Biyu Babu

_________Page 3&4

by @hammaabdul

       ⏳⏳ BIYU BABU ⏳⏳

MALLAKIN:DAN SALMA

~MARUBUCIN"~

*INUWAR KAKA

FANSAR JINI

AZUMIN LADO

GURBIN MASOYA

AND NEW

BIYU BABU

*

_____________3&4

​Kafin macen ta tura ƙofar gabaɗaya, Adnan ya lallaba ya faɗa ƙarƙashin babban teburin katako na ofishin. Ya takure kansa, ya riƙe numfashi har sai da ya ji ƙirjinsa yana neman fashewa.

​Ƙaras! Ƙofar ta buɗe.

​Takun takalman macen—masu sauti mai kaifi—suka fara dukan dambar dakin. Tak! Tak! Tak! Ta nufi inda kabot ɗin takardun yake, daidai inda Adnan ya bar shi a buɗe. Adnan ya rintse idonsa, yana addu'ar da duk tazo bakinsa.

​"Wanene ya bar nan a buɗe?" Macen ta yi magana da kanta, muryarta cike da zargi.

​Ta gyara takardun, sannan ta tura kabot ɗin ya rufu da ƙarfi. Adnan ya ga takalman macen ta ƙarƙashin teburin, suna nufin fita. Amma kwatsam, sai ta tsaya. Ta juyo ta kalli teburin da yake ƙarƙashinsa. Da alama ta ga wani abu—watakila wani guntun tsumman share-share da ya fito.

​Zuciyar Adnan ta buga Laf-daf! Laf-daf! Kamar za ta fito waje. A daidai lokacin da take shirin sun kuyawa don dubawa, sai wayarta ta fara ruri.

​"Hello? Ranki ya daɗe... Yanzu zan kawo muku fayil ɗin zuwa dakin taro. Minti biyu kawai."

​Ta juya da sauri, ta ɗauki wasu takardu a kan teburin (daidai saitin kan Adnan), sannan ta fice ta ja ƙofar.

​Adnan ya fito daga ƙarƙashin teburin yana haki kamar wanda ya yi tseren kilomita goma. Jikinsa duk ya jike da gumi, har kayan "cleaner" ɗin sun manne a jikinsa. Ya san ba shi da lokaci. Cikin sauri ya sake buɗe kabot ɗin, ya fisgo jan fayil ɗin nan, ya tura shi cikin tsumman share-sharen da yake turowa a kan kekensa.

​Ya fito daga ofishin, kansa a ƙasa. Kowane ma'aikaci da ya wuce sai ya ji kamar yana kallonsa ne. Ya isa wurin "lift", ya danna ƙasa. Lokacin da lift ɗin ya buɗe a babban falo (reception), ya ga Musa tsaye a nesa, sanye da tabarau, yana kallon agogo.

​Musa ya yi masa alama da ido. Adnan bai tsaya ba, ya fice waje ya nufi motar da ta kawo shi. Direban ya buɗe masa baya, Adnan ya faɗa ciki ya watsar da jan fayil ɗin a kan kujera kamar ya taɓa wuta.

​"Mun gama," Adnan ya ce, muryarsa tana karkarwa. "Kai ni gida. Bana son sake ganin wannan fayil ɗin."

​Direban bai kai shi gida ba maimakon haka, ya kai shi wani gidan gona (farmhouse) a bayan gari inda Musa yake jiran su. Musa ya karɓi fayil ɗin da wani irin murna wadda ta ba Adnan tsoro.

​"Adnan, yau ka tabbatar min da cewa kai gwarzo ne!" Musa ya buɗe fayil ɗin.

​Adnan ya leƙa shi ma. Idanunsa suka gano wasu hotuna da kuma wasu takardun banki (bank statements) na biliyoyin nairori. Amma abin da ya fi razana shi, shi ne ganin sunan wani babban mutum da duk garin suke girmamawa a matsayin "Adali"—

​"Wannan ai... wannan ai Alhaji Shehu ne!" Adnan ya ce cikin mamaki. "Musa, ashe satar kuɗin talakawa yake yi?"

​Musa ya yi dariya, dariyar da take sa jikin mutum sanyi. "Kowa yana da farashinsa, Adnan. Shima wannan Alhaji Shehun, wannan takardar ita ce za ta zama silar rugujewarsa, mu kuma silar arzikinmu. Idan muka nuna masa wannan, zai biya mu duk abin da muke so don mu binne maganar."

​A nan ne Adnan ya gane cewa ba wai "daukar takarda" ya yi ba; ya zama "Blackmailer" (mai neman kuɗi ta hanyar barazana). Ya shiga wata harka da ba a fita lafiya.

​"Musa, ni ba zan iya wannan ba," Adnan ya ce yana ƙoƙarin tashi. "Na riga na kawo maka, yanzu ka ba ni ragowar kuɗina in tafi in nemi lafiyar mahaifiyata."

​Musa ya daka masa tsawa. "Zauna! Kariga ka shigo, Adnan. Babu fita a wannan wasan har sai mun gama. Kuma ka sani, yanzu hotunanka na shiga ofishin nan suna hannuna. Idan ka yi kuskuren guduwa, kai ne za ka fara zuwa gidan yari, ba ni ba."

​Adnan ya koma ya zauna. Ya kalli hannunsa, ya ga kamar akwai jini a jiki, ko da yake babu komai. Ya gane cewa lallai, "Kwaɗayin samun ƙari, shi ne silar babban rashi." Ya samu kuɗin Inna, amma ya rasa ’yancinsa.

​Shin Alhaji Shehu zai amince ya biya kuɗin da musa zai nema?

Ko dambarwa zasu buga?

Inna Halima fa, me zai faru idan ta gano asalin inda kuɗin suka fito?

Tunda ga duk kan alamu adnan ya faďa, mummunar tarko da komai zai iya faruwa?

​Adnan ya tsinci kansa a cikin guguwar da ba ta da burki. Yanzu maganar ba ta neman kudin Asibiti bane, magana ce ta rayuwa ko mutuwa. Musa ya riga ya gama ɗaure shi da igiyar da ba za ta tsinke ba.

Alkalamin Hamma Abdul (Dan Salma)................🖊️