AKASIN TSAMMANI (Beyond All Odds)
Page 3
Zahra na shigowa babban parlour ta tarar da duka ‘yan gidan a zaune har da yayyunta maza da kananan mata. Ta ji gabanta na faɗuwa, zuciyarta na bugawa tamkar ana kwankwasa gangar duma. A hankali ta nemi guri a ƙasa kusa da ƙafafun Daddy ta zauna, ta haɗa hannuwanta guri ɗaya, kanta a sunkuye kamar wata mai laifi.
Da ƙasa da murya ta ce
“Daddy... ka ce a kira ni.”
Daddy bai ce uffan ba, sai ya ɗan ɗaga kai yana kallon Habiba da gefen ido.
“Je ki faɗa wa maman ku ita muke jira.”
Sai da aka ɗan yi jinkiri na kusan mintuna biyar kafin Mama ta shigo cikin falon, sanye da doguwar rigar bacci . Tana wani hura hanci da juyar da ido ta zauna akan one-sitter kusa da mashigar falo.
Daddy ya gyara zama, ya ɗan shafa gashinsa da hannun hagu, ya ce
“Da sunan Allah mai rahma, mai jin ƙai. Ina godiya ga Ubangiji da ya bani ikon kula da wannan gida. Na tara ku ba don komai ba, sai don in jaddada wasu muhimman abubuwa da suke da nasaba da zaman lafiyar gidan nan. Wannan gida nawa ne, kuma duk wani hukunci da ake yanke sai bayan nawa.
“Na ji wasu maganganu da suka tayar min da hankali, suka hana zuciyata nutsuwa. Na shirya cewa wannan taro za a yi shi gobe, amma da na kwanta bacci, zuciyata ta kasa yin shiru. Sai nace... what if ban wayi gari ba? Wannan dalili ne ya sa na kiraku cikin daren nan."
Yayi shiru na ɗan lokaci, yana kallon kowanne ɗaya bayan ɗaya cikin ido kafin ya ci gaba
“Dukanku ‘ya’yana ne, babu wani bambanci. Ina so ku gane cewa ku 'yan uwan juna ne.Daga yau, kanku dole ya zama guda, idan ɗaya ya sami farin ciki, ku taya shi; idan ɗaya ya shiga damuwa, ku shiga da shi. Ku daina ƙiyayya da juna, ku daina zagin juna a bayyane ko a ɓoye. Kun fahimta?”
Suka ce a tare
"Mun fahimta Daddy.”
“Toh madalla. Abu na gaba, Musharraf, daga yau za ka kwashe kayanka ka koma BQ. Laurat da Habiba za su dawo ɗakin Musharraf domin samun isasshen sarari da tsari.
“Kuma na ji cewa an kai maganar saɓani har iyayen ku mata sun saka wa ‘ya’yansu iyaka. Wannan magana ta ƙare. Wannan gidan ɗaya ne. Mu’amala dole ce a tsakanin ku tun daga yau. Idan kuma na sake ji ko ganin akasin haka, ba ku san yadda zan ɗauki mataki ba.”
Ya juyo yana kallon Mommy da Mama.
“Ke kuma Amina da ke Sahura kowane kalma da kuka faɗa wa ‘ya’yan da ba ta da amfani ku janye. Ni ina ƙoƙarin haɗa kai, ku kuma kuna rarrabuwa. Ba zan amince da haka ba. Kowa ya sa hannu ya gyara inda ya lalace. Akwai mai ƙarin bayani?”
Mommy ta ce da nutsuwa
“In shaa Allah za mu gyara komai, Allah ya ƙara mana zaman lafiya.”
Wasu daga cikin su suka ce:
“Aameen.”
Daddy ya kalli Mama:
“Sahura, kina da abin faɗa?”
Ta ɗaga gira, ta ce:
“A'a, ba komai.”
Sai ya juyo ga yaran
“Ko a cikin ku akwai wanda ke da magana?”
Habiba ta ɗan nisa, ta ɗaga hannu tana kallon Zahra da ido cikin ido.
“Daddy gaskiya... Zahra ce ke kawo mana matsala a gidan nan. Saboda—”
“Shhhh! Ya isa!” Daddy ya katse ta cikin sauri. “Ba na son jin wani ba’asi. Daga yau ku koyi zaman lafiya da juna, ko kuwa...?”
Yayi kallon tsanani, kowa yayi shiru.
Mama ta zaro ido cikin fushi ta ce
“Yaya? Yarinya za ta fara bayani sai ka katse ta? Da dai Zahra ce da ka barta ka ji ba’asi har sai ta ƙare!"
“Sahura... ki tuna da abin da na faɗa miki. Kin ce ba ki da magana, don haka ban son na ji muryar ki. Ku kuma tashi ku fita!”
Dukkansu suka tashi a hankali, suka nufi ɗakunan su. Sai gashi Mama ta miƙe da sauri za ta fita itama, Daddy ya ce
“Dawo Sahura, ban gama da ke ba.”
Ta dawo kamar wadda aka yi wa dole, ta zauna ba tare da ta ce komai ba. Daddy ya sake jaddada musu
“Idan na sake samun wani yaron da rashin biyayya ko nuna ƙiyayya, sai na ɗauki mataki mai tsauri. Wannan gida nawa ne, ku dai dai ta!”
**
Zahra da ta koma ɗaki, ta kasa bacci. Kwance take tana kallon fan da ke juyawa a rufin ɗakin. A ranta, tana cewa
"Ya Allah, wannan wane irin rayuwa ce? Me yasa iyaye ke ƙin fahimtar cewa gaba ba ta haifar da ɗa mai ido ba? Yaushe za mu zauna lafiya kamar yadda nake gani a gidajen wasu?"
Bacci ya saceta a cikin wannan tunani mai nauyi.
Washegari da safe, bayan sallar asuba, ta yi lazimi akan darduma, sai bacci ya sake ɗaukarta saboda daren jiya bata samu isasshen hutawa ba. Har ƙarfe tara na safe kafin ta farka.
A hankali ta miƙe, ta gyara gadonta, ta nufi bathroom ta ɗauko kayan laundry, ta sorting farare da kala daban daban. Ta saka fararen a cikin washing machine. Ta share ɗaki, ta canza zanin gado, ta feshe shi da turare.
Daga nan, ta ɗauki bucket ɗin kayan da ta wanke, za ta kai su backyard don shanya. A lokacin, sai ga Farida cikin wando mai matse jiki da riga mara kyau tana shirin fita.
Zahra ta ce da ita
“Farida, ba da wannan shiga zaki fita ba, ko?”
Farida ta ce babu ko tsoro
"Da shi zan fita mana,kuma babu ruwanki.”
Zahra ta ƙaraso daga stairs:
“Idan har ba za ki canza kaya ba, ba za ki fita ba.”
Zahra ta fita ta rufe ƙofa da key, ta tafi ta shanya kaya. Farida na son fita, ta tarar da ƙofa a rufe. Tana dukan ƙofa tana faɗin
“Mama Ladi! Ina key! Kun tsaya kallo kamar ana kallon film ne?!”
Mama Ladi ta ce
“Hajiyar ƙarama ta tafi da key.”
Farida ta hau fushi tana bubbuga ƙofa tana faɗin
“Zahra! Ki zo ki buɗe kofar nan!”
Hayaniya ta tashi a gidan. Mama da Mommy da Daddy suka fito daga ɗakuna.
"Me ke faruwa anan?"
Daddy ya tambaya.
"Zahra ce ta rufe ƙofa ta tafi da maƙulli." Farida ya faɗa kamar za ta yi kuka.
"Saboda me?"
"Wai babu wanda ya isa ya fita a gidan nan yau.
"Amina kira min ita a waya."
Mommy ta yi ƙoƙarin kiranta a waya, ba ta ɗaga ba.
"Ba ta ɗaga ba" Mommy ta faɗa cikin damuwa.
"Kira Musharraf ya na da spare key a wajen shi."
Mommy ta kira Musharraf ta ce masa ya zo da spare key ya buɗe musu ƙofa, Zahra ta rufe su ta tafi da maƙulli.
Musharraf ya kalli zahra da bata daɗe da shigowa shashin ba daga wurin shanya.
"Me ya sa kika rufe mutane a cikin gida?"
"Farida ce bana son ta fita saboda ba ta da kunya."
"Wannan kuma ku ta shafa, yanzu dai tashi muje ki buɗe ƙofa."
Suna tsaye cirko cirko Sai Musharraf ya shigo da Zahra daga shashinsa.
Daddy ya kalle su sosai kafin ya ce
“Zahra, me ya sa kika rufe ƙofa da key kika fita?”
Zahra ta tsaya cikin nutsuwa ta ce
“Na rufe ne saboda Farida ta ƙi canza kayanta da suka saɓawa tarbiyya. Na ce ta canza, ta ƙi. Sai na ɗauki mataki domin gyara,ba domin raini gareku ba.”
Daddy ya juya kallonsa zuwa Farida da ke sunkuyar da kai, sai yanzu ya kula da kayan da ke jikinta.
“Wannan shiga makaranta zaki je da ita?”
Farida ba ta iya cewa komai ba.
“Sahura, me yasa baki sa ido a ‘ya’yan ki ba?”
Mama ta ce
“farida guda nawa ta ke da zan sa mata ido,duk abinda ta ke yi yaranta ne za ta daina idan ta girma. Ita ma Zahra munafuncin da ta gado ne kawai ke damunta.”
“Toh! Kin kyauta.” Ya juyo ga Farida
“Wuce sama ki canza kayan nan kafin in miki abinda ba ki taɓa tsammani ba.”
Musharraf ya ce
“Allah ya kyauta,” ya fita. Zahra da Mommy suka haura sama.
Daddy ya kalli Mama da fuska a ɗaure
“Sahura zaki gan matakin da zan ɗauka a kan ki.”
Wannan page ɗin na musamman kyauta ce ga Meeyra Abdul