MASARAUTAR KAIZUR

MASARAUTAR KAIZUR 6

by @nusybee143

👑🗡️ MASARAUTAR KAIZUR 🗡️👑 





✍️Nusy bee 
❤️ Young talented writers association YOTA ❤️ 




Page 6




Tana daf da sauke takobin a tsakiyar kan Kazuzi,wanda yake zaune kawai ba tare ya yi wani yunƙuri don kare kanshi ba,kuma har yanzu ko kallon sashen da take bai yi ba,kawai ta ji an riƙe hannunta ƙam

A hargitse ta juya don ganin wanene ya yi mata wannan shishshigin,da tsananin mamaki da kaÉ—uwa take kallon mahaifinta sarki Iyaad da fuskarsa take a matuĆ™ar haÉ—e tamkar hadarin da ya gangamo yake daf da fara zubar da ruwa, ba tare da ya yi magana ba ya fincike ta, bai yi wata-wata ba ya É—aga hannu da niyyar sauke mata mari,amma ya ji an riĆ™e masa hannun 

Da tsananin mamaki ya É—ago yana kallon Kazuzi da ya riĆ™e masa hannun,ba shi ba ma,duka ilahirin dakarun da kuyangin da ke tsaye kallon Kazuzi suke yi da tsananin mamaki,ya durĆ™usa a gaban sarki Iyaad yana faÉ—in 

"Ka gafarce ni ya shugaba na!mace ce,duk inda mace take ana son a É—aga mata Ć™afa saboda rauninsu"ya faÉ—a kanshi a Ć™asa 

A hankali sarki Iyaad ya sauke hannunshi,a wani irin fusace Hayat ta ce"ina ruwanka da abin da ya shafe ni da abbana?

Me ya kai ka shiga tsakani na da uba na tunda kai ka yi silar barin mahaifiya ta duniya?

Kai musiba ne,kuma ibtila'i ga rayuwa ta! menene dalilin da ya sa za ka rinƙa shiga abun da babu ruwan ka?zindiƙi kafiri azzalumi?? menene......"

"Hayat!!!"sarki Iyaad ya daka mata tsawa,ta kalle shi da rinannun idanunta,sannan ta sake mayar da hankalinta ga Kazuzi da kanshi yake ƙasa har yanzu,babu alamun ya san abin da take cewa a kan fuskarshi,bata damu ba ta cigaba da faɗin "karo na farko kenan da mahaifina ya ɗaga hannu da zummar duka na, karo na farko kenan da mahaifina ya daka min tsawa,kuma duka a gaban hadimai na!!!

Saboda kai,kai dai,na yi maka alĆ™awarin sai na wulaĆ™anta rayuwarka,tabbas hakan ba zai tafi a banza ba"tana kai wa nan ta juya ta fice daga É—akin tana hawaye,hadimanta suka rufa mata baya,sarki Iyaad ya bi ta da kallo yana É—an murmushi 

Shima bai sake magana ba ya juya ya fice daga É—akin,ragowar dakarun da suke tsaye a É—akin suka bi bayanshi, suka bar Kazuzi a zaune kanshi a Ć™asa 

Kai tsaye É—akinta ta shige bayan ta kori kuyanginta,ta faÉ—a kan gadonta tana kuka sosai,bata taÉ“a jin ta tsani wani mahaluki a rayuwarta ba kwatankwacin yadda take jin tsanar sadauki Kazuzi,kuma alĆ™awari ta É—aukarwa kanta tabbas sai ta ga bayanshi 

Tana ta kuka bata san da shigowar sarki Iyaad ba ma,sai da ya sanya hannu ya É—ago ta,tana kuka sosai,ya zaunar da ita yana magana cikin taushin murya 

"Allah ya huci zuciyar gimbiyar Tayaar, albarka kuma alfaharin Tayaar,kuma jinin sarki Iyaad,ki yi haƙuri ki daina kukan nan,za muyi magana"

Ba tare da ta tanka ba ta kama goge hawayenta,sai da ta goge hawayen sannan ta kalli sarki Iyaad cikin raunin murya ta ce"Abby na tsane shi tsana mafi muni 

Menene dalilin da ya sa tunda ya shigo cikin Tayaar na daina farin ciki ne?

Abby ka yanke masa hukunci, idan ba za ka yanke masa hukunci ba ka kore shi ya bar garin nan,na tsane shi,na tsani ganinshi,bana ƙaunar na tuna cewa akwai wata halitta da ta wanzu a cikin masarautar Tayaar wadda take amsa sunan Kazuzi"

Murmushi sosai sarki Iyaad ya yi yana riƙo hannunta,a ranshi yana sake yarda da maganar Kazuzi da yake cewa mata suna da raunin da ya cancanci a ɗaga musu ƙafa saboda shi,ya ce"tashi mu yi magana ƴata"

Babu musu ta tashi zaune tana goge idanu,sarki Iyaad ya dube ta sosai ya ce"yanzu wacce shawara gare ki da kike ganin za'a yiwa Kazuzi?

Kar ki manta daular Tayaar a duk nahiyar nan babu wani gari wanda yake faÉ—a da zalunci irin namu, alhamdulillahi kuma muna yin nasara

Ba mu kawo Kazuzi cikin daular Tayaar ba sai don mu cusa masa sha'awar musulunci, tunda kamar yadda muka sani musulunci ba'a yin shi da dole,kuma ko da ana yinshi da dole har yanzu Kazuzi bai yi lalacewar da za'a saka shi yin abu da ƙarfi ba

Amma ke menene shawararki?"

Kallonshi ta yi, cikin raunin murya ta ce "Abby ya nuna baya ra'ayi, meyasa ba za ku ƙyale shi ba?"

Murmushi sarki Iyaad ya yi,sannan ya sake dubanta ya ce"kina da labarin Sarkin yaƙi da ya rasu,wato Sadauki Ilyas?"

Take fuskarta ta washe da murmushi, idanunta akan shi ta ce"na sanshi, idan ban manta ba da ni da yaya na Yarima Nashwaar ya É—auke mu a matsayin jikokinsa,yana matuĆ™ar kula da mu a wancan lokacin 

Na sani shi ma mun rasa shi a wani yaĆ™in da Tayaar ta gwabza da Baruda "ta Ć™arashe fuskarta tana nuna alhini 

Sarki Iyaad ya ce"to shi wannan bawan Allan da kika sani mahaifina a ribar yaĆ™i ya samo shi kamar yadda aka samo Kazuzi,babban mayaĆ™i ne,kuma fitaccen jarumi a daularsu kamar dai Kazuzi,amma da babana sarki Nufail ya yi duk mai yiyuwa sai gashi an samu abin da ba'a yi tunani ba,bayan kasancewarshi Musulmi mai ibada a kowanne lokaci ya kasance shine mai jagorantar yaĆ™i,kin san menene ya janyo mana nasara a wancan lokacin?"ba tare da ta yi magana ta girgiza kai a hankali 

Sarki Iyaad ya ce"to jimirin jira ne,don sai da Sarkin yaƙi Ilyas ya shekara bakwai da mu yana bin addinin shi na bautar wuta,a wancan lokacin mahaifina ya fuskanci ƙalubale da dama,ya jure maganganu daga wajen mutane,amma sai gashi rana tsaka burin shi ya cika,sadaukin ya karɓi musulunci,har ma ya ja Sallah a masallaci,shin ni ba kya son na kafa wannan tarihin ne?"

Cikin sanyin jiki ta girgiza kai,sarki Iyaad ya ce"to ki É—auki Kazuzi a matsayin da kike É—aukar kuyangin ki da dakarun da suke tsaron lafiyarki, yadda kika mayar da su aminanki,masoyanki,makusantanki haka nake so ki mayar da Kazuzi,in sha Allah lokaci yana zuwa da za mu samu nasarar canja masa ra'ayi kamar yadda muka chanjawa sadauki Ilyas"

Rissinawa ta yi tana faÉ—in "fatan nasara mai É—orewa Abby!"

Sarki Iyaad ya yi É—an murmushi yana faÉ—in"fatan rayuwa mai albarka da ma'ana yata "daga nan ya juya da niyyar ficewa daga É—akin 

Gimbiya Hayat ta bi shi da kallo,ta gamsu da maganarshi,amma tabbas sai ta hukunta Kazuzi ko yaya ne, musamman da ya janyo Abby É—inta abin alfaharinta ya É—aga hannu da niyyar marinta 





*DAULAR KAIZUR*

"Ya shugaba ta!mai martaba ne ya ce a yi masa iso"

ĆŠaga kai gimbiya Amna ta yi tana kallon jakadiya da kanta yake a Ć™asa,ta ce"ki yi masa iso Nayyab"Nayyab ta sake rissinawa sannan ta miĆ™e ta fice daga turakar 

Bayan ƴan daƙiƙu sarki Mu'iz ya shigo da sallama, sarauniya Amna ta rissinar da kai ta amsa,ya ƙaraso ya zauna kusa da ita, cikin girmamawa ta ce"Barka da zuwa ya shugaba na"

"Barkanki da warhaka sarauniyar Kaizur!"

"Jakadiya ta ce ayi maka iso"

Sauke ajiyar zuciya mai nauyi ya yi cikin damuwa,ta É—aga kai tana kallonshi,a hankali ya furta"na kasa jurewa ne,dole na taho mu yi magana"

"Kan batun yarima Sahal?"ta faÉ—a a raunane tana kallonshi 

Shiru ya yi kanshi a ƙasa,ta yi ɗan murmushi mai ciwo tana girgiza kai ta ce"tunda na ji a jikina a kwanannan,na yi mafarkai da yawa,ga yawan faɗuwar gaba na san ɗana ya faɗa mugun hannu,zuwa yanzu na san na rasa Yarima na"zuwa lokacin sosai take kuka

Girgiza kai sarki Mu'iz ya yi da sauri,ya ce"wannan hasashe ne kawai sarauniya,ina cikin damuwa ne kawai saboda tsawon lokacin da muka É—auka muna neman shi amma har yanzu babu labari,na yi duk mai yiyuwa amma babu nasara 

Yarima Sahal yana raye,shine kawai tabbacin da nake da shi,amma banda haka da tuni na haƙura,komai na bawa muƙaddari ne"

Sarauniya Amna ta jinjina kai ta ce"haka ne mai martaba

Amma idan da hali ina so mu gana da Munaya, wataƙila mu samu wani haske "

Sarki Mu'iz ya girgiza kai ya ce"babu Abin da ganawa da Munaya zata haifar sai damuwa,da alamu waÉ—anda suka saka ta aikin sun shirya, shiyasa ita ma ta shirya,sam bata tsoron ko da mutuwa, shiyasa bana son abin da zai haÉ—a ni da ita yanzu"

Girgiza kai sarauniya ta yi,ta ce"kar mu yi haka, abu ne na ribar mu,idan yarima Sahal ya salwanta mu ne muka shiga matsala,idan ya bayyana amfanin mu ne,mu je mu tattauna da ita,ina fatan zata yarda ta ba mu ƙarin haske"

Girgiza kai sarki Mu'iz ya yi,ya ce"mu je,amma bana jin hakan gaskiya, amma ni na riga na yanke hukunci,ba zata ƙara shekara ɗaya a ɗaure ba,zata baƙunci inda su Umayr da Ya'aƙub suka je"bata yi magana ba sai jinjina kai,sarki Mu'iz ya miƙe tsaye, itama ta miƙe suka fice daga turakar





*DAULAR TAYAAR*

"Barka da warhaka ya shugaba ta"

Kallonshi ta yi sosai, kafin ta fara magana a dake"ribatattun yaƙi da aka kamo daga Baruda,an raba musu wajen aiki ne?"

Dakare Amjad ya ce"tukunna dai ya shugaba ta,amma yau in sha Allah za'a raba musu"

Sauke ajiyar zuciya ta yi,kai tsaye ta ce"to wannan zindiƙin badakaren,ina so a saka shi cikin jerin masu yi min hidima "

A firgice shugaban dakaru Amjad ya kalle ta,a É—an tsorace ya ce"ranki ya daÉ—e babu kasada a cikin hakan?"

"Umarni na bayar,bana buĆ™atar a tambaye ni,saura kuma ka kai ni gaba,tashi ka fice,na sallame ka "babu musu shugaban dakaru ya rissina sannan ya miĆ™e ya fice daga lambun nata cikin zullumi da fargaba 

Har yanzu sadauki Kazuzi abin tsoro ne, ba'a gama sanin wanene shi ba,ta yaya ita mace mai rauni ta ce wai a saka Kazuzi ya yi mata hidima?shi dai yana ganin da kuskure a hakan 

Hakan ne ya saka ya yi fatali da umarninta,bai yi Ć™asa a gwiwa ba ya samu Sarkin yaĆ™i da maganar 

Murmushi sarkin yaĆ™i ya yi,a ranshi yana fatan abin da yake gani ya tabbata, gimbiya Hayat ta sauĆ™aĆ™a musu hanyar jan ra'ayin Kazuzi,don haka ya ce"ka bi abin da ta ce, sauran kuma mu bar wa Allah, in sha Allahu babu wata matsala"dakare Amjad ya rissina sannan ya miĆ™e ya bar wajen 

A ranar aka rabawa sababbin bayi wajen aikinsu,ciki har da Kazuzi,da aka tura shi tsaron lafiyar gimbiya Hayat 

Ta ji daÉ—i sosai da labari ya iske ta, tana zaune a Ć™awataccen lambunta,amintattun kuyanginta sun kewaye ta ta aika É—aya daga cikin asalin dakarun da suke gadin lambunta cewa ya kira mata Kazuzi 

Babu jumawa suka Ć™araso,a fizge ta kalle shi sannan ta mayar da kanta gefe Ć™irjinta yana bugawa,tsawon lokacin da ta É—auka tana yi masa tijara bata taÉ“a Ć™are masa kallo ba sai yau 

Cikakken namiji mai cikar zati,dogo ne sosai,mai Ć™irar jiki mai matuĆ™ar kyau,duk da cewa sanye yake cikin kayan bayi amma sai taga sun yi masa kyau tamkar ba bawa ba,sosai ta ga ya yi mata kwarjini tamkar ba bawanta ba,dogon gashinsa da ya É—aure a tsakiyar kanshi ya sake shi ya zuba gadon bayansa,iska sai kaÉ—a shi take yi 

A dalilin haka ta kasa yi masa rashin mutunci da ɗiban albarka da ta shirya,yana zuwa gabanta bai yi wata-wata ba ya zube a ƙasa, kanshi a ƙasa ya ce "Barka da wannan lokaci ya shugaba ta!"

Shiru ta yi da farko tana bin shi da kallo, kafin ta yi juriya ta ce"ka iya ladabi kamar gaske,amma ka haÉ—a ni faÉ—a da mahaifi na!"

Bata yi tsammanin zai ba ta amsa ba,amma ta ji ya ce"ki gafarce ni ya shugaba ta"

Da mamaki take kallonshi kafin ta ce"na san zuwa yanzu ka yi nadamar abin da ka yiwa É—an'uwa na da mahaifiya ta ko?"

Ba tare da shakkar komai ba ya ce"Kazuzi baya aikin nadama ya shugaba ta"

Da mamaki take bin shi da kallo,su ma kuyangin nata kallonshi suke yi, kafin ta sake dakewa ta ce"anjuma za mu fita yawon shaƙatawa zuwa dajin Lahur,sai ka kasance cikin shiri"

Ya sake rissinawa gami da amsawa da faÉ—in "an gama ya shugaba ta"

Cikin ƙosawa ta dube shi ta ce"na sallame ka, za ka iya tafiya"

Ya sake rissinawa ya ce"na barki lafiya ya shugaba ta"daga haka ya miĆ™e tsaye, cikin takunshi na dirarren namiji mai izza ya bar wajen 

Da yamma ta shirya kamar yadda ta saba lokaci zuwa lokaci,ta yi ado mai kyau,suka shiga keken dokin da suke fita da shi ita da kuyanginta, Kazuzi da wasu dakaru su biyu suka bi bayansu a dawakai zuwa dajin Lahur 

Hayat tana tsananin son ganin tana yawatawa yadda take so, amma mahaifinta sarki Iyaad bai cika son hakan ba, shiyasa yau da ya yarje mata take cike da farin ciki 

Daga ita har kuyanginta da ta mayar da su tamkar Ć´an uwanta sai shawagi suke yi cikin kwanciyar hankali,sam ba su kula da wata damisa da take fakon gimbiya Hayat ba,sai gani aka yi ta daka tsalle cikin zafin nama ta yi kanta.....



(Damisa zata lamushe gimbiya 🥹🥺)




#Nusy_bee