Bayan Murmushi

Chapter 26

by @zahrabmrs02

page 26💬⌨️


Cikin tattali AK yake rike da hannuna har zuwa motar da zata maida mu gida .bayan munyi settling AK ya juyo yana fuskantata.you look very tried wifey ,Kina zuwa apartment kiyi wanka da ruwan dumi and sleep .ni a Gidanmu Zan kwana Yau .nace masa a marairaice,no wifey gidanku ba space Kin sani ,yan biki Sun cika ko ina ,ciwon kai zasu sa miki kuma Kinga gobe budar kai  you need a full time rest .gabana ne ya fadi ras da yayi maganar budar kai ,an canza schedule din zuwa sokoto ,a gidansu AK na abuja zaayi budar kai.inda  zaa fara kaini gidansu AK idan an gama sai a wuce dani gidanna ,shikenan ta faru ta qare na ayyyana a Raina .hawayen yanzu wannan shine reality dina ya zuba a fuskata.ba na hanaki deep tunanin ba,firgit muryar AK ta dawo dani daga tunani na.Uhmm tunanin diddi nake  zanyi missing dinta na qara marairaicewa .ba zato ba tsammani  naji ni kwance a jikin AK fuskata a saman kirjin sa .a hankali yake shafa bayana cikin sigar rarrashi ,it’s fine duk sanda kike son ganin ta zaki iya zua ni bani da problem you’re free kije Dik inda kk so.kaina na gyada ina shakar Kamshin sa me dadi….a hankali bacci ya fara daukata ..gajia ce sosai a jikina.tapping dina naji anayi a hankali  bude ido nayi caraf muka hada ido da AK,wifey mun iso 30:min ago naga baccin ya miki dadi shiyasa ban tashe kiba,friends dinki su wuce apartment.na kawo ki Wajan diddi ne ku dan taba hira ,Zan jira ki na mayar dake apartment din.Ak can be very sweet and lovely idan ya so. Su anty Nafeesa na tarar gida ya kaceme ana hirar dinner .dakinmu na shige tare da cire Wedding gown dina da ta dameni tuntuni.old pajamas dina na lalubo tare da wanke fuskata , ruwan zafi nake bukata dole sai na koma apartment zanyi wanka ,dan bani da energy din daura ruwan zafi da daddaren nan .dazu period dina yazo da safe ba damar sallar.joining dinsu nayi a falo tare da shigewa jikin diddi .

Ke maman mijinki ta amsa number na ,anty Nafeesa tace Tana juyo da attention dinta kaina ,har kishiyarki tayi introducing dinmu ,gskia farhana sai kin qara dagewa dan wallahi uwargidan sa is classy Gata yar gayu ce sosai , Uhmm Allah ya bani iko nace nonchalantly   . Filina Zan siyar na siya wasu golds din .Mun zama in-laws din masu kasa ,so nake idan kin haihu farhana su ganni da sabbi,dan ma meenat qawata ta fitar Dani kunya ta bani Aron nata nayi dinner dasu ,nawa Naga Sun zama  old models ne  ,anty Nafeesa Akwai son kai kanta inda Allah be kaita ba.Yauwa  Ina taso na maku magana na manta ,dazu munje gidan farhana dan turara mata daki ,Munga an canza komai da muka kai,abin ya bamu mamaki ,Akwai wani empty room da muka gani lokacin jere ,dazu da muka bude nan muka ga an mayar da furnitures din, naso fadi miki diddi Muna dawowa aka fara shirin dinner ,inna Jamila tace with all her seriousness ,shiru dakin ya dauka , sai ranting suke wanan ay wulakanchi ne ,Sun Raina arzikin mu kenan .diddi zatayi magana kenan muka ji sallama ,muryar Ak ne ,ni wallahi na manta yana jirana a waje .qarasowa yayi Bayan an masa iso.cike da ladabi ya gaishe dasu diddi ,caraf anty Nafeesa ta chafe,Yauwa yanzu kuwa muke maganar Ka ,dazu su jamila  sunje gidan farhana surprisingly suka ga an canza furnitures da komai da komai ,meke faruwa ne?

Ba komai anty Wanda aka canza sunfi dacewa da tsarin gidan ne ba Wai Raina kokarin ku nayi ba ,ko daya wallahi,hasalima Kunyi kokari duba da yarda bikin yazo cikin lokaci kankani,gashi baa dade da auren Adda Sabrina , Allah ya saka muku da alkairi .ni auren farhana da aka bani kadai fiye mun komai ,ku fahimce ni pls ya qarasa zancen cikin muryar ladabi,duk hargowarsu shiru kake ji ,ya gama kashe masu jiki da dadin baki ,amma mai mahaifiyar Ka zata ce idan tasan da maganar nan Ak?anty nafeesah ta qara tambaya ,ban fada mata ba,ba Wanda yasani wallahi Ak ya qara fada with frustration voice din da ni kadai na fahimta .sallama muka masu inda inna Jamila ta jadddah Philip driver ya kawo ni zuwa karfe 10 na safe dan shirin kaini budar Kai da azahar ,daga nan  a kaini gidana zuwa magrib 

Har bakin kofar dakin apartment Ak ya rako ni,saida ya tabbatar na shiga kana ya juya.

a gidan Ak su yaya Safiyya zasu kwana suna falon kasa tare da hanadi ana ta maida zancen familyn farhana .hanadi seems cool Kamar bata da wata damuwa ,amma deep down zuciyata Kamar an zuba ruwan zafi ,murmushin yake kawai take wa su yaya ramla ,hankalinta na kan AK karfe 12:30am har yanzu be shigo ba,lna ya tsaya?kar dai ace yana tare da farhana all this while?kai Anya Abdulkadir din da Tasani will never do that ,sallamar sa taji da Sauri da nufi shi cike da kissa,turus tayi ,ganin farar shirt dinsa da foundation marks harda jan baki a jiki ,kuma gashi taji sai kamshin wani turare yake da ba nasa shi ba,daga ina kk haka yaya ramla ta tambaya AK tana maida full attention dinta gareshi ,hannun hanadi ya riko suka qaraso cikin falon ,ji wata tambaya dai ramla ,yaro ne ni da zaki tambaya daga ina nake,anyways ina tare da wifey na kaita gida daga nan na jira na maida ta apartment Wajan friends dinta ya fada nonchalantly,kallon sama da kasa ramla ta masa,da yake farhanar bata da Kamun kai shine ta kwanta a jikin Ka Kafin tariya ,harda barin shaida mu gani ko?look ramla bana son tashin hankali yanzu sai na Kira daddy ,a Kira mijinki ki bar mun gida, ayiwa papa hakuri yaya ramla ba lefi yayi ba dan ya kula da safety din amaryarsa,ga shi daga gani a gajiye yake ,hanadi tace kice da kissa ta qara da cewa muje kayi wanka Ka huta ,harara ramla ta zabgawa hanadi ,Dama ke bakya ganin lefin sa ana kokarin kwato miki yanchi bakya gani.ufan yaya safiya bata ce ba.

Water temperature hanadi ta tanadar masa Bayan Sun shiga daki ,wanka AK ya shiga yana picking dinta a goshi.murmushin fuskar hanadi ya dauke dif Bayan shigar AK bandaki ,wayarta ta dauko ta fara typing :jinin Tuareg  ke yawo a jikina fa Anastafidet“(Anastafidet… suna ne da ya fito daga sahara, kamar iska mai É—auke da Ć™ura da sirri. Idan ta wuce, kamshin hamada da azurfa kan biyo bayanta.”duk wani matakin da ya dace Zan dauka cikin ruwan sanyi ….hanadi ta qarasa rubutawa da mischievous smile.

Bayan na fito daga wanka su zee nayi joining aka cigaba da hira  Yau gaba social media auren AK da farhana ke trending .wayata dana ba precious ajiya na amsa tare da duba messages ,you look happy :sms din farooq na gani ,wato Shima yagapics din bikin kenan .kaine farincikina Lamido abinda Ka gani facade ne na masa reply tare da ajiyye wayar .sama sama naji precious na kananan mita Akan rashin zuwan su hamma sajid  dinner ,ba yarda banyi ba suke ce Wai taron mata ne,ban San Yaushe dinner ya zama taron mata ba .bacci me nauyi ne ya dauke ni ba shiri 


Author’s Note:

Assalamu Alaikum đźŚ™đź’›

Yan uwa masu karatu, bari mu É—auki É—an lokaci mu yi Addua a wannan watan mai albarka.

Mu roƙi Allah ya kawo zaman lafiya a Arewacin Najeriya, ya kiyaye iyalai da rayuka, ya albarkaci duk masu bukata.

Ku haÉ—a da ni a wannan Addua, domin zuciyarmu ta sami kwanciyar hankali da bege. Amin đꤞ