ZAINAZAIN

05

by @jamilaumarjanafty

*ZAINAZAIN..!*
_(Is a love Story and Betrayal)_

*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janaftyshakira*❤️


*BOOK 1*

            0️⃣5️⃣

"Dr.Abubakar Saulawa yafi kowa Murna da wannan Sabon Hadin kai Tare da alkawarin Dake Tsakanin Hajiya Fatima da Hajiya Aisha,sai dai kuma ya katse musu Hanzari Wajen basu Umarnin kowacce ta Shayar da Abunda ta Haifa da kanta Ammh alkawarinsu na nan bai Tashi ba Da Suka nemi sanin Dalili sai yace musu Saboda Halin Rayuwa Ko bakomai Tunda Dukkansu Suna Raye ya Zama Dole kowacce ta Shayar da Abunda ta Haifa da wannan matsayar aka Tsaya Inda aka Mikama Fatima Zainullahi ta Shayar dashi Ita kuma Aisha aka Mika mata Zareena ta bata Nono kuma Dukkansu suka kama Bayan Sun gama ba Jaririnansu Nono ne bayan sun Samu Natsuwa aka Sallamesu suka Dunguma Zuwa Gida Cikin Tsantsan Farincikin da baki bazai iya Furta shi ba.

Kafin kace kwabo Haihuwan Tagama Karade Dangi kafin Suna ta Zagayo yan"uwa na Nesa Dana Kusa Sun iso kamar su Hannatu da Rukayyah Bashir da iyalansa Hakama Aliyu Shima Da nashi Iyalin Wacce Itama Cikinta Dan Kimanin Wata Shida ya bayyyana Dukkansu Sun Taru Domin Taya Dan"uwansu Murna samun karuwar ya"ya a karo na Biyu bayan Matansa Daya Aura Rana Daya.

Ranar suna ansha Shagali Abunda sai wanda ya gani bayan Raguna Harda sa Dr.Saulawa ya sa aka Kada Saboda Haihuwan Jikokinsa aka Rabama Takalawa kowa fa ya Shaida wannan Haihun matuka kuma kowa ya Fahimci yadda Dr Saulawa ya Dauki Haihuwan da matukar Muhimmanci Shi da Hajiya Mama.

Bayan Suna Baki da yan'uwa kowa ya koma Gidajensa aka bar masu Jego Maryama na Tare Dasu na Kula da yara Sai kuma Atine Dake zuwa Tana yima Su Hajiya Fatima wankan Tare da Umarnin Hajiya Mama ganin Maryam bawata Babbace bace Sai aka bar mata kula da yaran Wanda ko yake Kiransu da yan Biyu ganin Rana Daya suka Zo Duniya Kuma Duk da kowa Uwarsa ke Shayar dashi Ammh Da Zarar Kowacce ta gama Shayar da nata Hajiya Fatima Zata Karbe Zareena Itama Hajiya Aisha Zata karbi Zainullahi Har suna Rige Rige Wani Lokacin Maryama Ke ganin Dirarmar nasu Tayi ta bama Alhaji Usman in ya Dawo Labari Shi kuwa yana Jin Labari Nishadi da kaunar matan nashi na Kara Wutar Ruruwa acikin Ranshi...

Wata Hudu da Haihuwan su Zareena Safiya Matar Aliyu ta Sauka achan Abuja Ta Haifi Santalelen Danta Jajir mai kama da Ubansa Wannan karon ma Dr.Saulawa ya Saka mai Suna Wato HADDIR ALIYU ABUBAKAR SAULAWA..!

Tun Daga sannan kuma Babu Wata karuwa da aka Kara samu Sai Duka Suka maida Hankulansu Wajen kula da yaran da Allah ya basu,Bangaran su Zareena da Zainullahi kuwa Maryama ce keda alhakin kula dasu Har ma Sun Saba da ita,domin itace komai nasu Wankansu Saka musu kaya kula da Cin Abincinsu da kuma Cire Musu pampers in sun bata Duka itace Lokaci kadan Yaran suka Shaku da ita Bama Ita kadai Harda Abdullahi mijinta Sun Shaku Dashi Domin In Tagama aikinta Sassan su Hajiya Fatima kwasan Yaran take su koma Barayinsu Su tayi ta kula Dasu Ita da Abdullahi Tunda Shima ba wani aikin yake ba kula da Kifaye ne,da basu abinci Safe da Yammah Da ka gansu zaka Fahimci Suna Cikin Farinciki da Jin Dadin Rayuwa.

Bashir Bai Haihu ba Sai da su Zareeena Suka Shekara Biyar a Duniya Yayinda Haddir keda Hudu da wani Abun Sun Girma Babu Inda kafarsu bata takawa Har an sakasu a Makaranta,Lokacin da Iklima ta Haihu Tasha Wuya Sai kuma Jaririn ya Fito bashi da lafiya haka akayi Suna yaro yaci Sunan Dr Saulawa Wato Abubakar bai kai Wata Biyar ba Allah yamai Rasuwa Tun kuma Daga Lokacin sai ya koma in ta Samu Ciki Sai ta Dinga Barinsa Ko kuma Sai yakai Wata bakwai ta Haifeshi Ba Rai,Sakamakon Ita Ikliman Binciken Likitoci Sun gano Tana da Raunin Mahaifa Sosai Gashi kuma ta Fara Palanning kafin Ta Haihu Shi ya jawo mata matsalan Bashir ya Damu Sosai Domin a Lokacin yana Bukatar Haihuwar ammh kuma Sai Allah ya Nuna ikonsa Dole babu yadda Suka iya suka koma Suka Rungumi Junansu Tunda bai isa ya Gujema Ikliman ba Koma meya Faru Shine Silan komai.

Su Zareena Da Zain nada Shekara Bakwai Aduniya Zain kamar yadda Zareena Take Kiranshi Tunda bakinta bai iya furta Zainullahi din Sosai ba,sai Sunan Gabadaya yabi bakin iyayen nasu kowa da Zain yake Kiransa Ita kuma Hajiya Aisha Zain ne Tunda ya Fara koyon mgana ya Fara Kiranta da NENE shikenan kuma Sunan ya Bita ayayinda Zareena ke kiran Hajiya Fatima da UMMAN ZAREENA,saboda yadda Duk Duniya Hajiya Fatima Bata da Abun kauna da Tattali Irin Zareena Shiyasa Dr Salauwa Ya sakamata Umman Zareena sai kuma ya Bita har ya"yan suka kama Maryama kuma Mama maryama Abdullahi kuma Suna Kiranshi da Baba ne ayayinda Suke Kiran Alhaji Usman da Abba Tun Suna yara.

Duk da kowa ya Fahimci mahaifiyarsa ammh yarintarsu bai Hana Sun Fahimci inda suka Fi Samun kulawa ba,Kowanne sai ya fi Nuna Doki ga inda akafi Jansa ajiki,Zain yafi Son Nene Saboda itace komai nashi Sai ko Mama Maryama Umma Zareena kuwa komai ta samu yarta ce Zareena Ko ta kan Zain bata Bi Tana mai alkunyar dan Fari da kuma Kawaicin Nuna ita Zareena ce yarta Da Farko Zain Din ya Fara nuna Damuwarsa Sai kuma Daga Baya da Nene itama Ta Tare komai nashi Sai Shima ya koma Tamkar itace ta Haifesa ba Umma ba.

Mama maryama kuwa Tamkar Uwa Haka Suka Dauketa Domin Itace Komai nasu Sun Taso Sun ganta ne Ita da Baba Abdullahi sai suke kallonsu kamar wasu iyayensu kuma na Dabam Tunda Watarana ma nan Shashen Maryama Suke kwana In Tatashi aikinta Daga Cikin Gidansu zata Shashenta sai su makale mata Sai Sun Bita su kuma iyayen suce Tatafi Dasu Haka zasu Bita suje chan suyi ta Kirniya Abdullahi na Biye Musu Har barci ya Daukesu Maryama ta kwashesu zuwa kan gado ta kwantar Dasu bayan tayi musu addu"an Barci Cikin so da kulawa.

Gidan Dr Saulawa kuwa Suna yawan Zuwa Musu Weekend ko Hutu Duk su nasu baya Wani Dadewa Suna kusa da gidan iyayensu Haddir ne kulafunci Zuwa Hutu Bauchi Saboda Su Zain Wadanda Tun Suna Yara mafarin Abotansu ta Fara Su ukun Haka mafarin Rayuwarsu Ta Fara Da Shakuwa da kaunar Juna Barin Ma Zain da Zareena Tamkar yan Biyu haka suke wanu bai isa ya Taba Wani ba acikinsu Hakama Haddir sunfi Shakuwa da Zain sosai kan Zareena,ita Suna yawan Fada Tunda Tana ganin yana so ya nuna yafita son zain sai suyi ta Fada Sai Maryama ta Raba Fadan ko kuma Chan Gidan Hajiya Mama ko Atine su Raba Tsiyan Da karfi da yaji Haddir ya Dawo Bauchi yaki Abuja Dr.Saulawa yace su kyaleshi cikin yan"uwansa Dole suka barshi Alhaji Usman ya Dauki Haddir ya sakashi makarantar da  su zain suke zuwa mai Suna International School Bauchi,Iyayensa basu wani Damu ba Tunda Lokacin Safiya Tana Goyon yarta mace Da Ta sake Haihuwa mai Suna Hamdiya.

Kwatsam Megadin Gidan Alhaji Usman yazo ya sameshi kan Zai ijiye aikinsa yana so ya koma Garinsu Mahaifinsa bai da lafiya karfi ya karemai zai koma yayi Jinyarsa Hakika Alhaji Usman Yaji ba Dadi Saboda Sun Saba Da Yusha"u megadi ammh Uba ya wuce wasa Hakanan yayi mishi Fatan samun Lafiya ga Mahaifinsa kuma ya Hadamai Sha Tara na arziki Suka Rabu Faruwar haka sai Alhaji Usman ya Fara Tunanin Samun wani Megadin Jin haka yasa Maryama ta Shawarci Mijinta kan me zai Hana Shi ya karbi Gadin Yayi Tunda dai ba wani aiki yake yi ba karamcin Su Alhaji Garesu yasa Ya amince mata kuma ya samu Alhaji Usman din da mganar da Farko yaso yaki Tunda ya Nuna Tamkar kani ya Dauke Abdullahi Shi kuma ya Dake sai yayi mgana dai Har ta kai ga Dr.Saulawa Da Mallam Umar Shi Mallam Umar shi ya kashe mganar inda yace Sai dai In Usman bai yarda da Abdullahi ba Ammh in ya yarda Dashi ya barshi yayi mai gadin Tunda Ba wani Abu yake ba Dole Alhaji Usman ya Amince ammh Har Cikin Zuciyarsa baya Kallon Abdullahi Da maryama wasu Bare yana kallonsu nr amatsayin Wasu Shakikan yan"uwansa..

Faruwar  Haka da wasu Wattani Ciwon Daji mai Tsanani ya kwantar da Mallan Umar da Farko Abun kamar Ba Ciwon Daji ba Sai da Dr.Saulawa yayi ta Shige Da Fice dashi a asibiti kana aka Fahinci Ciwon nashi Duk da kokarin da Dr Saulawa ya Dinga yi Bai Hana Mallam Umar Rokon alfarman Su barshi ya koma ga Ahalinsa yayi Jinyar achan ba,Yana Tunanin Ciwonsa bana Tashi bane Da Farko yaki Sauraransa ammh ganin yadda ya dinga Rokonsa sai bai ki ba Lokacin da Mallam Umar da Atine zasu koma Gada da Zama Gabadaya Ahalin Dr.Saulawa Sun Girgiza Sakamakon Sabo Ammh ba yadda zasu yi Tunda Mallam Umar ya nuna musu ko basu ga Abdullahi da Maryama nan Tare dasu kuma in da Rai  ba"a Rabu ba.

Suna ji suna gani Haka zamansu ya yanke a garin Bauchi Ashe kuma ta Har Abada ne,Da komawarsu Garin Gada da Rasuwar mallam Umar Kwana Ashirin ne yace ga garinku ne hakika ba Yan"uwan Mallam Umar kadai sukai Rashi ba Hadda Dr.Saulawa da Duka iyalansa,domin dasu akayi zaman gaisuwar har akayi bakwai Saboda Atine wacce Tunda Taji Mutuwar Mijinta ta yanke jiki ta Fadi ko da ta Farfado ba Baki Ance Jininta ne yayi bala"in Hawa.

Bayan addu"ar Bakwai su Hajiya Mama suka Dawo Bauchi Harda Abdullahi da Maryama Saboda Yara,Wanda Suna Gida Tare da iyayensu sai dai suna Ta Kuka da kiran sunan maryama din Da Abdullahi,Allah mai Gagara Misali Rasuwar mallam Umar da Wata Biyu itama Atine ta Bisa kuma ta Rasu ne Akarkashin Kulawan Likitocin asibitin na Dr Saulawa Tunda yaje garin yaga Halin Datake Ciki ya Daukota ashe bazatayi Tsawon Rai ba Duka Duka kwanta Biyu a asibitin tace ga garinsu nan.

Duka Chan suka Tafi Gada Tunda Dangin nata sun Nuna Chan suke so ayi mata Sutura Hakika Hajiya mama tafi kowa jin Mutuwar Atine awannan karon sai kuwa Abdullahi Daya Dawo Maraya Sadakar uku kawai Sukayi suka Dawo ammh Sun bar Abdullahi da Maryama achan sai da akayi bakwai suka koma Cike da alhinin Rasa Iyayen nasu Domin Ita kanta Maryama Bayan yayarta Halima bata da kowa sai iyayen Mijinta Abdullahi.

Bayan Dawowarsu ne kuma Umma Zareena ta Fara Laulayin Ciki wannan karon ita kadai ce Sai kuma Matar Bashir itama Iklima da ta Fara Nata laulayin Cikin,Kwanci Tashi ba wuya a wajen Allah Umman Zareena ta Haihu Da kwana Uku iklima ta Haihu kuma Duka maza Suka Samu Bashir sai ya maida ma Dansa Sunan Dansa na Farko Daya Rasu Abubakar hakama Abba Usman Shima Abubakar din ya saka ma nashi Suna Kiranshi Sadiiq Babba Yaron Wajen iklima kuma Suna Kiranshi Sadiq karami.

Wannan karon ma Nene tayi Ruwa Tayi Tsaki kan Abata Sadiq Babba Har Dr.Saulawa da Jikokinsa ke kira Alhaji Tsoho yayi mata Lakabi da Nene Uwar Maza Domin Allah ya Doramata Son Haihuwan ya"ya Maza Sai dai kuma Allah bai bata ba Shiyasa,Zain da Sadiq babba Suka koma Tamkar sune ya"yanta Ita kuma Umman Zareena Dama Uwar matace Domin Itama Tafi son ya"ya mata Sai aka Raba kowa yaja Nashi Cikin zaman lafiya da kwanciyar Hankali.

Sadiq Babba nada Shekara Daya da wani Abu Ciki ya Bulla ajikin Maryama Murna Wajen Nene da Umman Zareena Ba"a mgana kamar su Za"ayi ma Haihuwan,Ita kanta Maryaman Tana Farinciki Domin Sosai Take son ganin kwan ta adunya koda Kwara Daya ne,Duk da Su Zareena Sun Debe mata wannan kewan komai Mama Maryama kinga Haddir ko.? Mama maryama Kinga Zain ko..? Mama maryama kin ga Xareena ko..? Aikinta kenan Cikin Rabon Fada da alkalanci.

Tunda Cikinta ya Fito yaran suka Fahimci Tana da Ciki suka kama Murna Kada ma zain yaji labari Domin Tun Sanda yaga Cikin Mama maryama yayi Girma ya Tambayeta ya yaga Cikinta yayi kato ko Bata da lafiya ne..? Lokacin Tana Shashen Su Umman zareena ne Nene ce Ta bashi amsa da Cewa kani za"ayi musu ko kanwa Yana jin Haka ya Bata Rai yace Shi Gaskiya Mata yake so Mama maryama ta Haifamai Kowa sai da yayi mamakin kalaman yaro Dan Shekara Takwas da Wani Abu sai dai Ba Abun mamaki bane sanin Halin manyance irin ta Zain kamar wani Babba Kowa ya Bude Baki Yana kallonsa Sai Mama Maryama Taja Jikinta Tana Fadin"Karka Damu D'ana zain...Nayi maka alkawarin in mace na Haifa Na baka Ita matsayin mata Ko da bana Raye in kuma Namiji ne zan baka shi a matsayin Karamin kani Wanda zai iya ma Yayansa Biyayyah Har karshen Nunfashimsa..!

Kowa ya Dauka kalaman Maryama da Zain amatsayin Wasa ne Har da Alhaji Usman ya Dawo Matansa ke gayamai yana ta Dariya,Ashe a Bangaran Maryama Da Zain ba Haka bane Shi da Gaske yake Cikin yarinta ita kuma Da gaske take Cikin Son Cikamai alkawarin Tana jin Babu Abunda zata mallaka wanda ba zata iya mallaka ma Iyalan Dr.Abubakar Saulawa ba.

Tunda ga Lokacin Komai Zain ya samu sai yace na Matar sane wanda Mama Maryama Zata Haifamai ko makaranta yaje baya kashe kudi wai yana Tarawa zai Siyama Matarsa Babyn Wasa,Komai dai ya Samu ko naci ne sai ya Tsakura yace na Matarsa Wacce Mama maryama Zata Haifamai ne,Tun ana Daukan Abun Wasa Har dai aka Fahimci Zain Da gaske yake Labarin kuma yakai ma Kowa,kowa kuma sai Dariyan Kuruciyar Zain yake da Shirmensa Lokacin da Cikin Maryama ke Wata na Shida Umman Zareena itama ta samu Ciki kuma kusan Lokaci Daya Suka Fara laulayi da Nene Wannan karon ma.

Cikin kwanciyar Hankali Duka Suka Cigaba da Rainon Cikinsu Har Cikin maryama ya Shiga Watan Haihuwarta sai Yayarta Halima tazo akan Tana son Tafiya Da maryama Chan Gida taje ta Haihu ammh Sai Alhaji Usman ya Hana yace Maryama Tamkar kanwa take garesa Saboda Haka anan zata Haihu Karamci Irin nasu yasa Halima Batayi Gaddama ba Ta Tsaya ta kwana Biyu Ranar Datayi Shirin komawa aranar Maryama Tatashi Da naguda aka kwasheta Zuwa asibitin Mallakin Dr Abubakar Saulawa.

Suna zuwa aka karbeta Sai Dakin Haihuwa Duka Gidan aka Tafi Umman Zareena da Nene,Sai Halima da Baba Abdullahi Da Direba Hajiya mama Tana Gida bata Taho ba Sai Dr.Saulawa Wanda Dama yana Cikin asibitin Alhaji Usman Daga baya Yazo Asibitin ganin Har Wajen Yammah Maryama Bata Haihu ba Sai Aka yanke Shawaran yimata aiki Zuwa Lokacin Hajiya Mama ta iso Ita dasu Zain Wadanda Tunda suka Dawo makaranta aka kaisu Wajenta Suke mata kuka Suna ta Kiran Sunayen iyayensu Dana Mama maryama ganin Haka yasa Ta lallashesu Ta Fada musu suyi ma Mama maryama addu"a Tana asibiti zata Haifa musu kani ko kanwa Jin Haka yasa Zareena da Haddir suka Fara Murna Shi kuma Zain sai ya Fara kuka yana Fadin Shi ba kanwa za'a Haifamai ba Mata da kuma kukan sai an kaisa yaga Mama Maryam Dole Hajiya Mama ta Tarkato su suka Taho Tare Duk da Dr.Saulawa Nata Fada ammh ganin yadda Yaran suka Sha kuka ne sai suka bashi Tsausayi.

Cikin Ikon Allah ana Kokarin Saka ahannu akan Takardan da za"ayi ma Maryama aiki Allah ya Sauketa Lafiya Inda ta Samu Haihuwar yarta Mace mai kama da Ita sak,sai Kuma Duhun mahaifinta Data Debo Saboda Maryama Faraace Sosai Sabani  Abdullahi Dayake bakin Fata Sai da aka gama gyarata ita da Abunda ta Haifa kana Nurse Ta Fito da Jinjiran a Hannunta Da Halima ta Faracin karo Zata mikamata Zain yayi azamar Mika Mata Hannu yana Fadin Ta bashi matarshi Tsaye Tayi tana kallonsa Cikin Mirmishi Dr.Saulawa yace ta mikamai Tako mikamai ya karba kamar zai Fadi Halima ta tareshi suka koma Suka Zauna kowa ya Kura mishi ido ana kallon yadda ya kurama Jinjiran ido yana kallonta da wani Mirmishi Kafin ya Dago yana kallon Abbansa Cikin Yarinya yace"Abba me sunanta...?

Kafin Alhaji Usman ya bada Amsa Abdullahi ya bashi amsa da Fadin"Maryama Ta gayamin in ta Haifi mace Sunan Yaya Halima Take son asakamata Saboda Haka Alhaji Dakta kayi mata Huduba da HALIMATUS SA"ADIYA..!

Gabadaya Murna Ta kama Halima wacce ya"yanta ke Kiranta Goggo Halima Cikin Jin Dadi Take fadin"Masha Allah..Allah ya Raya Halimatu.."Zain kawai akaji yace"Ba Sunanta Halima ba Abba..Ni Matata irin Sunana gareta..!?
Cikin mamaki Nene tace"Irin Sunanka Da'n Nene..? Wani Suna kenan..?

Cikin Kura ma Jinjiran ido yace"Tunda Sunana ZAIN ita kuma Sunanta ZAINAH daga yau ba Halima ba...Kunga Zainazain kenan..!gabadaya al"ajabi da Mamaki ya kama kowa Dr.Saulawa yana kallon Zain da wani Farinciki acikin Ransa kafin ya Dafa kansa yana Fadin"Allah ya maka albarka...Karka Damu Sunanta Halima ammh Kai mijinta me kuma ka zaba mata Suna ai Shikenan kowa ya Shaida Sunan Matar Zain Zainah ko..?

Yafada yana kallonshi Washe baki yayi yana Daga sai Abun ya basu Dariya Dakyar Dr.Saulawa ya iya karbanta Suka Dunguma Dakin da aka maida Maryama Suka Iske ta Farfado agabanta yayi ma Jinjiran Huduba da Halima ya Dago Yana Fadin"Allah ya Raya Halimatus Sa"adiya..!

Karaf Zain yace"Ba Sunanta Halima ba Sunanta Zainah nace muku..!Maryama ke neman karin Bayani Nene ta Koramata yadda akayi Dariya Tayi Tana Fadin"Gaskiya ne Yarona..Sunan da aka Zabamata yayi Daidai da..Sunanka ina Fatan ko bayan Raina zaku Tabbatar da Halima amatsayin matar Zain..?

Tafada Tana Tsare Duka yan Dakin da Ido Kowa sai yaji Abun Wani iri Baba Abdullahi ne yayi Mirmishi yana Fadin"Kema yarintar Zain din zaki mana..? Kai ta girgiza Tana Fadin"Ba yarinya bace..Ku kalli Idanuwansa Tsabar gaskiyansa yake Fada..Nidai Nayi alkawarin Tun Kafin Ta Fito Duniya na Bama Zain ita amatsayim Mata Har Abada Ko Bayan Raina Abdullahi ka Tayani Sauke nauyin Dana Dauka..!

Kowa adakin Sai da Jikinsa yayi Sanyi Dr.Saulawa ne yace"Karki Damu Maryama...Insha Allahu da kanki zaki Hada Hannun Zain da Halima amatsayin ma"aurata."Wani Sanssayar Miemishi Tayi kafin tace"Allah yasa Ina Fatan Haka.."Daga Haka bata kara cewa komai Suma ba wanda ya kara mgana sai aka koma Raba Rigima Tsakanin Zain da Zareena Inda Take Rigiman sai ta Dauki Halima karama ammh Zain ya Dafe gadon da Maryama ke kai yace bamai Taba mai Mata Tun Abun nashi na basu Dariya Har suka zo suka Tabbatar ma kansu zain Da gaske Acikin Ran Dr.Saulawa kuma yana Ta auna Abubuwa afili ya Furta Haka Allah ke al"amarinshi Daman.

Kwana Daya Maryama Tayi a asibiti Aka sallamota ta koma Gida aka cigaba da karban yan Barka Gabadaya Kulawanta ya koma Karkashin Nene da Umman zareena Duk da suma Suna Fama da kansu Goggo Halima Sai dai kallo Domin ko Tace su barshi Sai suce sai sunyi ai maryama Tamkar kanwa Take garesu Hakama Hajiya Mama Tana iya bakin Kokarinta,Zain kuwa ansha Fama Dashi Domin Tunda akayi Haihuwan sai Ansha Fama Dashi yake zuwa makaranta sai ya Fara kukan Sai dai ya Tafi da ita da Dubara yake Tafiya yana Dawowa kuwa Shashen Maryama yake yada Zango Daga ma Karshe chan ya koma da kwana Saboda Zaina Ba Wanda ya Damu da Hakan Domin Kowa yana ganin Maryama da Mijinta yanzu Suna Cikin Ahalin Dr.Saulawa Tsudum.

Dr.Saulawa da ya"yansa sun ma Maryama kara Sosai Da Abun arziki Sai wanda ya gani Musamman ma Alhaji Usman da Matansa Sunfi kowa Rawan gani Haka da yan Gada suka zo Suna suka koma da Fadan Irin Dimbin karamci da Dattako irin na Iyalan Dr.Saulawa Goggo Halima ma Bayan Suna Ta koma Itama da Sha Tara na arziki Tana Ta Godiya Aka bar Maryama da yarta Halimatu Sa'adiya wacce Taji Tudu Biyu Sunan Goggo Halima kuma Sunan Baba Atine na gaskiya.

Kwanci Tashi ba Wuya awajen Allah Zaina nada Wata Shida Aduniya Nene ta Haifi Yarta mace Wacce taci sunan ZAFEERA bayan Haihuwanta da Kwana Hamsin Ita kuma Umman Zareena ta Sauka Wannan karon ma Namiji ta samu Yaci Sunan Mallam Umar suna Kiransa Faruq,kamar dai yadda Tsarin yake Nene uwar Maza Taja Nata itama Umman zareena Uwar mata taja nata Tunda Lokacin Zareena ta Girma Suna Cikin Shekaru na Goma da Haihuwa sai Tattalin ya koma kan Zafeera Yadda kukasan kwai haka Umman Zareena ke ji da Zafira kamar Tsoka Daya amiya Zain kuwa da karfi Da yaji ya zama Dan Shashen Maryama Saboda zainarsa Reno kuwa Tare sukeyi da Maryama Tun baya Iya Daukanta Har sai da ya iya Haka zai zauna yana ta mata wasa Tun Kafin ta isa Cin Abinci Zain ya Fara bata kayan zaki Ko Iyayen nashi na Fada Maryama Ta kanyi Mirmishi Tace su kyaleshi Mutum da matarsa Saboda Hakama Ta Riga ta ganeshi Da Taji muryansa zata Fara wuntsila kafa Tana Babban Dariya irin na Jarirai yana Daukanta kuma Shikenan Haka zasu yi ta Rigima da Zareena kan sai ya bata ta Dauketa In Kuma akaci Sa"a ya bata Zareena na Daukanta sai ta Fara kuka Sai Zain ya Fara Dariya Haddir dai yana Gefe Shi baima Cika cewa zai Dauka ba Ganin yadda Zain din ya mamaye komai Sai dai yayi tama Zareena Dariya ita kuma Taji Haushi Ta Fara kuka Maryama Ce mai Raba Fada ta kuma Shiga Ciki Tayi alkalanci.

Shekaran Halima Daya da Wattani Maryama ta kara samun Ciki Sai dai kuma yazo da matsala Tunda Tayi ta Ciwo sai da akaje asibiti nan aka gano Tana da Cancer Mahaifa Hankakula Suka Tashi barin ma Abdullahi,Ammh Dr.Saulawa da Alhaji Bashir sukayi Tsaye sai da akayi mata aiki taji Sauki Bayan an Fitar da wanchan Cikin,Dalilin wannan Ciwon sai Dawainiyar Halima Ya koma Hannun Umman Zareena Tunda Allah ya Doramata kaunar Yarinya Ta Hadasu ita da Zafeera Tana Rainonsu Tare Zain na Tayata Domin Dakyar ma ya bari Umman Zareenan ke Daukan Halimar har ta goyata Ganin Mama Maryaman Bata da Lafiya ne Shiyasa.

Bayan Taji Sauki ma Hakan bata Chanza Zani ba sai dai in Tana kuka akaita Maryama Ta bata Nono a maida mata Ita,Cikin ikon Allah ba Dadewa Maryama ta Sake samun Wani Cikin Wannan karon Da Sauki Abun Sun dai koma asibitin anyi Gwaje gwaje aka Tabbatar da Maryama zata iya Haihuwa ba Matsala Da haka tacigaba da Rainon Cikinta Gefe Daya kuma Dawainiyar Halima yana Hannun Umman zareena Cikinta na Shiga wata na Shida Ta Yayeta Ta Damkama Umman Zareena Ita,wacce ake ma Lakabi da mai Rainon Yan Biyu Sakamakon Zafeera akwai Girman Jiki Har ta kamo Zaina a Girma Ita har ta Fara Takawa Halima din ce Take Ta Rarrafe.

Acikin Wannan yanayin ne Wani al"amari ya Faru wanda iyalan Dr.Saulawa suka kasa mantawa Dashi Shine Wata Ranar Asabar da Misalin karfe 2:00pm na Dare yan Fashi Suka Shigo Gidan Alhaji Bashir da Manyan makamai Lokacin da Suka shigo Gidan Abdullahi ya Tashi gaban get ya Shiga Gidan Wajen Maryama Dama Hakan yake yi sai asuba kuma yake Dawowa,Duka ya Kulle get Din Haurowa sukayi suka Shigo kamar Wasa Dama Tunda ya Shiga Ciki bai kwanta ba,Alwala ya Dauro ya Fara Sallar Nafila yakai Raka"a na Biyu yaji motsin Takun Kafafu Da Sauri ya Sallame ya Dauki Fitilansa da Sandansa zai Fita Sai maryama ta Farka ganin zai Fita yasa Ta Tambayeshi sai yace mata yana Zuwa ya Fita da Sauri Yana Fita kawai yaci karo da Wani katon Mutim Cikin bakaken kaya ya Haskeshi da Fitila yana Tambayan waye Kafin ma yaji wani Abu Daga Bayansa yaji an sakarmai Harshashi aciki nan Take ya Fadi matattace Jin wannan karan Harbin Shi ya Rikita Maryama Ta Fito Da Gudu Ga Ciki Tana kuka Itama nan Take wani ya sakarmata Harshashi aciki Itama Ta Fadi ba Rai.

Innalillahi Wa"inna illairaju"un wannan ahali Sun ga Tashin Hankali kwarai yan Fashi Sun Shiga Har Shashen Alhaji Usman basu dai kashe kowa ba ammh Sun Karbi kudaden Daya Dawo Dasu Daga Tafiya yana Shirin Washegari zai kai Banki,sai kuma Dan kunnayen Zinaren su Nene da wasu kudaden Dake Hannunsu Sukayi ma Alhaji Usman Dukan Tsiya sai da ya Suma kana suka Tafi Su Nene suka Rude sai kuka Ga su Zain Suma kukan suke Zaina da Zafeera kuwa sai kuka Suke na Tashin Hankali Umman Zareena ita Tayi Hausan Kiran Wayar Dr.Saulawa ta Na kuka Tana gayamai Halin daSuke Ciki Cikin Tashin Hankali Shida Hajiya Mama suka Nufo Gidan Domin Daman Kaf an anguwan ba wanda bai ji karan Harbi Biyun Da sukayi ba.

Abun Tsausayi Suna Zuwa Gidan suka ga Get a wangale Hankalinsu ya Tashi ai basu Rude ba sai da suka ga gawan Maryama da Abdullahi kwance afarfajiyan Gidan cikin Jini Sai Zuciyoyi Suka Raunana Idanuwa Suka Zubda Kwallah Su Nene sun Rude matuka ga Halin da Suke Ciki ga mutuwar Maryama da Mijinta Sun Rasa Ina zasu Tare Hawayensu ne,Wanda ke zuba ba kama Hannun Yaro ganin Alhaji Usman baya Cikin Hankalinsa ne yasa aka Tattarashi Zuwa asibiti Dr.Saulauwa ya Kira yan Sanda suka zo Suna Ta Binciken gawan su Maryama Abun gwanin Ban Tsausayi Hajiya mama Kuwa Ta Rude sai kuka Take tsakanin ita dasu Nene an Rasa mai bama wani Hakuri.

Sai da yan Sanda suka gama Bincikensu kana suka Tafi da Cewar Insha Allahu za"a kama Yan Fashin da sukayi wannan aikin Sai alokacin Dr.Saulawa ya iya Kiran Chan Gada suma ya Sanar dasu wannan Mugun labari Fadar irin Tashin Hankali da Suka Shiga bata baki ne Mota Guda sukayo suka zo Goggo Halima da Hajiya Mama suka Yi ma Maryama Sallan gawa yayinda Wasu mazan Daga Gada sukayi ma Abdullahi wankan gawa aka Sallacesu Zuwa Gidansu na Gaskiya Allahu akbar.

Duka da su Bashir akayi Sallar gawan Domin Duk sunzo Hannatu ne kadai bata zo ba Ammh Rukayyah itama ta iso Tuni Zukata suka Raunana Sai ma in ka Tuna da Ciki Maryama ta koma ga Allah ga Yarta Karama wacce ko Shekara Biyu bata gama kaiwa ba Sai kaga yadda Zain da zareena da Haddir suke kuka Kamar Ransu zai Fita Duk da Suna Yara sun Fahimci Mama Maryama da Abdullahi Sun Tafi Tunda Hajiya Mama Ta gayamusu sun Tafi inda ba Dawowa Umman Zareena Goye da Zafira Zain kuma ya kama Halima ya kamkame yana kuka Abun gwanin ban Tsausayi.

Anan Gidan Alhaji Usman aka yi Karban gaisuwa Duk da Shi yana asibiti sai da akayi uku ya Dawo Gida Domin ba Laifi Ya Daku Allah yasa ba karaya sai Gocewar Kashi,Shi kanshi Yayi kuka Zuciyarsa ta Raunana da Wannan Mummunar kaddaran Data Fada musu,Sai da akayi bakwai kana yan Gada sukayi Shirin komawa nan Goggo Halima tace abata Halima ta tafi da ita ta Riketa,Tana ta kukan Bayan Maryama Bata da kowa Duka iyayensu Sun Rasu Su bata ita ko In ta ganta zata Dinga Tunawa da ita Da Farko Dr.Saulawa ya karbi Rokonta yace Umman Zareena ta Hadoma Halima kayanta ta bama Goggonta Tatafi da ita Umma Sai ta Fara kuka Tana Rokon Itama abar mata Ashe Zain yalura Da Sanda Goggo Halima Ta karbi Zainarsa Sai ya Fara kuka yana Kokarin son Karbanta Duk yadda akayi Tunanin Abun ya Wuce wasa Dr.Saulawa yabama Umman Zareena Hakuri yace Ta barma Goggo Halima Rikon Halima Tunda Ita ga Zafeera ma Tana Raina Hakanan ta Hakura Tana ji Tana gani Ta Hado kayanta tabama Goggo Halima Dakyar Aka Rike zain wanda ke kuka yana Birgima kan ba"a Tafi da Zainarsa ba Ganin Har Goggo Halima ta Shiga Mota sai Numfasa ya Fara Daukewa kafin kace kwabo ya Suma Wannan Dalilin Shi Ya Hana Goggo Halima ta Fasa Tafiya da Halima ta Sauko Ta Damkama Umman Zareena ita tana kuka Tana Fadin'Naga Soyayya da kaunar Halima I idanuwan wannan yaron Tun Ranar datazo Duniya..Bazan so na Raba wannan kaunar ba..Gata Hajiya Fatima Allah ya baki ikon Riketa da Amana..!

Ba wanda Baiyi kuka ba awajen Zain kuwa yana Farfadowa Daya ga Zainarsa sai ya Karbeta ya Rumgumeta yana ta kuka Zareena da Haddir ma suka Taru Kusa Dashi Suma Suna kuka ahaka yan Gada suka koma Chan garinsu daDacin Mutuwar Maryama da Abdullahi.