Bayan Murmushi

Chapter 28

by @zahrabmrs02

chapter 28⌨️💬

bakin naji suna gabatar da kansu a matsayin dangin AK ,kuma sunzo daukar amarya ne ,daya daga cikin su ta gabbatar da kanta a matsayin yayar AK wato ramla .qarasa fita daga gidan mukayi still har yanzu kuka nake ,su nene da mami already sun shiga cikin mota.
message ne ya shigo wayar hanadi already tana gidansu AK suna jiran isowar amarya ,vidoe ne yaya ramla ta turo mata with caption:kalli gidansu amaryar AK da emoji din dariya ,bude videon hanadi tayi tana qarewa gidansu farhana kallo ,yaya ramla dama tace zata je dauko amarya ne don taga gidansu farhana ,gashi kuwa har da tsarabar vidoe ,ta tabbata har mommy sai an turawa .kwata kwata hanadi bata da wata qawar da zata nuna tace gata ,su yaya ramla ne friends dinta ,bata da saurin sabo shiyasa friends dinta na school daga gaisuwa sai gaisuwa ba wani doguwar alaka ,akwai dai wata coursemate dinta jauhar da suke waya time to time .
anty Nafeesah ce ta yaye min laffaya daga ni saita sai kuma anty hadiza a motar ,kayan makeup ta dauko daga handbag dinta inda ta fara min dan touch up kadan a cewarta duk nayi kozai kozai sabida kuka.wata karamar bottle din turare da dauko tana qara goge min a wuya na da jikina take kamshi mai dadi ya gauraye motar.dik kamshin da nake kafin mu fito daga gida turaren ya ninka shi.dan Allah karki sake kuka farhana ,ki daure mu gama abinda ya kawo mu ,na tabbata zaayi pics at lest ki zama presentable wajan dangin miji ,kai na gyada mata 
su meenat qawata already sun isa yanzu naga text dinta tace an cika amarya ake jira .
 motar muce ta tsaya, take kuma naji ana announcing zuwan amarya,wai ashe budar kan ma taro ne,farfajiyar gidansu AK me girman gaske na hango daga cikin tented motar da muke ,an yi decorating filin .bude motar akayi ta gefe na ,kamshin AK na shaka ,daga jiya zuwa yau har na haddace kamshin sa ,taimakamin yayi na fito hannuna a cikin nasa ,kaina a sunkuye rufe cikin Laffaya 
leading dina yayi har zuwa sit dinmu nida shi still ban dago ba .shi ya taimaka min har na zauna .an bude taro da addua ,yau ba kida amma akwai mc .
isowar mommy akayi announcing inda suka zo dan bude fuskar amarya.adudu ne a gefenmu .mun siya bude fuskar amarya a kan naira million 2 naji anyi announcing ,tafi naji an dauka ,a hankali naji an yaye laluben laffayata,tare da dago min fuska,ido biyu mukayi da mommy ,saurin kallon kasa nayi da ido na  tare da gaisheta .welcoming dina tayi tare da mana addua zaman lafiya da kuma yar  nasiha. an cigaba da event peacefully kowa wacce daga family AK na zuba kyautar a cikin basket.shawara aka kira wata tsohuwa ta bayar inda ta fara mana nasiha nida uwargida
“daga karshe dai ina muku fatan zaman lafiya ,sannan amarya kar ki zake ,Abdulkadir  da hanadi ko ba komai yan uwane dik inda aka je aka dawo tare kika gansu .dagowa nayi na kalli wacce ke maganar sai a lokacin na qarewa wajan kallo sosai.mutane basu 40 ba gaba daya .su precious na hango a nutse a gefe ,ga abinci nan daga wani table
inda kowa ke serving Kansa.

murmushin yake hanadi take  ,tana daga gefe zuciyarta na kuna ,yadda taga Ak yana gyarawa farhana zaman laffayarta ,da yadda yake mata rada a kunne.sai kaffa kaffa yake da ita kamar kwai.duk wanda yaga AK yaga wanda ya tsunduma cikin soyayyah.yaya ramla ce ta hana hanadi zuwa table dinsu AK ,a cewarta farhana ce zata biyo hanadi har sit dinta,
hannun farhana yaya ramla ta ja har zuwa gaban table din da hanadi take ,gaba daya kallo ya koma kansu.da Sauri hanadi ta taso tare taro farhana into a warm hug.sit da jawa farhana ta zauna ,microphone mc ya mikawa hanadi ta mike tsaya fuskarta cike da murmushi  bakar abayar ta haska hanadi kuwa ,sai walwali take .barka da zuwa amarya ina miki fatan alkairi ,naji dadi kwarai da kk shiga cikin rayuwar papa,ina fata Allah ya bamu zaman lafiya baki daya,kausar da intisar yarankine ,ban miki iyaka dasu ba,haka zaliki ni sister dinkice ,duk abinda darling yake so nima ina tayashi sonsa ,welcome to the family once again
hanadi tace tana mikawa farhana hannu ,mikewa tsaye farhana tayi ,ba tare da bata lokaci ba hanadi ta qara hugging dinta karo na biyu.ba wanda zai ce hanadi bata birge shi ba a wajan ,hatta Ak yana gefe hanadi tayi mugun birgeshi,tafi aka fara wa hanadi,akwati ne guda mai tsada hanadi ta gabatar a matsayin gift din amarya ,haba take waje ya qara kaurewa da tafiii.anyi pics kala kala ,da amarya da dangin miji ,hanadi ta tattaro su kausar anyi pics dasu da amarya.
bayan an gama cikin main building aka shiga  magrib ta dusau ,salla zaayi a fara shirn kai amarya .inda nene kamar zata cire wuya sai kalle kalle take ,gashi an gabatar da ita wa mommy haba baa cewa komai .
part guda aka warewa dangin farhana ,inda anty nafeesa tace sai farhana ta qara wani wankan ta canza kaya kafin a kaita.kowa a dangin farhana yabon hanadi yake ,anatayiwa farhana murnar dacen abokiyar zama….gifts din da farhana ta samu a dangin mijinta an danka hannun anty nafeesa da adda sabrina .zasu tafi dashi gidan farhana .salla sukayi aka sake shirya farhana ,sunfito mommy’ da jamaarta suna falo aka qara gabatar da farhana gaban mommy  ,to ga uwargida dai a nan,kusan yar gidace, ko kunje kai amarya ba kowa a gidan ,tun dik an hadu a nan ,muma hutawa zamuyi yaya safiyya ta tsoma baki .ba komai hakan ma yayi cewar mami a mutunce. hannun farhana mami ta ja zuwa jerin motoci.

tafiyar 15 min ta kawo su gidan farhana dan ba nisa daga gidansu AK,kuka farhana take tin bayan barinsu gidan su Ak ,mami ce yanzu a gefen  farhana,bismillah shiga da kafar dama
kiyi addua kuma mami tace tana rike da hannun farhana.