MASARAUTAR KAIZUR 5
by @nusybee143
👑🗡️ MASARAUTAR KAIZUR 🗡️👑
✍️Nusy bee
❤️ Young talented writers association YOTA ❤️
Page 5
*DAULAR TAYAAR*
"Barka da warhaka ya shugabana!"Sarkin yaƙi Ra'uf da yake zaune yana hutawa ya dubi badakaren da ya ce a yi masa iso,ya ce"Barka dai Amjad!
Ina fatan komai lafiya"
"Da sauƙi dai ya shugabana"a cewar Amjad "tsawon kwanaki biyu kenan yau amma badakaren Baruda ya ƙi cin komai,ya ƙi shan komai,kuma ya ƙi yiwa kowa magana"
Shiru Sarkin yaƙi ya yi yana nazari, kafin ya ce"to babu matsala, za'a san yadda za'a yi,
Zan je na samu mai martaba in sha Allahu"dakare Amjad ya rissina sannan ya miƙe ya bar wajen
Har fada Sarkin yaƙi ya je don ya gana da sarki Iyaad,bayan an yi masa iso ya shigo ya rissina ya yiwa sarki Iyaad bayanin halin da ake ciki
Sarki Iyaad ya ɗan yi shiru, kafin ya ce "babu komai,zan same shi da kaina,za muyi magana ta fahimtar juna da shi,in sha Allah komai zai warware cikin sauƙi,kuma za'a ci riba in sha Allah,za muyi nasara"Sarkin yaƙi ya rissina yana faɗa "Allah ya ba ka nasara Sarkin daular alkhairi,sarki mai adalci, Sarkin sarakai "daga haka ya miƙe ya fice daga fada
Bayan sallar la'asar dakarun tsaron lafiyar sarki Iyaad suka raka shi zuwa É—akin hukunci inda aka kai Sadauki Kazuzi aka rufe,su dai dakarun bin shi suke yi kawai,amma a tsorace suke da Sadauki Kazuzi
Kamar yadda suka saba ganinshi yau ma a haka suka same shi,kanshi a ƙasa, baƙin yalwataccen gashinshi ya zubo ya rufe masa fuska,sarki Iyaad ya dube shi,da tausasawa ya ce"amincin Allah ya tabbata a gare ka ya kai wannan jajirtaccen gwarzo
Daular Tayaar tana maraba da jarumin jarumai Kazuzi "kamar yadda suka yi tsammani haka ya faru,ko motsawa bai yi ba ballantana su suka ran zai amsa
Sarki ya dubi shugaban dakaru ya ce"a kwance masa sarƙar "duk da tsoron da yake ji hakan bai hana shi kama sarƙar ba,ya yi amfani da mabuɗan hannunshi ya kwance ƙarfafan kwaɗunan da aka yi amfani da su don ɗaure sarƙar
Sarki Iyaad ya sake duban Kazuzi da ko motsawa bai yi ba har yanzu,ya ce cikin tausasawa "za mu iya tattaunawa yanzu?"
Ga mamakin dakarun sai gani suka yi ya buÉ—e kyawawan idanunshi, waÉ—anda suka É—an canja kama saboda halin da yake ciki,ya É—ora su akan Sarki Iyaad,wanda har zuwa lokacin yanayin annurin fuskarshi bai canja ba,a karo na farko tun bayan shigowar shi Tayaar,a hankali,kuma cikin sautin shi mai cike da mazantaka ya ce
"Da gaske kana son yin magana da ni kuma?
A hakan?"
Duk da cewa dakarun sun san wanene Kazuzi amma hakan bai hana su zabura ba suka yi kanshi,sarki Iyaad ya yi azamar dakatar da su,shi kuwa Kazuzi ko motsawa bai yi ba,asalima da wani irin kallo na izza yake bin sarki Iyaad
Shugaban dakaru Amjad ne ya ce cikin fusata
"Zuwa yanzu ya kamata Kazuzi ya san cewa nan ba Baruda ba ce,kuma shi yanzu ba ɗan mafarauci Murad bane,bawa ne,maƙasƙanci kamar kowa,kuma nan daular Tayaar ce, don haka ya iya bakinshi!"
Ba tare da ya kalle shi ba, cikin nutsatstiyar muryarshi ya ce"da sarkinka nake magana,ka yi shiru,bana magana da mata!!!"
Kamar an caka masa mashi a ƙahon zuci haka ya ji,wai shi babban badakare kuma gwarzon mayaƙi ake kira da mace,lallai dole ya ɗauki mataki
Sarki Iyaad ya dubi Kazuzi,a hankali ya ce"me kake buƙata?"
Kai tsaye Kazuzi ya ce"a bamu waje!"ba tare da sarki Iyaad ya yi magana ba suka juya suka fice daga É—akin,amma fa suna fargabar abin da zai biyo baya
Sarki Iyaad ya dubi Kazuzi, cikin tausasawa ya ce "a karo na uku ina mai sake yi maka sha'awar shiga addinin salama,addinin musulunci,amma zaɓi yana hannunka"
Rissinawa Kazuzi ya yi,abun ya bawa Sarki Iyaad mamaki,amma bai bari hakan ya bayyana akan fuskarshi ba,ya ce"gaisuwa gare ka ya shugaba na!
A halin yanzu bani da ta cewa game da abin da kuka yanke, zaɓi kuma ku zan dawowa da zaɓin, tunda na taso a rayuwa ta rana ita ce abar bauta ta,sai tekun Baruda,barin wani addini wanda ba addinin Baruda ba tamkar BUTULCI ne a gare ni, don haka yanzu kuna da damar bari na na rayu a cikinku a matsayin bawa,ko ku yanke min hukuncin da kuke ganin ya yi daidai da ni"
Shiru sarki Iyaad ya yi na É—an lokaci,kafin ya ce"Sadauki Kazuzi!
Na san ka so a kama ka ne shiyasa ka kamu,sannan yanzu na sake tabbatar da hakan ta hanyar maganar da ka faÉ—a na cewa ba za ka amshi addinin Musulunci ba,amma idan kana da wani hanzari ina da jimirin saurara"
Wani miskilin murmushi Kazuzi ya yi, kafin ya ce"kana zargin zan iya yaudarar ku don na cimma wata manufa ne?"
Sarki Iyaad ya ce"eh!haka nake zargi,ka fitar da ni duhu kafin na yarda da kai"
Kazuzi ya ce"menene dalilin da ya sa sai na yi zamba cikin aminci zan yi nasara a kanku?
Idan na yi niyya ni kaɗai zan iya ƙarar da dakarun ku gaba ɗaya,kuma a cikin ƙanƙanin lokaci,na gwabza da rundunar da tafi taku ƙarfin runduna da ƙarfin mayaƙa na yi nasara,to menene dalilin da zai saka na shigo garin nan a matsayin bawa don kawai na cimma abin da na saba cimmawa?
Yaudara ba siffar Kazuzi ba ce, tabbas akwai dalilin da ya sa na zo garin nan a matsayin bawa,amma ba dalilin yin nasara a kanku bane, saboda tawa rayuwar ta ƙare ne, don haka daidai ne ku yanke hukunci irin wanda kuke so akaina
Amma ku sani, Kazuzi bai taɓa yin abin da ya yi nadama akai ba"yana kai wa nan a zancenshi ya ja baki ya yi shiru,sannan ya jingina kanshi da jikin bango yana lumshe idanunshi,da alamu akwai abu mai zafi da yake yi masa yawo a rai
Nannauyar ajiyar zuciya sarki Iyaad ya sauke,sannan ya ce"shikenan,babu komai
A ƙa'idar dokar ƙasar Tayaar duk lokacin da aka kamo ribar yaƙi muddin bai amshi addinin musulunci ba a take ake yanke masa hukuncin kisa
Amma akanka zan É—aga dokar,ko ma na soke ta baki É—aya "
"A shawarce ya shugaba na,ka yi abin da yake doka ce,kar hakan ya janyowa kujerar sarautarka tangarÉ—a,don na ga sarakunan nan kuna da maitar son mulki "
"Sai ka cire ni a ciki,don ni na fi ƙaunar zaman lafiya da maslaha akan ƙujerar da zan mutu na bari"
Sarki Iyaad ya gyara zama yana kallon Kazuzi da idanunshi ke kallon wani wajen, cikin sanyin murya ya sake faÉ—in
"Labari ya zo mana na cewa tsawon kwanaki biyu da zuwanka daular Tayaar ba ka cin abinci ko ka sha abin sha,zan iya sanin dalilin hakan?"
Kazuzi ya rissina ya ce "a yi min aikin gafara ya shugaba na,ina cikin ruɗani ne,amma yanzu zan karɓi duk kyautar da ta fito daga adalin sarki irinka "sarki Iyaad ya yi murmushi irin nasu na manya,sannan ya miƙe yana faɗin"na bar ka lafiya ya kai babban sadauki, babban baƙo a birnin Tayaar "
Kazuzi ya sake rissinawa ya ce"a sauka lafiya ya shugaba na"
*DAULAR GAYUR*
"Barka da warhaka ya sarkin muminan aljanu! faÉ—a taka cikawa tawa mai martaba!!"
"Shabbir!
Ina so na san a wanne hali amanar Gayur yake?
Mun san dokar ƙasar ta Tayaar,duk wanda suka kamo a ribar yaƙi matuƙar bai yi imani ba suna datse kanshi ne
A wanne hali ake ciki yanzu?"
"Ya shugaba na!a halin da ake ciki yanzu dai sarki Iyaad ya kwaɗaita masa addinin musulunci,sai dai abin baƙin ciki bai yi imani ba,asalima ya fara magana ma akan abin da ya shuɗe,ya ce ba zai iya cin amana ba ko da ace babu daular Baruda a doron ƙasa"
Shiru sarki Laimus ya yi yana nazari na wasu ƴan daƙiƙu, kafin ya ce"to wanne hukunci sarki Iyaad ya yanke?"
Sai da Shabbir ya yi murmushi mai kayatarwa kafin ya ce"shi sarki Iyaad sarki ne da a wannan nahiyar babu wani sarki bil adama da ya kai shi adalci da kaifin tunani,ya yarda da maganar Kazuzi,har ma ya ba shi dama,yanzu haka akwai yarjejeniyar Kazuzi zai cigaba da zaman shi yana bin addinin shi,shima sarki da muƙarrabanshi za su ɗauke kai daga gare shi,shima kuma zai riƙe amanar sarki Iyaad "
Sarki Laimus ya yi murmushi, cikin jin daɗi ya ce"bana jin duk wani jinin SUHAIF BIN YASSAR akan cin amana,ba su taɓa kafa wannan tarihin ba,kuma bana jin har abada za suyi,don haka kai dai ka cigaba da saka idanu akan ajiyarmu kawai"Shabbir ya jinjina kai,ya ce"gaisuwar ban girma gare ka shugaban muminai!
Na bar ka lafiya adalin sarki!"daga haka ya buÉ—e fuka-fukanshi ya fice daga cikin fadar
*DAULAR KAIZUR*
Ranshi a ɗan ɓace yake kallon matar da ta tunkaro inda yake,sanye da tufafi baƙaƙe,ta rufe rabin fuskarta da baƙin yanki, idanunta akanshi kamar yadda yake kallonta
"Uwar shaiÉ—anu!
Adalci kenan da kika shanya ni a wajen nan?"
Wani miskilin murmushi ta yi,ta ce"uban sharri!da ni da kai wanene ya gaza yiwa wani adalci?
Na gaji da ɓata lokaci da wahalarwa tsawon shekaru ashirin,na bayar da dukkan wani goyon baya da dabaru kun kawar da abin da zai kawo mana tarnaƙi, menene abin da ya yi saura kuma?me kuka tsaya yi da ba ku kawar da shamakin da ya tare mana cikar buri ba?"
"Akwai matsala ne!akwai abin da yake faruwa da aikin mu,zuwa gobe zan koma wajen boka lamzur don ya bincika min abin da yake faruwa,don shi da kanshi ya ce mana kar mu yi gaggawa "
Girgiza kai uwar shaiÉ—anu ta yi tana kallonshi,kafin ta ce"boka lamzur yana ja mana rai da yawa,sam bana gane kan waÉ—annan abubuwan da suke faruwa,bani da ishashshen lokacin jira,a yadda na tsara zuwa yanzu nima na samu nawa Yariman....."
Uban shaiÉ—anu ya katse ta da faÉ—in"sai ki kashe ni ki gaje kujerar ko?"
A razane ta kalle shi zuciyarta tana bugawa,ya yi É—an murmushi ya ce"wasa nake yi,nima zan yi alfahari a ce ga É—ana ya mulki kaizur,don haka ke dai ki je ki fara shiri,ko ba daÉ—e ko ba juma tabbas za ki haifi naki gwarzon,wanda zai kawo babban sauyi a kaizur,a kawar da wannan uban isa da mallakar "
Ƴar dariya ta yi cikin jin daɗin maganar tashi,ta ce"Allah ya nuna mana lokacin,amma tabbas na ƙagu na ga na zama uwar sarki a wannan daular"
Ya yi ɗan murmushi ya ce"lokaci ne, lokaci yana zuwa da za mu ture wanna baƙin mulkin, mu yi tawaye wa wannan mulkin na zalunci "
Jinjina kai ta yi cikin gamsuwa, kafin ta ce"yanzu zan koma, sai mun sake haÉ—uwa "bata sake magana ba ta juya ta bi duhuwarda ta biyo ta koma inda ta fito,ya bi ta da kallo yana wani irin murmushi da shi kaÉ—ai ya san ma'anarshi
*DAULAR TAYAAR*
A matuƙar fusace ta fito daga sashenta, ɗauke da takobi a cikin kubenta, cikin ɗimuwa dakaru da kuyanginta suka rufa mata baya, shugaban dakaru Amjad ya yi saurin shan gabanta,ya durƙusa yana faɗin
"Ya shugaba ta......"
Wata uwar tsawa da ta daka masa ce ta dakatar da maganar ta shi,cikin tsananin fushi da ɓacin rai ta dube shi ta ce"tashi ka ba Ni waje!
Da alamu ku ne masu kai Abby hanyar da kuke so, saboda ba É—anku ko mahaifiyarku kuka rasa ba,bani da lokacin sauraren duk wata magana daga gare ku,ba ni waje"
Bai daddara ba ya sake dubanta da girmamawa ya ce"a yi min afuwa ya shugaba ta!
Yara uku Kazuzi ya kashe min,Sarkin yaƙin garinsu Anudu shine silar mutuwar mahaifina,amma hakan...."
"Ina rantsuwa ga ubangijin talikai ko dai ka tashi ka ba ni waje ko na raba kanka da gangar jikinka idan ya so nima sai a yanke min hukuncin kisa"ta faÉ—a cikin hargowa tana zare takobin daga cikin kubenta
Babu shiri dakare Amjad ya miƙe yana faɗin "a yi min afuwa ya shugaba ta"bata saurare shi ba ta shige gaba,suka bi ta a baya,kai tsaye suka nufi ɗakin duhu
Yau ba kamar kowanne lokaci ba,an samu canji,yana zaune ya jinginar da kanshi a jikin bango yana ƙarewa ɗakin kallo,amma da alamu ba ɗakin yake kallo ba,wani abu yake tunani dabam
Kayan jikinshi ba su bane wanda yake jikinshi jiya,sannan damtsen hannunshi na hagu an nannaɗe ciwon da Sadauki Waleed ya ji masa,ya saki dogon gashin kanshi zuwa gadon bayan shi,wani kuma ya zubo da shi zuwa gabanshi kan ƙirjinshi
Sam bata damu da canjin da ta gani ba, tana zuwa ba tare da tunanin komai ba ta nuna shi da takobin hannunta, cikin tsananin ɓacin rai ta fara faɗin
"Dama an tabbatar min da cewa ku manyan matsafa ne baya ga kasancewar ku azzalumai,to yanzu na gani,ka tsaface babana da manyan dakarun shi suna É—aukar ka a matsayin wata tsiya
Ni yanzu zan gani ko za ka yi galaba a kaina,zan raba kanka da gangar jikinka da sunan Allah,zan gani ko za ka iya ƙwatar kanka da tsafin!"ta ɗaga takobin da ƙarfi tana kwarara kabbara,kai tsaye ta nufi wuyanshi ta sauke ta .........
#Nusy_bee