AKASIN TSAMMANI (Beyond All Odds)

Page 1

by @jikargarba001

Ƙarar alarm clock da ke kan side drawer ya ci gaba da tashi. Wani hannu mai kyau da ɗaukar ido ya fito daga cikin bargo ya kashe alarm ɗin. A hankali ta yaye bargon da ta rufe jikinta da shi, daga kai har ƙafafu. Ta sauke ƙafafunta kasa tana laluben bedroom slippers ɗinta. Ta kunna side lamp, ɗakin ya ɗauki haske mai laushi.

A hankali ta miƙe tsaye tana murza idanuwanta kafin ta buɗe su gaba ɗaya.

Kyakkyawar budurwa ce ‘yar kimanin shekara ashirin da biyar. Ba fara sosai ba kuma ba baƙa ba — tana a tsakani. Bata da ƙiba kuma bata da rama. Tsayinta madaidaici ne, fatarta kuwa fara ce tsab babu wani tabo ko ƙanƙani. Idanunta manya ne, farare ƙal, gashinta na idanunta dogaye masu kyau wanda ke ƙara ma idonta kwarjini. A taƙaice dai, she's naturally beautiful.

A hankali cikin natsuwa ta shige bathroom, ta yi brush sannan ta yi alwala. Da ta fito, ta shimfiɗa darduma, ta saka dogon hijabi a kan kayan baccinta, sannan ta kabbara sallar nafila. Bayan ta idar, ta ɗauko Qur’an tana karantawa har sai lokacin sallar asuba ya yi.

Tana cikin karatu, ƙofar ɗakin ta buɗu. Wata kyakkyawar mata in her forties, ta shigo.

"Ashe kin tashi? I thought you were still on bed," matar ta ce.

Zahra ta girgiza kai tana rufe Qur’aninta.

"A’a, yau ban makara ba. Barka da asuba, Mommy."

"Kin tashi lafiya?"

"Alhamdulillah. What about you? Hope you slept well?"

"Yes dear, my night was awesome. Lokacin sallah ya yi, ki tashi ki yi naki," Mommy ta faɗa tana rufe ƙofar.

Zahra ta miƙe, ta yi sallar asuba sannan ta zauna tana lazimi har ƙarfe shida. Daga nan ta linke kayan sallar ta ajiye su yadda ya kamata. Ta fita daga ɗaki, ta ɗauko vacuum cleaner daga corridor, ta koma ɗakinta ta share, ta gyara komai. Duk da akwai masu aiki a gidan, ta fi son yin gyaran ɗakinta da kanta.

Bayan ta gama tsaftacewa, ta wuce ta gyara bathroom, sannan ta yi wanka.

Few minutes later, ta fito daga bathroom daure da towel wanda ya tsaya mata a daidai cinyarta. Wannan ya bayyana kyawun jikin da Allah Ya yi mata. Fatarta na sheƙi, tana da kyawun halitta mai ɗaukar hankali. Ƙamshin shower gel da ta yi amfani da shi ya cika ɗakin.

Ta zauna a gaban mirror, ta shafa mai sannan ta yi skincare routine ɗinta. Ta ɗauki wani simple red three-quarter gown da aka ƙawata da black flowers, ta saka. Ta gyara gashinta wanda ke baƙi ƙirin, mai cika da tsawo, ta ɗaure shi a tsakiyar kanta. Sannan ta fesa turarenta masu daɗin ƙamshi.

Wayarta ta yi ƙara. Ta ɗauka ta saka a handsfree.

> "Hello Zahra, ba ki ga message ɗina bane?"

"Good morning," ta faɗa.

"Sorry good morning, please, ki tura min PDF na next paper ɗin mu. My niece mistakenly deleted mine."

"Ok," ta amsa a gajarce.

"Please send it now."

"Uhum," ta ce, ta kashe kiran.

A kitchen, masu aikin gidan sun fara ayyukansu. Wata na shara, wata na wanke kwanuka, wata kuma na zuba breakfast a food flask.Zahra ta shiga kitchen domin ɗaukar cup.

"Barka da safiya, Haj ƙarama," Mama Ladi ta gaishe ta.

"Ina kwana Mama Ladi. Ya aikin?"

"Alhamdulillah. Me za a baki?"

"Kofi zan ɗauka."

Ta ɗauki mug ta ɗauraye, ta fita zuwa dining area ta haɗa tea.

Wani saurayi ya sauko daga bene, ya tako a hankali zuwa bayanta. Ya rufe mata idanu.

"Yaya Musharraf, kamshin turarenka ya fallasa ka fa," ta ce tana dariya.

Ya murmusa, ya ja kujera ya zauna.

"Gaskiya zan canza turaren nan. Ki haɗa min breakfast."

Ta zuba masa fried Irish da catfish pepper soup, ita kuma ta ci gaba da sipping tea ɗinta.

"Wani lokaci za ki je makaranta yau?"

"Bani da exams yau, sai ƙarfe huɗu zan je library."

Miƙewa ta yi zata tafi. Musharraf ya ce

"Ina za ki tafi?"

"Ɗaki na."

"Me za ki yi a ɗakin?"

"Babu komai."

"To zauna in gama tukunna."

Ta zauna tana latsa wayarta, shi kuma yana cin abinci.

Wata budurwa ‘yar kusan shekara 18 ta shigo dining area tana amsa waya. Bayan ta gama, ta ɗauki plate, ta zuba abinci ba tare da ta gaishe kowa ba.

"Good morning, Habiba," Musharraf ya ce.

"Good morning, Ya Musharraf," ta amsa sannan ta koma parlor da abincinta.

Musharraf ya murmusa, ya miƙe tsaye ya share bakinsa.

"Sai na dawo, ƴar ƙanwata," ya faɗa yana jan kumatunta.

"A dawo lafiya, yayana," ta ce tana tura baki.

Musharraf ya fita, ita kuma Zahra ta haura sama. Ta duba ɗakin Mommy, ta same ta tana bacci, sai ta ja mata ƙofa sannan ta shiga ɗakinta.

Ta zauna a reading corner nata, ta ɗauki Harrison’s Principles of Internal Medicine ta ci gaba da karatu. Ta tuna da PDF da Sofi ta nema, ta tura mata, sannan ta ci gaba da karatun.

Karfe goma da minti biyar ta fita zuwa parlour. Ta san Daddy zai kasance a nan yana breakfast.

A parlour ta same shi tare da matarsa, wato ƙishiyar mommynta, tana kallon wani Indian series.

"Ina kwana Mama," ta faɗa ba tare da tsayawa jiran amsa ba, ta wuce zuwa dining.

"Good morning, Daddy," ta ce tana zama kusa da shi.

"Morning my dear Mom, hope you slept well?"

Zahra ta gyaɗa kai kawai.

"Ya jarabawar, yaushe za ku gama?"

"Nan da sati biyu Insha Allah."

"Ok, Allah ya ba da sa’a. Hope you are reading well?"

"Yes I am. Kar dai ka manta da alkawarin da ka ɗauka."

Ya yi dariya. "Ba zan manta ba, Manana. Where’s your mom?"

"Ta na bacci lokacin da na dubo ta."

"Ok. Just eat your food."

Bayan sun gama, Daddy ya wuce office. Zahra ta koma ɗakin Mommy, ta same ta tana gyara wardrobe.

Ta rungume ta daga baya ta kwantar da kanta a kafaɗarta.

"Mommy, ya baki fita breakfast da Daddy ba? Don’t tell me you’re still angry at him."

Mommy ta juya tana kallonta.

"Zahra, ban san me matar nan take nufi da ni ba. Na jima ina hakuri, amma yanzu daddynki yana ganin laifi na. Ya zan yi da raina?"

"Mommy ki yi hakuri. You know Daddy is not always like this. Maybe idan ya dawo sai ku zauna ku yi magana. Fushi is not a solution."

Mommy ta shafa kanta.

"I can tolerate anything a gidan nan, amma ban da cin zarafin ‘ya’yana ba. Addu’ata kullum Allah ya ba ku abokan zama nagari."

"Mommy kenan."

"Au ba za ki ce ‘Ameen’ ba?"

Zahra ta murmusa ba tare da ta ce komai ba, ta miƙe ta cigaba da jera mata kaya a wardrobe.

---

4:00 na yamma

Zahra ta fito cikin wando palazzo dark brown da rigar light brown, ta yafe kanta da dark brown veil. Ta shiga ɗakin Mommy a hankali, ta ji tana cikin bathroom, sai ta lallaɓa ta ɗauki maƙullin motarta ta fice da sauri tana dariya.

A kitchen ta shiga ta tarar da masu aiki suna girkin dare.

"Mama Ladi, idan Mommy ta fito ki ce mata na tafi makaranta."

"Toh shikenan. A dawo lafiya."

Gaban hostel ta yi parking, ta fito daga mota, ta ɗauki wayarta, ta rufe motar. Ta shiga ɗakin su Sofi da sallama, ta gaishe da mutanen ɗakin sannan ta zauna a gadon Sofi.

"Please, where’s Sofi?"

"Ta tafi corner shop siyan abu." Wata a ɗakin ta amsa mata.

"Ok, thank you."

Tana cikin jiran Sofi sai gata ta shigo.

"Ashe kin riga kin zo?"

"Karfe nawa na ce miki zan zo? Dalla ki shirya mu tafi. Time is not by our side."

"A shirye nake. Daman na je na siya miki Coke. Gashi."

Zahra ta karɓi ledar, ta fita tana dariya.

"Ina jiran ki a waje. Roommate, goodbye!"

A mota Sofi ta same ta, tana shan Coke. Tana shiga suka bar hostel zuwa library dake cikin makarantar.