JINSI BIYU

5&6

by @autaralheri

💦💦 *JINSI BIYU*💦💦


Romantic love with sexy story 🥳🥳

    Writer by
        
          Autar alheri✍️

💦💦💦💦
💦💦💦
💦💦
💦

Marubuci yar 👇
IZZAR MULKI
AL'AJABIN MASARAUTA
ME & MY LION 
SIRRI ƁOYAYYE
    AND
OTHERS 🤷

Yau kuma munzo da wani sabon kabcen💃 wanda bazance komai akaiba sedai kawai mu kabta aciki masu karatu domin ku ganewa idonku👀 abinda yazo dashi. 

*HAPPY SALLAH OLL MY LOVELY MUSLIM*🤝❤️

Bismillahirahamanirahim. 


Ya Allah yadda zan fara book ɗinnan cikin amincinka da yaddarka rabbi Ka nunamin nagama lpy cikin sahalewarka alfarmar sayidissadati. 🤲

Book 1

Page 1&2

"Ƙasar Siriya, wata hamshaƙiyar masarauta na hango wanda faɗin girma da tsaruwarta ɓata lokacine, sedai kallo ɗaya zakama masarautar ka tabbar da cewar babbar masarauta ce me ɗimbin tarihi a cikin ƙasar Siriya, masarauta ce wadda babu kamarta a duk faɗin ƙasar. Bayi da hadimaine keta kaikawo a farfajiyar masarautar, yayinda fadawa da barori kowa keta aikin gabanshi. 

Daga gefe kuwa wata matashiyar mata ce ke tsaye cikin shiga ta alfarma hadimai kusan goma na zagaye da ita. Sun tattara rigar jikinta me ɗauke da ado na zallar kwal sunriƙe ahannunsu kowacce kanta a sunkuye tana jiran umurnin daga wannan shaha rarriyar gimbiyar. 

Gefe ɗaya kuwa wata babba ce daga cikin hadiman gidan ke zube aganta  tana sauraren abinda take faɗa cikin girmamawa... Cikin harshen Larabci take faɗar "lulah inaso kikawowa memarta yarinya ƙarama wadda zata kula da part ɗinshi, kana kihaɗo da manyan mata ko uku ne kafin jakadiya tasamu lafiya, ina Fatar kin fahimta. "Eh ranki yadaɗe yadda kikace hakan za'ayi yanzu zankawo in sha Allah. Wannan gimbiyar batace komaiba ta juya zuwa cikin part ɗinta, itakuwa shugabar hadimai tanufi ɓangarensu domin cika umurninta. 

Cikin sauri wata hadima tashigo cikin parlo tare da zubewa ƙasa tana faɗar "hutawarki lpy uwar gijiyata ga gimbiya balilah tana neman izinin shigiwa. Hannu kawai datti juwar ta ɗaga mata batare da tace komai ba idonta kace akan tangamemen agogon zinarin dake manne abangon parlo. 

Cikin sauri hadimar ta koma batafi minti biyu datafiyaba sega wannan matashiyar data gama bawa shugabar hadimar umurni tashigo parlo. Gimbiya balilah kenan uwar gidan matashin sarkin Siriya na wannan lokacin, MEMARTABA SARKI AFIF MUHAMMAD IDRIS NA 6. Ƙarasawa tayi wuri  wannan dattijuwar kana tazube agabanta tana fadar "barka da hutawa Lilli. "Hannu kawai Lilli taɗaga mata cikin izzi da ƙasaita irinta sarauta ta ɗago tana kallonta kafin ta ɗauke kanta cikin isa tace "balilah. "Na'am lilli. Ta amsa cikeda girmamawa. "Miyasa kika kwana turakar afif kwana takwas da suka wuce? Ta tambaya fuskarta ahaɗe tamkar hadari. Gaban balilah ya yanke goma yafaɗi cikin tsoro da farga take duban Lilli Abu kamar aljana kome akayi seta sani ko bayan idonta akayishi kuwa. " Amsarki nake jira bawai kimin shiruba balilah, shin ko kinmanta haɗarin dake cikin kwana turakar afif ne? Miyasa kikeson jefa rayuwarki cikin haɗarin dazaki kasa fita ne? Shin tun farko bana garga ɗeki akan haka ba? To miyasa zaki aikata? Taƙarasa zancen afusace. 

Cikin mugun tsoron tsohuwar gimbiya balilah tace "tuba nakeyi Lilli wlh bansan yadda akayi bacci ya ɗauke ni ba sedai ban ƙarasa kwana acanba domin koda na farko a sashena naganni shiyasa nashiga kokwanto ko ba acanne bacci ya ɗaukeni ba amma amin aikin gafara bazan ƙara kwatanta hakanba. 
Tana magana tana kuka domin tafi kowa sanin haɗarin lilli. 

Adake lilli tace "gargaɗi na ƙarshe agareki domin kinsan wannan ko umurnin waye kuma shi ne wanda ya ɗaukeki yamaidaki turakarki domin bashine abinda kikajeyiba gidanshi, ayanzu iname umurtarki kimaida hankali kan aikinki domin kusamu kyakkyawar rayuwa keda mijinki na nangaba idan kuma ba hakaba kiƙarasa rayuwarki akushewa yayinda yaruwar ɗana zata haska tamkar hasken rana asararin samaniya. 

Cike da ladabi gimbiya balilah tace "in sha Allah zan kiyaye lilli domin ina matuƙar kaunar deen acikin rayuwata. Wani mugun kallo Lilli tayi mata kafin tace "ya aikin dana sakaki ai gabatar? "Eh an gabatar domin kuwa yanzu nagama bawa shugabar hadimai umurni. Shiru lilli tayi bata ƙara cewa komai ba hakama gimbiya balilah dake cikin fargaba. 

Nijar 

Dakudun bala'i miƙiyar ke shillawa asararin samaniya gudu takeyi sosai har seda ta sauka acikin magar ƙamar ta Turai. Tana sauka acikin magar ƙamar hankalin kowa yadawo kanta, hadda masu tsaron fursunonin ma duk seda suka juya suna kallonta domin dama can mikiya tsuntsuwa ce me matuƙar kyau da ɗaukar hankali acikin tsuntsaye. 

Ahankali ta taƙanta har inda fursunoni kecin abinci tana tsintar na ƙasa tanaci, abin mamaki wanda ba'ataɓa ganiba agun wannan tsuntsuwar, sedai basu damuda sakanba atinaninsu tasauka domin buƙatar abinci. Shi yasa kowa ya maida hankalinshi kan abinda yakeyi aka  ɗauke ido akanta. Kusan minti biyar, ana hakan, sedai abin mamaki kamar daga sama suka ga ta ɗauke wani matashin saurayi tayi sama dashi tamkar walƙiya. Ihu ya saka domin yayi masifar tsorata. Cikin mugun mamaki da ruɗani mutane sukayi kanta yayinda ma aikata suka shiga harbinta tako ina amma sam kamar abanza sukeyi, cikin ƙanƙanin lokaci talula sararin samaniya taɓacewa ganinsu Sam. Aiko cikin ƙanƙanin lokaci labari yakaraɗe gabaki ɗaya ilahirin magar ƙamar cewar mikiya ta ɗauke Amar. Wannan labarin yayi bala'in jijjiga mutanen magar ƙamar domin kuwa dudda akasan cewar mikiya tsuntsuwace me masofar ƙarfi acikin tsuntsaye amma sam babu me tunanin zata iya ɗauke mutum sukurun tayi sama dashi. Anandai aka gargaɗi kowa akan cewar arufe wannan labarin karma yafita agari balle ma'aikatam susamu matsala, tun da damacan wanda ta ɗauke ɗaurin rai da rai ne akanshi, sabida hakan babu wanda zeyi tunanin fitarshi balle rashin ganinshi yazame musu matsala. 
Fofa.

Gudu sosai wannan tsuntsywar ke cillawa asararin samaniya seda tabar gabaki ɗaya ilahirin ƙasar Niger hakan take gudu dashi harta nausa cikin chadi tukunnta tafara saukowa ƙasa hankalin harta sauka cikin gari ɗan Sena da gari kaɗan kana tasauka ƙasa gaba ɗaya tasaukeshi, wanda yarigada yasuma shi tuntuni, ruwa ta ɗebo da bakinta taso tazuba mishi, aiko yafarka afirgice tana zare ido tamkar wanda yayi wa sarki ƙarya cikin mugun tsoro da firgici, yanabin wannan mikiyar da kallo me ɗauke da maɗaukacin tsoro... Juyawa tayi deda taɗanyi nisa dashi kaɗan kana rayi wata irin girgiza segaya ɗai ta koma matashiyar muduryar yar buzuwa me masifar kyau da ɗaukar hankali.. ido yawaro cikin mugun sabon tsoro da ɗimauta yake nunata da yatsa baki narawa yace "za..za..zarah. wata irin dariya takece data ita wadda taƙara fito da asalin kyawunta me fisgar ruhu da zuciya dudda take ƙaramar yarinya amma hakan be hana kyakkyawar ƙirarta bayyana ba, seda tayi me isarta kafin tace...! 

















Autar alheri ✍️