MASARAUTAR KAIZUR 11
by @nusybee143
🗡️👑 MASARAUTAR KAIZUR 🗡️👑
✍️Nusy bee
❤️ Young talented writers association YOTA ❤️
Page 11
Shiru ilahirin wajen ga ɗauka duk da yawan mutanen,jikin yarima Jamal yana rawa ya miƙe ya nuna ta a kiɗime,ya ce"me kike nufi?
Annamimanci za kiyi mana? ƙasƙantacciyar baiwa irinki zata ƙulla makirci a cikin masarautar nan? wacece ke da kika isa ki raba abin da kika zo kika samu tsawon shekaru?"
Kallonshi ta yi kai tsaye ta ce"Allah ya taimake ka,a tsawon zamana a kaizur ba'a taɓa kama ni da wani laifi mai kama da makirci ko tuggu ba, kuma ko yaudara da cin amana da ake zargi na da shi ina da tabbacin za'a gane gaskiya nan da ɗan lokaci ƙalilan
Kamar yadda na faɗa da farko,ya shugaba na a jarraba,a gwada binciken"
Sarki Mu'iz ya dube ta a fusace ya ce"Munaya!
Zuwa yanzu ya kamata ki gane mu ba ƙananan yara bane!har tsawon wanne lokaci za ki ɗauka kina raina mana hankali?"
"Ka gafarce ni ya shugaba na,ban kai na raina muku hankali ba,iya abin da na sani nake faɗa "
Sarki Mu'iz zai sake magana sarauniya Amna ta dakatar da shi,da hawaye a idanunta ta dube shi ta ce"a jarraba bincikawar ranka ya daɗe, ba'a ƙin ta mutum "ta dubi dakarun da ke tsaye suna jiran umarni ta ce"a mayar da ita inda take kulle,a canja nau'in azabtarwa,a rinƙa ba ta abinci sau ɗaya a rana,ruwa ma haka,kar a dake ta, a yi mata wannan horon na tsawon sati guda mu gani, sauran al'umma kuma za su iya tafiya,an sallami kowa"tana kai wa nan dakarun suka rissina,suka kama Munaya suka wuce da ita kurkuku, sauran mutanen suka fara watsewa suna tsinewa da yiwa Munaya Allah wadai
*DAULAR TAYAAR*
Tunda Kazuzi ya zo Tayaar ba'a taɓa shayar da shi narkon azaba irin wanda ake yi masa yanzu ba, gaba ɗaya ya fice a hayyacinshi,banda aiki mai tsanani ga horon yunwa,ga wahalhalu kala-kala,haka ya kasance a cikin wannan halin tsawon kwanaki uku bisa jagorancin badakare Amjad wanda duk da wannan azabar da yake gana masa har yanzu nazari yake yi ta hanyar da zai ga bayanshi
Daga ɓangaren gimbiya kuwa,tsawon Wadannan kwanakin tana ƙarasa jinya ne,bata fita ko'ina,kuma idan sarki Tayaar ya shigo inda take baya taɓa yarda ya ba ta dama ta yi masa magana akan Kazuzi,hakan yana matuƙar damunta
Sauran kuyangin nata abin ya yi musu daɗi, saboda yawancinsu sun tsani Kazuzi saboda halayensa,don haka sun yi farin ciki sosai da halin da Kazuzi yake ciki,a cikin su Huda ce kawai bata cikin farin ciki, asalima tunda aka kama Kazuzi bata ƙara kwana guda cikakke ba da farin ciki,kuma hakan yana da alaƙa da yadda ta ga uwar ɗakin nata Hayat
Yau kam Hayat ta tashi da wata iriyar damuwa,ko abinci kasa ci ta yi,sai kuka kawai,har lokacin abu biyu yake damunta,cin amanar da dakare Amjad da kuyangarta Humaida suka yi mata,don tabbas ta ji komai,sai kuma kama wanda ya ceci rayuwarta har sau uku a matsayin mai laifi dalilin haka yau ta kasa cin abinci,ta kasa walwala yadda ya dace
Huda ce ta kai wa jakadiya Rubayya labarin abin da yake faruwa,babu ɓata lokaci ita kuma ta nemi iso wajen sarki da yake zauren shi na hutawa yana miƙe ƙafa, kuma ba tare da ɓata lokaci ba ta sanar masa da abin da ya faru
Cikin damuwa ya ƙaraso zuwa ɗakin gimbiya Hayat,da a yanzu iya Huda ce kawai baiwarta da ta yarda ta raɓe ta,bayan sarki ya shigo da sallama Huda ta rissina ta gaida shi,ya amsa sannan ta fice daga ɗakin
A gefen gadon da Hayat take zaune ya zauna, cikin rarrashi da nuna ƙauna ya dafa kafaɗarta,bata yi wata-wata ba ta faɗa jikinshi tana kuka mai tsuma zuciya
Ɗan bubbuga bayanta ya fara yi alamar rarrashi,a hankali kukan nata ya fara raguwa, cikin kwantar da murya ya dube ta ya ce"yanzu gaya min, Wanene ya taɓa gimbiyar Tayaar ne?"
"Abby don Allah ka sa a sake shi, don Allah Abby"ta faɗa cikin kuka
Da kallon mamaki ya bi ta,kafin ya ce "Wanene kike magana akai?"
"Kazuzi Abby
Haƙiƙa Abby baka yin abu ka yi nadama saboda dogon nazari da kaifin tunani irin naka,a wannan karon ma ina roƙon ka yi amfani da wannan baiwar taka akan Kazuzi,kar ka yanke masa hukunci daga baya ka zo kana yin danasani"
A hankali Sarki Iyaad ya girgiza kai ya ce "laifin Kazuzi ya kai na hukunta shi ne gimbiya
Menene dalilin da ya sa kaf matan masarautar nan babu wadda ta yi masa sai ke?
A matsayin shi na bawa,kuma wanda bai amshi musulunci ba?
A ƙa'idar Tayaar,ke ma kin sani da tuni ba ya raye,amma na saka aka ɗage hukuncin don kawai na nuna masa ƙauna,ya ji cewa duk da kasancewarsa wanda bai amshi addinin musulunci ba amma hakan bai saka na ƙyamace shi ba,amma sai gashi na ganshi a ɗakinki,ya kike tunanin zan ji?kuma me yake nufi da abin da ya faɗa kafin dakaru su fitar da shi?"
A hankali tana girgiza kai hawaye suna zubo mata ta ce"ba abin da kake tunani bane Abby
Da za ka ji abin da ya yi godiya za kayi masa,ba ka sa a kama shi ba, Abby kar ka manta a baya na tsani Kazuzi,amma nagarta da halayensa ya sa yanzu ina ganin ƙimarshi, Abby ko don darajar sayar da ran da yake yi a kaina duk da kasancewar sa bawa a wannan masarautar me zai hana a ba shi wata dama?
Maganar abin da ya gaya min kamar yadda ya ce zan ba wa masu laifin damar ƙarshe don su gyara kurensu,idan ba su gyara ba kuma zan ɗauki mataki,ko ma na gaya maka komai akansu"
Sarki Iyaad ya jinjina kai ya ce"to babu matsala
Na yarda da maganarki,zan saka a sake shi,amma zan saka a saka masa idanu"Hayat ta rungume sarki Iyaad tana murmushi da hawaye ta ce"na gode Abby
Amma ina roƙon alfarma daga gare ka"
Sarki Iyaad da yake cike da mamakin yadda ta damu da Kazuzi ya ce"ina jin ki ƴata"
Hayat ta gyara zama ta ce"waɗanda za ka saka su su kula da shige da ficen Kazuzi ka haɗa da sarkin yaƙi Ra'uf, badakare Adnan da kuma shugaban dakaru Amjad "
Bai yi wani dogon tunani ba ya ce"to ƴata, idan na yi hakan ya yi Miki ko?"
Tana murmushi sosai ta ce"ya yi min Abby, Allah ya tsare ka daga dukkan sharri "ta sunbaci goshinshi sannan ta ce"Abby bari na je da kaina na fito da shi,dole na nuna masa ban manta sadaukar min da ranshi da ya yi ba har sau biyu"sarki Iyaad ya yi murmushi sosai,bai kawo komai ba a ranshi sai halayen mahaifiyarta da ta ɗauko na tsananin tausayi da girmama ɗan adam
A keken dokinta ta je har ɗakin hukunci inda aka kulle Kazuzi ana yi masa azaba iri-iri,ba iyaka badakare Amjad ba,har wasu daga cikin masu azabtar da shi suna matuƙar jin haushinshi,don ma wani lokacin Ra'uf yana hana wasu abubuwan,shi dama banda dalilin doka ce daga sama da so ya yi ya ji hanzarin Kazuzi,duk da cewa shima Kazuzin wani lokacin murɗaɗɗe ne ba lallai ya faɗa ba
Tare suka tafi da amintacciyar baiwarta Huda,kanta tsaye ta shiga ɗakin hukunci bayan dakaru sun buɗe mata ƙofa,tana shiga ta bi Kazuzi da kallo gabanta yana faɗuwa ganin yadda aka mayar da shi, muryarta na rawa ta ce"ku kwance shi"
Babu musu aka kwance shi,duk da halin da yake ciki sai da ya durƙusa a gabanta ya ce"Barka da wannan lokaci ya shugaba ta"
Bata iya amsa wa ba,sai zuba masa idanu da ta yi tana mamakin ƙarfin halinsa,suna cikin wannan halin ne badakare Amjad ya shigo ɗakin a gaggauce,labari ya same shi cewa gimbiya Hayat ta shiga ɗakin duhu, cikin girmamawa duk da yadda ranshi ya ɓaci ya dube ta ya ce
"Ya shugaba ta wannan umarnin mai martaba ne,shi ya ce a hukunta shi saboda abin da ya aikata a gare ki,ya shugaba ta kin san hukuncin mazinaci a cikin Tayaar, ballantana kuma wanda ya yi nufin aikatawa da gimbiya,a gafarce ni idan na faɗi abin da bai dace ba ranki ya daɗe"
Kallonshi take yi zuciyarta cike da matsananciyar tsanarsa,bata manta abin da ta ji ba,sannan ta sake titsiye Humaida ta gaya mata gaskiyar abin da ya faru na shirin da ya yi ba tare da ita kanta Humaida ɗin ta san niyyar shi ba,ba tare da tunanin komai ba ta ɗaga hannu a fusace da niyyar ɗauke shi da mari,amma ta ji an riƙe hannun
Da sauri kuma a fusace ta waiga, Kazuzi ne,ya sakar mata hannu sannan ya sake rissinawa ya ce"ina roƙon a yi masa afuwa ya shugaba ta,ina roƙar masa alfarma a duba shekarunsa,komai ya yi a ɗaga masa ƙafa "
Ƙasa magana ta yi da farko, ƙwalla ta cika mata idanu ta dube shi ta ce"ai ka san komai, menene dalilin da zai saka ka yi tunanin zan iya girmama tsufansa?"
Kan Kazuzi a ƙasa ya ce"wani lokacin maƙiyi shiru shine yake firgita shi, musamman idan ya gaza nasara akanmu,a jarraba hakan ya shugaba ta"goge ƙwallar idanun nata ta yi ta ce"haka ne,to biyo ni,ina son mu yi magana da kai"daga haka ta juya ta fice daga ɗakin,sauran dakarun suka bi ta da kallo,kansu a ɗaure saboda maganganun da suka yi da Kazuzi yanzu,wanda ke nuni da wata a ƙasa tsakaninsu da badakare Amjad
Shi kuwa badakare Amjad ji ya yi kamar ya nutse saboda kunya da tashin hankali,a zuciyarsa tsanarsu ta ninku,amma sai ya dake,ya juya ya fice daga ɗakin ba tare da ya kalli kowa ba
Kai tsaye ɗakin Kazuzi suka nufa,yana shiga ya samu waje akan daɓen ɗakin ya zauna,a ranshi yana ɓoye mamakinsa ganin an sauya masa kayan kwanciya,ya nuna mata makwancin nashi ya ce"Barka da zuwa ya shugaba ta,ga waje ki zauna"
Girgiza kai ta yi ta ce"ba zama zan yi ba,kawai tambayarka zan yi,ya aka yi ka gane cewa dakare Amjad ne yake neman rayuwa ta?"
A hankali ya lumshe kyawawan idanunshi ya sake buɗewa,ita dai Hayat ta shagala da kallon ikon Allah, saboda zata iya cewa a tarihin rayuwarta bata taɓa ganin namijin da ya amsa sunan kyakykyawa mai cikar zati irin wannan sadaukin ba,a hankali ta ji muryarshi yana faɗin
"Babu wani tsafi da za'a yi wanda Kazuzi bai san yadda yake ba,bai san makarinshi ba
A iya tsawon rayuwata ilmi uku na samu daga wajen babana, shine ilmin tsafi,ilmin yaƙi da na farauta,na koyi yaƙar duk abin da ya saɓa da tsarina,na koyi farautar dabbobi masu haɗari tun ina ɗan ƙaramin yaro, kazalika na koyi ilmin tsafi don kariya,da kai farmaki
Babu wani kalar tsafi da za'a yi na kasa ganewa,da damisa da macijin da suka farmake ki duk ba na gaske bane, dukkansu tsafi ne,kuma da an bar su wajenki kawai za su zo ba za su cutar da kowa ba, tunda dama don ke aka turo su
Da ya ga na yi nasarar rusa shirinshi har sau biyu shine dalilin da ya sa ya sake shiri,ya yi amfani da kuyangarki Humaida ya ba ta ajiya ta ajiye a ɗakinki,a ƙarshe kuma da na yi masa magana don ya warware aikin ya ƙi har ya shirya min makirci
Ya so ya yi nasarar yaƙa ta da tsafi,sai dai shi a ilimin tsafin babu abin da ya sani,don a bayyane yake babu tsafi a musulunci,ba kamar namu addinin ba da ya zama tamkar ibada,shi bai san haka ba, shiyasa ya yi tunanin ya tsaface ni,amma haƙanshi bai cimma ruwa ba"yana kai wa nan ya lumshe idanunshi kawai ba tare da ya sake magana ba
Shiru ya biyo baya na ɗan lokaci,tuni gimbiya Hayat ta samu waje ta zauna tana kallonshi, kafin ta katse shirun da cewa "to yanzu ta yaya kake ganin za'a hukunta shi?"
Buɗe idanu ya yi,kanshi a ƙasa ya ce"lokaci ne zai hukunta shi ya shugaba ta,ina ganin a ba shi dama ko zai gane ya dawo hanya
Babu abin da hukunci cikin fushi yake haifarwa sai nadama da danasani,da ace zan yi masa hukunci cikin fushi da yanzu ba ya duniyar "
Girgiza kai ta yi a sanyaye ta ce"ba laifinsa bane kama ka da azabtar da kai,abbana ne,ka yi masa aikin gafara ya yi ne a rashin sani da son yin kishin tilon ƴarshi,daga gare ka kam na tabbatar Amjad ba zai iya yin nasara ba"
A hankali Kazuzi ya girgiza kai ya ce"azabtar da Kazuzi ba shi da bambanci da sanya ƙarfe a wuta,duk juyin da zai yi sai dai ya canja na ɗan lokaci ƙanƙani,amma ba za'a kassara shi ba
Sai dai tuni Kazuzi a kassare yake,kuma ba kowa bane ya kassara shi sai Amjad "ya yi ɗan shiru yana sauke numfashi cikin damuwa,kafin ya sake faɗin"ya kashe Malli!
Ita ce farin cikin Kazuzi,amma a yau babu ita, tabbas rayuwar Kazuzi bata da amfani,bata da alƙibla muddin babu Malli a cikinta"
#Nusy_bee
***