardon ikonsa Ya Hallaci Seminar Seminar ba adadi,Kuma Sunansa yayi Fice Tunda Har ya goggayan Da manyan Likitoci,Tarruka na mussaman na karama Juna sani Duk yana Hallata Saboda Sanin irin gwazonsa da kuma irin yadda yake aikinsa da Jarjircya Hatta Asibitin na General ta san da zaman Dr.Saulawa Wanda Abubakar din ya bace sai dai kaji Ana Kiran Dr.Saulawa.
Bashir Nada Shekara Uku Duniya Amina ta kara samun Wani Cikin Lokacin ma Dr.Saulawa na Shirin nema mata makaranta ne sai kuma ga wani Cikin bai nuna komai ba Sai Jin Dadin Domin yace yafi son Haka yadda ya Dade bai yi Aure ba yana so kafin karfinsa ya kare ya"yansa Su more Lokacinsa Kamar kuwa ya amsa gaban yan Ameen Bayan Bashir Sai Kuma aka samu USMAN,Daganan Haihuwa ta Bude ma Amina ba Daga Kafa Daga Usman Sai Tayi ALIYU sai kuma ta Sirka ma Mata Tayi HANNATU sai kuma Tayi Autarta Ta karshe Wacce Daga Ita bata kara Haihuwa ba RUKAYYAHTU.
Da wadanan Ya"ya Biyar din Dr.Saulawa ya Godema Allah Suka Cigaba da Rayuwarsu Suna Tarbiyantan da ya"yansu Zuwa Lokacin Allah Duk Ya Dauki Sauran iyayen nasu Mata Sai suka Rumgumi maraicinsu Su da Amina Suna Cigaba da Rayuwarsu gefe daya kuma suna Bama ya"yansu Duka kulawansu.
*****
Shekaru Talatin da suka Shude..
Zuwa Lokacin Zan iya cewa Duka Buri da kuma Fata na Dr Saulawa ya Cika Domin ya Kamallah Ginin Kayattacen asibitinsa mai Suna SAULAWA SPECIALIST HOSPITAL BAUCHI...!
ya kuma Gina wani katafaren Gida a GRA gida ne Ginin zamani mai kyau da Tsari Tunda Duka yayansa Sun Girma Bashir Shine Babba Chemical engneering yayi sai Usman Wanda ya karanci Fannin Na"ura sai Aliyu Wanda Karanci karantun Lauya,,Hannatu da Rukkaya kuma kowace Tayi Aurenta Tana Cigaba da karatunta a Dakim Mijinta.
Rukayyah Tayi Aure agarin Kanon Ta Dabo ne,Tana Auran wani Dan Siyasa ne sai Hannatu Wacce ta Lula garin lagos Tana Auran wani Dan Canji ne Dukkansu sun gama Degree dinsu Basa dai aiki ammh kowacce Tana Kasuwancinta ta Tsaya da Kafafunta.
Dr.Saulawa yaso Dayan Burin nashi ya Cika Na samun Daya Daga Cikin ya"yansa wani ya gajeshi ya zama Likita koda ta wani Bangaren ne ba Bangaransa ba Ammh kana naka Allah na nashi ne,Hakan bai samu Tunda Duka ya"yansa Nashi basu da wannan Ra"ayin sai ya kyalesu ya Binne abun Aransa yana Tunanin inda da Rai da Rabo Allah zai cikamai Burinsa ko ba akan ya"yansa ba akan Jikokinsa da zai samu ta Tsatsansu Tunda shi karfinsa karewa yake bawai Raguwa ba.
Asibitin Daya Gina ya samu karbuwa Domin ya samu Shawara da kuma Taimakon manyan Likitocin Duniya musamman Likitocin kwakwalwa Shashi Guda aka Bude acikin Asibitin Saboda masu Wannan Fanni Dr. Saulawa da kansa yake Attending Din patient dinsa Sauran Bangarorin kuma ya kawo Likitoci Masu kwarewa Da Taimakon Abokan aikinsa da Abokan karatunsa da kuma yan"uwansa Harda Taimakon ya"yansa Dana Matarsa Tunda Da Farko yana ganin kamar bazai iya ba Sai kuma gashi Da Taimakon Allah da kuma ganin Niyyarsa komai ya zama Sai Tarihi.
Dr.Saulawa Mutam ne nagari kuma Mai Daraja acikin Idanun Mutane da suka sansu su kuma San Labarinsa,Game da ma"aikatan Gidansa Shi mai Kirki game da Likitocin Dake aiki Dashi asibiti Mai kirki ne kama Daga ma"ikatan lafiya zuwa masu matsayin Aikin Share Share da goge goge da kuma Masu kula da Shige Da Fice Duka Sun Shaida Dr Saulawa mai Kima ne Haka game da patient dinsa zakayi mamakin ganin yadda yake Tafiyar dasu ba kyama ba wani Girman kai Zai koma Kamrsu Suma Ya Shiga Cikinsu Domin mema musu lafiya Shiyasa Lokacin kalilan indai Haukan naka bq Tuburan bane Dr Saulawa zai Taimaka wajen Dawowa Dakai Cikin Hayyacinsa awannan Fanni Shi kwararre ne kuma Haziki ne.
Dr.Saulawa yana da Wani Megadi Wanda yake gadin Gidansa Mai Suna Mallam Umar Gada Wanda Dan asalinsa Haifaffan Garin Gada ne Dake Jahar ta Sokkoton Shehu,Talauci da kuma neman kudi ya barosa da Garinsa da ya"yansa zuwa Garin Bauchi yayi gadi a gidajen masu kudi Dadama da yan Siyasa bai ji Dadi ba Sai da Allah ya Hadashi da Likitan kwarai likitan Takalawa Wato Dr.Abubakar Bashir Saulawa Ya Bugeshi da Mota Lokacin yana Kokarin Komawa garinsu ne wajen iyalansa Abun ya Faru,Dr Saulawa ya Dinga Kula da Mallam Umar a asibitinsa Duk da bai wani ji Rauni ba Karaya ce da Gocewar kashi,Dashi da matarsa Hajiya Amina Wacce Mijinta da ya"yanta ke Kiranta Hajiya Mama Sunsha Dawainiya Dashi Bayan an sallameshi Dr.Saulawa da Matarsa Suka Dauki Mallam Umar har garin gada suka sadashi da Danginsa da Iyalansa.
Wannan Abun Da yayi ma Mallam Umar Shi ya karamai kima adanuwansa da kuma na Danginsa dana iyalansa Bakinsa ya Dinga Fadin Alherin Dakta Garesu,domin Da suka maidosa Gida bai barsu Haka ba sai da yayi musu Sha Tara na arziki balle ganinsu Cikin Halin Talauci da Wahalan Rayuwa Abun bai Tssya nan ba kowani Lokaci in Dr Saulawa ya samu lokaci zai zo ya Duba Jikin Mallam Umar kuma baya zuwa Hannu Rabbana kafin Mallam Umar ya warke yaga karammawa da kuma Karancin Irin na Likitan Mai Hangen nesa da Taimakon Takalawa ba Shi kadai ba yan"uwansa ma Suna yaban Hallin kirki irin na Dr Saulawa da matarsa.
Bayan Mallam Umar ya Warke sai Dr.Saulawa yazo ya zauna Dashi anan ne ya Fahimci ba wata kwakwaran Sa"ana da kuma Dalilin Daya kaishi Garin Bauchi Jin Haka yasa sai Dr Saulawa yace in bazai Damu ba yazo Gidansa ya Zauna Shida iyalansa Da matarsa Allah barshi sai ya Dinga Mishi gadi matarsa kuma ta Rika Shiga Tana Taimakama Amina Tunda Bai yi karatun Boko ba Ballatana ya Taimakamai ta wani Fannin.
Wannan Albishir din yafi komai yima Mallam Umar Dadi Yan"uwansa ma Sun Tayashi Murna,cikin Abunda bai fi Sati Daya ba Dr.Saulawa ya Turo Mota aka kwasheshi Shida Matarsa Atine da kuma Dansa kwara Daya Daya mallaka Abdullahi Zuwa Bauchi Gidan Dr.Saulawa aka kuma Saukesu a Shashin Boysquaters Inda Aka Jikasu da komai na Bukatan Rayuwa Mallam Umar da Matarsa Atine suna kuka suna ma Dr Saulawa Godiya na Irin karamcinsu garesu shi kuma yana Fadin karsu Damu.
Mallam Umar shi ya Cigaba da gadin Gidan Dr.Saulawa awanchan Lokacin bayan ya sallami megadinsa Dama Buzu ne, zai koma garinsu,Cikin Jin Dadi da kuma Cigaban Rayuwa ita kuma Atine ta zama yar gida Tunda Ta zama yar Dakin Hajiya Amina kusan a Shashensu Take wuni Abdullahi kuma anyi anyk a sakashi makaranta Boko yaki wai karatun allo yake so ganin Haka yasa mallam Umar ya Tattarasa ya maida gada inda chan aka kaishi argungu yana Makarantar allon Dayace Ita yake so.
********
Bayan Shekaru Biyar..!
Abubuwa Dadama sun Faru Cikin Gudun wannan Shekarun Ciki kuwa Harda kamallah Duka karatun Ya"yan Dr.Saulawa Duka Zaratan mazan nasu Wadanda Dukkansu suke da Qualification din Masters dinsu Wato Bashir ne Babba wanda ya Samu aiki agarin kaduna A Refenaring,sai Usman Wanda Ke Bimasa Wanda Shi ya samu aiki a anan garin Bauchi a wata ma"ikata Inda Suke Wallafa Littafan karatun na makarantu Dabam Dabam a matsayin Manajansu sai Karamin su Aliyu Wanda Shine Lauya Mai zaman kansa.
Dukkansu sun yi Aure Sai Dai Aliyu ya Rigasu yin Aure da Matarsa Safiya,suna Zaune agarin Abuja,Sai Usman Wanda Dr.Saulawa ya Aurama Mata Biyu arana Daya Wato Fatima da Aisha kuma Dukkansu yan garin Bauchi ne Wadanda Dr.Saulawa yayi zaman Amana da iyayensu,kuma yaji yana Sha"awar Hada zumunci da ya"yansa da Farko Fatima ce ta Usman Aisha Ta Bashir ce wanda ko kafin Dr.Saulawa ya gabatar da ita ya Riga ya gabatar da matar da zai Aura Iklima Wacce itama yar Kaduna garin gwammace Koda Dr.Saulawa ya Kawo maganar Aisha sai Bashir din ya Nuna Ita Iklima din yake so sai ya kyaleshi Ganin ya Riga kuma ya Furtamai iyayen Ita Aisha sai ya Nemi Usman din Daya Hadasu Duka Biyun ya aura bai yi gaddama ba ya amince Dr.Saulawa ya Aura masa Fatima da Aisha Arana Daya Bashir kuma sai bayan Shakara Daya da wani Abu da Auran Usman kana yayi Auransa Tunda Daman Shi Duk yafi su akidan Boko ita kanta Ikliman yar Boko ce Tunda itama ma"ikaciyar gwamnatice.
Usman yana Zaune nan GRA inda ya Gina Gidansa kusa da iyayensa Tunda Shi kadai ne ke Zaune garin Bauchi sai yaga gwara ya zauna kusa da iyayensa Tunda Shi kanshi babu wasu Dangi Duk Sun kare ammh Har yau bai manta da garin katsina ba yana zuwa kuma Hannunsa na kaiwa nan yake Zaune Shi da Matansa Tamkar Tagwaye Wato Fatima da Aisha.
Ayayinda Bashir ke garim kaduna Shima ya mallaki gidan Kansa da Motar Hawa haka ma Matarsa nada Motarta Sai Aliyu Barrister kenan yana Zaune agarin Abuja Shida matarsa Safiya Suna Zaune a Maitama Abuja Shima Din ya mallaki gidan kanshi Da Motar Hawa Rayuwa Dai ta inga Su Rukayyah kuwa da Hannatu kowacce Tana Gidan Mijinta ta Haiyayyafa Suna kuma Cikin Jin Dadi sai wanda ya gani.
Dr.Abubakar Saulawa ya Samu Duka Cikar Burinsa Shiyasa Shekara na Zagayowa ya Tattara Duka iyalansa da matansu sukaje kasa mai Tsarki suka Sauke Farali,Shi dai Dr Saulawa da Hajiya mama Gida suka Dawo Ammh Su Bashir Kowanne kasar Dayake Muradi ya Wuce Shi da iyalansa Haka ma Su Rukayyah kowacce da Mijinta da ya"yanta Tun a Saudiya sukayi sallama da Junansu kowanne ya yada Zango a Inda ya Tsara zashi Su dai su Rukayyah da Hannatu da Mazajensu sun koma Gida da Wuri ammh Su Usman kam sai da Dr.Saulawa ya Dinga Musu waya yana Fadin Sun bar ayyukansu sun je wani kasa Sun Tare,Maza su Tarkato su Dawo wannan Dalilin yasa suka Tattaro Suka Dawo Kasar su ta Haihuwa kowanne na amsa Sunan Alhaji matansu ma na amsa Sunan Hajiya.
Duk acikinsu Matan Usman ne suka Fara samun Ciki Wato Fatima da Aisha kuma duk atare,Murnan wajen wannan Ahali ba"a mgana barin ma Dr.Saulawa Farinciki ya Cikashi zai Fara samun Jikoki,samuwar Cikinsu da Wata Biyar sai ga Wani albishir din Safiya ma Matar Barrister Aliyu itama ta Harbu Sai Farincikin ya ninku,Bashir dai Shuru Dama Shi yace Tsarin iyali zasu yi ba yanzu zasu Fara Haihuwa ba sai zuwa gaba koma sun Fara 3 Childeeen ya Ishesu.
Samuwar Cikin Fatima da Aisha Sai kuma Lalura ta karu gasu dama su kadai agidan ba yar aiki Tunda Tun Farko sun Nuna basu bukatar Wata yar aiki su Zasu Dinga aikinsu da kansu,sai kuma ga Samuwar Cikinsu Lokaci Daya kuma Dukkansu Suna Fama da lailayi sai Hankali Alhaji Usman ya Tashi kwarai yaje ma da Hajiya mama da Batun Samun mai Taimaka ma su Fatima kafin komai ya Daidaita ita kuma sai ta gayama Dr.Saulawa Batun Shi kuma sai yace Abun bana gaggawa bane gwara a tsaya a samu mai amana Tunda zata zauna da iyalansa ne.
Da wannan Mganar Alhaji Usman ya bar komai a Hannun Dr.Saulawa Da Hajiya Mama kwatsam Atine taji Hajiya Maman na Zencen sai tayi karaf tace In suna so ga Matar Dansu Abdullahi wanda yayi Aure Shekaru Uku da suka gabata ya Gaba Karatun allo ya koma Gada ya Fara Sa"anan sai da kayan Dinki Wanda Dr.Saulawan ne ya Tankamai Jali Tunda yaki Karatu kuma Har yau har gobe akwai amana Tsakaninsa da Mallam Umar da iyalansa Atine kuma ta zama kamar yar gida.
Wannan Mganar ta Atine Hajiya Mama ta kaima Dr.Saulawa Shi kuma yayi Na"am acewar Iyalan Mallam Umar Abun so ne Takalawa ne masu Wadatar Zucci da Dr.Saulawa ya Tuntubi Mallam Umar gada da mganar sai yaso yamusa saboda yace Kada Maryama Tayi Nesa da Mijinta Jin haka yasa Dr.Saulawa yace kada ya Damu Duka da Maryama da Abdullahin Zasu dawo nan gidan Usman da zama kamar yadda shi da atine suke zaume agidansa Dama yaji Usman Din na neman mai kula mai da Kifayen Dayake Kiwo Faduwa tazo Daidai da zama Mallam Umar Bai iya mgana ba,sai Godiya kamar yayi kuka na Karamcin Dr.Saulawa agaresu.
Koda Dr.Saulawa ya Tuntubi Usman da mganar bai yi gaddama ba Saboda Baba Atine kamar Wata Babba yaya Suka Dauketa Shi kanshi Mallam Umar ba"a Matsayin Megadi suke kallonsa ba Suna Kallonsa ne Kamar kanin Mahaifinsu Baba Umaru ma Suke Kiranshi Batare da bata Lokaci ba Dr Saulawa ya Saka Mallam Umar ya Kiramai Abdullahi sukayi mgana Dayaji labari murna ta Cikashi Dama Tun bayan da yagama Almajirancinsa ya Dawo Bayan yayi Sauka ya Dinga Nadamar kin karatun Boko da yayi Tunda ya Fahimci yanzu Rayuwat bata Tafiya sai da Duka Fuka fukan Biyu gashi kuma Lokaci ya kuremai Dole dai Kanwar naki ya zauna chan Babban Gidansu a Gada ya Auri Wata yar"uwansa Maryama Bayan Dr.Saulawa ya Tankamai Jali ya Fara Sana"an kayan Miyan Jin wannan Rokon alfarman ta Dr Saulawa Sai Abdullahi yaji kamar an sakashi a aljannah ko kwana Uku basu yi ba ya Tattaro maryama Zuwa Bauchi bayan yayi sallama da Yan"uwansa ita kuma maryama Tayi sallama da yar"uwanta kwara Daya Tal aduniya wato Halima wacce ke Aure a nan garin Gada.
Direct Gidan Alhaji Usman aka yi musu masauki,awani Shashe Dake gefe wanda bama Boysquaters bane Flat mai kyau aka kuma ingantasu da komai na More Rayuwa,Babu Abunda zasu iya cema Iyalan Dr.Saulawa sai Fatan gamawa da Duniya Lafiya,Cikin ikon Allah Maryama ta zama mai Taimakama Fatima da Aisha Duk da kasancewarta yarinya Domin Lokacin bata wuce Shekara 19 ba ammh akwai kwazo na matan kauye da kuma Biyayyah gata Shuru Shuru ba Ruwanta ga kwaici ga kunya,Anty Fatima Anty Aisha Sama Shi kuma Alhaji Usman Daga ita Har Abdullahi Yaya Suke Kiranshi yayinda Suke Kiran Dr Saulawa da Alhaji Dr.
Ayayinda Gefe Daya kuma Abdullahi na Cigaba da kula da Kifayen da Alhaji Usman ke kiwo aikinsa kenan,Gidan Dr.Saulawa kuwa kowani Lokaci Suna Zuwa Shida Maryama Domin ganawa da iyayensa Danginsu na chan gada kan kawo musu Ziyara Lokaci Bayan Lokaci Ita ma Maryama Yayarta Halima tazo Taga inda take ta Dinga murna da Fatan alheri Ganin Maryama ta samu iyayen Daki na Gari Tunda Daga Fatima Har Aisha Suna matukar Tsausayin Fatima Shiyasa komai suka samu itace Shi kanshi Alhaji Usman din kallonta yake kamar Hannatu ko Rukayyah Shiyasa suka Rikesu Hannun Bibbiyu tun Bale ma Dr.Saulawa wanda akullun Usman yaje gaisheshi sai yayi Fadan Kula da Hakkokin mutanen Dake kansa Tunda Tamkar Amanace gareshi.
Sannu Sannu Bata Hana zuwa sai dai Adade ba"a je ba Cikin Hajiya Fatima da Hajiya Aisha na kara Girma suna kuma samun Dukkan kulawa Domin Likita guda Dr.Saulawa Ya samu Daga asibitinsa tana Zuwa Duk bayan 4 weekes Tana Dubasu Tana musu awo Hankalinsu kwance Har Cikinsu ya Shiga Watan Haihuwa Wata Ranar Jumma"a Babba Rana Allah ya Saukeki Hajiya Fatima Lafiya inda ta Haifi santalelen Danta mai kama da Dr Saulawa,ko Mintuna Talatin ba"ayi ba itama yar"uwanta Hajiya Aisha ta Haifi Santaleliyar yarta mace mai kama da Alhaji Usman acikin asibitin Daya ke mallakin Surukinsu Wato Saulawa Speacialist Hosp Bauchi.
Dama Hajiya Fatima na Fara mukurkusun naguda Abu kamar wasa Maryama ta Kira Hajiya mama ta gayamata Tunda Alhaji Usman baya Gida Ita tazo Da Direba ita da Atine Bayan ta Kira Dr.Saulawa yace ta kawosu nan asibitin yanzu,kamar wasa fa Harda Hajiya Aishan da Maryama Suka Shiga Motar zuwa asibiti sai dai kafin su kai asibitin Itama Hajiya Aishan Ta Fara Nagudan maimakon Hajiya Fatima Sai Dr Saulawa yaga Duka Surukan nashi ne ke kan gwiwa ganin haka yasa aka Shiga Dasu Bangaransu masu Haihuwa Domin basu Taimakon gaggawa.
Haihuwan batayi Tambari ba Sai da aka gama Shirya masu Jego da yaran kana Hajiya mama ta Shiga kiran Waya tana Fadan Haihuwa murna ba"a mgana Alhaji Usman haka yazo asibitin kamar bakinsa zai Yage saboda Murna Maryama ita ke Tare da masu jegon a Dakin Hutu kuma Duka Jariran na Hannunta itama bakinta yaki Rufuwa iyayen Dakinta sun Haihu...
Atare da Dr.Saulawa da D'ansa Alhaji Usman Suka Shigo Dakin na musamman da aka Kai su Hajiya Fatima,Hajiya mama da Atine na Binsu abaya suna Shiga bayan sannu da Barka daya Biyo baya sai Dr.Saulawa ya kalli Maryama yana Fadin"Maryama Mikominsu nan naji Dumin Jikokina..Allah yakai Raina.!
Tana Mirmishintaa na kunya ta Tashi Ta mikamai Su Duka ya Hada ya Dauka Har Hajiya Mama namai Tsiyan bai bari Uban Yara ya Dauka ba yayi mirmishi yana Fadin"Nima Uba nake garesu Amina..Ko ba Haka ba Usman Bin Fodiyo..?
Dariya yayi yana Fadin"Kwarai Abba..Tabbatas kai Uba kake garesu kai zaka musu Hudubu yanzu yanzu ka Sa ka musu Sunan da kaga yayi maka..Ai Dani da Matana Da ya"yan Dana Haifa duk ikon ka ne..!
Kowa Mirmishi yake adakin Dr.Saulawa ya kalleshi yana Fadin"Allah yayi maka albarka kaida Matanka Usman Fodiyo..!
Duka suka amsa da Ameen kujera Usman ya bashi ya Zauna ya Fara Daga macen ya mata Huduba aduka kunnuwanta kana ya Matsamata Dabino a baki kana ya mikama Usman yana Fadin"Allah ya Raya ZAREENA USMAN ABUBAKAR SAULAWA..!
Ya karbeta yana Fadin"Masha Allah Ameen Ameen Abba.."Namijin ya Daga Shima yayi mai Huduba kuma ya Bashi Dabino Shi harda Ruwan zamzam ya mikama Alhaji Usman yana Fadin"Wannan yaron Magaji na ne..Tun a Suna na sakamai DR.ZAINULLAHI USMAN ABUBAKAR SAULAWA..Allah ya Rayamana Shi.."
Gabadayansu suka amsa da Ameen kafin ya mike Alhaji Usman ya mikama Hajiya mama Jaririan ta Dauka kana ta mikama Atine itama ta Dauka ta saka Albarka kana ta mikama Maryama su Wanda Ta Nufi Hajiya Fatima Ta mika mata Zainullahi sai taki karba sai kawai ta saka Hannu Ta karbi Zareena Tana Fadin"Nifa ga yata nan..Mikama Aisha yaronta..!
Kowa sai ya saki baki yana kallonta Jin Haka yasa Hajiya Aisha Tace"Naji bakomai..Maryama Mikomin Da'na..Dama mun Riga mun gama mgana nayi miki alkawarin in mace na Haifa taki ce Har Abada ke kuma in kika Haifi Namiji nawa ne Har Abada..Allah ya cikamana Burinmu sai dai muyi Fatan Allah ya tayamu Tarbiya..!
Maryama Tana Mirmishi Tace"Nice Shaida..Ni kuma nayi alkawarin Tayaku kula dasu Tankamar ya"yan da zan Haifa da Cikina..!
Gabadaya Dakin suka amsa da Ameen Mirmishin Farinciki da kuma Annushuwa ya wanzu a zuciyar Dr.Saulawa hakama Hajiya Mama da Atine Shi kuwa Alhaji Usman mamaki ya kamashi na yarda har suka Tsaida wannan alkawarin bai sani Hadin kan matanshi na Burgeshi kuma yana jin Duk Duniya ba wanda yakai shi Dace..