Chapter 27
by @zahrabmrs02
page 27 💬⌨️
Small noise din qawayena ne ya tashe ni ,wayata na janyo daga gefe na tare da duba time .8:30am gaskiya nasha bacci
Fateeha da precious ne Ashe suka tashi,zee da nusaiba na bacci , farhana ina da magana da ke fateeha tace Bayan nayi brush ina shirin wanka .dayan empty room din muka nufa ,Kina jina ko?so nake na qara baki shawara ,kiyi hakuri ki kwantar da hankalin ki ,aure an Riga an daura ,ki manta da zancen bakya son AK ,am sure kuma bakya kinsa.kina da kalubale wallahi ,yana da mata kuma ance cousin dinsa ce ,yana da yara so dole a dan zaman da zakiyi a abuja ki kauda kai ,ku zauna lfy .zuciya tana son mai kyautata mata Dik son da kk ga yana miki idan bakya kyautata masa a hankali zai gushe,we don’t want you to bora a gidan miji ,kar ki sake ki Bari kishiyar ki ko yan uwansa su gano ba auren soyyaya kikayi ba,kuma stand for yourself kar ki bari su Raina ki . zanyi missing dinki farhana . tace tana rungumeni ,ina kuka tana kuka.haduwarmu na farko nake Tinawa, yadda ta dinga bani attitude amma kalle mu yanzu yadda muke kukan rabuwa da juna ,Nagode fateeha ta ,Zan dauki duk advice dinki inshaAllah ,kuma aure bazai raba mu ba,muna tare har jikoki .rungume ta na qara yi,fateeha Nada zurfin ciki ,bamu taba Jin ta bamu labarin yan gidansu kodawasa ni ko waya ban taba ji sunyi ba,amma shes living luxury .akwai hidden pain a tare da ita ,da har yanzu bamu sani ba. Naso na bata labarin abinda nusaiba tayi na chatting da farooq amma nayi tunanin zata ga Kamar ina stalking din farooq ne ,gaba daya nusaiba ta canza ,har precious jiya ke mun gulmar Kamar hassada nusaiba take ,kwata kwata taki sakin jiki a bikin.
wanka na shiga nayi zuciyata cike da tunanin mai zai faru ,Yau Zan tafi gidan AK ,ya rayuwata a Chan zata kasance?ya komawar mu USA zai kasance ?yanzu shikenan da gaske AK ne mijina ?duk soyayyar da mukayi da farooq?
Ban zachi na dauki lokaci a toilet ba ,sai da naji precious na knocking tana cewa hour na daya da shiga .
Duk mun shirya Muna zaman jiran Philip kiransa ne ya shigo wayata ,muka sami security mace a gaban mota .
Zee Adatayo ke ta mun rada a kunnena ,na yarda Zan gyara shimfidar mu nida AK.dalla kyale nace Bayan ta qara Baro wani zancen Wai ina kk San abubuwanan ne?na tambaya ina tsare ta da ido .dey dia tace Tana daukar wayarta.
Mun iso gida ,da nene na fara cin Karo,wani irin masifa ne wanan ana auren ki amma kinki zaman gida sai bin qawaye kk harda arna a cikin qawayen naki ,ko amsa gaisuwata batayi ba ,ta fara bambami,ba lefin ki bane RUKAYYAH ce bata baki tarbiya ba, haka Sabrina keta zarya sai kace ba kwanaanan aka yi bikinta ba ,yanzu ma tin karfe 8 tayi sammako tazo gidan nan .ah ah nene dakata anty Nafeesa ta chafe ,kar ki qara cewa diddi bata basu tarbiya ba,fadan ki ya tsaya iya jikokin ki don’t even start .mukus nene tayi Tinda anty Nafeesa da bikin nan 20k taba nene gudunmawa,Dama ita mai kudi baya lefi ,da dai inna Jamila da yanzu nene ta tara mata mutane .
Luxury abayar dake kan gadon ta hanadi ke Kallo,150k(as of 2016 ake magana ) tayi order ,tasan kowa atamfa zai sa Yau da budar kai,so dole ta zama unique ,gifts dinda ta tanadar wa amarya take Kallo Tana murmushi .shawarar Anastafidet kenan ,lalle Anastafidet ta zama jigo na rayuwarta ,bata Jin maraicin uwa Sabida yadda take bata shawara da kawo mata mafita a Dik lokacin da ta shiga cikin damuwa .
Tinda na shigo gida ake ta qara gyara min jiki ,anyi wa Kayan da Zan sa kabbasa Nima an turara ni ,Dik inda na motsa kamshi nake ,inna Jamila ta shirya ni cikin atamfah milk color da ratsin green ,sai Laffaya ta milk color itama da green flowers a Edges ,fuskata ba makeup daga kwalli sai lipgloss Wanda ya bayyana anihin zallar kyauna,skin dina sai glowing yake ,hanchi na ya fara fitowa zirr ,Kallo daya zaka mun Kaga cikakar bafulatana gaba da bayanta.tin Ana shirya ni nake kuka ,yayyi na maza ne suka shigo dakin diddi inda ake shirya ni hamma fahad ya rungume tsaf yana mun nasiha,hamma sajid da Muhammad ma suna gefe a sanyaye Kamar zasu fashe da kuka.suna kofar gida ku fara fita muryar anty Nafeesa ta karade dakin ,kankame hamma fahad na qara yi ina kuka,hamma ina abbi ?ban gansa ba,Abbi yace zai zo gidanki ya ganki bazai iya gani ki Kina kuka ,dan Allah ku kirashi hamma na qara fashe wa da kuka ,nene ce ta bankado dakin ,diddi na Bayan ta Idonta yayi jajir,Yauwa RUKAYYAH shiyasa na nemo ki ,su fahad Sun rike farhana sun hana ta fita Ana ta jiranmu tin dazu kuma kin san masu kudi basa san jira ,ita kuma taki tasowa wai iro take jira, zoki tsawarta masu Tinda sunfi karfina.da Sauri na qarasa jikin diddi ina kuka,ki yafe min diddi duk lefin da miki dan Allah nace cikin muryar kuka,na yafe miki Maryam Allah ya baku zaman lafiya Da zuria dayyiba ,abbi dinki yace yana nan zuwa har gida ya ganki ,Jan hannuna anty Nafeesa da anty hadiza sukayi zuwa falo ,kusan duk yan bikin Sun shige mototocin da aka kawo ,Adda Sabrina muka tarar a falo da wasu mata su uku .da Sauri anty Nafeesa ta ja laffaya ta ,tana rufe mun fuska