Kuncin zuci
by @bintuuu
Eid Mubarak Everyone.
Washegari da safe Na'ima na tsaye acikin closet dinta tana duban kayan da zata saka Ahmad ya shigo room din cikin shirinsa na dark brown half jumpa sai tashin qamshi yake, sai ya tsaya a bakin qofan shigowa closet din yana bin towel din jikinta da kallo, idanunsa ne suka rinqa rumming a jikinta yana kallon figure dinta tun daga qasa har sama, da sauri ta juya ta gansa tsaye bakin kofan har da harde hannu a qirji yana kallontan, sai ta hau gyara zaman towel dinta ta kwabe fuska tace "Shiryawa fa zanyi" sai yayi murmushi yace "Babe ban hanaki ba fa" tace "Nidai toh ka juya" sai ya rufe idon yace "Bana ganinki to" dariya ce ta fara zuwa mata sai ta danne kawai ta nufi gurin jerin hijabs dinta ta dauko daya nan ya bude Ido yace "Hijab kuma" dariyan ce ta kubuce mata tace "Kana kallona ashe" sai ya girgiza kai yana murmushi ya juya yana fadin "Na fita to" dan ya sani idan ya qarasa gareta a yanayin da take toh fitan zata iya fasuwa gaba daya, ganin ya fice sai Na'ima ta hau duba kayan ta da sauri gudun ya dawo ya sake samunta daure da mitsitsin towel din, sai da ta saka atamafan nata da rigan da ta kasance knee length da kuma straight skirt sannan ta fita daga room din tana qoqarin qarasa zuge zip din da ta kasa, Ahmad ta samu tsaye a dakin yana jiran fitowan ta hannunsa riqe da waya yana dannawa, sai ya saka wayan a aljihu ya matso gareta ya fara qoqarin tayata zuge zip din ta bar masa ya qarasa, kallon kayan nata ya rinqa yi da itan kanta sannan yace "Babe you look stunning" tayi murmushi tareda nufan mirror ta tsaya ta fara gyara gashinta, nan ma shi ya tayata kamawa bayan ya gama tayata saka ribbon din sai ya sunkuya ya mata kiss a wuya yace "I pray that our kids will have your beautiful hair jewel...I love it so much" sai ta miqa hannunta ta shafo gefen fuskarsa tana murmushi, wani irin qauna takewa Ahmad da bata jin akwai kalman da zai misalta adadinta, shima yana kallonta ta cikin madubin ya sarqo hannunsa a waist dinta sannan ya sake burying fuskarsa a wuyanta yanajin sanyin sonta har zuwa ruhinsa, saida suka bata lokaci gurin lalacewa junansu a dakin sannan suka fice compound yana riqe da hannunta, sai taku take cikin hill shoe dinta mai kyau Ahmad na riqe da jakan nata da mayafi, da suka qarasa parking space kuma yaga jikinta yayi sanyi lokaci daya, sai yace "Babe what's wrong?" ta girgiza kai kawai bata amsa ba, sai ya matso daf da ita yace "Fadamin menene?" A shagwabe ta dago kai tace "Ni kunya nakeji yanzu kuma" sai ya fara murmushi yana saka mata gyalen yace "Na me kuma?" sai da ta gama gyara zaman gyalen a jikinta sannan ta kallesa tana kwabe fuska, bai bar murmushin ba yace "Seriously bansan me kike nufi ba" ahankali tace "Sun san me ya faru?" sai ya cigaba da kallonta, ta sake cewa "Asibiti" aikuwa nan ya fara dariya sai ta juya zata bar gurin yayi saurin kamota ya jinginata da motan yana danne dariyan, sai kuma ya kwantar da murya yace "Kina nufin sun san me mukayi lokacin?" ta kauda kai tace "Me kayi dai?" nan ma ya fara dariya qasa qasa yace "My Na'eemahhhh....ba'a ganewa a fuska ai" ta juyo tace "Amma ai sunsan meya faru" ya girgiza kai yace "Su Baba basu sani ba, believe me Babe" kallonsa ta tsayayi while shima haka, sai ya tallafo fuskanta yana shafa kumatunta bai bar kallon idonta ba yace "We did it for love Baby, ansan zamuyi hakan ai aka mana auren" cikin sanyinta tace "Kunya fa nakeji" sai yayi murmushi yace "In mukayi ciki fa" da sauri ta kwantar da kanta a qirjinsa tana murmushi tace "Please stop" sai yayi wrapping bayanta yana dariya kadan, anutse yace "Babu komai Babe, it's a normal thing, haka rayuwan take tafiya wani abun ko kasanshi sai ka basar kinji" sai ta gyada kai ahankali, da haka ya jata other side of the car ya taimaka mata ta shiga sannan shima ya zagaya ya shiga tareda tada motan yayi reverse, da sukazo fita daga gidan ya tsaya da motan while securities din suna gaishesa ya amsa tareda ciro kudi daga wani qaramin drawer na gefen seat dinsa ya miqa musu ba tareda ya qirga ba, suna godiya suka dan matso suna gaishe da Na'iman sai ta amsa musu da gaisuwa itama tana kallonsu dan sai ranan ma ta ga kamanninsu me kyau wanda dukansu sun kasance kabila ba Hausawa ba, ahanya kafin su qarasa gidan ta kallesa tace masa "Bazamu siya musu fruit ba haka?" ya kalleta kadan shima yace "Okay" da haka suka qarasa gurin wani babban trader kafin a qarasa arean gidansu Ahmad din, sai taga shida magidancin suna gaisawa da juna cikin sanayya sannan Ahmad yace "Baba a hadamin" me tradern yace "Kamar na ko yaushe?" ya amsa da "Eh" sai Na'ima taga yanata saka Apple me yawa a ledan, Ahmad na ganinta yace "Mamma tafi son sa sosai" ta gyada kai kawai, da suka isa gidan yayi parking sai ya juyo yana kallon yanda taketa gyara gyalen nata, dariya ce ta zo masa amma ya danne sai ya miqa hannu yana tayata gyara gyalen yace "Toh ki janyoshi kawai ki rufe fuskan taki, ta hakan ne bazasu gane me kikayi ba" sai kawai ta samu kanta da hararansa, nan ya hau dariya qasa qasa yana kallonta yace "Babe you're making it obvious for them to notice something" kamar zatayi kuka tace "Toh ka fara shiga sai in biyo bayanka" yace "We are going in together my love" da haka ya kamo hannunta a tausashe yace "Babu komai kinji" nan ma ta gyada kai ahankali, da haka ya bude side dinsa ya fito kafin ya zagaya side dinta ta bude motan ta fito, atare suka nufi gidan hannunsa riqe da ledan fruit din, suna shiga falon kuwa suka tarar har Baba yana zaune tareda iyalen gidan kasancewan weekend, Fatima da Adam ne kawai basanan, sai duk suka dago kai suna kallonsu dasauri Na'ima ta sunkuyar da kanta kunya na cikata, Husna ta fara fadin "Oyoyo Anty Na'ima" tareda miqewa ita da Ummi dan su karbo kayan hannun Yayan nasu, har suka qaraso cikin falon kan Na'ima a duqe, Baba da Mamma cike da fara'a suke mata iso, tasamu guri nan qasan carpet kusada Ummi ta zauna, sai Ahmad ya nufi gefen Baba shima ya zauna a qasan kusada kafafunsa da haka suka fara gaishe da iyayen nasu, Na'ima kanta a sunkuye take gaisuwan su Mamma na kallonta fuskokinsu dauke da murmushi, sai da ta jira ta gama gaisawa da Baba sannan ta amsa da "Lafiya Na'ima, ya baqunta" murmushi tayi batace komai ba Anty tace "Sannu da zuwa Amarya" nan ma ta kasa amsawa duk Ahmad na lura da ita while yana magana da Baban, Salma sai kallonta sukeyi itada twins ganin idon Yayan nasu sai tayi saurin gaishe da Na'iman itama, bayan Husna ta kawo musu refreshment basu dade nan zaune ba Adam ya shigo falon hannunsa riqe da babban leda shima, nan ma Ummi ta miqe ta tarosa tareda karba, Mamma tace "Ina ta tunanin inda ka shiga yau, and it's weekend" yayi murmushi yace "Na dan fita ne" sai Ummi ta miqa mata ledan da ya kawon taga shima fruits ya siyo musu me tarin yawa, godiya ta masa sannan sumayya da ummi suka nufi kitchen riqe da ledojin, Baba ne ya fara miqewa zai wuce falonsa sannan Ahmad da Adam suka bisa aka abar sauran mutan gidan zaune tare da Na'ima, Mamma ta kalleta tace "Na'ima hau kujeran abunki kinji" sai ta girgiza kai tana fadin "A'a nan ma yayi" Ummi ce ta dawo gefen ta tace "Anty gashi har kin zo bamu samu munje ba" Na'ima tayi murmushi tace "Mu tafi tare to" Anty tace "kike biye su" Husna tace "Ma shirmata ba, kunji kunya dai" Ummi da twins suka fara dariya Safiya tace "Kai Anty Husna" Salma tace "Nima sai nan da two weeks zanzo Anty Na'ima" sai Na'ima tayi murmushi har sannan tana jin nauyin yin magana, sunanan zaune su Ahmad suka fito daga part din Baba shida Adam, Mamma ta dan bi fuskan Ahmad da kallo ganin yanayinsa sai kuma basu tsaya anan falon ba suka fice compound...
Fitar su sai Adam yace "Man..Menene ya faru?" Ahmad miqa masa wayar hannunsa yace "He text me just now" in confusion Adam yace "Wa kenan" yace "Smoke" sai Adam yayi saurin karban wayan yana kallon content din da kyau sannan ya kalli Ahmad yace "Ahmad karka bar yaron nan a hannunka, munyi maganar nan dakai ka amince da hakan fa, it's too risky..this case is beyond us to handle, ka kira Mazzy kace suyi linking yaron nan ga hukuma" sai Ahmad yayi shiru yana kallonsa, can kuma ya karbi wayansa da Adam din ya miqa masa ya danna kiran Mazzy, suna nan tsaye a compound din ya gama magana da Mazzy sannan suka wuce side dinsu wanda a yanzu Adam ke zama shi kadai a cikinsa..
Wunin ranan har zuwa bayan azahar Na'ima ta ga karamci gurin 'yan'uwan Ahmad tareda mahaifiyarsa, daga karshe part din Mamma ta koma suka zauna anan babban falon ta suna hira dasu Husna da Ummi bayan sun cika mata gabanta da kayan ciye ciye, Ahmad ne ya shigo Mamma ta kallesa tace "Na zata kun fice ai" sai da ya zauna bisa kujera sannan yace "Munanan" tace "Bari akai muku abinci toh" sai ya girgiza kai yace "Bansan ba ko Adam, I'm okay. Zamu dan fita ne yanzu ma" da kamar Mamma zata tambayesa ko Lafiya ganin har sannan yanayinsa ba daidai ba, sai ta fasa kawai tace "Toh ai zaku kai dare ko?" ya amsa da "In sha Allah" sai ya dan kalli Na'ima dake kallon Tv wadda tun da ya shigo taqi kallon inda yake, da haka kuma ya miqe ya fice daga dakin, sake komawa bangarensu yayi ya jira Adam ya shirya sannan suka fice tare zuwa police station.
A hanyarsu ta tafiya kiran smoke ya sake shigowa wayan Ahmad ya dauka sai smoke din yace "Laila did this, that bitch paid tiyaga itada Mamanta, your sister is a messed up person Boss" sai Ahmad yayi shiru har hakan yasa Adam dake tuqin motan ya juyo ya kallesa, can kuma ya bude baki a hankali yace da smoke din "Thank you Smoke" da haka ya kashe wayan sai Adam yace "Yadai? Me yace?" sai Ahmad ya girgiza kai yace "Mu qarasa station din first" da haka kuma bai sake cewa komai ba har suka isa a inda suka samu tiyaga har yayi laushi a hannun yaran su Rabi'u, har office din Rabiu aka shigo dashi gurin su Ahmad din suna zaune aka duqar dashi anan tsakiyar dakin, bai boye komai ba ya fadi wa'inda suka saka shi aikin wanda hakan ba qaramin shock ya saka Adam ba while Ahmad din na zaune so composed babu alamun shock atare dashi, sai dai ta ciki wani irin turiri zuciyarsa keyi kamar ya bude ido yaga qanwar tasa a gabansa, bai wani jira ya gama sauraron bayanin da su Rabi'un ke masa ba akan batun zasu sanar da su Baba da Abba, kawai ya miqe ya fice daga office din tareda nufan gurin motarsu dake compound din station din rai a bace, da sauri Adam ya biyosa sanin duk shirun da yayin na bacin rai ne sai ya samu har ya tada motan tareda yin reverse ya fita daga station din gaba daya.
Tafiyar kimanin Minti arba'in da biyar ce ta isar dashi gidan Daddy, isarsa kofar gidan bai wani damu ya shigar da motan cikin gidan ba ya fito ya barta nan bakin gate sannan ya taka ya shige cikin gidan bayan ya gaisa da mai gadi, kansa tsaye ya nufi main building din gidan ya tura kofan falon ya shiga sai ya samu me aikinsu ce kadai take goge goge, sai da ya qarasa tsakiyan falon ta fara gaishe batareda ya amsa ba yace "Laila na nan?" Ta amsa da "Eh" sai yace "Inane dakinta" da farko shiru me aikin tayi sai ya sake cewa "Nace Ina ne dakinta" da sauri ta nuna masa upstairs tace "Daki na biyu in ka hau sama" da haka ya nufi stairs din kansa tsaye ya isa bakin second door din ya murda sai yayi sa'a a bude kuwa, Jim kadan kuwa ihun Laila ya fara karade gidan Mummy ta fito daga part din Daddy da sauri tana kallon mai aikinsu dake tsaye bakin stairs cike da tsoro, da saurinta ta qaraso tace "Meye nakeji kamar ihun Laila a gidan nan Abu" sai me aikin ta amsa da "Dan gidan wan yallabai ne ya shigo.." Mummy bata jira jin ba'asin bayanin ba ta nufi kofar dakin Lailan tana bugawa da qarfi yayinda Laila ke kuruwan ihun dukan da Ahmad ke mata a cikin dakin nata, rai a bace Mummy tace "Ahmad ka bude dakin nan, Wallahi in ka kashemin yarinya sai na ga bayanka kaima" ta cigaba da buga kofan iya qarfinta kuma Ahmad bai fasa dukan Lailan ba yana fadin "Sai kin fada min a gidan wa kika koyi dabbancin nan" "How can you be this Evil as a woman" Tana kuka a zaune nan tsakar dakin nata Babu bakin magana sai Mummy da Daddy kawai take kira, Adam ne ya shigo Falon shima da saurinsa sai Mummy ta nufesa tana sauqowa daga stairs din a rikice tace "Kace ya barmin yarinya ta, Wallahi in ya kasheta sai na ga bayansa shima" Adam bai kai ga amsawa ba Ahmad ya bude kofan dakin ya fito hannunsa riqe da belt yana huci idanun nan sun kada, da sauri Mummy ta qarasa garesa amma kafin ta kai ga riqosa ya kusa bangaje ta ya nufi fita daga falon tabi bayansa tana fado duk zagin da yazo bakinta, har yazo ya wuce Adam din bai ce komai ba ya fice fuskarnan tasa kamar zatayi aman wuta, sai Adam ya bishi da kallo har ya fice ya kasa bin bayansa dan be san me zeyi a wannan lokacin bama, Mummy kuwa ganin maganan nata ma a banza takeyi yasa ta koma gurin 'yarta da sauri dan ganin halin da take ciki.
Har bayan la'asar Na'ima na zaune a falon Mamma, zuwa lokacin Husna tayi bacci akan kujera Na'ima kuma na zaune qasa tana taya Mamma mixing wasu turaruka a kwalabe daban daban, Baba ne ya shigo dakin tareda yin sallama a nutse, bayan sun amsa sai Mamma ta dago kai tana kallon yanayin fuskarsa, sai yace da Na'ima "Abokiyar hiran taki bacci tayi kuma" tana dan murmushi ta sunkuyar da kai batace komai ba, sai Mamma ta fara kokarin miqewa da haka Baban ya juya ya fice ta bi bayansa, Na'ima na zaune kuma can ta fara jin qaran shigowan motoci cikin gida sai kuma ta miqe ta nufi window ta dan leqa, da Anty Amnah idonta ya fara tozali sai Anty Fatima wanda suka iso tare amma a motoci ma banbanta, barin bakin windown tayi ta koma ta cigaba da aikin da takeyin kuma bata daina jiyo shigowan wasu motocin cikin gidan ba, sai da ta share tsahon minti talatin sannan Mamma ta dawo falon..